Bai bar masallacin ba sai da gari ya gama wshewa, ya nufi sashin Ummita, tunda ya gaishe ta ya tsuke baki, takaicin duniyar nan ya ishe shi, me ya sa ya aikata haka? Me ke damunsa? Me ya sa ta shammace shi?
Lokaci-lokaci yakan yi tsaki, duk Ummi na lure da shi, sai ta ke jin ba dadi, da na sani ta fara yi, da alama dan nata ba ya jin dadin zama da Nabila. Ita kanta sai yanzu ta lura da wasu halayyarta, rshin tarbiyya, kazanta ba kamun kai, ga yawan sakin zance. Dadin dadawa ba ta da kunya, ba kuma ta kula da shi yadda ya kamata. Ta sani Deedat na da zurfin ciki tun yana karaminsa, ko da abu zai dame shi ba zai taba furtawa ba, sai dai ta ga yanayinsa ya sauya, gurin rashin walwala, kebance kansa, da ma bai cika fara’a ba.
Ta numfsa, “Ahmadu, lafiya na ganka ba kuzari?”
Ya yi yake, “Ummi, bana jin dadi ne, cikina ne ke yi min ciwo”.
Ta yi shiru tana nazarinsa.
“Ka sha magani?”
Ya ce, “Eh”.
Ta sake cewa, “Ka ci abinci?”
Ya ce, “Ai ba ta farka ba”.
“Kana nufin har yanzu?”
Ya jinjina kai kawai.
“Sai dai ka fita ka barta tana baccin asara ko?”
Ta kara jin tausayinsa.
‘Ummi, ni zan fita, muna da baki yau”.
“Ba zai yiwu ka fita ba cin abinci ba”.
“No, kada ki damu, da na fita ofis zan ci”.
Ya mike. Ta bi shi da kallo cike da da-na-sani, tana jin tashin motarsa ta nufi sashensa tana mita.
“Idan ba za ta iya ba, ni zan sanya ya rabu da ita, amma zan sa ya kawo mata abokiyar zama na tursasa an yi auren nan don samun nutsuwarsa maimakon haka sai damuwa ta biyo baya? Zan jure komai amma ba zan dauki wannan ba”.
Ta yi sa’a kofar ko karo ta ba a yi ba. tana tsoma kafa a harabarsu ta soma jin maganganunta, da alama waya ta ke, kalmar da ta ji ta furta ne ya sa ta dakatawa.
“Kai Aisha magani ya yi aiki, kin ga yadda ya rikice ? A jiya ya gane kurensa, sai dai gayen Zaki ne, duk jarabata sai da ya kawar min da kwadayi, kai yana da zaki tamkar zuma. Gwarzo ne, ya shallake tunanina, maganin nan ko nawa ne zan siya, ki samo mini sai na hana shi sakat, sai shiga sashen uwar tasa ma ya gagare shi. Sai na zame masa kaska! Ba kuma zan sake bari ya kwana shi daya ba sai na gigita tunaninsa… oho! Kabir ba, eh zai tsaya takarar majalissa… eh… dole ne ya amince, haka ne kawai zai ba mu damar fantawama, zan sauke shi daga kan layin da ta dora shi, yadda kanta yake cikin duhu ya sa ta ke son hana shi walwalawa, duk sai na rusa. Zan shagalar da shi, mun gama shirya komai da Kabir, yana kaunar Kabir fiye da komai, ba zai juya wa umarninsa baya ba, musamman da yake shi ne gaba da Yaya Deedat din”.
Ummi da kunnenta ya gama jiye mata komai, gaba daya ta gama jikewa sharkaf da gumi, ta ji kafafunta kamar ba a jikinta suke ba.
Yadda kanta ke juya mata ne ya sa ta yanke shawarar komawa baya, ba za ta so Nabila ta san ta ji shirinta ba.
Da kyar ta daddafa bango ta koma sashenta. Zubewa ta yi a kan kafet, kuka ta ke yi sosai, ta yi da na sani babu adadi, ta fyace majina.
“Ka fi ni gaskiya Ahmad, ka gano abin da na kasa ganowa, na cutar da kai na cutar da kaina. Kabir da kai za a hadu a cutar da dan uwanka? Wayyo Allah kaicona!”
Ta gama fita hayyacinta cikin lokaci kankani ta zabge ta yi zuru-zuru.
A haka Nabila ta riske ta, yau kam ta fi koyaushe fara’a, kanta sai faman rawa yake, wake-wake kam in ta sauke wannan sai ta dau wannan.
