Skip to content
Part 28 of 31 in the Series Kyautar Zuciya by Bilkisu H. Muhammad

Karensa ya hango hakanne ya tabbatar masa da ba mafarki yakeyi ba, arude ya mike cikin tsananin faduwar gaba da wata matsanan ciyar kunya ya yi saurin matsawa ga mamakinsa bacci yaga tanayi ya sauke ajiyar zuciya bed room dinsa ya koma ya shiga Kai koma mamaki da tsoro sun kasa barinsa shin Mai yaso aikatawa,mai ke damunsa ,kadafa sonsa ya watsar mata da rayuwa yaja tsaki bazai taba barin hakan ta faruba ya dubi agogo karfe takwas da rabi na dare ras gabansa ya sake bugawa yasani kawo yanzu iyayenta suna can suna nemanta fitowa yayi yana neman hijab dinta acan harabar gidan yagani ya komo inda take har yanzu bata farkaba ya zauna a gefenta cikin kura mata ido yasani wannan abin da ya faru tana dauka cewar a mafarkine ,abin zai tafi a haka,amman yanzu Yaya zai yi da ita .

acan cikin bed room dinsa yake waya da salim ya shaida masa duk abinda ya faru.

” Jina nakeyi kamar na bar kasar da ita banajin zan barta ta koma,da gaskene nasake jin labarin cewar zasu bar garin da wannan zaruk din,Ina da komi bazan bari wani abin yafi karfi naba daga baya zan shaida musu cewar nine Didat._

“Kada ka mance ka siyarda wannan sunan ga dan uwanka mai neman takarar gwamna Kuma kowa yanzu ya yadda shidinne dan haka baka da wannan damar ,Kuma ni bana tare da Kai acikin wannan shirmen naka,kawai abu daya zakayi sabida ita ka fito ka nunawa duniya cewar Kaine Didat wannan ne kawai mafita .”

Zai yi magana Salim ya katse wayar ya dinga sintiri a dakin ya hada wani uban gumi kawai mafita yake nema.

“bazan iya tozarta yaya kabir ba kodan darajar ummina,nasani ummina na mutukar kaunar danta ta danne sonne sabida ni ta zabi ta rayu dani dan ta zamo kariya agareni .”

“Amman zan kwato soyayyata ta wata hanyar bata wannan ba Salim,na hakura da wannan sunan.”

Ya fito adakin ta baya yabi inda bazata ganshiba daya daga cikin amintattun gidan ya samo ya karanto masa duk abinda yake bukata akan Nurat ya sake komawa tanata mutsu mutsu alamar zata farka wuf ya fada bedroom yana iya hangota ta kofar glas din dakin Wanda ita bazata taba iya ganin saba yana kallo ta mike zaune.

duban ko Ina takeyi kamar wata zararriya da gudu ta dauki hajab dinta ta yafa addu,ar neman tsari takeyi arude yana iya jinta gaba daya tausayinta yakeji daidai lokacin amintaccen yaron sa ya kutso setting room din.

“Baiwar Allah lafiya daga Ina wa kike nema tayaya kika iya shigowa Nan.?

duk ya watsa mata wadannan tambayoyin alokaci guda duk tagama dabarbarcewa.

“ke nake sauraro.”

Muryarta na rawa ta soma magana.

“ina neman Ahmad Didat ne.”

“to Amman da izinin wa Kika shigo,Kuma waye yace miki muna da Ahmad Didat a gidannan?

“Ina da tabbacin haka dan Allah ka taimaka min Ina son magana dashi,dan Allah takara sa maganar cikin muryar kuka.”

ayadda take maganar ta yi mutukar bashi tausayi.

“Kiyi hakuri baya gari Kuma bazai dawo nan kusaba.”

“zan jirashi zan jira ko yaushe zai dawo zan jira.”

yayi bala,in sassauta murya.

“gaba daya baya kasar Amman nayi Miki alkawarin muddin yadawo zan sanar dake yanzu kibani number wayarki kinji.”

ta dinga jinjina kai,.

“Babu inda zan tafi.”

“to shikenan,Amman dai kinsani kin karya doka ko,Kuma idan nakira security zasu iyayin komai sabida kin shigo ta barauniyar hanya alhalin bamusan wacece keba.”

duk wannan barazanar da yayi hakan Bai tsoratata ba tamkar ma tirata akeyi da gaske har zuciyar ta tanaji komai zai faru sai taga wannan Didat din.

