“Ya isa haka, ban sanki da karya ba”
“Meye hujjarka?”
“Ga su nanan kuru kuru a cikin idanunki idan kina musu ki tam bayi yayarki, za ta fada miki”.
Wani tsoro ya dirar mata, muryarta ta soma rawa.
“Da gaske ka ke yi? Na shiga uku, ina jin tsoro, ka gaya min ya zan yi? Yan zu kana son ka ce kowa ya san ina son ka?”
“Ya isa haka kwantar da hankalin ki, zan fada miki yanda za ki yi kowa ba zai gane ba”
“To ka gaya min”
“Okey kafin nan ina son sai kin gaya min gaskiya kafin na sama miki mafita,”
“Ina jin ka”
“Ki fada min gaskiya, kina sona?”
Ta yi dum, kamar ba ta kan wayar, ya numfasa cikin kokarin maida dariyar da ke kokarin kwace masa.
“Shi kenan, sai in kyale ki ai ta ganewa ke zaki kwana ciki, ni sai an ji ma,”
“Tsaya ka da ka ajiye, amman ina, um um, ina, kai ni bn san yadda a kayi ba, amman na da mu da kai”
“Na sani, amman ba wannan na tambaya ba, kina sona?”.
Wani kuka y kwace ma ta.
“Yaya Adamu, ina son ka, ba’a son raina ba ne, ban san me yasa zuciyata ta yi min haka ba, ina cikin hatsari ina jin kunya”.
Deedat yayi dariya mai isar sa, wani irin ni shadi ya dinga ji, ya samu farin ciki mara misaltuwa.
“Ka da kiji tsoro kin ji,? Ina so ki saki jikin ki”.
“A’a bana so, ina neman tsari da soyayyar ka,”
“Shikenan na ji tun da haka ne, gobe zan gaya ma, yayar ki cewar ina son ki kuma ke ma ni ki ke so”.
Ta sa ke gigicewa.
“Wallahi a’a bana…”
“Ki yi shiru indan ba ki sa ki jiki dani ba zan gaya ma ta, ina son ki dinga yin duk binda na tsara miki idan kika yi min gadda ma zan gay ma ta, kina son in sanar ma ta?”
“A’a”
“To ki dinga bin abinda na umarce ki,”
“To”. Tace
“Yanzu ki kwanta ki yi bacci, king gobe a kwai makaranta ko?”. Tace
“Eh,”
“To ki yi min sallama”.
Ta ce, “To sai da safe”.
“No, ba wannan ba, sallama irin ta masoya”.
“Ni ban iya ba, ban san me zan ce ba’.
“Cewa za ki yi I lobe you”.
“Wayyo Allah, ka yi hakuri”.
“Okey, shi ke nan Allah ya kai mu gobe zan fasa kwai”.
Ba ta san sa’adda ta furta kalmar ba. ya lumshe ido yana nanata kalmar a ransa, kalmar ta yi zaki a bakinta, yanayin da ta furta, yadda muryarta ta yi rawa yayin ambata hakan, abin ya yi armashi. A hankali ya furta, “I lobe you too”.
Wani irin abu ta ji yana yawo a ko’ina na jikinta. Duf! Ta ji wayar ta yanke, ta koma ta kwanta ga hawaye na kwaranya a gefen idonta, can karkashin zuciyarta kuwa tana ta dawo da kalamansa, tana jin wani sanyin dadi na ratsa zuciyarta. A haka bacci ya yi awon gaba da ita, bacci mai cike da mafarkan Deedat.
*** *** ***
Suna tsakiyar rubutu principal ya shigo ajinsu, ya yi umarnin da ta same shi a ofis. Nan da nan ta gigice, ‘yan ajin kowa ya jajanta abin da Principal zai zo da kansa ya kira ka, to al’amarin ya tsananta.
Cikin rashin kuzari ta fita, duk jikinta a sanyaye, babu abin da ba ta saka a zuciyarta ba, kaf! Ta gama tunaninta ba ta san laifin da ta yi ba.
Tana tura kofa suka yi ido biyu da Deedat, ta kasa motsawa, wannan Adamun ya fara sa mata shakku, yadda ya fada game da shi ta soma zargin karya yake yi, shigar daya yi yau ya sanya mata shakku. Sanye yake da wata hadaddiyar shadda, ta sha wani lafiyayyen dinki.
