Skip to content
Part 26 of 27 in the Series Kyautar Zuciya by Bilkisu H. Muhammad

Nurat na zaune a takure a bisa gadonta a dakinta.  Wayar da ke gabanta ta fara ruri, ta zabura ta duba sunan  zaruk ne    ta ja da baya daga kusa da wayar kai kace hannu zai zuro daga cikin wayar ya kama ta. Har wayar ta katse bata amsa ba

” Aazeem ta fado dakin tana faman haki my sweet sister kinsan Mai ke faruwa?

kuwa ,Nurat kawai ta bita da ido hadi da Dan kada kai,

“burina zai cika anyi garkuwa da babar Didat nasami damar da zansan wayeshi  wani farin ciki ya lullube Nurat tabbas idan hakan ya kasance zata Sami yancin kasan cewa da Didat Kuma tasan yadda yayar ta ke kaunar ta zata iya taimaka mata gun ruguza batun zaruk ta saki murmushi

“naji dadi yayata to Amman ya zakiyi da adamu?

” Nurat ban tabbatar da Ina son adamu ba sai da nasami labarin Didat, nasani idan na bincika nan kusa kusa zan hadu dashi nasani Kuma zai Soni sai dai gaba daya na canza sheka bazan iya rayuwa Babu Shiba,zanso Naga Didat kodan nayi masa tambayoyin da ya Dade azuciyata

Nurat taji kanta yayi wani irin sarawa

“Amman idam Kika ga yayi Miki fa?

“uhm,ai Babu guri,ke kinsan kuwa mahaukacin son danake ma adamu,koda yake bazaki game ba ta Dan bubbuga kafadar ta tayi waje tana faman taunan cingam Nurat ta kife Kai agado tashiga rigzar kuka,

“yayata na tabbatar na fiki son adamu akansa na soma jin yadda so yake,ni yanzu Yaya zanyi”

Koda takoma setroom ta Tara’s da Aazeem nata buge bugen waya duk akan yadda zata hadu da Didat ta koma ta hau yanar gizo duka nanma binciken takeyi kowani shafi ta bude hirar garkuwar da akayi da maman Didat ake sai dai har kawo yanzu ba,a dora hoton Saba ta koma ta ajiye wayar tana dariya har da bubbuga kafa da tafa hannu

“karyar ka ta kare oga Didat domin duk bala,inka wannan karon sai munsan waye Kai.”

tamike ta sunkuci Jakarta tayi waje ammi da Nurat suka bita da kallo ammi ta dubi Nurat

“na rasa inda tasa gaba ta sauke ajiyar zuciya Allah ka shirya min.”

“Didat kabi komi ahankali komi zaiyi daidai ka dubi fa yadda kabi ka firgice nayi imanin cewar Babu abinda zasuyi mata wa,annan kudaden sunyi yawa munemi sasanci milyan dari uku haba Ina mamakin wannan lamari mtss Ina mamakin rashin imani irin na wa,annan mutane Allah sai ya saka mata,

“no Salim a hada kudin kawai akai musu bana son ma ta cika wa,adin da aka dibar mata,inajin tsoro suna can suna azabtar da ita komeye zan bada bazan iya jurewa ba kawai a basu pls,”

“ni abinda yasa nace mubi ahankali na tabbata irin yadda akeyin bincike Nan danan za,a damkesu.”

wani irin kallo Kabir ya watsa masa

“dole ne kace haka to tunda ba uwar ka bace ko, salon a kawo Mana ita amace

“no Yaya Kabir Salim yayi gaskiya inaga mubari zuwa ranar da suka diba Mana da izinin Allah Babu abinda zai sameta kaji”

“bazai yuwu ba sabida ba ita ta haifeshi kaba inda itace ta haifeka na tabbata ko kwana daya bazaka bari tayi ba ai daman tsintaccen mage bata mage kada Allah yasa ka Kai kudin butulu kawai shege Mara asa—-