Komawa tayi ta zauna,Didat dake tsaye tin lokacin da suka fara jayayya da amintaccen nasa Bai bar gunba asalima shine yayi masa nunin daya kyaleta yanzu kam bashi da zabin daya wuce ya bayyana agareta.

tana zaune ta hada Kai da gwiwa taji antsaya a kanta kamshin turaren adamu taji ras gabanta ya buga da sauri ta dago Kai hadi da mikewa tsaye.

dukkanin su sun kasa magana sai shine daga karshe ya numfasa.

“Kece wadda akace kina nemana,gaya min lafiya kuwa.?

yasani ana cewa wane na kama da wane Amman ba,a kama sak,to wannan sak ne sai dai kudi daya banbantasu to amman takasa amincewa da bashine adamu ba, wannan adamune ko dai sonda takeyi masa ne yasanya komi yake rikide mata ya koma shi.

“Adamu!

“Sunana Didat ba adamu ba,kina bukatar taimako ne,gaya min dan Ina sauri ne kada jirgin mu ya tashi.”

binshi kawai take da kallo bakinta na motsawa sai dai ta kasa furta komi,hatta muryarsu babu banbanci.

dafe kai tayi wani irin juyawa kanta keyi tanaji a ranta tagama haukacewa.luuu tayi zata Fadi yayi sauri zai tarota Ina tariga tayi kasa goshinta na fidda jini sabida bigewa da tayi da tebur

yajanyota jikinshi baki daya Yana jijjigata.

“Nurat!!Nurat ki bude ido nine sunana Didat,sunana adamu kinji kitashi Nurat pls ki bude idanunki,nima bazan iya rayuwa batare dake ba kinji .”

Ahankali ta ware idanunta a kan fuskarsa yadda ta ganta ne lakadan kwance a cinyar sa yasa ta mike a zabure.

ga jini na gangarowa kan fuskarta bata son hada ido dashi duk da cewar bataji sun batun da yakeyi ba lokacinda ta fita a haiyacinta neman hanyar fita take.

“zan kaiki gun adamu kada kitafi kinji.”

ta tsaya tsam takasa motsawa yayi tattaki ya Sha gabanta ta kasa hada idanu dashi ya Kai hannu kamar zai goge mata jinin dake fita a goshinta irin firgicin datake cikine yasashi kasa aikata hakan hankicif ya dauko daga cikin aljihu ya Mika mata ta karba ta goge.

“Mai yasa kike neman dan uwana,Allah yasa ba laifi yayi ba.”

ta dan dago Kai ta dubeshi idanunsu suka gwuraya da sauri ta sake dauke Kai.

“Kinyi shuru ko baki damu da son ganin saba.”

“Idan kina so ki zauna muyi magana kinji.”

Babu musu ta nemi gu ta zauna gaba daya ta takure gu daya tana kallo ya shiga ciki sai ga shi yadawo rike da wani  cup da soft drink akan plete ya ajiye agabanta ya koma ya zauna.

“Ina jinki .”

Ta soma magana.

“nashiga rudu inajina kamar na haukace kila nice kadai nake ganin haka.”

“Mai kike gani.?

“Komi naku iri daya kamannin ku muryarku,dan Allah Ina son tambayarka akwai wanda yataba cewa da Kai kana kama da wani?

“ban taba cinkaro da Wanda ya ce hakaba sai dai ke to shi din waye dinki.?

bata iya bashi amsaba ya sake maimaita maganar nan ma shuru.

Yayi murmushi.

“To ko dai masoyinki ne?

ta sake dukar da Kai tana wasa da yatsunta.

wannan kunyar tata shiyafi kauna fiye da komi yanajin zuciyarsa na kara haukacewa da sonta ya dan yi murmushi.

“Ok to shikenan tunda shi wancan ya gujeki kilama yaudararki yazo yayi yanzu ni gani Ina sonki,kilama yaudararki yazo yayi yanzu ni gani Ina sonki,ba kince kamarmu daya ba,nasani sai nafi baki kulawa Kuma Zaki fi Sona sabida Ina da komi na mallaki komi Zaki soni?

gabanta yashiga dukan uku,uku tayi saurin mikewa ta yadda ba kama sukeyi da adamu ba ,kawai son da takeyi masa ne yasanya kowa keyi mata gizo.

“Ina Kuma zakije kina son kice baki amince dani ba.*

“Kayi hakuri nayi kuskuren shigowa gidanka dan Allah zan tafi.”

Shima ya mike.

“To ya batun soyayyar mu?

“kayi hakuri.

Ta yi saurin barin shashin sai dai me ko Ina yayi baki Kirin duka fitilun gidan a kashe ga karnika nata faman haushi da sauri ta komo ciki Yana nan inda ta barshi.

