Skip to content
Part 2 of 10 in the Series Kyautar Zuciya by Bilkisu h muhd

*****

Karfe tara ta iso gida a gajiye, Haj Rahma ta dago kai tana dubanta cike da takaici, ga wani kaskas da ta ke yi da cingam. Ta jinjina kai tare da maida idanunta kan talabijin da suke kallo.

Nurat ce zaune, daga gefenta tana tilawa a zuciyarta, sai Alhaji Usman shi karanta jarida yake.

“Wash!” Ta ce lokacin da ta zube a kan kujera, ta dauki remote.

“Yaya Aazeen Ammi ce fa ke kallon tafsir, da kin koma daki inyaso sai ki kalli tashar da ki ke so”.

“A nan na ga damar yin kallon”. Ta fada tana ci gaba da lalubo tasha.

A daidai Arewa 24 ta ajiye rimot, “Wow na so na yi missing”.

Nurat ta tsuke baki ba ta sake tanka mata ba, ta dubi Hajiya Rahma.

“Sorry my Mom, ban son komawa dakin, na fi son na yi kallon a nan, am sorry… Sannu Dad”.

“Sai yanzu ki ka gan ni?”

Ta karasa gabansa ta zube, hannayenta a cinyarsa.

“Dad, ina son programme din gayen, kullum ina ji a jikina kamar zan rayu da shi, dole zan sauke shi daga layin da yake kai. Ban taba ganin mutum irinsa ba, ina da tambayoyin da zan yi masa bila adadin, ban san me ye ribarsa na boye kansa ba”.

“Rangida na fi tunanin asalinsa talaka ne, kai ni gani nake ma kamar babu shi, kawai ana son yawo da hankalin mutane”.

“No Dad, na ji a majiya mai karfi akwai shi, duba ka ga yadda yake sakar wa Malaman addini miliyoyin kudi duk wata, sauka ko musabakar alkur’ani da za a yi sai ya kashe miliyoyi. Na fi tunanin kila aljani ne. In ba aljani ba, waye zai yi abin da yake yi? Duk wani mai kudi yana so idan ya yi abin bajinta a san ya yi. Yana son duk inda ya sanya kafarsa ana girmama shi”.

“Dad su ma wadanda suke program din nan ba su sanshi ba kenan?” Nurat ta tambaya.

“Haka na ji ana cewa”.

Aazeen ta ce, “To me ye amfanin abin da suke yi?”

“Saboda suna son ya san taimakon da yake yi, sako na isa gare su”.

“Mtsew! Ji wani shashanci”.

Alhaji Usman ya ci gaba da fadin, “Wannan da zai fito ya zama dan siyasa ba zai wani sha wuya ba, don abin ma da yake yi zai zamo kamar kamfen ne”.

“Dad bana ji an ce ba shi da aure ba, kuma mara aure ba ya tsayawa takarar neman gwamna?”

“Wannan ai mai sauki ne, daga ya amice cikin lokaci kankani zai iya yin aurensa”.

“Dad idan na kwanta ina mafarkin ya zama mijina. Dad ina ma zan ganshi ko da sau daya ne?”

“To Dad ta yaya taimakonsa ke isa hannun mutane?” Nurat ta sake tambaya.

“Ya kan kintaci duk lokacin da yake da bukata ya je inda yake bukata, bayan kiran assalatu yake isar da zakkarsa ko sadaka, sai dai ka ji an dan kwankwasa maka kofa. Kana budewa za ka ci karo da abin da yake rabonka, duk nacinka ba za ka ga kowa ba. Da yawa an sha yin dako sai kun gama hada target da inda za ku ganshi, sai kawai ya sauya yanayin lokutan rabon babu zato babu tsammani ka ke ganin kayan arziki, kama buhun shinkafa, taliya, kudi, sutura da sauransu. Ba kananan kudi yake badawa ba, kudi ne wanda zai ishe ka ka ja jari, wanda in ka yi dace ka yi sallama da talauci. Dadin dadawa yana da asibitoci, makarantu wadanda an gina su ne kawai saboda talakawa”.