Salim ya katseshi da wani irin mari Wanda sai da yaga wilkawar wuta a ida nunsa sai kokawa ya sarke atsakaninsu Didat yashiga tsakaninsu yana  sharar kwallah ya janye Salim suka shige mota haka suka baro Kabir nata faman zage zage da bankade bankade Salim ne yayi dreving har suka Isa gida bai daina kukaba

a harabar gidan suka riski nabila tanata faman jin kide kide tana bin waka ba abinda ya dameta lokacin da sukayi ido biyu da Didat gaba daya tatsorata da yanayinta Babu Wanda ya kulata Koda tayi musu sannu da zuwa basu amsaba suka wuce shashinsa

A setroom dinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye idanunnan sun yi bala,in rinewa tamkar anwan kesu da ruwan barkono, handset dinsa ce ta Fara ruri Salim ya dauki wayar .Ya dubi Didat.

“,Nurat ce ke kira”

“kada ka daga”

“Nurat ce itace farin cikin ka, kada kaki dagawa bakasan Mai ke tafe da itaba Kai da kanka kace bata kiranka sai abu Mai muhinmanci.”

ya taso da kyar ya karbi wayar ya ratsa Kore zai kafa akunne kawai sai yayi cilli da wayar ya koma ya zauna yana haki, yasoma magana cikin wata iriyar murya Yana Mai zubar da kwallah.

“Ni ba komi bane face shege Kabir yayi gaskiya Amman sai dai ni ba laifina bane Mai yasa zaidinga yi min gori,bani da masaniya akan komi ubangiji shiya tsara min rayuwata bansan waye niba tabbas idan ban ceci ummi naba bani da amfani zan baiwa mutanennan duk abinda suke bukata,batun Nurat na janye duk inda naje sai an bankada min asirina Wanda ada yake alullube.”

ya rushe da wani irin kuka .

“,wallahi na tsani kaina ubangiji inhar mutuwata zata zamo min alkhairi ka dauki rayuwata na huta banajin zan iya rayuwa batare da ummina da Nurat ba sune farin cikina idan har ban rayu da Nurat ba na tabbata bazan tsinci komai aduniyar nan ba asalina bazai sa abani itaba dan haka zan shafe babinta,Koda ummi ta dawo gareni zan nisanta da ita.”

” nabila itace wadda tasan wayeni zan rungumeta.”

samir ya goge kwallar dake faman tsinkowa daga idanunsa ya karasa ga Didat ya riko hannunsa cikin muryar lallashi.

“. kada kace zaka juyawa rayuwar ka baya kada ka karaya Kai mutunne kamar kowa kafita da ban Kai din nagartacce ne Ina tare da Kai cikin kowani yanayi haka wasuma deyewa suna tare da Kai fiye da tunaninka kada ka karaya .”

text din daya shigo wayar sace ta katse musu maganar tasu.

Salim ya dauki wayar bakuwar lambace da sauri ya bude.

“Lokaci na dada kurewa muna bukatar akai Mana kudin namu kano a yau dinnan idan ya Kai gobe komi zai iya faruwa .abinda wasikar ta kunsa kenan

*****

Wani tangamemen gida Mai kama da gidan shugabannin kasa kafin ka Kai ga cikin gidan sai ka wuce get get guda biyar kowani get sojoji hudu ne ke gadinsa .

Acan wani bangare daga gidan wani tangamemen set room next wanda ya gaji da haduwa aminai uku wa and tsananin kaunarki juna da sukeyi ko ciki day suka fito sai haka tun karfe hudu suke faman neman mafita akan matsala daya Amman sun kasa samun matsaya.

