Wayarsa ta dauki ruri, ya daga. Muryar Nurat a sanyaye.
“Mu yi addu’a, za mu samu mafita ka ji, ka ga Yayata tana sonka, a dalilinka ta canza, kowa na jin dadin canzawarta kada ka dauke mata farin ciki. Kai ne farin cikinta…”
“Ni kuma ke ce farin cikina, don haka ina son kaina”.
“Ina jin yadda ka ke ji… zan ajiye waya na ji Ammi tana kirana”.
“Zuciyata na yi min ciwo, na rasa da me zan sanyaya ta”.
“Ni ma ina jin haka na ce da kai, cutuka iri-iri ne, amma ba na tunanin akwai mai zafin cutar so. Zan ci gaba da sonka cikin kowane yanayi”.
Ya yi murmushi kamar a gabanta yake.
“Na gode, na yi murna sosai, sai anjima ko?”
Da kyar ya katse wayar, ta mike ta tafi amsa kiran Ammi.
*****
A mota Zaruk da Aazeen na ta hira, ita kam Nurat ta yi gum da baki. Zaruk na ta satar kallonta ta madubin motar, so yake yi ko sau daya ne ta dago, amma fir! Ta ki.
Daidai Dijah Beauty Saloon ya yi fakin, gaba daya suka fito.
“Ina za ka bi mu?” Aazeen ta fada.
Zaruk ya san me ta ke son cewa.
“Kada ki damu, tun jiya na zo mun gama magana da Deejah, bana son kowa ya kasance a gurin saboda zan kawo matata, zan zauna ne sai an yi komai a gabana”.
“Okey, ba ka da matsala.
Aazeen aka fara yi wa dilka, halawa, da wankin kai. Ta fito tas! Kamar wata amarya.
Tunda aka fara hira suke da Zaruk har yanzu Nurat ta ki sanya musu baki, sai da aka zo kanta ta ki mikewa.
Aazeen ta shiga kiciniyar cire mata hijabi, ta rike gam! Kokarin saka kuka ta ke har sai da ta kular da Aazeen.
“Amma Nurat ba ki yi ba, ban taba ganin bagidajiya kamarki ba”.
Deejah ta dubi Zaruk.
“Malam Zaruk ko za ka ba mu guri?”
“Okey, kada ki samu damuwa”.
Ya dubi Aazeen.
“Ki same ni a mota”.
“Me zan zauna in yi? Mu je mota kawai mu jira ta”.
Ai ko suna fita da kanta ta cire hijabin, Deejah da kanta ta dinga jinjina kai ganin halittar da ba a jikin kowa ba, gashi har gadon baya, mai santsi da sheki, jiki sumul-sumul, diri da kugu, mazauna ta ji ana cewar dan Adam tara yake, to sai dai hakan, amma komai na Nurat ya gama haduwa, sai dai ba ta sani ba ko ta bangaren halayya za a samu matsala.
Ta sauke ajiyar zuciya tana goyon bayan yadda Nurat ta yi, don irinsu idan ba su boye halittarsu ko’ina suka shiga, ba za a iya kawar da kai ba.
Kwance ta ke lakadan a kirjinsa, sun dade suna tafka ta’asarsu cikin shakakkiyar murya Aazeen ta fara magana.
“Ina tsoron kada ka maida kanwata mai jire gida, sam ba kalarka ba ce, ba za ka samu yadda ka ke so ba.
Tunda ka fara magana na nusar da kai, amma ka kasa ganewa, Nurat na da kafiya, kai ma ka sani, kana ma gani. Ina gargadinka ka sake tunani tun kafin zuwan wannan rana”.
Ya shiga yi mata kallon ba ta da wayo, ita ba ta san cewar hakan ne ke kara wa Nurat kima a zuciyarsa ba, in ma za ta fi haka gidadanci, zai fi murna. A zahiri ya ce da ita.
“Kada ki damu, ni fa namiji ne, na san yadda zan bida ita”.
Dago kan da zai yi, ya hangi Nurat tsaye a bakin shago. Zo ka ga zarran kyau, gabadaya ya gama kidimewa, yadda ya saki baki ne ya sanya Aazeen maida hankalinta kallon gurin da ta ga yana kallo.
“Wow! Kyau!” Ta lakuce masa hanci.
“Yaro ka nace”.
Ya numfasa, “Zan auri Nurat na rayu da ita ko da ba za ta bari na kusance ta ba, in dai za ta bari na dinga kallonta. Ina son Nurat”.
