“Atika ammi na bata so na, tafison farin cikin yayata fiye dani kullim kokarina in faranta mata amman ta zabi farin cikin yayata Mai yasa zatayi min haka tsananin son danakeyi ma adamu na fito na nuna mata tsantsar son da nakeyi masa amman bata tausaya min,inata fama da zuciyata akan na saka masa kin adamu,sai dai kullim abu na kara ci gaba,Ina Jin azuciyata bazan iya rayuwa batare da Shiba bazan iya ba.”
Kuka ne ya kwace mata kuka takeyi sosai .
Atika ta sassauta murya.
“haba tawajene kin fi kowa sanin ubangiji Yana tare dake zai amsa Miki rokonki kedai ki zuba ido ki gani wallahi Zaki bani labari.”
Ta Kai hannu tana goge mata kwallah.
“Ke dai kada ki gaji Kara dagewa Zaki Sha mamaki,Kuma ma ammin bazata yanke wannan hukuncin haka kawaiba tayiwu tana da dalili.”
“Amman kinaji fa gobe su zaruk zasu kawo lefe,kina tunanin ahaka komi din zai dawo daidai?
“andaura aure ma an Kuma warware,anzo daurin aure an fasa,kedai kawai kici gaba da addu,a
***. ***. ***
“Naso na baki abinda kikeso,da ace shi wannan Didat din yakawo kansa wallahi Koda Aazeem zata mutu sai na bakishi amman yanzu bana son nayi saki na dafe ko Kuma nayi biyu Babu dan haka kiyi hakuri da zaruk gobe da safe zasu kawo lefe.
Kada nayi saki na dafe,nayi biyu Babu wannan kalmar ce ta dingayi mata yawo a kwanya,shin Mai yake nufi,wa annan wani irin iyayene Allah ya hadata dasu.
haka yagama soki burutsunsa bata tanka masaba kawai binsa take da kallo idanunnan sunyi luhu luhu sabida tsabar zubda kwallah.
Adaren zaruk yazo da katin daurin aure dana na party, party har kala biyar za,ayi sai wani rawar Kai yake.
Ya kafeta da ido yagano tsananin ramar da tayi tabbas ya yadda da labarin da Aazeem ta bashi ya saki murmushin mugunta.
“Yakamata yau na Sami kalamin soyayya daga bakinki koba komi zan Sami kwarin gwiwa”
Wani irin duba tayi masa Mai tattare da tsantsar tsana inama zata iya data sanar dashi yadda ta tsaneshi.
“My queen kinki cewa komi,ko bakya farin ciki?
Tadan jinjina Kai a hankula.
” Yanzu ki sanar dani Mai kike bukata.?
bata ce komiba ya sake cewa.
“Ina tayamu farin ciki zamu zama mallakin juna Mai Kika tana dar mini amaryata,
Ta daga ido luuu gaba daya idanun sun rine.
Matsowa yayi zai rike mata hannu tayi saurin ja da baya yayi murmushi
“Kwantar da hankalinkiki babu abinda zanyi Miki da banyi ba sai yanzu.”
“Kaina Yana ciwo Ina son naje na kwanta.”
batajira Mai zai ceba sauri, sauri gudu gudu tabar gun kawai yabi bayanta da kallo shi kadai yasan abubuwan da yake aiyanawa.
Washe gari gida ya fara cika da abokan arzikin masu karbar lefe gaba daya gidan ya kacame anata faman aiki Nurat nacan daki tayi kuka harta gaji ammi ta turo kofar Nurat tayi saurin sunkuyi da kai batason hada ido da ita
Kallo daya tayi mata tagama nazarinta ankya Bata zalinci Nurat ba kuwa ita asaninta zaruk da ita suna da fahimtar juna sun shaku dashi tin tana karama,batasan Mai yasa ta tsaneshi hakaba
Zama tayi akusa da ita ta sanyaya murya.
“Ki gaya min meye ne aibun zaruk da bakya sonsa?
Babu abinda fadar zai amfanar lokaci yariga ya kure.bata iya Bata amsaba juyin duniyar nan Nurat taki magana.
Allah sarki Nuratu na bantaba ganin fushinki ba sai yau.ammi ta fada a zuciyarta .
“ammi shi kuka zabar mini Ina sonsa,ku kyaleni haka dan Allah kinji.”