Rashin ganin fuska a gurin Ummi bai dame ta ba, miji ne ta riga ta aura, ta gama yi mata fadanci ko a ina ne mata ta fi uwa, idan tana son danta ya bi ta, dole ta dinga lallaba ta, in ba haka ba za ta janye mata da. Yanzu ba da ba ce, musamman yadda ta lura da Deedat mai bukata ne, a yanayin da ya nuna mata jiya tana ji ana fadin namiji mabukaci ya kan zama bawan mace.
“Ummi, na ga kamar ba kya jin dadi, zan koma ni kaina a gajiye nake, da yake ban wani samu baccin kirki ba”.
Ta fada tare da nufar kofar sashenta.
Ummi ta bi ta da kallo kawai ba tare da ta ce da ita komai ba, wata irin tsanarta ta ke ji.
*** *** ***
Bai iya katse shi daga duk abin da yake cewa ba, sai dai ya tabbata abin da ya zo da shi ba zai taba yiwuwa ba.
Kabir ya ce, “Da ma iya abin da nake son sanar da kai ke nan”.
Deedat ya sauke ajiyar zuciya, cikin dubansa, “Ka sani wannan ba ra’ayin Ummi ba ne, duk abin da ta hane ni ba zan saba mata ba. asali ma ban taba sha’awar shiga siyasa ba, ba zan kuma taba ba”.
“Deedat ina son ka fahimce ni, ka ga babu abin da ke ci yanzu sama da siyasa, muddin ka saka min hannu ba ni da fargaba zan haye”.
Shi kam ya zai billo wa al’amarin? In akwai abin da ya tsana shi ne ya ga ya bata wa Kabir, babu abin da Kabir zai zo masa da shi ya kasa yi masa ko da abin kenan da shi.
‘Yaya Kabir, ka je ka samu Umminmu, idan ta amince ba ka da matsala”.
Ya yi murmushi, ya sani dabara kadai zai mata ta amince.
“To Deedat, zan same ta gobe zan zo gidan”.
KANO
Cikin muryar kuka ta ke magana.
“Ni ce na san waye Yaya Zaruk, idan za a bi diddigi na haramta a gare shi Ammi, na tabbata Yaya Zaruk yana da boyayyen tabo, idan ku ka dage sai na aure shi wataran za ku yi kuka, saboda a nan ne za ku gane waye shi. Ni kuma ba zan taba yin farin ciki a rayuwar aurena da shi ba. Wallahi zan amince ko da za ku aura min Bala mai wanki, zan zauna. Zan yi…”
Ji ta yi an wanke ta da wani azababben mari da ya haddasa mata ganin wulgawar wuta, daga ita har Ammi razana suka yi.
Alhaji Usman suka gani tsaye a kanta yana tsuma.
“Ban yi tunanin ke ‘yar bakin ciki ba ce sai yau. Ban san haka ki ke ba, kin ba ni kunya, kuma har yaushe ki ka yi bakin da za ki iya bambance so da rashinsa? Ina yi miki kallon karamar yarinya, ban taba ba ki fuskar da za ki tsaya da wani ba, kullum ina yi miki kllon jaririya ban yi zaton kina da wayon da za ki tantance so da rashinsa ba, ashe nan kina yi min kallon soko?
To shi da ba kya so din gaya min dan iskan da ki ke so, gaya min zabinki wanda ya fi zabin ni ubanki mara mutunci”.
Ya juya ga Hajiya Rahma.
“Ai da ma na sani ke ki ke warware min tufkata, duk wata kutungwila ke ce ke dora ta a kai, idan kuma na yi magana ki ce ita din nawa ta ke, kuma kullum gani ki ke yi ita din ta fi kowa tarbiyya, yanzu ki gaya min wannan ce tarbiyyar? Abin da ake nufi da tarbiyya shi ne, da ya bi zabin iyayensa musamman uba, duk girman ‘ya iyaye kan yi mata zabin miji balle ke ficiciya da ke.
Kuma wallahi idan za ki mutu sai kin auri Zaruk, idan ma ki ka yi wasa ranar baikonku za a daura aure, inyaso ki mutu, munafuka tana yawo cikin hijabi simi-simi kamar ta gari”.
Kwallo ya yi da ita, ta kife gefe, kukan ma ya ki zuwa. Ya shige yana faman huci.
Tunda ya fara kallonsa Hajiya Rahma ba ta yi ba, sai da ta tabbatar ya fita ta dago Nurat tana lallashi. Hawaye sun cika mata idanu, ta yi saurin gogewa da bayan tafin hannunta gudun kada Nurat ta gani. Sai dai ta makara, domin hawayen sun ki boyuwa.