“Tab! Ka ce shi kawai don taimako aka halicce shi?” Aazeen ta fada.

“Kila ma na sanshi”.

Alhaji Usman ya yi dariya, “Babu mamaki don an ce yana nan yana mu’amala da mutane ba tare da sun sanshi din ba ne”.

“Gaskiya wannan batan basira ne, shi ke nan ya dauki kansa kamar kowa, ba ya son idan ya shiga guri a dinga nuna shi ana b shi girma? Shi sam bai damu da ya yi suna ba Dad? Wadannan abubuwan fa su ne jin dadin, kamar ni in na shiga guri za ka ga yadda ake girmama ni, ina taka duk wanda na so”.

“Yaya Aazeen wannan riya kenan fa, kuma duk mutumin da yake riya ladansa iya nan kawai za ta tsaya. Sai dai mutane su yabe shi. Shi ya ji dadi gurin Ubangiji komai fanko yake”.

Ta ja tsaki, “Ai kin ji irinta. Dad shi ya sa na ki amincewa da makarantun nan, islamiyya tahfiz, makarantar magriba ko yaushe ba ta da hutu tana zuwa ana dura mata al’adun mutan da. Ta sauke abin da aka ce an fi bukata, wato alkur’ani mai girma, amma har yanzu ta ki ta hakura”.

“Ke ma da a ce kina zuwa duk za ki watsar da wadannan shirmen da ki ke yi”. Hajiya Rahma ta fada.

“Hum Ammi kenan, da girmana da komai kawai sai na je na zauna ana koyar da ni salon kowa ya raina ni? Ita dai da ta ga za ta iya sai ta je ta kara ta”.

“Da Allah malama rufa mana baki”. Ammi ta ce da ita.

A take ta ji haushi, Alhaji Usman ya dubi hajiya Rahma.

“Ba kya kyautawa”.

“To yanzu me na yi ne?”

Bai ce da ita komai ba ya mike ya rufa wa Aazeen baya.

A lokacin da kowa ke bacci, a lokacin ta ke sake sabon zama a gindin akwatun talabijin, a nan ne ta ke cashe mata kallon. Karfe goma sha biyu tana zaune a sitroom dinta ta dora kafa daya kan daya, lokaci-lokaci ta kan dauki tea ta kurba. Rimot ta dauka tana canza tashoshi. Ta ji dadin film din da ta ga ana yi. Ta ajiye rimote din gaba daya hankalinta ya karkata daidai lokacin da aka nuno jarumin da budurwarsa rungume da juna suna yi wa juna wani irin wasa, yadda jarumin yake ba ta wani hot kisses tare da sake rungume ta tsam-tsam cikin wani irin salo, ji ta yi gaba daya hankalinta na neman fita a jikinta.

“Wayyo! Tana son wannan rayuwa, su kam Turawa sune suka zo duniya a sa’a, sukan yi duk abin da suka so a gaban kowa ba su da shamaki da duk wata rayuwa da holewa.

Ta lumshe ido tare da kwantar da kai a allon kujera tana saukar da numfshi, ina ma a Turan aka halicce ta? Ba za ta iya jurewa ba. ta zaro waya ta shiga lalubar wata lamba.

Ringin daya aka dauka daga dayan bangaren aka ce, “Ya na ji muryarki haka? Me ke faruwa?”

“Komi ma ya faru. Ya za a yi ka zo gare ni?”

“Ke ba ki da hankali? Idan na zo in ce me? Ba ki ga dare ya yi ba? ki lallaba zuwa gobe, amman gaya min duk me ya janyo hakan”.

Ta ja tsaki hade da katse wayar. Ta yi lamo cikin wani irin shauki, shi ne kawai yake dan kwantanta yadda ta ke so, shi ne yake fahimtar feeling dinta, shi ma din tana tunanin don ya yi karatu a Turai ne.