Mikewa ya yi ya matso kusa da ita, a hankali ta dan ja baya.
“Ina kwana?” Ta ce da shi.
“My lobe da fatan kin tashi lafiya?”
Ba amsa ta dukar da kanta kasa tana wasa da gefen hijabinta.
“na zo ne kawai gurin maigidana don na ganki, na sha wahala kafin ya amince”.
Juya masa baya ta yi.
“Yaya Adamu don Allah ka yi hakuri nan makaranta ce, ina jin tsoro”.
“Okey, mun hadu a gida kenan ko?”
“A’a ba haka nake nufi ba”.
“Ya isa, mu barshi haka. Don Allah kina nufn in daina sonki?”
Da sauri ta amsa da, “Eh”.
Ya kafe ta da ido.
“ba zan iya ba, ke ce ki ka dasa min don me ya sa za ki guje ni?”
“Ta ya? A ina muka taba haduwa?”
“A waya mana, da bakinki ki ka hillace ni har sai da na afka a soyayyarki. Dole ne kuma mu dora in kuma ki ka yi min gardama na gaya miki zan sanar wa Yaya Aazeen”.
“To shi kenan na ji, ka yi hakuri. Yanzu don Allah ka tafi ka ji”.
Hannu ya sa cikin aljihu, wani cakulet ya dauko.
“Ga wannan”.
Ya mika mata.
“Na gode, amma bana shan zaki”.
Ya yi murmushi, “Yau zan koya miki Nurat dina, ina son zaki ke ma za ki koya”.
“Ikon Allah, don Allah ka taimaka ka fita a rayuwa ta, na roke ka”.
Kawai ta fashe da kuka, hankalinsa ya yi matukar tashi.
Durkusawa ta yi a gabansa.
“Ina jin tsoro, ina tsoron Dad, ina tsoron Yayata, tana matukar sonka, amma ni din ban taba sonka ba. ina yi maka kallon Yayana”.
Shi ma durkusawa ya yi.
“Kuka ki ke yi Nurat? Me ya sa za ki cutar da rayuwarmu? Na sani kina sona, ki bar min komai a hannuna, komai zai tafi daidai, amma don Allah kada ki cutar da mu, kin ji? Wallahi ban taba cin karo da abin da nake so kamarki ba”.
Cikin muryar kuka, “Na yi da na sanin shigowarka rayuwata, ban san al’amarin zai juye haka ba. ina rokonka ka cire ni a ranka, wallahi ba zan iya rayuwa da kai ba, ka haramta a gare ni”.
Kalamanta sun harzuka shi.
“haka ki ka ce ko? To saurara ki ji, gwara ma ki shirya gina rayuwarki da ni, sai na mallake ki, ba zan taba rasa ki ba kin ji ko?”
Tuni Nurat ta sake rudewa, idanunta da fuska gaba daya suka rine suka yi ja, muryarta na rawa.
“Yaya Adamu ka haukace, ba ka san me ka ke cewa ba?”
Bai sake ce mata komai ba ya watsar da cakulet din hannunsa a gurin, a fusace ya yi waje.
Kuka bai kamace ta a gurin ba, idan Principal ya riske ta me za ta ce da shi? Ta yi saurin goge fuska tare da daidaita kanta ta yi waje tana faman ajiyar zuciya irin na wadda ta gaji da kuka.
Ko da aka tashi a harabar makarantar ta ci karo da shi a tsaye. Ko kallon inda ta ke bai yi ba tamkar bai santa ba, hakan ya yi bala’in tada masa da hankali, tana jin tsoro kada ya huce haushinta a kan yayarta gurin kin zuwa gidansu.
Tana dawowa gida ta ga alamun kowa na gidan na cikin farin ciki, musamman Ammi.
“Ammina, ban ga komai a dinning room ba yau, ina jin yunwa sosai”.
Ammi ta riko hannunta.
“Farin ciki ba zai barmu mu ci abinci ba, yau Dad dinki ya mallaki kamfanin da ya kwashe shekaru yana burin mallaka, Dad din Zaruk ya bda kaso ashirin cikin talatin, yayin da Dad dinku ya bada kaso goma kurum. Yanzu kamfanin ya zamo mallakinsa, duk a dominki, ke din nan ke kadai, ba don ke ba da ba mu kai haka ba.