Daidai lokacin ta isa gindin motar, wannan karon gidan gaba ya bude mata.
“Baby kin yi kyau”.
Ta dan saki fuska.
“Na gode’. Ta ce ba tare da ta dube shi ba.
“Ni ma na yaba”. Aazeen ta ce tana murmushi.
Zaruk ya ja motar.
A kwanaki ukun da suka rage, zaman lafiya ya gagara tsakanin Hajiya Rahma da Alhaji Usman, duk a kan maganar Zaruk, inda Alhaji Usman ya kekashe kasa cewa ita ke goya wa Nurat baya a kan ta bijire wa umarninsa, don haka yau Hajiya Rahma ta turje.
Nurat kuka ta ke yi sosai kamar ranta zai fita, hankalin Nurat da Aazeen ya yi matukar tashi.
“Nurat din da kullum ki ke yabo ga ta kullum ita ke sa ki a matsala. A dalilinta kullum sai kin yi kuka”.
“Ammi na tuba, zan yi duk yadda ki ke so, na yi miki alkawari ba zan sake sanya ki kuka ba, in dai a kan Yaya Zaruk ne na amince. Ko yanzu za ku iya daura min aure da shi”.
“Dallah Malama saurara, mu ba wannan muke bukata ba, ki saki jiki ki daina yi masa fitsarar nan taki. Ki daina nuna masa cewar tursasa ki aka yi”.
Nurat ta maida kallonta ga Ammi, ita ma Ammin kallonta ta ke ta jinjina kai.
“Abin da nake so kenan. Zaruk ba ya iya boye damuwarsa, ba ya magantuwa a duk lokacin da ki ka bata masa, amma sauyawarsa na tabbatar ma da iyayensa cewar ya ki samun hadin kanki, yadda Dad dinsa ke kaunarsa ya sanya ba ya jurewa dole sai ya sanar ma da Dadynku, idan kuma ki ka tsananta tsakanina da shi komai zai iya faruwa’.
Ta dan ja numfashi.
“A yanzu Dad dinku shi ne komai nawa, ba ni da uwa ba ni da uba, ko da ma suna raye su din ba komai ba ne, domin a cikin bakin talauci suke, irin talaucin da ban taba karo da shi ba, idan kuma ki ka tsananta allura ce za ta tono garma, idan ki ka tsananta gaba daya gidan nan za mu iya tarwatsewa, bakin ciki ne za a maye gurbin farin ciki da shi. Bakin ciki na har abada, ina tsoro don Allah ki taimake ni”.
Kukan Nurat ya tsananta.
“Ammi, ki daina rokona, in dai Yaya Zaruk ne zan canza masa, na yi miki alkawari”.
Ta shafa gefen fuskarta.
“Na gode sosai, Allah ya yi miki albarka”.
“To amma Ammi ina son karin bayani a kan ikirarinki da ki ka yi na fadin allura za ta tono garma?”
Gabanta ya fadi, ya aka yi ta saki layi haka? Me ya sa ta ke neman burma wa kanta wuka? Nan da nan yanayinta ya sauya, ta firgice. Cikin daga murya ta ke magana.
“Kada ki sake tambayata! Kada ki kuskura, kada ki sake in ji kin fada wa wani haka”.
Ta mike a zafafe ta bar gurin.
Aazeen da Nurat suka bi ta da kallo cike da fargaba.
Saura kwana biyu a kaddamar da kamfani tare da birthday da baiko, ko ina ka juya tashar rediyo sanarwa ake yi, har kawo yau din nan, wato ranar da za a yi wannan bikin.
Zaruk har ya gaji da haduwa, yana jin kamar yau ce ranar bikinsa da burin ransa. Abokansa na kasar waje da na nan gida duk sun hallara, lokaci-lokaci suna yin waya da Aazeen, sai dai yanzu ya gagara samunta, da alama tana busy sosai.
Daga bangaren Aazeen gaba daya ta shiga damuwar rashin karasowar deedat, tunda suka yi waya da shi yake ce mata yana hanya, ba ta sake jinsa ba, gaba daya ya kashe wayoyinsa.
Nurat da aka dauko mata shahararriyar mai kwalliyar nan Billy, wacce ke zaune a unguwar Sharada kwalliyar ake mata, amma gaba daya hankalinta ba a jikinta yake ba, tunani biyu ta ke yi. Ya za ta yi da alkawarin da ta daukar wa Ammi? Ya Adamu zai yi? Me kuma ya hana shi zuwa? Lokaci-lokaci ta kan leka bangarensa na online sai dai babu alamarsa, tun tana rubuta sako har ta gaji.
