Wata iriyar kunyace ta lullubeta ta dukar da kanta kasa,haj zainab ta tallafo fuskarta.
“Ganin farko danayi mishi naji araina cewar dake ya dace.”
Nurat ta dubeta wani matsanancin kunya ya rufeta.
“Zan yi addu,a idan har kasancewar ki da shi akwai alheri ubangiji ya tabbatar “
Yana faman Kaikomo cikin tashin hankali yanayi yana duba agogo Kiran Salim ne ya shigo da Sauri ya ratsa kore ya kafa wayar a kunne.
“Har yanzu basu sakota ba?”
“Salim nakaraya ina Jin tsoro kada su cutar. min da iya.”
“domin su Sami kudi sukayi kidnapping dinta an kuma basu zata dawo da izinin Allah mukara musu lokacin.”
Wani kiranne ya shigo daga daya wayar tasa yayi saurin katse Kiran salim tare da daukan daya Wayan.
“Young billonions baka yi mana godiyar dawo mana da. mahaifiyar kaba.”
Cikin sarkewar murya da kagwuta.
“Yaushe, bata dawo ba har yanzu ita nake jira dan Allah kutaimaka min.”
Dariya ya dingayi masa haka Didat yaji zuciyarsa tamkar zata fashe.
“Kana son mamanka dayawa na dade banga irin kaba,tayuwu batasan inQda kanta yake bane,kadan dudduba bayan lambun gidanka kila kada ce kuma__
Bai tsaya Jin karashen maganar ba yayi cilli da wayar ya yo waje da gudu
Kwance yaganta tana faman numfarfashi kamar wadda ake Shirin fidda ranta gaba dayanta ya sunkuce ta tamkar wata jaririya cikin daren ya kira likita dan aduba lafiyar ta ,inda likita ya tabbatar da lafiyar ta kalau kawai tana cikin firgicine yayi treatment dinta sannan yayi mata allurar bacci
Zamayi yasata agaba cike da tsananin tausayi wani irin kaunar tane ke kara ratsashi waya ya dauka Kabir ya kira ya sanar dashi cewar tadawo inda Kabir ya nuna farin cikinsa sosai ya Kuma tabbatar masa da cewar gobe zai shigo kanon sannan ya koma ya kira Salim da duk abokan arzikin sa.
“Bazai yuwu adalilinka wani Abu ya sake samun taba bazan sake wannan ganganci ba,lada ya isa haka nima sai ka bari in Sami damar neman nawa albarkar ko Daman ninafi cancanta na riketa dan haka zan maida ta gidana.”
Yasani Kabir yafishi iko da ita bashi da damar da zai hanashi ita a wannan karon,sai dai Yana tinanin ta yadda zai iya rayuwa Babu umminsa.
“wai Kai Yaya Kabir wata iriyar magana kakeyi haka ne.”
“bana bukatar sake dogon zance,idan Kai baka fahimya ba shi ya gane dan haka bana bukatar sake maimaitawa.”
so yake kawai Didat ya sake magana inyaso ya amayo da abinda ke cikinsa dan haka yaci gaba da watso masa maganganu masu zafi .
Duk da yanajin zafi Amman bai iya maida martani ba koba komi ummi ta koyar dashi girmama nagaba.
“To ai sai kabari Idan ummin ta farka sai ta zabi da Wanda zata zauna,Salim yace dashi.
Kabir Yana faman huci.
“Kasani ko kuna so ko bakwa so dolene intafi da ita koda ita din bata amince ba ehe.”
yayi tattaki ya karasa inda ummin tasu ke kwance ya shiga tashinta ahankula ta bude ido.
Ahmad,Ahmad!
da sauri Didat yamatso kusa .
“Zasu kasheni.”
“No ummina yanzu kina tare damu ,Babu abinda zai sameki kinji.”
