Skip to content
Part 3 of 10 in the Series Kyautar Zuciya by Bilkisu h muhd

“Nurat ina son dora girki”.

Cikin tausayawa, “Haba ta ya ya za ki iya wani girki? Ki bari ni zan yi kokari in ga na yi”.

“A’a Nurat, ki rufa min asiri”.

“Kada ki damu babu wanda zai fahimci haka. Ina zuwa… amma dai akwai duk abin da zan bukata ko?”

Ladidi ta jinjina kai.

“Ok, yanzu ki kwanta ki huta kafin ki tashi na gama kin ji”.

“Na gode Nurat”.

Ta bi Nurat da kallo tana jin kaunarta a ranta. Halayyarta daban da na iyayenta, kamar yadda ta lura kowa na gidan bai damu da damuwar wani ba, sun dauki rayuwarsu tamkar na turawa, musamman Aazeen wadda duka dabi’unta irin na ubanta ne. Ita kam Hajiya Rahma babu wanda ya fahimci inda ta sa gaba, ba za a dai a kira ta mara kirki ba, kodayake ba lallai a fahimci wace ita ba, saboda ba ta cika shiga shirgin mutane ba, sabanin Nurat wadda ba ta wuce shekaru sha bakwai ba, yarinya mai mutumci da shiga rai, wadda ba ta dauki kanta da zafi ba, ba ta da wahalar sha’ani, kunyarta shi ke kara mata daraja a idanun jama’a, don hakan ya zame mata tamkar wani ado.

Tazarar da ke tsakanin kicin da dakunan da ke gidan ya sanya babu wanda ya lura da kai-komonta. Wanke-wanke ta fara yi, ta ci uwar damara. Bayan ta gama ta shiga dogon tunanin abin da za ta dafa wanda ba zai ba ta wahala ba. taliya ta ayyana a ranta, amma ta ya ya za ta sarrafa kayan miya? Ita ba ta taba kwatanta shiga kicin don sarrafa wani girki ba.

Komawa ta yi dakin Ladidi, don ta gaya mata yadda za ta yi. Bacci ta ke yi lakadan, har da su minshari. Murmushi ta yi ta koma ta shiga tunanin yadda za ta yi. Tunawa ta yi da tana da littafin girki, da sauri ta nufi ma’ajiyar littattafanta. KADARAR KITCHEN wanda Bilkisu Salisu Funtua ta rubuta ta nemi guri ta zauna, tare da dubo abin da ta ke son dafawa. Ta mayar da littafin ma’ajiyarsa, ta koma kicin ta debo kayan miya ta wanke, ta soma yanka albasa.

Ji ta yi wuka ta shige hannunta, ta kwalla kara tare da sakin wukar yadda ta ga jini na zuba ne ya sanya ta rudewa.

A sukwane Zaruk ya dano kicin din ya kai hannu zai riko hannunta. Da sauri ta maida hannun baya cikin tsananin tsoro.

“Ki bari in gani, ba ki ga jini ne ke zuba ba?”

Ta yi saurin maida hawayen da ke kokarin silalo mata.

“Kada ka damu, kawai jinin ne, amma ai babu zafi”.

“Oh God! Wai ke me ma ya kawo ki kicin? Wa ya aike ki?”

Ta fara in’ina, ya daure fuska.

“Na ce da ke waye ya aiko ki kicin?”

Za ta yi magana ya mike a fusace zai fita.

“Don Allah ka yi hakuri, zan gaya maka. Ka dawo don Allah Yaya Zaruk”.

Ya koma ya zauna cikin kafe ta da idanunshi.

“Ke nake ji”.

“Ladidi ba ta da lafiya shi ne nake taya ta”.

Ya sake daure fuska.

“Ita din ce ta ce ki taya ta?”

Cikin rawar murya, “A’a, ta gaya min”.

Dole ta zabi ta ba shi labarin yadda abin ya faru. Ya ja tsaki ya janyo mata kujera.

“Maza zauna”.

Ba ta da zabi dole ta bi umarninsa. Komawa ta yi ta zauna, nade hannun rigarsa ya yi ya shiga aiki tukuru. Ta dinga kunshe dariya a ciki, ga mamakinta Zaruk ya iya komi.