Sanat ya sauke ajiyar zuciya ya koma ya numfasa

“Nasani abinda na aikata ne ke faman bibiyata taba hafizan alkur,ani irinta dolene in dandani kudata tunda abinnan yafaru na auri mata sunfi guda goma Sha biyar duk wacca na haihu da ita sai yar ta mutu duk nan ban sadudaba haka nayi ta saki Ina Kara aura atinanina mutuwar daga jikina take ga shi yanzu bani da kowa narasa kowa sai dai kudina da dangi da malamai suke taci.”

Alhaji Atiku ya dafa kafadan sanat .

“shi ubangiji ba hakaba yakeba wannan abinda ka aikata na sani kadade da yin nadama shi ubangiji Mai gafara ne muntaso tin muna yara kana kyamar fasikin mutum sai Kai Kuma ka jarabtu da hakan dan haka kaddarar kace tazo ahaka kayi hakuri.”

” Ni abinda nake gani kawai yaje ya bayyana kansa ga Didat dan sane jinin sane zai fahimce shi.”

Sanat ya kada Kai cikin rashin gamsuwa da shawarar Dr Hamza.

“Bazan iyaba kunsani nadade Ina bibiyar sa yarone Wanda yafita da ban ya banbanta da kowa nasani yanzu aduniyar nan ya tsaneni fiye da komi bazan taba dosar Saba Koda kuwa ace zan mutu.”

Kallonsa sukeyi kamar zasu saka ihu suna Jin shigar maganar sa har cikin ransu domin sun maida matsalar dayansu na dukkanninsu sun kudurce azuciyarsa da yaddar Allah zasu daidaita komi muddin suna a raye sai sun dawo masa da farin cikinsa da wanna kudirin suka rabu.

Adai dai babban titin dake sharada na hauren wanki tana cikin adaidaita maimaita Kiran laying Didat takeyi Amman swich up tacije lebe ta doan rintse idanunta wasu irin kwalla na faman tsinkowa daga idanunta kirjinta yayi mata nauyi da soyayyar Didat bata taba sanin haka sonsa yayi mata illah ba sai da yayi mata nisa aina zata ganshi ahankali ta Kai hannu ta shafi mararta ta dan saki murmushi cikin kuka can wani tsoro ya mamaye zuciyar ta da sauri ta dauke hannu tana share kwallar fuskarta  idan tarasa Didat tasani mutuwa zatayi.

Wata katuwar moto shake da buhunhuna ita ta haddasa goslow  kusan mintina goma motoci basu motsaba kowa ya gama kosawa tasoma leko da Kai dan ganin karshen goslow din

Ras Taki gabanta ya yi wani irin bugawa ta rufe ido ta bude Yana nan dai a cikin motar

“Adamu.

Tafada acan karkashin makoshinta.

“Kai wannan bashi bane daman ance ana samun mutane masu kamanni daya shidin wanna yafi adamu fari da komi gashi cikin tsadaddad mota fuskarshi sanye da glas adamu baya saka glas Kuma shi dan gayu ne adamu kuwa babu ruwansa.”

“Magana kekeyi ne?

Drive ya tambaya.

“Mai kaji nace?

“Magana naji kinayi jinakeyi dani kike,yauwa motar data hada goslow din ta wuce yanzu zamu Sami sa ida.”

Dai dai lokacin motar Didat dake daya titin ya dinga kusantar su Aiko ta Kara kafe shi da ido,

Jikinta yagama bata cewar wannan jinin adamune Wanda shi yake rayuwa a birni

“Dan Allah mubi wancan motar.”

“Ai ba haka mukayi dakeba idan hakanne to kudinki zai ninka.”

“Ko nawane zan baka dan Allah kayi sauri kada ya bace Mana.”

“To Amman kinsan iya Nissan inda zashi?

“Dan Allah kada ka isheni,Kai dai ba nema ka fitoba ko karshen duniya zashi mubishi.”

“Angama.