Wannan Abu ya Kona wa Kabir rai wato kam shi Didat ko yaushe shine kadai da sabida shi din mai kudina
Azafafe ya karasa gareta ya shiga kiciniyar dagora
“Tashi zakiyi mutafi nine dolenki Kuma kiyi hakuri da abinda nake dashi ,nima zanyi iya kokarina na baki irin cimar da yake baki har Kika zabeshi fiye da ni dinnan.”
Kwacewa tayi daga hannunsa.
“Mai kakeson cewa ne,wannan wani irin shashanci ne Wai shin Kai baka girma ne?
“ummi nima wannan karan Ina bukatarki Zaki taho tare dani inhar ba so kikeyi duniya ta zageni ba.”
“Ina son kashiga hankalinka kama daina ambato abinda ba zai taba yuwuwaba.”
Yakufula sosai.
“Sabida ni bamai kudi bane shiyasa kike guduna,Wai shin ke waca iriyar uwace?
“Ya Isa haka Kabir,ya Isa kasan abinda zaka dinga firta mata,kabita a hankula”.
Ya dan rankwafa Yana yi mata magana kasa,kasa.
“Ummi Kabir shine babba Ina son kibashi dama ko da sai dayane dan Allah kibishi kuje zuwa wani lokaci ba dadewa zakiyi ba kinji.”
haka yaci gaba da lallashinta har sai da yashawo kanta.
Da kansa yayi dreving dinsu zuwa airport sai da yaga tashinsu ya juyo cike da kewarta da Kuma godema Allah Wanda ya kubutar da ita
***. ***.
Abubuwa dayewa sun faru yayinda a koda yaushe Didat ke kokarin goge Nurat daga cikin zuciyar sa sai dai abin kamar tiri ko yaushe yana keeping din kansa bizy ko ya sami sa,ida Amman haka ya gagara yakan sanya hotunan ta agaba yayi kallo cike da kewarta
Yana zaune akan darduma da alkur,ani agabansa yana karantawa yaji kiranta batare da ya dubi wayar sa ba sabida ringing dinta ya banbanta dana kowa takira yafi sau akirga karshe sai ya kashe wayar baki daya.
Ya maida alkur,anin ma,ajiyarsa ya koma gado ya mike zuciyar sa nayi masa zafi
Yaja tsaki bazai iyaba ya dauki wayar ya kunna shogowar text yaji yayi saurin budewa.
“Allah yasa bawani abune ya faru da kaiba Ina jin tsoro,zan kasance mai nema maka sassauci agun ubangiji nasani haka kawai bazaka nisan ceni ba nasani kana mutukar kaunata,inayi maka fatan alkhairi.”
Kalamenta sun tsaye masa arai zuciyarsa ta raunana ,ya sauke ajiyar zuciya.
“Kiyi hakuri Nurat,burikan mu bazasu taba cikaba Ina sonki,Amman dolene nayi da kaina kafin ayi dani.”Yana kwance zuciyarsa nata faman tafarfasa yau da kansa yake bukatar hawaye a idanunsa yanajin hakan zaisa yasami saukin zugin da yakeji a zuciyarsa, idanunnan sunyi bala,in rinewa kansa nayi masa wani irin sarawa tamkar ana buga masa guduma.
yariga yagama saddakarwa karasowa ne kawai mutuwa batayi ba,amman daf take data zo gareshi domin daukarsa ,mikewa yayi ya nufi makasar fitila ya kashe gaba daya dakin yayi bakikirin ya koma ya kwanta Yana jiran tsammani wayar sace ta fara fidda haske alamar ana Kira Yama koma ya juyawa wayar baya har wayar ta katse wani Kiran ya sake shogowa itama tayi ta katse haka Kira ya dinga shigowa babu kwaikwaitawa ya ja tsaki ya Mika hannu ya dauko wayar da zummar kashewa Kiran Nurat ne ,wani irin tausayin sune ya kamashi akalla Shima yau yana son Jin muryarta Koda bazai ce komiba ya danna kore ya Kara a kunne.
