Skip to content
Part 34 of 34 in the Series Kyautar Zuciya by Bilkisu H. Muhammad

Deedat na zaune a office din likita suna tattauna yadda za,a bulluwa lamarin likita ne ke bada shawarar cewar dole sai an fita da ita kasar waje dan gyara mata fuskar sai da suka gama tsara yadda za a yi likitan ke sanar dashi tayi barin cikin dake jikinta.

Allah yasa hakane yafi alkhairi ya fada a zuciyarsa ansa ranar da za,a fita waje a inda aka shiga fafutukar biza.

daya bangaren Aazeem tayi free a inda aka dingayi wa Nurat san barka da ba ita wannan tsautsayin ya hau kantaba.

ana igobe za,a fita waje da nabila rigima ta kaure tsakanin deedat da iyayen nabila inda suka dinga surutun cewar akan me baza,aje dashi ba dolene ya bisu amatsayinsa na mijinta.

umminsu tasashi agaba tana faman fadan dolene shima ya bisu anan ya sanar da ita ya dade da sakinta yayi  shurune sai ta haihu zai sanar mata.

ta maimaita innalillahi bata taba zaginsaba amman yau sai da ta zageshi.da cewar sai ya maidota saki daya yayi amman ya kara biyu duk dan kada ta ce sai ya maidata yariga yasan kafiyarta muddin ta kafe sai ya maidata.

Nurat ta kadu da Jin wannan sakin har ga Allah bataji dadiba,itama tasani wataran hakan zai iya faruwa da ita tunda ya kasance mai sakin matane.

dole haka suka tafi batare dashiba.bayan sun tabbatar da nabila ce da laifi sannan da jin labarin sakin da yayi mata.

Ko yaushe Nurat na gudun deedat duk sanda yazo bata bari ta kebe dashi dan ma kada ya takura mata bata rabo da cikin jama,a ko waya ya Kira bata dagawa hakane kawai yasa ya kyaleta yasan dole za,a share makoki ta koma gida.

daga bangaren Aazeem Kuma idan ka ganta bazaka ce itace wannan tantiriyar ba ko yaushe rike da carbi tana ja salatin annabi S.A.W ya Kara tausasa zuciyarta gaba daya ta cika da tsoron Allah ga dana sani da kunkyar rayuwar da tayi abaya,takanyi kuka Mai isarta sai ammi ce ke faman kwantar mata da hankali idan kaganta kullim cikin hijabi zumbulelen  Nurat ce ke koyar da ita karatun alkur,ani Mai tsarki.

Kwance tashi yau sati biyu da rasuwar a inda deedat ya nuna Yana son komawa Abuja da amaryarsa ita Kuma ta dage bazata koma ba sai anyi arba in sai da ammi tayi mata tatas sannan ta hada komatsenta.

har suka Isa Abuja tana baccin karya dan kada ma ya kulata.

tafito daga wanka daure da tawul ta tsaya a bakin wadrop tana dubo kaya ta ya rungumota ta baya ya shiga yi mata rada a kunne ta rintse ido gam tana Jin kunkyar a yadda ya ganta.

“Na damu da ke tsananin sonkine yasaka bazan iya barinki acanba,kiyi hakuri dan kwanakin ma danayi bana tare dake na sha wahala,Nurat kece ruhina banajin zan iya rayuwa batare da keba,pls ki daina fushi dani haka bawai na saki nabila haka kawai bane na yi hakuri da ita alokacin da na rasaki hadaki da wata bazan iya yin adalciba idan Kuma kina so sai na auro wata.

batasan sa,arda ta bude idanuntaba Yana kallonta ya kunshe dariya aciki.

“hakan yayi Miki?

banza tayi masa da kansa ya shiga lalubo mata kayan baccin da zata saka wata doguwar riga ya dauko wanda babu abinda ya tare.

“Wannan Zaki saka mini my baby.

“Kayi hakuri bazan iyaba.

ya marairaice murya.