Ya ko dauki hanya gudu yake kawai har suka isa daidai nasarawa bomfai wasu irin maka makan gidaje suka dinga wucewa adaidai wani hamshakin gida Didat yayi faking wasu sojoji ne guda biyu suka bude masa get din ya danna han in motarsa ciki suka maida get din suka rufe .

daga dan nesa sukayi parking ta bude Jakarta dubu daya ta Mika masa bata sake bi ta kansaba yaja ya tafi.

Akofar get din ta tsaya daya daga cikin sojojin ya taho gunta hannunsa rike da sigari Yana zuka tare da furzar da hayaki

Kallonta yakeyi sama dakasa,tana jin kamar zata kwara amai sabida warin tabar.

Cikin lalatacciyar hausar sa

ya ce.

“Kina neman taimako ne?

Ta kada Kai yayinda take faman daddauke numfashinta.

“Sonakeyi kagaya min sunan wannan Wanda ya shiga ciki.”

“sabida me kina binsa bashine?

Ta kada Kai.

“Dan Allah sunan sa kawai nake sonji,sabida kamar nasanshi.”

“To wannan ba Wanda Kika sani bane wannan kusane Wanda baya shiga lamuran mutane bama anan take da zama ba lokaci lokaci yake zuwa,dan haka wuce kiyi tafiyarki pls.”

batasan sa,ar da ta durkusa Akan gwuwarta ba.

“Dan Allah ka taimake ni sunansa kawai,

tasa hannu cikin jaka ta dauko kudi.

“Kada ki soma bamu karbar cin hanci oganmu baya goyon bayan haka domin ya sauke Mana dukkan wani hakkin mup sai dai idan kyauta Zaki bamu shine kawai muke karba.”

Da sauri tace.

“KYAUTAR nabaka.”

“Karya kikeyi zan gaya Miki sabida Allah sunansa Ahmad Didat.”

“Kataimakeni na ganshi Ina son zamuyi magana.”

“Wannan ne Kuma Baki Isa ba,pls wuce kitafi tinkan na sakar Miki bullet dina.”

Zata kara rokonsa ya daka mata wani uban tsawa kamar zai cinyera da sauri tabar gun.

daya sojanne ya karaso gunsa.

“what is wrong.”

sajan ya kwashe labari ya gaya masa.

“Hoh na oga., Kasanshi Yana Riki dewa .

“Nima I think so but Amman kasan oga baya son damu Kuma baya son asanshi,idan kasanshi shine idan baka sanshi”

” To bashi bane.”

daya sojan yafada gaba daya sukayi dariya hadida tafawa.

“gaba daya kin sauya kin koma tamkar bakeba kinki Kuma sanar dani damuwarki ko kina sonne kema ki zamo Yar uwarki.”

Tayi shuru tana kallon Nurat wadda keta faman kuka.

“Kigaya mini Ina kikaje?

Takaici yasanyata ta finciko ta tare da kofa mata Mari duk da haka taki magana

“Shikenan,na shiga uku kema kinfi karfina nasani bazaku taba bina ya ubangiji natuba ka yafe min sharrin zuciya ne,kada kayi min wannan jarrabawar Nurat ita kadai ce take bina itace take sanyaya min Raina gashi yanzu tana neman gur bacewa.”

Ta rushe da kuka Mai ratsa zuciya ta fice da sauri tana sharar kwallah.

“Rangida gaba daya kin daina jiyar dani dadi kin daina bani Ina dandana , rowa kawai kikeyi min why?

Tayi masa wani irin duba ta kwace daga rikon dayayi mata ta danyi tattaki zuwa gaban windo yabi mazaunanta da wani mayen kallon Yana lasan lebe abubuwa iri iri yake aiyanawa

Wallahi da ace bata haramta agareshiba kome za ayi sai ya aureta zaibi da ita ta yadda takeso muddin bazatayi mishi rowa ba

Ya tashi ya karasa gareta ya rungumota ta baya hannayensa akun tudun kirjinta wa danda suke aciccike

“nariga na Saba kin sangarta ni dayawa pls duk abinda kikeso zan baki.”