“Kin gani, karamin abu yana son zama babba. Ban ga aibun Zaruk ba, yaron kirki ne, yana da asali, ga shi dan dangi ne, ba shi da halin tur!”
“Ummina ku yi hakuri, ba zan sake ba”.
Ta fada murya kasa-kasa.
Jikin Ammi a sanyaye, tsananin tausayin ‘yarta ta ke yi.
‘Nurat, ba ki taba yin soyayya ba, da a ce akwai wanda ki ke so wallahi sai inda karfina ya kare. Amma yanzu in ma na ki waye zai maye miki gurbin Zaruk, babu. Wannan ne kawai zai dakatar da ni, don haka Zaruk shi ne kaddararki, ina yi miki fatan alkhairi, amma in kuma akwai ki sanar da ni”.
Idanunta suka yi raurau, ya za ta yi ta shaida musu Adamu ne zabinta? Ko dai ta rufe ido ta shaida mata duk abin da ma zai faru ya faru, ta sani za a shiga rudani, sai dai na dan lokaci ne, wataran zai wuce, komai ya komo daidai.
Ta sani Ammi za ta fahimci feeling dinta, za ta shaida mata labarin komai, za ta gaya mata suna son junansu, za ta gaya mata idan ba ta samu Adamu ba za ta mutu, za ta gaya mata yadda ta haukace a kan sonsa.
Za ta gaya mata ta yadda suka faro, za ta gaya mata ba tare da ta sani ba ta yi wa Yayarta Aazeen KYAUTAR ZUCIYA.
“Akwai magana a bakinki, ki gaya min, kada ki yi shakka, na yi miki alkawari zan tsaya miki a kan komai, kada ki ji tsoro, na fi kowa kaunar farin cikinki. Na fi kowa sonki, zan sadaukar da farin cikina a gare ki”.
Ji ta dinga yi kamar tana yi mata allurar kwarin gwiwa, wasu zafafan hawaye suka silalo kuncinta, za ta gaya mata.
Ta motsa labbanta kamar za ta yi magana, Aazeen ta fado dakin.
“Wow Ammina, yau ina cikin farin ciki”.
Ta rungume Ammi ta baya.
“Dad ya amince, zai ba wa Adam dina manaja, kuma ya yi min alkawarin aura min shi, kin ga tare za a hada bikinmu da kanwata, gaba dayanmu za mu tafi mu barki”.
Ammi na dariya cikin kwalla.
“Ina kuma mutumin da ki ke buri, Ahmad Deedat?”
“Ke manta da wannan, ya yi min nisa. Ni tuni ma na shafe shi a babin rayuwa ta, soyayyar Adam ta kore komai. Ina mamakin yadda nake ji a raina shi ne rayuwa ta, ba zan taba jure rashinsa ba, wallahi Ammi Adam ya yi min ko da ba shi da komai zan iya aurenshi, inyaso ni na zamo namijin in dinga fita ina nema mana kudi, na dinga yi masa komai, in ba shi abinci, ya kwanta in nemo sai dai ya yi kwalliya ina kallonsa ina jin dadi”.
Ta dubi Nurat.
“Ko ba haka ba kanwas?”
Cak! Ta yi shiru lokacin da ta hangi kwalla na faman tsinkowa daga idanunta.
“Oh God, what’s wrong, me kuma yau? Ke kullum kuka ba kya ko gajiya, me ke sa ki kuka? Bana son haka, Ammi ke ce ko?”
Ammi ta kada kai.
“Ba ta jin dadi ne, amma ta sha magani yanzu komai zai yi daidai”.
“Ya kamata na kai ta asibiti, kada abin ya zamo babban abu’.
“Ki bari tukunna tunda ta sha magani, idan abin bai lafa ba gobe sai mu je asibitin”.
“Taso yanzu ki je ki dan kwanta zuwa anjima idan kin samu sauki Zaruk zai kai mu gidan gyaran jiki”.
Ta kama hannunta har zuwa bedroom dinta, ta kwantar da ita tare da lulluba mata bargo. Kokarin barin dakin ta ke, wayarta ta shiga ruri. Ta dubi fuskar wayar.
“Wow, my darling”.
Ta kara wayar a kunne.
“Yau saura kwana hudu birthday din Dad, tare da baikon kanwarmu, kuma akai sauran albishir sai ka zo”.
Daga bangaren Deedat ji ya yi kirjinshi ya buga, ya ce, “Okey, ba damuwa. Amma ina kanwar tamu?”
“Ga ta nan a kwance, ba ta da lafiya”.