“har kin mance da wasiyar daddy yana fa jinki.

mamaki takeyi yadda akayi yasani..

Kafeta yayi da ido yaga yadda ta kadu,tabbas yasani har yanzu yarinkyace idan ya hada da dabara zai iya cin gala a akanta.

“Yanzufa Yana kallonmu,zai ji dadi Kuma baza,ayi masa azababa inhar Kika sakani farin ciki idan Kuma kina son yayi fushi dake sai na kyaleki haka.

ta yadda yanayinta ya sauya ya bashi dariya.

“Nifa ina kaunar daddy dan haka kikaga inata binki amman tunda bakya gani shikenan.

Ya juya ya soma tattaki.

“kayi hakuri ,gaya min ya kakeson nayi?

“a,a bashshi kawai.

Ya koma ya zauna abakin gado gaba daya ya koma mata kalar tausayi.

“Kayi hakuri bazan sakeba kaji,yanzu ka gaya min abinda kakeson nayi?

Sai da yadan ja aji,sannan yace.

“ni wannan kayan kawai nakeson ki saka.

Dole haka tasaka wayyo zo kaga yadda kayan sukayi mata mutukar kyau tazama abar sha,awa yana daga zaune baisan sa,ar da ya zabura tsaye ba.

Tsarki ya tabbata ga ubangiji  ya dingaji aransa yafi kowa sa,a ya godewa Allah da wannan tukyicin,komi na Nurat Mai kyaune halinta surarta da komi nata tattaki yayi ya karasa gareta tayi saurin nade hannayenta a kirjinta hadida rintse idanunta yayi murmushi rungumeta yayi ajikinsa tare da nitsa yatsunsa cikin lallausar gashinta Yana yi kamar yanayi mata susa.

“Nurat! Ina mutukar sonki,Ina sonki fiye da komi da kowa,nayi Miki alkawarin bazaki taba dana sanin kasancewa ta abokin rayuwarki ba,ki bude idanunki pls.

Ahankali ta ware idanunta yanzune tasakeyin alkawarin bazata sake jayayyaba idanunsu suka gwuraya jiyayi gaba daya tsigar jikinsa sun tashi bai San sa arda ya sungumeta kamar wata jaririyaba ya direta a tsakiyar gado ya komo ya kashe fitila ya dawo ya kwanta tare da janyota jikinsa ya lullubesu da bargo yadda yaji jikinta na rawa ne yasa yashi ya fasa kudurinsa ya koma shafa bayanta kamar wata jaririya har saida bacci yayi awon gaba da ita,shi kuwa bai iya rintsawaba sabida farin ciki..

da asuban fari ta dire daga gado batason wayar gari da wannan kayan bathroom ta shiga tayi wanka ta dawo ta sauya kaya,shi ma Kiran sallar asubane ya farkar dashi har Yana neman makara da sauri ya daura alwala ya nufi masallaci

Lokacin daya dawo yataras da ita ta fara bacci akan darduma cak ya dauketa ya maidata gado ya sake mannata ajikinsa ya lullubesu.

“Nurat dina zan iya rayuwa dake ahaka batare da na kusance kiba ke kawai nakeso ba jikinki ba kekadai nakeso in budi idona kawai Ina ganinki tare da rayuwa dake a gu daya zaifi komi sani cikin farin ciki.ya dinga shafa gashin kanta abinda yafi komi birgeshi ajiki ta kenan . Sam baya yunkurin taba wani abu ajikinta tunda yafahimci tsoronsa takeji.

gaba daya ya koma bata tausayi kusan satinsu biyu cikin wannan yanayi gashi tayi mugun sabo da jikinsa bata iya rintsawaba inhar bata jita a kirjinsaba kamar wata mage hakan din kan bashi dariya da yadda ya lalatata da son jiki.

Cikin shirinsa ya fito rike da katuwar jaka.

Kawai ta bishi da kallo.

Ya kunshe dariya aciki zama yayi akusa da ita suna duban juna ido cikin ido.

nasan bazaki bukaci komi daga waje ba idan Kuma hakan ta kama akwai mukullina ahannunki sai ki dauko kudi ko.