Kawai tabita da kallon mamaki,yau Nurat dintace mai yi mata magana a tsatstsaye haka.ta kada kai.
“To ki shirya zaruk yana get ke yake jira zaku je unguwa.
nan ma bata ce komiba yadda take haka ta mike abinda bata tabayi ba doguwar rigace ajikinta sai dan siririn gyalen data yane kanta dashi haka tayi waje babu musu tanayin abu kamar wata mahaukaciya.
Yana zaune akan mota tunda ta toho ya kafeta da ido ankya kuwa Nurat dinsa ce,ashe haka ta nuna komi yagama ji daman shegen hijabin nanne yake boye mata abubuwan sa Kai amman ya ji dadin haka,inbadan hakaba da tini ankawo mata hari,yanzu shi kadaine a zaisan kayansa Babu wanda yasan ya kirarta take babu wanda yasan kalarta
Kara sowarta ne ya katse masa tunani ya diro daga kan motar ya bude mata gidan gaba ta shiga kawai yaja motar.
tafiyar kurame suke babu wanda ya tamkawa dan uwansa zaruk ya katse shurun da fadin
“Ki gaya min duk abinda kike so yau zanyi miki nayi alkawarin haka kinji.”
Wani kallo datayi mishi sai da gabansa ya buga ga wani irin kyau da kallon yayi mata dole ya tsuke baki ya kunna music irin Mai sanyin nan hand set dinsa ne ya fara ruri aboki yaga an rubuta a fuskar wayar ya ratsa Kore tare da karawa a kunne
daga daya bangaren akace
“naji ance kunfita da madan ko?
“Eh muna tare kasani yau ake Kai lefe Kuma bana son jama,a su dinga ganne min ita shine zamu dan fita.
Ok to dan tsaya gefe zamuyi magana Mai muhinmanci.
Parking yayi a gefen titi ya fita acikin motar.
yanayin sa baki daya ya sauya ya dingajin zufa, kansa ya fara wani irin sarawa wani irin sabon kaunar Nurat da sonta ya dinga yaduwa a koina na sassan jikinsa.
“Kanason kace wannan adamun shine deedat?
Sai da ya gama tabbatar da hakan sannan ya katse wayar nan danan ya Kira dad dinsa yadda abokinsa ya gaya masa haka ya sanar da shi.
Yakoma mota ya zauna Yana faman tufka da warwara,gaba daya ya rasa tudun dafawa
bazai taba bari ya rasa Nurat ba Koda za,a mutu bazai bar wannan ba dolene sai ya auri kamila, yasani babu wadda ta rike budur cinta kamar Nurat dashi kadai ta dace ya dan dubeta jikinta ne ya bata Yana kallonta ta dago ido,idanun nasu suka gwuraya,gaba daya yaji tsigar jikinsa ta tashi hannunsa ya dauka ya dora akan nata da sauri ta janye hannunta hadi da daure fuska tam yayi murmushi mai ciwo har yanzu tunanin inda zai kaita yakeyi.
*** ***. ***
“inda ace yarinyar nan batayinka zan baka goyon baya da ka hakura amman kana son cutar da kanka da ita,wannan shawarar da na baka muddin kabishi komi zaiyi daidai.”
“Salim zanyi yadda kace amman bazan tozarta dan uwana ba”
“Kai kanason farin cikinsa bakason tozarta shi,amma shi baya kaunar ka.”
“amman mahaifiyarsa tana kauna ta,zanyi komi domin ta ,dan haka murufe maganarnan,kodama ace zan bayyanawa duniya amman ai ni babu siyasa agabana.”
“ok shikenan amman ka amince zakaje ga mahaifin ta da sunan deedat.?
Tunda su deedat suka bar gunsa ya kasa zaune ya kasa tsaye,ya dinga zaga office dinsa cike da doki.”
“Zasu wani ce nayi tunani,na riga na san dacin talauci na Kuma San dadin kudi,na fahimci banbancinsu duka dolene na amince da arziki a garin wasu gwara a naku.”
cike da shagwaba take sanar dashi yau zasu hadu da deedat ,sai dai tana tsoro dan ta dade da fahimtar soyayyar dake tsakanin sa da kanwarta.
“Kinsani dukkannin abinda na zartar dole shi za,abi muddin bai amince da keba sai dai yayi biyu babu bandama abinsa ai shidin yafi karfinta.”