Za a yi bikin mallaka mana kamfanin tare da birthday din cikar Abbanki shekaru hamsin rana ita-yau. Sannan hade da baikonki da Zaruk”.
“Abubuwa uku a lokaci guda?”
Aazeen da ke shigowa ta fada.
“Dole ne mu yi gagarumin biki’.
Nurat kawai ta dinga binsu da kallo,
“Ammi duk kun ce a dalilina, hakan na nufin kun ba su ni? To idan Allah ya kaddara ba ni ce zan aure shi ba fa?”
Aazeen ta yi saurin amshe zancen da fadin, “Allah ma ba zai sa haka ba, ya zama dole ki aure shi. Ba za mu bari hakan ta far ba, wannan ai babban abin kunya ne. daga yau zan fara yi miki gyaran jiki, abokan Zaruk za su san cewar ya zabi mace ‘yar gaske. Sai na tatso ki, shi kanshi ba zai gane ki ba. zan sa a yo miki odar kayan da za ki sanya”.
Tuni Nurat ta sake rudewa, kanta ta ji yana sarawa, numfashinta ya dinga shirin daukewa. Ta bude baki kamar za ta yi kuka.
“Ammi na gaji, kaina na yi min ciwo, bacci zan yi”.
“Ke da ki ka ce kina jin yunwa? Ki sha ko da tea ne”.
‘Kaina cwo, ba zan ci komai ba, na koshi”.
Ta nufi bedroom, Aazeen da Ammi suka dubi juna.
“Ban san me ya sa Nurat ba ta son Zaruk ba”.
“Ammi ki daina karaya, hakan shi zai sa ta samu mafaka, ki kyale ta, za ta daina ne”.
Tsananin yunwar da ta ke ji ya karfafa ciwon kan nata, ga wani irin zazzabi da ya rufe ta, haka ta dinga jin rashin nutsuwa da kwanciyar hankali, komai na rayuwarta ya tsaya mata cak! Ga wani irin mummunar faduwar gaba da ta ke fama da shi, haka ta rasa me ke yi mata dadi, ta kuma rasa da me za ta ji, tunda ta shiga dakin ta tare gurin kiran Deedat a waya, ya ki daga mata duk kuwa da yau ne karo na farko wanda ta kira shi a wayar da yake mallakinta, hakan bai sa ya dokanta ya daga ba, hakan na nufin shi din yana fushi da ita?
Ta tura sakonni amma babu amsa, ta rasa wa za ta fada wa damuwarta, ko da ma tana da wanda za ta fada ma, wannan damuwar ba ta tunanin duk duniyar nan akwai wanda za ta iya shaidamawa, ta sani duk wanda ya san wannan labarin dole zai yi Allah wadai da ita, ko da kuwa damuwar za ta kashe ta ba ta jin za ta iya fasa shi.
Ta share kwallar fuskarta, don me ya sa zai dinga ganin laifinta? Me ya sa ba zai ji tausayinta ba?
Karfe takwas na dare Deedat ya isa gidan su Nurat, a dokance Aazeen ke labarta mishi farin cikin da ya tunkare su.
‘Ka ga komai zai yi daidai, za ka samu babban aiki, kai ne za ka zamo manaja, yadda ka ke so haka za ka zamo zuwa wani lokaci ka zama kiyaya”.
Shi kam hankalinsa ba ya kanta, tunda ta fadi maganar baikon Nurat komai ya dagule masa, yana tunanin ta ya zai samu damar ganinta. Ya dan dube ta cikin kokarin boye damuwarsa.
“Na yi mata murna, ya kamata ki hada ni da kanwar tamu in taya ta murna”.
Ta tabe baki.
“Kyale ‘yar rainin wayo, wahalalliya, tunda ta samu labarin ta shige daki, ko abinci ta ki ci ta kulle kanta baki daya ni na rasa dalilin da ya sa ba ta sonshi, kowa mamaki yake, duk gidan nan babu wanda tasu ta zo daya da Zaruk irin Nurat, haka ne ma ya sanya Dad ya bada amanna”.
“To amma tunda ba ta so me ya sa ba za a janye ba?”
“Tab! Ai ko za ta mutu dad ba zai janye wannan ba, wannan mutumin shi ne komai na Dad…”
Ya katse ta, “No kada ku amince da hakan, komai na iya juyawa, amma kada ku cutar da ita ku ba ta abin da ta ke so”.