Aiko idanunta suka firfito.

“bangane ba Yayana?

“tafiya ce ta kamani ba dadewa zanyi ba wata daya kawai zanyi .

idanunta sukayi raurau zatayi kuka

amman aikasan Ina Jin tsoro.

baki da matsala indai wannan ne zan sa  ummina ta turo miki wadda zata tayaki kwana.

“Nidai zan bika.

“Amman ai banga amfanin da zakiyi min acan dinba.

“kawai kiyi hakuri ni zan wuce taho nan muyi sallama babu musu ta taso ya saki jakar hannunsa ya rungumeta sun dade ahaka .

“Zanyi kewar ki,ko ta Yaya zan iya bacci yau .

Sai ga kwallah sharshar na bin kuncinta.

“dan Allah ni zan bika.

” hakuri kawai zakiyi.

ya dago kuncinta ya sumbaceta a kan labbanta.

Ya koma ya kinkimi jakarsa ya roko hannunta suka fito harabar gidan a get din da zai sadata da ma aikatan gidan ya yi sallama da ita kuka takeyi amnan ko sake sauraronta baiyi ba ya yi saurin ficewa.

Aazeem taci gaba da gudanar da aiyukanta a kamfanin da deedat ya mallaka mata gaba daya ma aikatanta na mutukar kaunarta sabida yadda take bi dasu gaba daya tayi sanyi kullim idan ta tina rayuwar datayi takanyi kuka Mai isarta haka ayanzu ta fahimci illar rashin ilimi ta tabbata da tayi makarantar addini duk bazatayi wadannan abubuwa ba ga alkur,ani ya gyara mata rayuwa ya tausasa zuciyarta sabida yawan karantashi akalla yanzu takan iya hada baki cikin lokaci kankani ta haddace aharari kawa,idi da sauran littattafai ko yaushe fuskarta dauke yake da hasken addini.

tana zaune a office da alkur,ani agabanta idanunta sanye da glas daya daga cikin ma aikatanta ya sanar da ita tayi bako tabada izinin daya shigo.

Zaruk ne bakon tayi farin cikin ganinsa ,sai dai jitakeyi kamar bashiba gaba daya ya sauya Yana rike da carbinsa sai famab ja yakeyi.

“ranka ya dade abokina Ashe Kaine.

Kallonta yakeyi cike da mamakin shigar da tayi ta koma tamkar kanwarta hijabi zumbulele.

“Wai da zuwa nayi mudan fita

da sauri ta katseshi.

“Please ka it’s bakinka idan ma katuna abinda ya faru abaya bazan yafe makaba Kuma Ina son kayi gaggawar barin office dina Kona saka ayi min waje da kai.

sakin baki kawai yayi Yana kallonta cike da farin ciki Ashe bashine kadai ya gane gaskiya ba Kai amman yayi farin ciki ya godema Allah.

“Kiyi hakuri kawata yanzun ba haka nakeba kawai Ina tsokanar kine Kuma naji dadi da wannan sauyin,amman Ina son zan tambayeki please.

Ta dan jinjina Kai alamar shi take sauraro.

” Ina rokonki da ki zamo matata,Zaki aure ni?

“Wai Mai yasa Kai komi sai kayi wasane.

“Wallahi bawasa nake ba Aazeem Ina sonki .

“dan Allah zaruk ka fita kada ka haifar mini da ciwon Kai.

duk yadda ya kaiga lallashi bata saurareshiba dole haka ya hakura.

acan gidansu deedat ne gurtane agaban ammi Yana Mika kokon barar zaruk

Ashe bayan barin zaruk gidan deedat ya Kira yake shaidawa daman tini ya nemi shiri da deedat gaba daya ya yada makamansa lokacin daya tabbatar da waye deedat din ya shige jikinsa ta hanyar yewan kiransa a waya da wasu harkokin nasama yakan tsoma zaruk din aciki.

yagama zayya newa ammi komi game da soyayyar zaruk ga Aazeem suna cikin haka Aazeem ta shigo.