“Mtsew!” haka ake ta faman son ta yi aure, to ta auri me? Babu abin da auren bahaushe ke haifarwa sai bacin rai. Su dai burinsu idan suka tashi da safe Allah-Allah suke yi su wuce gurin neman kudi, idan suka tashi a kasuwar su wuce majalisar gulma, wanda su abokan nasu ke dora musu wani tunanin ko layin rashin mutunci. A nan suke koyon tsumulmula, suke koyon son mata. A nan ake cusa musu ra’ayin su kara aure, ba za su tashi dawowa gida ba sai matar ta yi bacci, yaransa sun yi bacci. Kai wani ma saboda tsabar kwarewa da yawon majalisa yaransa ba su gama sanin waye shi ba, wani fannin in matar ba ta samu damar yin bacci ba, daga ta yi musu sannu da zuwa a ciki za su amsa suna faman cika da batsewa, wai kada ta raina su, za su baka ci abinci idan ba masu ci a waje ba ne, da zarar sun dirka a ciki sai kwanciya, sai dai ka ji yana jan minshari, shi ke nan ke an mayar da ke dutse kin zamo mai zaman ‘ya’yanki.

“Ammina ta kasa gane inda na dosa ita dai kullum na fitar da mijin aure, ba zan taba biye mata ba. Mijin da zan yi rayuwa da shi dan gaske ne, wanda zai ba ni hakkina a duk lokacin da na bukata. Ai ni da na ga mijin da zai iya ina ganewa, har yanzu ban ganshi ba”.

Tana matukar son namiji wanda ya kai kololuwa gurin haduwa, kau, suffa da na aljihu, shahararren mai kudi shi ne burinta, don haka a kullum ta ke mafarkin kasancewa da Ahmad Deedat. Tana ji a ranta kamar shi din ajiyarta ne.

Kiraye-kirayen sallah ne ya katse mata tunani. Mikewa ta yi hade da kashe kayan kallon ta nufi dakin Ammi, wadda da alamun kiran sallar bai ratsa ta ba. Ta shiga dukan filon da Ammin ke kwancea kai.

A firgice ta bude ido, tana tunanin ta makara. Jin alamun za a tada sallar a masallaci ta yi, da sauri ta mike har tana ture Aazeen.

“Haba Ammi, ki bi a hankali mana, ba fa ce miki aka yi tashin alkiyama za a yi ba”.

Ba ta bi ta kanta ba ta fice abinta.

Aazeen ta koma bedroom dinta ta mike a gado, tuni bacci ya yi awon gaba da ita.

Karfe goma da rabi sun hallara a dinning room, Alhaji Usman ya dubi Hajiya Rahma, “Ya dai?”

“Me ka gani?”

“Na ga kamar kina da damuwa”.

Ta kada kai, “Ko daya”.

Nurat ko littafi ne a hannunta tana dubawa.

“Nurat ki aje littafin nan ki ja abinci duk kin daga hankali, in dai ba kya cin abinci zan fa hana ki”.

Ta ajiye alkur’anin a gefe tana cin abincin. Tana leka surar da ke a bude.

Aazeen ce ta fito cikin kayan bacci manne da waya a kunne. Da alama waya ta ke amsawa, gabadaya ita suke bi da kallo.

Bathroom ta nufa.

“Ran gida me ya samu bathroom dinki?”

“Ina ganin kamar rariyar ce ta toshe”.

“Ok”.

Ta shige bathroom din. Mintina biyar ta diba a ciki ta fito da kayanta a jike sharkaf! Wai nan alwala ta daura.

Ammi ta cika fal da takaici, kokarin zama ta ke a dinning.

“Kin ga ki fara sitirta jikinki, idan ki ka yi sallah sai ki yi break din”.

“Tab! Ammi, sallah ba zai yiwu cikin wannan yanayin ba, kin ga kuwa yadda nake jin yunwa?”

Kokarin zuba dankali ta ke a plate.

“Magana fa nake yi”. In ji Ammi.

“Oh my Mom, please ki kyale ni”.

“Haba Rahma ke kuwa ki kyale ta mana, ai shi ci shi ne gaba da komai”.