Ya janyota jikinsa,cikin wani irin salo tare da cigaba da alkawarta mata cewar ko yace bayayinta zai bi ta hanyar malamai dole ya amince ko badan Allah ba
deedat da babbar yarinya ya dace ba bera irin Nurat ba .”
Yadda yake lasa mata zuma abakine yasa ta saki jiki dashi fiye da koyaushe,sunyi bala,in shagala da alamar salon yau ya banbanta da koyaushe.
Ammi nata faman sallama bataji motsin kowaba ta nemi gu ta zauna tare da yada gyalenta kusur kusur taji daga shashin yallabanta ta yi mamaki dan bai cika dawowa a irin wannan lokacin ba ta mike ta nufi shashinsa tin daga set room taci karo da kayan mata barbaje akasa ras gabanta yayi wani irin bugawa gaba daya jikinta yagama yin la,asar jitakeyi tamkar an tsintsinka mata jijiyoyin jikinta,kuka zai kwace mata tayi saurin toshe baki tazo daf da kofa zata kutsa sai taga bazata iyaba komawa tayi da baya ta zauna a kujera jikinta sai tsuma yake tana son ganin waca fitsararriyar ce wannan wadda kebin namiji har gidan aure
Kusan awa guda tana zaune duk da tana cikin halin damuwa haka bai hana ta jinjinawa ko waceceba sabida dadewar da sukayi.
Tagama kosawa zuciyarta sai faman tafarfasa takeyi,bata iya rashin mutunci ba,amman sai tayi mata abinda har ta mutu bazata mance ba darajar yaransu ne kadai yasa batayi musu ihuba idan tayi haka ko ba komi ta haifawa yaranta abin kunya da gori.
Aazeem ta fito daga ita sai pant ido biyu sukayi da ammi tinda ammi take sai yau ta taba ganin razana da tsoro a idanun Aazeem inda kasan mutum mutumi haka ta bushe agun takasa Koda kwakkwarar motsi
Shima yallabanta yarufa mata baya har da yan wake wakensa dan shi tunda Nurat tayi gamdakatar yake cikin farin ciki.
akaro na biyu Shima sukayi ido biyu da ita ai kuwa ammi ta saka hannu aka ta rusa wata gigitacciyar ihun da gidan ya dinga amsawa sai gata zube akasa ko numfashi bata yi.
“daddy ammi zata mutu,mu kaita asibiti kada ta mutu
cikin muryar kuka take magana.
“Ki kwantar da hankalinkiki babu abinda zai sameta kiyi maza ki kintsa jikinki bara na Kira Dr Nasir .
tasani duk inda aka Kira da hotel ba gun arziki bane,hakan tagani arubuce kwaro,kwaro arubuce a inda taga yana kokarin danna hancin motarsa .
Lokacin daka dauko ni daga gaban iyayena bacewa kayi dasu zaka kawoni gun watsewa ba ,dan haka dan Allah ka maidani gida.”
Ya marairaice murya.
Kina ganin kamar zan cutar dake ne,kefa matata ce shaura kwanaki hudu kacal ya rage a daura aure,kinga gashi kinsa sai kallonmu akeyi”
“Na rantse da Allah bazan shigaba ka maidani gida.”
“Kinsan gidan gaba daya cike yake da jama,a.”
munyi waya da ammi lokacinda ka fita tace Babu kowa duk suntafi.”
“toshikenan naji amman da sharadi sai dai nawuce dake gidan mu.
Da sauri ta kada kai alamar ta amince dole ya juya akalar motarsa badan yasoba
“Tazo kenan har abada bazata koma gidan suba,itadin tawace dad,in banda karanta taya za,ayi min haka tin tana karama nake sonta,na rayu da sonta bazan amin ceba bazata komaba ai anyi Mana baiko.”
Haka yayita yiwa dad dinsa soki burutsu kamar wani tababbe.
” Ya Isa haka zaruk,duk mai yakawo wadannan maganganun waya ce da Kai za,a hanaka ita,ai Nurat takace bazan bari hakan ta faruba ka kwantar da hankalinka,ai ba,a tabayin haka ba,saurafa kwana uku kacal ta halatta agareka dan haka kasha kuruminka.