Ya dube ta a sakarce, “Nurat, fito ki yi dariyarki a bayyane”.

Ta dabarbarce, “Da gaske Yaya Zaruk ba dariya nake yi ba”.

Jalof din taliya ya yi, sai plaintain da ya soya farfesun kifi. Ya diba a cokali ya mika mata. Ya yi mata alama da ta yi testing.

Ta karba tana dandanawa. Ya kafe ta da ido.

“Ya ki ka ji?”

“Yaya Zaruk, ashe ka iya girki?”

Ya harare ta, “Uanzu je ki yi maza ki shirya dinning ko?”

“An gama Yayana”.

Da sauri ta yi abin da ya ce. Bayan ta gama shirya komai ya ce da ita, zai je ya siya ma Ladidi magani. Yana fita ta shiga wanka.

Zaruk ta hango da Hajiya Rahma zaune suna cin abinci, ta sakar masa murmushi. Karasawa ta yi ta zauna. Ba a jima ba Alhaji Usman suka shigo da Aazeen rike da ledoji a hannu, su ma joining suka yi zmaan cin abincin.

“Yau Rangida babu korafi, da alama abincin ya yi dadi”.

Nurat ta dubi Zaruk ya sakar mata murmushi.

“No Dad, kawai dai ina jin yunwa ne”.

“Da ma ai ke ba a taba iya miki”. Hajiya Rahma ta ce da ita.

“Ladidi ta cancanci tukwici kenan?” In ji Zaruk yana kallon Nurat, ya faki idonsu a hankali ya dinga motsa baki yana nufin zai fada.

Ta yi saurin kada kai tana rokonsa. Mikewa ya yi tsaye.

“Ni zan wuce Ammi, a yi wa kuku godiya sosai”. Ya fada yana murmushi.

ABUJA

“Ummi ya kamata ki saba, na yi tafiya zuwa kasashen waje bila’adadin, na zaga duniya komai bai same ni ba, nan zuwa Kano tafiyar mintina ne, da zarar jirginmu ya sauka shi kenan an wuce gurin. Ko kina tsoro ne kada jirgi ya fado da dan lelenki?”

Deedat ya fada yana kokarin tallafo kuncinta da hannayensa biyu. Ta sauke ajiyar zuciya cikin damuwa.

“Ba haka ba ne, kawai dai ina tsintar kaina cikin rudu duk lokacin da ka ambata cewar za ka Kano. Bana samun nutsuwa, ban san me ya sa haka ba”.

Ya yi murmushi cikin kokarin kwarara mata gwiwa.

“No, Ummina kada ki mance kirarina, in ka san ni ni ne, in ba ka sani ba, ba ni ba ne. Ba ni ba ne Ummina. Kowa ya san ba ni ba ne, kin ji sam ba ni ba ne babu wanda ya san ni, kuma ma ban da ke da abinki addu’arki fa na tare da ni, ba zan mutu ta hanyar da ki ke tunani ba, a kan gadonki zan mutu, a kan kafafunki, yanzu ki yi min addu’a zan tafi kwana bakwai kacal zan yi ai kamar yau ne ko Tawan?”

Ta dinga murmushi a gefe daya kuma idanunta na fidda kwalla ta shafa sumarsa.

“Ka kula da kanka yarona, Allah ya yi maka albarka”.

Gaba daya suka dunguma har zuwa get inda ya shiga mota zuwa airport,  ba ta bar get din ba har sai da motar ta bace ma ganinta, ta juyo gida cike da kewarsa.

Hango shi ta yi zaune ya dora kafa daya kan daya yana kada su. Gabanta ne ya yi wani irin bugawa, ta shiga maimaita innalillahi…

Ya mike ya karo gabanta yana tintsira dariya.

“Ya yi babar mai kudi, babar Richman da kyau”.

Ya sake tintsirewa da dariya.