“ya akayi kin sake shawara ne?

“Dan Allah Ina Jin tsoro nakasa gane hanya Ina son ka sa a nuna min hanya.

batayi aune ba kawai sai taji caraf ya danko hannunta kam ta Sami damar yin magana ya soma Jan hannunta sabida tsananin rudewa kukanma ta kasayi kawai binshi take duk inda yajata suna ta keta duhu kam ta dantse idanunta tana ta faman Jan duk addu,ar da yazo bakinta.

jitayi sun tsaya a wani guri lokaci daya gidan ya kaure da haske a harabar da ake ajiye motaci ta ganta motocine birjik agurin ya bude daya daga ciki da kansa ya sakata aciki.

“Naga ke yarinya ce bazaki isheni ba Kuma gaki da kyau wannan Karan kin tsira Amman muddin Kika Kara tako min gida saina bata Miki rayuwa bazan kyalekiba wancan Karan naji ance kinzo yanzuma gashi kin sake zuwa idan Kika Kara bazan sake bari kikoma gidan kuba anan zanyita ajiyeki bani da kirki Kuma ni bani da wani wanda nake kama dashi ni kadai ne .”

ya rufe kofar motar da karfi har sai da ta firgita  kawai jitayi an figi motar batare da sanin lokacin da drive ya shigaba ai kuwa ta fashe dawani kuka Mai karfi sauri sauri Didat ya bargun yanajin zuciyarsa tamkar zata faso kirjinsa.  ___________

Tabbas yanzune ya tabbatar ya cika mutum mai cikakken yanci tabbas da Ashe baisan duniya ba yanzu yashiga cikin Yan siyasa Yana gogaiya da masu kudi yasake sabobbin abokai ayanzu idan ya sanka a baya in kuka yadu nunawa yakeyi tamkar Bai taba ganin kaba sai dai in dama can Mai kwandala ne Kai yan mata kuwa binshi sukeyi tamkar kiyashi abinka da mayen mata rayuwarsa ta koma sabuwakal,har ya saki matarsa Wai sabida bata wayeba dabi,un da bashi dasu ada duk ya ara ya yafa baya ganin darajar kowa.

Tana zaune akan darduma duk tafita a haiyacinta tayi baki ta rame kullim addu,a takeyi Akan Allah ya kubutar da ita yanzu ta soma tamtama akan shidin jinin tane kuwa ,sabida ko a tatsuniya bata taba Jin inda akace wani yayi garkuwa da mahaifiyarsa ba,yau inbadaban tsoron ubangijin taba da,da kanta zata sanya masa guba cikin abinci yaci ya mutu inyaso itama akasheta

addu,ar data Saba yima Didat shi takeyi hannunta a sama tana kuka daidai nan kabir ya kutso kai zaman dirshan yayi agabanta cikin daure fuska

“Inda bakyajin cewar kece Kika haifeni,nima bana Jin cewar kece mahaifiyata Kuma shi Didat din sai na batar dashi,sai na haukatar dashi.”

“Albarkata tana tare dashi Babu wani dan Adam din da zai cutar min dashi.”

Ya kyalkyale da dariya Yana buga kafa a kasa.

“Mamana kenan bakisan cewar shege baya Jin addup,a ba.”

ya sake titsirewa da dariya

“Kuma bara kiji nabila tana tare dani kinga kuwa yaga ma shigowa hannuna.

hand set din sace ta dau ruri ya latsa Kore hadi da karawa a kunne.

“Bakuwar ta iso fa”

“Ok to Ina zuwa.

ya mike ko bi takan umman tasu Bai karayiba.

“Ya ubangiji idan yaronnan Mai shiryuwa ne ka shirya min shi.

Ta mike ta shiga zaga ko Ina na gidan dukka ko Ina a kulle .ta koma ta zube a kasa tana kuka.

Gaba daya tagama zayya ne masa tsohon lokacinda ta Kai tana nemansa,tare da gaya masa yadda ya birgeta yaji dadin hakan sosai ajinta da gayunta shiyafi komai dauke mishi hankali ga kuma wayewa blata da kunya kokadan abinda yafi bukata kenan a dare daya sun gama sanin junansu tare da gamsar da juna

Sai dai acan karkashin zuciyarta tayi malejine kawai

dan sunansa sai dai ko kadan bayyi mata ba jinsa yafi ganinsa kwana dayan Kuma datayi dashi taga halaiyarsa sun banbanta da yadda takeji ana fade

Yana kwance a kan gado Yana faman zukar sigari Aazeem ta fito daga bathroom daga ita sai dan pant ko bra babu ta zauna a gefensa tana shafa Mai kur ya kafeta da ido yanaji aransa bazai bari wannan damar ta wuce Shiba irin ta yakeso yatsani mace mai kunya ya mike ya zagaya ta baya ya rungumo ta

“Jiya na fara ganinki amman jinakeyi tamkar mun shekara da ke .”