Ta ture hannayensa daga jikinta ta dauko siket tana kokarin zirawa.

“Nifa Allah nasoma gajiya,nace da Kai kabari in gama kawas da matsalar dake gabana in ba haduwa nayi da wannan Didat dinnan ba bazan Sami nutsuwa ba kawai ni ka kyaleni.”

Ya hadiyi wani katoton yawu yadi da sassauta murya.

“Nifa nafara gajiya da jin labarin wannan Didat din sai naji gaba daya na tsaneshi kamar mutuwa ta.”

“Sabida kana ganin shine zai kawo karshen alakar mu ko.”

“To bari kaji adamu nake so zanje na nemi soyayyar Didat ne sabida in Kara ginuwa Ina son na shahara Ina son duniya ta goga dani Ina son adama dani mayi suna kamarshi,na Kuma saukeshi daga kan wannan banzan halin nasa,zan to masa kwanciyar mage Mai daukar Rai dazaran na sami yadda nake so sai na koma na auri adamu kaga babu abinda zamu fasa kenan ko.”

Ya jinjina kai Yana murmushi.

“Good, na gamsu,zan tayaki nemansa kada ki damu zanyi da jikina da aljihuna.”

Acan cikin cikin dakin larai Mai aikinsu Nurat na kwance akan cinyar larai kuka takeyi sosai

“Nice da kaina nayi kyautar zuciyata bazan iya rayuwa babu Shiba kowa na gani gizo yakeyi min da kamanninsa,larai Ina ganin sauran kiris na haukace bansan haka so yake da zafi ba,yanzu bazan iya hakuri ba bazan cutar da kaina ba Ina sonsa Ina murukar sonsa ,ya dade Yana cewa Dani na bari shi zai fada da kansa,”

“Rayuwar sa data yayata ta banbanta shi din kamiline, nice da kaina na dauki wuka na daba ma kaina nayi wauta bansan haka abin yakeba.”

Ta mike zaune ta riko hannun larai

“Ki gaya min yazanyi Ina jin tsoron papana zai iyayin komi akan abinda nake neman aikatawa.”

“Always sarkakiya cikin wannan lamari bansan meye abinyi ba mahaifiyarki tafi kowa sanin ciwonki ita zata warware Miki komi kada ki boye mata ki sanar da ita kinji.”

Tayi saurin kada Kai.

“Ina jin kunyarta bazan iyaba bazata taba fahimtata ba.ke ce kadai nake neman shawararki,kinfi kowa Sona kinfisu sanin muhinmanci na sudin Aazeem kadai sukeso.”

Haj zainab dake labe ta cusa hannu abaki gudun kada sujiyo kukanta da sauri ta koma shashin ta cike da tsoron da Kuma tsananin tausayinsa Nurat,bataji dadin yadda ta fahimce suba akan me zata dinga ganin kamar Aazeem kadai sukeso hakika tayi musu bahagon fahimta,batasan cewar kaunarta da tarbiyar ta ne kadai ke zaune da ita agidan ba,batasan cewar gudun rushewar tarbiyar tane yasanya Taki barin gidan ba,yanzun yazatayi Dan ta tabbatar mata da cewar itace mafi soyuwa agareta.

darduma  Idanunta da kar take iya budesi sabida kumburin da su kayi har kawo Yanzu hawaye basu daina tsinkowa daga idanun ba

Amminsu ta shigo akusa da ita ta zauna ta kafe ta da ido cikin nazarin ta, ta numfasa

“A kullum na fi son farin cikinki fiye da komi, nice mahaifiyarki, aminiyar ki nafi kowa kaunarki, nasan ciwonki domin nice mahaifiyarki, da ace tin farko kin sanar dani da yanzu munyi maganin matsalar, gaya min shima yana sonki?

<< Kyautar Zuciya 25Kyautar Zuciya 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×