Ta tintsire da dariya.
“Ita din babu wanda ta taba tsayawa da shi balle mu yi zargin ko akwai wanda ta ke so, kawai dai tana son wahalar da mutane”.
“Yanzu ko zan iya ganinta?”
“Zan jarraba don wani fannin kana ganinta haka akwai ta da kafiya”.
“Zan lallasar muku ita, komai zai yi daidai, ke dai ki bar ni da ita za mu saka labule”.
“Shi ke nan bari in je na tura ta”.
Lokacin da Aazeen ta sanar da ita cewar ta je za su yi magana da Adamu, ta una kamar ba ta son zuwa, amma a can karkashin zuciyarta wani farin ciki ne kwance, rashin amsar wayarta da bai yi ba ya kara tabbatar mata da yadda ta damu da shi, yau ta tsorata da tsananin son da ta ke wa Deedat, kamar ba ta so ta yi waje, don har sai da Aazeen ta hada mata da lallashi, a bakin kofar ta tsaya ta kasa karasawa. Yadda ta ke shakar kamshin turarensa haka ta ke jin kwararan sonsa a ranta.
Ji ya yi a jikinsa tana tare da shi, ya mike a dokance ya daga labule idanunsu suka gauraya. Wani murmushi ya sakar mata. Da sauri ta maida kai kasa.
“Iyakacinki nan?”
Jin haka ya sa ta shigo. Zama ta yi a kan kafet.
“ki zauna a kan kujera mana”.
Ta kada kai.
“Shi ke nan, ni ma bari na sauko kasa”.
“Yi hakuri, bari na koma kujerar”.
“Okey, na gode”.
Ta koma kujerar.
“Kin yi min nisa, ya kamata a ce a nan ki ka zauna”.
Ya nuna kujerar da ke kusa da tasa. Ba ta yi masa musu ba ta koma.
“Me ya hana ki cin abinci?”
Ta yi shiru.
“Idan ba ki yi magana ba yanzu zan kira ta in gaya mata cewar, ni ki ke so”.
Ai ko da sauri ta dago kai tare da zaro ido a nan ya ga ramarta.
“Oh God! Dubi fa yadda ki ka rame, me ya yi zafi? Ki bude baki ki yi magana, in ba haka ba zan kira ta…”
“Um, me ya sa ba ka daukar kirana, ba ka ba ni amsar sakonnina?”
“Saboda b shi da amfani, ko dubawa ban yi ba, na san bacin rai kawai zan gani, kuma ma ko da na bude ba zai wuce ki ce kina jin tsoro ba. Ko ba haka ba ne?”
Ya karasa zancen cikin kanne mata ido.
“A’a da ka sani ka bude”.
“Ba zan taba bude sakonki ba, saboda za ki haifar min da bakin ciki ne”.
“Na daina, ka ji?”
“Kin tabbata?”
“Eh”. Ta ce.
Ya dan matso kusa da ita inda suke iya jin hucin juna.
“Na ji wani labari, wai za a yi baikonki da Zaruk, kina farin cikin hakan?”
“A’a”. Ta ce da shi kai tsaye.
“To me ya sa?”
Ta ce, “Kawai”.
“Ke kenan ba ki da wanda ki ke so?”
Ta sake cewa, “A’a”.
“To wa ki ke so?”
Ta ce, “Ya fi karfina, ya yi min nisa, ya haramta”.
“No, wanda ki ke so bai yi miki nisa ba, za ki mallake shi, lokaci kawai muke jira sai kin zamo tawa”.
Ta yi murmushi mai ciwo.
“Kana nufin za ka auri Ya da kanwa ne?”
“A’a, kanwa kadai zan aura, ita kadai nake so”.
Ya sauko a kan kujera ya durkusa a kan gwiwarsa.
“Don Allah Nurat na roke ki, ya isa haka, ki daina azabtar da ni. Wallahi ban taba son wata ba, ban san me ake nufi da so ba sai a kanki, ina son ki ba ni hadin kai, komai zai yi daidai”.
“Yaya Adamu, ni ma ina sonka, ina matukar sonka! Amma ban san ya za mu yi ba, wallahi ina sonka, haduwa ta da kai rayuwata na cikin garari, Yaya Adamu da ma ban sanka ba…”