“Da alama kina cike da kewarsa, kina tsoron kada ya mutu ko? To ai da saura, domin har yanzu ba wanda ya san shi ne da zarar an fahimci waye shi ina tabbatar miki ko awa daya ba zai kara ba, ni ne kuma zan tona masa asiri, ni din nan ni ne ajalinsa. Yanzu ki shiga ki debo min rabona in tafi, na sani ke ma saboda wannan din ki ke nuna mishi cewar kin fi kowa kaunar…”

Kyakkyawan marin da ta wanke shi da shi ne ya sanya shi kasa karasa maganarsa. Daki ta shiga, sai ga ta da bandir din ‘yan dubu-dubu guda biyu.

Cikin muryar kuka ta soma magana, “Bana son ka kara minti daya a gidan nan, ka bace min da gani”.

Ya karbi kudin ya cilla su sama ya cabe, ya sumbaci kudin.

“Kin fanshi danki, sai gani na biyu”.

Durkushewa ta yi ta dora kai a kujera, ta rushe da wani irin kuka.

KANO

Gida ne madaidaici ba za a kira shi na masu kudi ba, daga waje gidan bai wani hadu ba, a cikin gidan duniyar ta ke, don duk wani abin more rayuwa an tanade shi a ciki. Mutane biyu ne ke kula da gidan wadanda suke amintattunsa ne, su ne ke kula da komai na gidan.

Tunda ya shigo Kano bai iso gidan ba sai da ya je ya gama duk wasu harkokinsa, sannan ya nufi gidan. A harabar gidan ya yi parking. Idris ya yi saurin karasowa ya bude masa murfin motar cikin yi mishi sannu da zuwa.

“Ya na ganka kai daya? Ina Adamu?”

“Ya fita karbo wa Madam take away”.

“Madan? Wacce?”

“Nabila”.

“Nabila kuma, yaushe ta zo?”

“Tun dazu”.

Nan da nan yanayinshi ya sauya, bai sake bi ta kan Idris ba ya yi gaba.

Ya yi arba da ita ta fito daga wanka daure da tawul. Ya yi saurin kawar da kai. Ya sake tamke fuska.

“Ke ba kya jin kunyar abin da ki ke aikatawa ko?”

Ta yi dariya, “Saboda na ganka in fita da gudu in dauko hijabi in yaba ko ya ya Deedat? To ma me zan boye maka? Ka yi min wanka, ka sanya min kaya, Yayana mijina. To me ya rage?”

“Wannan abubuwan duk sun faru ne lokacin da kina karama, yanzu kin girma, ya kamata ki kiyaye”.

Ya shige bed room.

Ta yatsina fuska, “Karamin abu kana son maida shi babba”.

Yana zaune a kan gado da laptop a gabansa yana tura wa abokan kasuwancinsa sako ta mailing dinsa. Ta shigo sanye da wasu fitinannun kaya, sai faman karairaya ta ke. Ta zauna a kusa da shi.

“Na tsorata da rashin dawowarka, har na soma tunanin yadda zan iya kwana a gidan nan ni kadai”.

Ya rufe laptop dinsa ya kallo ta.

“Wannan ya zamo zuwanki na farko da na karshe a gidan nan, muddin ki ka kara tako kafarki gidan nan wallahi sai kin yi da na sanin zuwanki. Kuma yanzun nan ki shirya na kai ki gidan Salim, gobe ki wuce gida”.

Kuka ta saka masa.

“Yanzu saboda na zo ne duk ka ke gaya min ba dadi? Mene ne laifina? Sati na biyu ban sanya ka a idona ba, na dawo gida a dokance a ka ce ka taho, ba zan iya kwana guda ba tare da na ganka ba shi ya saka na biyo ka, kuma ai Mom ta san da zuwana, kowa ya san gurinka na taho”.

“Okey su su Mom sun san gaskiya suka take? Ina ganin hakan bai dace ba”.

“Ai su ma sun san abin da ya dace, amincewa da kai da suka yi ne ya sanya su barina na taho”.

“Idan sun amince min ke kuma fa? Shin ba su san ke din fitinanniya ba ce?”

“Yaya Deedat ka san abin da ka ke cewa kuwa?”

Mikewa ya yi zai fita, ta yi saurin shan gabansa.