“Ba ni ita na yi mata sannu”.
“Ba ka da matsala”.
Ta mika wa Nurat waya.
“Za ku gaisa da mijina”.
Wayyo! Ji ta yi kamar ta jefe ta da kututturen icce wanda ke ci da wuta.
Ya yi bala’in tausasa murya.
“Gaya min me ke damunki, kada ki boye min”.
Kuka ya kwace mata.
“Kada ki yi min haka, ina wayarki?”
Tana son yin magana, sai dai Aazeen ta kasa ba ta damar hakan, domin ta kafe ta da ido. Kawai sai ta mika mata wayar, ta kifa kai a filo tana shessheka.
‘Nurat! Nurat!! Kina jina?”
“Aazeen ce”. Ta fada a dakale.
Wani shock ta ji yadda yake ambatar sunan kamar shi ya kirkiri sunan.
Ko a jikinsa, bai wani razana ba, duk kuwa da yanayinta ya nuna ta dan ji ba dadi.
“Ya ki ka karbe wayar muna magana?”
Ta yi dariya, “Na ga alama ka fi lallaba kanwar nan taka a kan matarka”.
Ji ya yi gaba daya ba ya son wasa, in ya ci gaba da sauraronta zai yi ba daidai ba, hakan kuma zai iya haddasa wa kansa matsala.
“Na yi baki, zan kira ki anjima ko?”
Bai ji ma amsarta ba ya katse wayar yana faman huci, yana ji kamar zai shake ta.
A ranar bai koma gida da wuri ba, saboda yana cikin damuwa, duk wanda ya gaya masa magana sai ya zama fushi, tilas kowa ya shiga taitayinsa.
Ba zai samu nutsuwa ba tare da ya ji yadda ta ke ba yanzu, lambarta ya loda a cikin wayarsa ya kira.
Ringin ne mai sanyi da shiga rai ya dinga tashi a hankali. Ta bude ido ta yi saurin mikewa zaune saboda sanin cewar Deedat kadai ta sanya wa ringin din. Ta yi saurin dafe kai saboda yadda ta ke ji kamar zai tarwatse, ta dafe gefen tana kokarin daga wayar ta manna a kunne, ba ta kuma ce komai ba.
“Nurat!” Ya ce cikin wata irin murya da ya sanya dukkan sassan jikinta amsawa.
“Kina jina Nurat?”
“Ina yini”. Kawai ta ce da shi.
Ya sauke ajiyar zuciya, wani sanyi ya ratsa shi.
Ya ce, “Sannu kin ji, ya jikin naki?”
Ta ce, “Yanzu na warke”.
“Na gode wa Allah da jin haka. Yanzu gaya mini kina son wannan baikon?”
Ta yi masa shiru.
“Ki bude baki ki yi magana kin ji, kina son Zaruk?”
Ta ce, “Ban sani ba”.
Ya ce, “Ban gane ba, kina sonsa ke nan?”
Ta ce, “A’a”.
“Good. To ki bar ni in gaya wa Dad dinki cewar ke nake so”.
Ta girgiza kai.
“Kada ka yi haka, zai kashe ni, yana fushi da ni saboda Zaruk, ba ya amsa gaisuwa ta don Allah ka rufa min asiri ka kyale ni”.
“In kyale ki kamar ya ya? Kina nufin na hakura da soyayyarki? Kina nufin in mutu za ki iya jure ganin mutuwa ta?”
“A’a, na ce a’a, ina sonka! Ina matukar sonka!!!”
“Na san haka, ke ce ki ka ja mana, ke ce ki ka assasa komai. Yanzu ki gaya min ya za mu yi? Ki gaya min komai zan iya yi a kanki”.
“Ban sani ba”.
“Okey, kin amince min in samu Dad dinku?”
“A’a, na ce a’a! Ka rufa min asiri”.
“To in zo na dauke ki mu gudu, mu tafi can wata duniyar mu yi aurenmu?”
Ta zaro ido, muryarta na rawa.
“Ba zan iya ba! ba zan iya barin Ammi ba, ba zan yi sanadiyyar gurbacewar dangina ba. sun fi komai muhimmanci, idan na gudu lokacin da ka juya min baya ko ta Allah ta kasance ina za ni, waye zai karbe ni? Don Allah kada ka sake ce min haka ka ji?”
Kamar zai yi kuka.
“Na yi kuskure ba zan sake ba, kin ji”.
Duf ya katse wayar, ya shiga sintiri, yana jin zuciyarsa na wani irin bugawa, shin wannan wace irin soyayya ce mai zafi haka Allah ya dora masa?