Cikin murya irin ta wadda taci kuka ta gaji ta soma maga lokaci lokaci tana ajiyar zuciya.
“abinda ke cikin zuciyata nake sanar da Kai kasani karya ba al,adata bace yau zan gaya maka inajin ajikina bazan iya rayuwa Babu kaiba Mai yasa ka nunan soyayya alhalin naka son bai Kai zuciba,adamu Kaine ka koyar dani sonka idan ka juya min baya ___
Kuka ya kwace mata irin Mai sheshshekannan.
bantaba nunawa ummina Ina son wani abinba sabida banason daga mata hankali alhalin Bata da abinnan,sai gashi yau da kanta tagano yadda nake sonka,na Kuma amsa mata sonka bazai Bari na Musa mata ba
Tayi shuru tanata faman sheshsheka tamkar zuciyarta zata faso waje.
“Adamu kaine kuwa ,inata magana kayi shuru,ka kyaleni ashe daman Kai mayaudari ne,shikenan wannan kaddarata ce wannan itace tawa jarrabawar,kila da ace na juyama babana baya akan zaruk da nayi dana sani zan amince zan Aure shi nan da sati biyu zamu bar kasar gaba daya sai kayi farin ciki,amman kasani sonka halittace a cikin jikina,jinin jikina.”
da kansa yayi saurin katse wayar sabida yadda zuciyarsa ke barazanar tarwatsewa hawaye ne ke zubowa ta gefen idanunsa.
“Rayuwar aure na Babu ci gaba tunda na aureshi duhu kawai nake gani,na toshe kunnuwana daga kananan maganganun mutanen gari,duk haka bazaisa ya dagan kafaba, sai yayita azabtar dani,ga cikinsa ajikina ko kadan Bai taba nunan farin ciki da samun dana halaliba ai yakamata ya godema Allah da dan baizo a yadda shi din yazo ba,kuma—
Wani azabbaben Mari ya dauke ta dashi Yana faman huci kamar Zaki wani irin kallon tsana yakeyi watsa mata.
“tabbas yau na tsani kaina da na dage alalle sai abokina ya aureki ashe ke din jahila ce baki taba shiga makaranta ba,aboki bai taba sakar wa aboki mataba,amnan yau badan darajar wannan cikin dake jikinki ba wallahi da sai na sakeki Kuma wallahi sai kin saku.”
Yaja tsaki ya juya zai shiga shashin Didat da sauri ta Sha gabansa tana muzu rai.
“Kana wani abu tamkar aminin arziki alhalin Kai dinma sabida abin hannunsa kake zaune dashi ko ka dauka ban sani bane .”
ya Jinjina Kai kawai .
“dakikiya ke Babu abinda zaki gane.”
Ta koma dakinta ta dauko jaka da key din mota tayi waje tana kuka.
“bani da sauran farin ciki a wannan duniyar banason ka dinga yaudarata da wadannan kalamen,kanayi ne sabida kawas min da damuwata inason ka daina wahalar da kanka domin damuwa ce zatayi ajalina nasani karshena ya zo lokaci kawai nake jira dan haka dan Allah kaima kaje ka kyaleni.”
Zai yi magana Didat yayi saurin dakatar dashi.
dan girman Allah ka kyaleni kaje bana iya gane komi.”
Juyama sa baya yayi yadinga magana juyin duniyar nan Didat Bai iya sake cewa komi ba dole haka ya fice .
Dariya Kabir ya dinga tintsirawa Yana buga kafa akasa .
Ashe Zaki dawo hanya da kin kuskura haka kasuwa zata watse miki batare da kin Sami ribar komiba.dan nasani koba dade ko ba jima wallahi nasani sai wannan yaron ya sakeki domin ko ni nasan ba sonki yakeyi ba kema kinsan ba sonki yakeba jama,a sun shaida ba auren soyayya kukayi ba,amman ke kin kafe kin dage.”