Ta dago kai da damuwa fal a ranta, Aazeen ta hango ta kasa zaune fuskarta kawai ta kalla ta san tana cikin matsananciyar damuwa.
An gama yi mata kwalliya, wata irin doguwar riga ta sanya mai hade da dan siririn gyale, gaba daya kallo ya dawo kanta, a gurin Aazeen kuwa sai Nurat ta zame mata kamar sabuwar halitta, gaba daya ta koma ta raina kanta.
Kiran Dad ne ya shigo wayarta inda yake sanar da ita su kawai ake jira, sabuwar motar da Alhaji Usman ya siya mata saboda rana irin ta yau ita suka shiga. Tana tuki tana faman tsaki, gefe daya tana ci gaba da kiran layin Deedat, kwalla ya cika mata idanu, al’amarin ya taba zuciyar Nurat, kai ta dade ba ta ga hawaye a idanunta ba, da wahala ka ga Aazeen na kuka, tana da dakakkiyar zuciya.
“Yaya Aazeen me aka yi miki?”
Shar-shar ruwan hawayen suka kwaranyo kan kuncinta, ta dan yi shessheka.
“Nurat, yau na yi wa Dad alkawarin gabatar masa da Adamu, yau Dad zai gabatar da shi a matsayin wanda zai nada manaja, ga shi duka ya kashe layukansa. Ina tsoron kada ya sake shawara a kaina, a halin yanzu ina jin ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba”.
A sanyaye ta ce, “Zai zo insha Allahu, ba zai ba ki kunya ba, kila ma yana gurin yana son ne kawai ya ba ki mamaki ne”.
Ta goge kwallar fuskarta, “Allah ya sa haka”.
Tun daga nesa suka hangi cincirodon mutane a get din kamfanin, ko’ina na kamfanin ya sha adon kyalkyali, motocin da suke ajiye a gurin ba za su kirgu ba.
Da kyar suka samu hanya bayan sun yi fakin ma jama’a ne suka rufe su, da kyar suka fito daga cikin motar. Da sauri ta ji an rike gefen rigarta. Daga kan da za ta yi suka hada ido da Deedat, bai saki gefen rigar tata ba yana janta har sai da suka bace daga cikin jama’ar gurin. A can wani loko suka tsaya ba lallai a iya kula da su ba.
Da sauri-sauri ya soma magana.
‘Ina son mu yi nesa da gurin nan, ina so za mu yi magana”.
“Duk abin da za ka ce ka ce a nan, amma ni babu inda za ni”.
Gaba daya fuskarsa ta rine, ba shi da sauran annuri idanun nan sun yi jajir tamkar ya yi kwalli da ruwan barkono. Cikin wata irin fusata da wata irin murya da ba ta sanshi da ita ba.
“Kin nuna wa kowa cewar kina farin ciki da wannan rana ko? Kin cire mutuncinki kin sanya wannan dan mitsitsin mayafi kina tallar tsiraicinki duk a kan zuwan wannan rana, kina son ya yaba halittarki, kin saka jambaki kin kara gashin ido”.
Ya koma ya daga murya.
‘Saboda me ki ka yi haka? Kina son ki ce kina sonsa ke nan?”
Ya daga hannu ya kai bakinta da karfi ya goge mata jambakin, cike da bala’i.
“Ba ki yi kyau ba, na ce ba ki yi ba! kina murna ko kina farin ciki shi ya sa ki ka yi kwalliya’.
Muryarsa ta sarke. Binshi kawai ta ke da kallo, ya koma tamkar tababbe.
Budar bakin ta yi za ta yi magana, “Shissssh! Nurat, bana son jin komai, bana bukatar wannan”.
“Adamu duk da haka ka saurare ni”.
“Ba zan saurari komai ba, kin cutar da rayuwa ta, na gani kowa yana kallonki, mutanen arziki suna Allah wadai da shigarki, wadannan iyayen naki wadanne iri ne?”
Kokarin gudu ta ke, tana jin zai iya aikata komai a kanta, kawai ta ji ya damki gashin kanta.
Aazeen ce tsaye tana kallonsu.
Turkashi!
Kada ku gaji, mu tara a littafi na uku don jin ci gaban wannan badakalar, shin zuciyar ta kyautu ko da sauran kuka an ci gumba an hana maye?
Mai kaunarku.
Bilkisu H. Muhd