Dole ta yi shiru tana jin zuciyarta duk a jagule. Ta sani tun farko shi ne masomin rusa tarbiyyar Aazeen, yadda yake yi din ne ya sanya ta ke tuhumarsa da abubuwa iri-iri. Ta sani wannan ba shi ne so ba, me ya sa ita Nurat bai ba ta irin wannan tarbiyyar ba? Shin a cikinsu waye ya fi so kenan? Yana nuna ma Aazeen duk wata gata da soyayya, ba ya son bacin ranta. Ita kuma Nurat tsangwama, da kyara. Yana shigowa gida sai ya fara tambayar ta yi sallah? Ta je islamiyya da ire-iren wadannan tambayoyin. Shin wa ke nan yake kauna?

“Dankali kawai na gani, ban ga farfesun da na ce ladidi ta yi min ba?”

“Kira ta, kila karasawa ne ba ta yi ba, ai babu wanda zai ketare umarninki Rangida”.

Ta bude murya baki daya cikin kwala mata kira.

A sukwane ta karaso tare da durkusawa a gabanta. Ta watsa mata harara.

“Ina kayan karyawata?”

“Yanzun nan na hattama, bari na kawo miki”.

Da sauri ta yi waje, sai ga ta da kayan karyawar ta jere a gabanta.

Janye plate  din Ammi ta yi a gabanta.

“Kada ki taba komai a nan ba tare da kin je kin sauya kayan jikinki ba”.

“Haba Ammi, kashe ni za ki yi? Na ce da ke yunwa nake ji. Ni kam gaskiya a’a”.

Ai kuwa ta shiga yi mata fada, takaici kamar Aazeen za ta mutu. Bakin cikinta wai Ammi ta yi mata fada a gaban mai aiki. Juyin duniyar nan ba ta mike ba, ta bude farfesun a kufule, cikin neman wanda za ta huce a kansa. Ta dubi Ladidi.

“Cewa na yi ki saka min curry? Uban waye ya sa ki? Kawai ba ki yi shawara da ni ba kin yi abin da ki ke so ko?”

A sanyaye, “Ki yi hakuri, na ga ai kullum ina yi miki amfani da shi”.

“Shut up! Ina magana kina yi?”

Gaba daya ta dauki plate din farfesun ta watsa mata a fuska. Wata gigitacciyar kara Ladidi ta saka. Da gudu Nurat ta mike tare da rungume ta a jiki. Ladidi na ta ihu tamkar wadda ake kokarin zare mata rai. Da taimakon Nurat suka nufi famfo.

“Man kana ganin abin da Aazeen ta aikata ko?” Hajiya Rahma ta fada tana kallon Alhaji Usman.

“Ita ta ja ma kanta. Ya kamata ta dinga kiyaye matakan aikinta, tunda ba kyauta ta ke aikin ba”.

“Dad, ina son gaya maka su Zee fa na tafe”. Aazeen ta fada ba tare da ta nuna nadama a abin da ta aikata ba. Gaba daya ma sun mance da ita Hajiya Rahmar, hirarsu suka shiga na yadda za su sauki bakin nata.

Mikewa ta yi cike da takaici, har lokacin tana jin ihun kukan Ladidi, Nurat na faman ba ta hakuri.

A can shashin masu aiki, Ladidi ta yi matashi da cinyar Nurat ta dage sai bushe mata idanu ta ke faman yi, hankalinta a tashe, yadda idanun suka kumbure sun yi jajir da kyar ta ke motsa su. Hawaye sai faman tsinkowa suke daga idanun. Cikin muryar kuka.

“Ladidi sannu, za ki warke. Yana yi miki zafi? Sannu”.

Ta rude matuka, jikinta sai bari yake, zuciyarta fal haushin Aazeen. Karin bakin cikinta shi ne na halin ko’inkular da akai wa Ladidi akalla ya kamata su zo su duba halin da Ladidi ke ciki, yanzu ya za ta yi idan Ladidin ta makance?

<< Kyautar Zuciya 1Kyautar Zuciya 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×