“Yanzu na fahimci hakan dan haka na komo goyon bayanka ,Kuma ma banda abinka ai ko yau kasuwa tatashi dan koli yaci riba.”
Yayi saurin dubanta.
“ban fahimtaba .”
hannu tasa ta shafo cikinta .
“Haba da Allah .”
“Da gaske nakeyi sai dai gaba daya bai taba nunan farin cikin saba dan haka ko me zakayi ina tare da kai.”
Gaba daya suka sheke da dariya .
“To yanzu ta Ina zamu fara,kasani fa nice woman leader .”
“Hajiyata sai yadda kika tsara,kece ta hannun damana.”
“Amman fa yayan mu kayi farar dabara da ka fito da sunan sa,kilama hakanne yasa Bai bayyana kansa ba,shi da nemowa Kai da handamewa,salonka na yin kyau nawajena.”
“shi ba sai ya zauna ba,wai shi mummuni rai non ummin mune akwai ta da takure yaro gashinan ya dibo halaiyarta tsaf har ya fita tsentseni .”
Suka sake shekewa da dariya.
“Kasan me?
“Sai kin fada.”
“Abinfa ya tabashi,ya firgita sosai.”
“hauka nakeso yayi ,tuburan nake so yayi.”
“Ah haba my brother yaron da zai zo duniya shikuma yayi Yaya kenan.”
“oh kina son kice ni din ba ubansa bane.”
Suka sake shekewa da dariya.
Kampen yayi nisa ko Ina ka duba hotunan Kabir ne inda yake amfani da sunan Didat hakanne yasaka jama,a ta ko Ina suke barkowa duk tashar sadarwa da ta.yanar gizo hirar tsayawar takarar akeyi da Kuma dunbun magoya bayan da yake dashi kowa yasani Koda Bai kashe kudiba akwai tabbacin zai iya hayewa.
“Sunana Alhaji atiku tsohon minister na kudi,na neme Kane domin muyi wata muhimmiyar magana da Kai.”
yadda Didat ya dinga amsa masa tambayoyinsa hakan yayi mutukar birgeshi haka Kuma ya tsaye mishi arai yanajin kaunar sa har cikin zuciyarsa.
“Sai dai Kuma baka binciken ka ji tayaya nasan Kai ne Didat Wanda kake tamkar mutumin boye.”
Murmushi Didatyayi .
” bana bukatar hakan domin Babu abinda yake dorewa nasani duk daren dadewa sai na bayyana ga mutanen.”
“kada ma ka damu nidin ma na kashe kudina na sha wahala kafin nasan Kaine,sai dai fa shi wannan ya bayyana kansa a idon duniya da zummar cewar Kaine shi, Kuma kowa ya gamsu da hakan.”
Yayi murmushi mai ciwo.
“Abinda yayi ni shi yayishi,dan uwa nane kaga zai iyayin duk abinda yaso.”
“Amman Kuma ko atarihi bantaba Jin inda akayi hakan ba,dan haka Ina baka shawara ka fito ka karyatashi.”
“Bazai yuwuba nine na bashi damar yin haka.”
mikewa yayi .
“Zan wuce ranka ya dade nagode.”
kawai yabishi da kallo Bai taba ganin baudadden mutum irin Didat ba,komi nasa irin na ubansa halaiyarsa kamanninsa, ya sauke ajiyar zuciya
“Allah ka iya Mana dan isar annabi.”
Duk motsin Nurat idanun amminsu na Kai ako yaushe tana binta ne kawai da addu,a kullim idanunta na kan hanya danganin zuwan Didat sai dai Babu duriyarsa haka itama Aazeem tana kokarin kiransa layikansa a kashe hakan bai dametaba sosai sabida neman yanhar da zatayi taga Didat ya dauke mata hankali gobene akayi mata alkawarin za,a kaita gun Didat sabida gobenne zai shigo kanon dan haka take a dokamce.