“Ko ma me ce ce ni ai mijina na yi mawa, aure ne kawai ba a daura ba, akwai baikonka a kaina. A wata ruwayar ma tamkar ka aure ni ne…”

“Shi ya sa ki ke ta bibiya ta? Ai don an yi baiko bai zamo lallai a ce ni din ne mijinki ba”.

“Hakan ba zai taba yiwuwa ba. Allah ma ba zai sa haka ba, na sani ina da rayuwa mai tsawo a gaba inda ba kai ne mijina ba, ba zan yi tsawon rai ba. Don kai Allah ya halicce ni, dole ne sai mun yi aure”.

Ta kuma sanyaya murya.

“Ka gaya min me ya sa ba ka damu da ni ba? duk lokacin da na yi maka maganar aure, sai ka nemi kashe min jiki. Zancenka kullum ba ya wuce aure nufin Allah ne, aure lokaci ne. ta bangaren iyaye ma kuwa cewa ka ke yi a kara maka lokaci, me ya sa ba ka jin tausayina? Me ye laifina? Ina son ka sani rayuwata ta ginu ne da soyayyarka, ban san me ake nufi da soyayya ba sai a dalilinka. Kai ne nutsuwa ta, idan ba ka son na ci gaba da bibiyarka ka amince a daura aure ko da ba a tare ba, zan iya jiranka zuwa duk lokacin da za ka gama shirinka”.

“Dadina da ke ba kya rabo da shirme. Kin cika shirme. Ba ni da lokacin tsayawa jin wannan maganganun naki, ni ban san me ye so ba, bana son kuma na sanshi. Zan yi aure kawai don cika umarnin Allah da Manzonmu. Ke ma haka nake so ki saka a ranki, sai ki samu sassauci a ranki. Kada ki kara yi min wani zancen so, don ba burge ni za ki yi ba, maimakon haka ma sai matsala da za ki kara ma kanki”.

Kokarin barin gurin yake yi, da sauri ta rike shi kamkam da karfin da bai san tana da shi ba.

“Nabila, me ki ke nufi da hakan?” Ya fada cikin kausasshiyar murya.

“Yaya Deedat, ni mace ce mai tsananin bukata, na kai kololuwa. Idan ba ka bari an yi auren nan ba, zan iya aikata komai. Ka tausaya min don Allah”.

Da karfi ya watsar da ita gefe ta zube a kan carpet, tana faman maida numfashi.

“Yaya Deedat karya ka ke yi, burga ka ke yi. Na sani kai namiji ne mai girman kai, amma akwai mutanen da suka fi ka girman kai, sai dai ba su nunawa a irin wannan lokacin, ko shi sarki idan aka zo wannan gabar sauke rawaninsa yake yi. Da farko na san ba za ka ce ba ni da kyau ba, na san kuma ina da kirar da duk wani namiji zai so ya mallake ni. Zan fi yarda da cewar sona ne ba ka yi sam! Bana kuma burge ka, to ina son ka sani, idan ba ka bari an yi auren nan cikin wannan lokutan ba zan samu hanyar da zan sama wa kaina mafita, kuma dole ka aure ni, ni din ajiyarka ce”.

Ta mike a fusace ta fita.

Ya koma ya zauna a kan gado, maganganunta ne suke dawo masa.

“Ummina, ban yi ma Ummina adalci ba”.

Da sauri ya mike, kokarin ficewa daga gidan ta ke. Da gudu ya cimmata ya damko hannunta ta shiga kiciniyar kwacewa. Tsawar da ya daka mata ne ya sa ta shiga taitayinta.

Bai saki hannunta ba har sai da suka dangana ga falo. Ya zaunar da ita, ya kasa zama sai faman kai-komo yake, ya koma ya dire gwiwoyinsa a gabanta yana son rarrashinta. Tausayinta yake ji musamman yadda idanunta suka tattasa saboda tsabar kuka. Ta ya ma zai iya wanke mata zuciya.

Ya lura Nabila babu abin da ta ke bukata irin tarayya da soyayya, ga shi bai iya ba, ya zai yi da ita? Ya dan cije lebe.

<< Kyautar Zuciya 2Kyautar Zuciya 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×