Motsin tahowar Aazeen suka ji ya mike ya koma kan kujera.
‘Ka tabbatar da taurin kanta ko?”
“A’a yanzu ki sa a kawo mata abinci za ta ci”.
Ta dubi Nurat, “Wai haka?”
Ta jinjina kai.
“Lallai ka ciri tuta”.
Ladidi ta kwala wa kira. A sukwane ta shigo ta durkusa.
“Ke me za mu samu a gidan?”
“Rangida kin sani yau ba a yi girki ba, amma za a samu cake ne kawai”.
“Oky za ki iya kawo mana, maza yi sauri”.
Ladidi ta tashi ta fita. Ba a fi mintina biyar ba ta shigo rike da filet. . .