Kwance a kan darduma ta kafe lambar Didat da ido hawaye ne keta faman tsinkowa daga idanun nata tana ta faman saka da warwara in tayi kamar zata kirashi sai ta fasa tasani Kiran bazaiyi amfanin komiba ta lura adamu Yana da tsatsatsaurar rayi bazata iyaba zata sake zuwa wannan gidan dataga Mai Kama dashi zata rokeshi ya kaita gun adamu tasani Yana da dangan taka da shi ta yi saurin mikewa kamar wadda aka mintsina ko hijab Bata cireba ta saci jiki ta bace batare da kowa ya gantaba.
Gidan bazai taba bace mataba har yanzu dai sojoji ne ke faman shawagi rike da bindigogi wasu mankyan treloli anata dibo kayan abinci daga cikin gidan ana durewa a cikin motar ta cigaba da tafiya da sanda tana faman labewa idan taga za,a ganta ahaka ta samo ta kutsa gidan girman gidan ya wuce tinanin ta wata hanya ta Mika Wanda Babu kowa ta gun.
Wani tangamemen setting room ta tsinci kanta aciki haduwarsa ya saka tayi mutukar rudewa tanajin kanta tamkar awata duniyar take,tasani ta taso agidan wadata Wanda duk wani kayan kyale kyale akwaisu aciki Kuma tazaga gidajen da akafi nasu iko,sai dai bataga kamar wannan ba tsarin gun da tsadaddun kayan gun sun wuce tunaninta anya kuwa wannan acikin duniyar nan take tasani takawo kanta mahallaka jikinta ne ya soma rawa tarude karshen rudewa motsin tohowa taji can sai taji an tsaya ta kamkame jiki hadi da rintse idanunta can ta daina Jin motsin ta fito daga maboyar ta da zummar ta bar gidan cikin sanda take tafiya wani kare tagani irin na turai dinnan jikinsa buzu buzu da gashi Yana nufota da gudu ta fice ai kuwa karen yarufa mata baya ta dinga kitsawa lungu da sako na gidan,ta sake fadawa want shashen da tafi wancan tsaruwa still Karen Bai daina bintaba sai ma ya koma haushi Ina ta cire takalmanta ta watsar ta koma gudu tamkar ranta zai fita jitayi ta kamkame wani abu idanunta a rintse Kam
Didat ne yayi mutuwar tsaye jin kome yakeyi tamkar a mafarki sai Kara shige masa takeyi tana kara kamkameshi sun dade ahaka yakasayin kwakwkwaran motsi daga bisani ya banbare ta daga jikinsa ahankali ya kafe ta da manyan idanunsa yana kallon inda ta rintsesu hawaye nata tsinkowa,yau ne yakara ganin tsagwaron kyau gashi har gadon baya kananan kaya ta saka ta dora katon hijabi akai ga hijabin yayi nasa waje daga ita sai kananan kayan rigane Mai yankakkan hannu sai wando Jen’s wanda yayi bala,in fito mata da duk wata halitta ta jikinta,kyawunta Mai sanyi ko in ce wani irin kyawu Nurat ta hada komi shurun dataji yayi yewa ne yasaka ta bude idanunta a hankali idanunsu suka gwuraya ,tana ganin komi tamkar amafarki sabida tasan wannan din bazai taba zama adamu ba dan haka ta maida Kai ta kwantar a kirjinsa hadida sake kamkameshi ta jita cikin wani yanayin da bata taba jinta aciki ba, wani shauki da bazai iya kwatantuwa ba ,shima yayi bala,in shagala dan shimadin jinsa yakeyi tamkar a mafarki baisan sa arda ya dauketa cak ba ya kwantar akan kujera dan mitsitsin bakinta ya nufa sa,annan ya luma hannayenta cikin lallausar gashinta wanda famkar dakin keta faman watsi dasu.
“Adamu ba zan iya rayuwa babu kai ba,na sani mafarki nake yi Ina fatan na dauwama da kai cikin wannan mafarki Allah kada ka farkar dani.”