“dad nasan wannan mutumin batin yauba mayen kudine zai iyayin komi ka kirashi kace dashi zamu wuce da ita Koda bananan yau za,a iya daura auren.”
Handset din dad din zaruk ne ya fara ringing .
“dad kagani ita yake nema Kuma ka daga kaji .”
Ya latsa kore ya Kara a kunne,
” Alhaji zaruk Yana tare da Kaine?
“Ya akayi?
” Mahaifiyar ta bata da lafiya tana bukatarta akusa pls ka yi masa waya yadawo da ita dan tana mutukar son ganinta.”
“Shikenan zan turosu yanzu haka muna tare.”
Ya juyaga zaruk ya shiga rarrashi hadida kwarara masa gwuwa har sai da ya amince masa da zai maidata gida.
dagacan shashin matar yayansa kalamen da take fadi game da zaruk ya Kara wa Nurat wutar tsanansa .
“Idan Kuma shi din Allah ya tsara zai zamo mijinki babu yadda zakiyi kullim Ina son ki dinga yin addu,a ubangiji zai rusa komi bazai baki miji kamar Saba,ni nasan bai dace dake ba baki dace da mutumin da bashi da maraba da dabbaba__
takatse maganarta sabida wani shaka da zaruk ya Kai mata Nurat ta hau kururuwa tana Kiran dad asukwane dad ya shigo yayi kan zaruk amman yakasa banbareta ajikinsa sai da ya dauki wani katako ya buga masa gaba daya jini ya gama wanke masa fuska ganin haka yasa Nurat ta yo waje aguje cikin yanayin firgici.
Acan bangaren su Aazeem komi ya rincabe rigama sosai tsakanin ammi da dad dinsu Nurat.
“duk yadda nake shiya maidani haka yafara mu,mu,amala dani tin banzama baligaba shune ya dorani akan wannan harkar,yasanar dani cewar ni ba yarsa bace,dan haka baharamun bane dan ya kadaice dani zai Kuma fifita ni bazai kyamace niba amatsayina na shegiya zai nunawa duniya shine ya haifeni da haka ya hillaceni .” Yace kinki sanar danine sabida kada na shiga damuwa Kuma yayi Miki alkawarin bazai nuna banbanci ba.”
Jikin ammi tana tsuma .
“Karya yakeyi kedin yar halak ce kinfi Nurat asali da komi,da bazarki yake rawa duk wannan arzikinki yake ci badan keba da haryanzu yana mutsiya cinsa.”
Jin maganganun nasu takeyi kamar saukar ruwan sama kwakwalwarta ta kasa dauka wani uban iyu tasaka
” Ki gaya min waye mahaifina,ina yake Yana Ina,kugaya min dan bazan cigaba da rayuwa da mutane irin kuba–
“itace ta kasheshi sabida cimma wani wani buri nata gatanan tagaya Miki gaskiya,ita ta kashe bawan Allah.
Idanun Aazeem gaba daya sunjuye da mosifa ta dubi ammi ido cikin ido
“Kigaya min gaskiya wannan mutumin yake fada!?
Ammi takasayin Koda kwakkwarar motsine hakane yabata damar barin gidan aguje kamar wata mahaukaciya.
ammi ta juya tana yima mijinta kallon tsana
yau nayi dana sanin kasan cewa da Kai,Kuma abinda kayi min sai Allah yayi maka karshenka bazaiyi kyauba sai kayi rayuwar kaskanci da wulakanci bazan yafe makaba,Kuma shidin Wanda kayin komi domin ya zamo mijin yarka bazai taba auren yar mutum kamar kaba Didat bazai auri Nurat ba.
Kana nuna mata doyayya ne sabida ka watsa rayuwar ta yayinda ka dinga tsangwamar yarka kana takurata akan ibadar ta da karatunta da izinin sai Kaga saka mako Allah bazai barkaba.
“Kanki akeji da “yata ta rasa gwara kowa ya rasa.”
Ya nufi hanyar fita daga gidan.
“bazan cigaba da rayuwa da Kai ba danayi hakan gwara na mutu domin baka da maraba da dabba mai abin kunkya kawai.”
Kuka Mai tsanani ya kwace mata .
Yana saka kafarsa a get ya hangi motar yan sanda suna nufowa gidan sa bai tsaya wata wata ba ya fice ta yadda basu iya hangoshi ba.