“In tambayeki mana.”

Ta Kai hannu tana zagaye bakinsa da dan yatsanta.

“Kai nake sauraro yallabai.”

“Zaki aure ni?

“Why not,zanyi farin ciki da haka sosai.”

“Ina mutukar kaunar ki .”

Kanka kasani amman ai nagaya maka na dade da Kai a raina,ko yanzu a Shirye nake da ka zamto nawa.”

“Kin tabbata.

Ta jinjina kai.

Lokaci daya suka kacame.

So kukeyi ku haifar min da wani ciwo ,Kaico ni kam banyi dace ba ku biyu kawai na mallaka a wannan duniyar yayarki ta tashi a watse kece kawai idan na tuna nake jin sanyi abbanku ya bata min  tarbiyar yayarki gashi kema kina son biye musu tafiya zanyi ni yanzu Babu abinda ya rage min zanyi nesa da ku domin nasani kazantar da baka ganiba tsabtace

Ta cigaba da share kwallar fuskartar tana hada kayanta.

Nurat kuka take sosai cike da dana sani.

“Ammina nayi Miki alkawarin bazan sake ba na tuba”

“ai nagaya miki muddin baki sanar dani inda Kika jeba wallahi sai na bar muku gida.”

tashiga kokarin karbe akwatun hannun amminsu

“Zan gaya miki nayi alkawari bazanyi miki karyaba.”

Ta koma ta zauna alamar ita take sauraro.

bata iya karyaba dan haka bazata iya boye mata komi ba,acan karkashin zuciyarta ta yi kamar ta saka ihu  tsoro takeji kada tarihi ya maimaita kansa ta razana  mosifar tashin hankalin data shiga yafi na halin da Aazeem ke ciki sai dai barnar da so  ke haifarwa yafi kowanne ban mamaki,don so na iya juya mummuni ya koma  tamkar ba Shiba so na lalata rayuwa muddin Allah Bai tseratar da mutum ba tayi mutukar tausaya mata don shekarunta sunyi kadan ace tashiga wannan yanayi ta Yaya zata iya sarrafa kanta sai dai azahiri daure fuska tayi

tana daga zaune a bakin gado ta zube kasa ta rushe da wani irin Kika.

“ammina nice yau nasakaki kuka,bazan yafema kaina ba,ammi kiyi shuru hawayenki agareni mosifa ne indai nice daga yau angama bazan sake ba zan mance da adamu daga yau yazamo tarihi nayi Miki alkawarin hakan.”

Rufa mata baya tayi tare da rike hannayenta itama kuka take sosai tamkar ranta zai fita tilas ammi ta sassauta.

“Kiyi min alkawarin cewar bazaki sake zuwa ba,kiyi min alkawarin Zaki mance da adamu Ki yi hakuri da zaruk

“ammi nayi mikii alkwari nayi miki,bazan sake ba.”

“nasani bakya ha,intata,ki kwantar da hankalinki ki mikawa Allah lamuranki shine zai iya idan ya kaddara ke din matar sace kina zaune komi zaiyi daidai kinji.”

Nurat ta dinga jinjina kai, cike da tsoro tayima ammi alkawarin mancewa da adamu gashi tanajin wani sonsa na dada jisgarta .

*****

“Ke! Ke! tsaya mana bakya ganine ji yadda kika fallatso mata ruwan cabi.”

yadda jama,a sukayi mata ca dole tayi parking ta fito a motar wata mata tagani wadda zasu iyayin sa anni da ita gaba daya tagama wanketa da cabi gaba daya jama,ar gun sun har zuka kamar suna jiran kiris abinka da ba garin kuba tagama tsorata sosai matashoyar data wanke da ruwan cabi ta lura da yadda Aazeem ta rudene yasa ta saurin sakin fuska .

“hajjaju ashema kece Kika yi min ado haka,aikuwa sai kin kaini har gida.”

Ta danyi mata alama da ido , Aazeem ta fahimci abinda take nufi.

“Nagode ma Allah Ashe kece ok shigo mutafi.”

Masu fushi da fushin wani suka soma watsewa yayinda matar ta shiga mota suka hau kolta.

<< Kyautar Zuciya 27Kyautar Zuciya 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×