“Kace mankyan baki ne agidan namu Ina Kuma kabaro mini kanwar tawa.

Yayi murmushi cike da jin dadin yadda ya ganta.

“tana Miko gaisuwa Kuma wannan zuwan nakine.

“Nawane Kuma?

“Eh Mana zaruk ya tasheni tsaye sai nazo na nema masa auren yayata .

“Idan har kana ganin yadace dani ai bani da zabi.

“Nagode da wannan matsayi da kika bani.

Deedat gurfane agaban daddinsa Yana rokonsa da ya shige gaba akan lamuran dan uwansa Kabir ya Sami Koda mukamin dan majalisa ne tunda ya lura da Kabir nason harkar siyasa.

Umminsu bata bata goyi bayan hakaba.

“nice na haifi  Kabir nafi kowa sanin wayeshi dan haka ni ban goyi bayan hakan ba.

“To amman ummi sabida meye ne?

“Kabir Yana da son zuciya baya tsoron Allah Kuma shi shugabanci baya bukatar mara amana Ina jin tsoron yaci amanar talakawa kaga zai fada a halaka domin shi ubangiji baya yafe hakkin wani.

“Ummi na fahimceki,Kuma ai Ina tare dashi daddy ma yana tare dashi zamu dinga nusar dashi.

Ya dubi dad dinsa.

“Ko ba hakaba my dad?

“Kwarai kuwa yarona yadda kace haka za, ayi.

***.                  ***.              ***

Karfe goma Sha biyun dare ya Isa Abuja acan shashinsa ya gama duk abinda zaiyi kama wanka sallah da sauransu sannan ya sanya kayan bacci ya nufi shashinta.

sabida zulumi da tsoro ta kasa aiwatar da komi ko sallolin da takeyi na nafila da karatun alkur,anin yau gagara yayi kuka kawai take famanyi idanunnan sunyi luhu luhu musamman ma da Taji wa,azin wani malami dayayi akan hakkokin namiji akan matarsa musamman a bangaren shinfida ta tabbatar da ta cutar dashi tasani son da yakeyi mata bazai iya tilasta mata akan abinda batasoba Koda Bata furta batasoba ai zai gani a fuskarta Kuma tasan abinda yasa yaki tafiya da ita kenan tunda gashi ya gaya mata magana yace bazatayi masa amfanin komiba sai yanzu ta fahimci inda ya dosa.

Kuka ne ya kwace mata ta hada Kai da gwiwa kamar daga sama tajiyo sallamarsa atsakiyar dakin

da gudu ta mike batasan sa,are data rungumeshi tana sumbatar sa ba. tsayuwar ma ta gagaresu.

Tadinga furta masa

“Yaya na Ina mutukar sonka Ina sonka ni din takace na baka kaina zaka iyayin  duk abinda kaso dani Ina sonka Ina mutukar sonka kada ka sake nesanta dani bazan jureba.

Yana dan dagota Yana duban ta cikin tsakiyar ido.

Kin tabbata kin bani kanki kinshirya karbata?

Ta jinjina Kai ya sake rungumeta wani irin sonta na cizgarsa sunfi minti biyar ahaka daga karshe ya jata bathroom suka dauro alwala sallah sukayi kamar yadda shugabanmu Annabi Muhammad S.A.W ya koyar damu yayinda dayan mu yayi sabon aure kafin ya kusanci amaryar tasa.

akan shinfida yarasama ta inda zai fara daga bisani ya koma bida ita wasu irin wasanni ya dinga kirkirowa akankansa yanayi mata Yana Kuma koyar da ita tabbas babu abinda so baya sakawa shidin kansa baisan zai iya hakan ba sannu ahankali yasami yadda yakeso batare da ya bari ta Sha wahala ba ya kyaleta wato ya barma wani lokacin yadda yake jinta aransa bazai karar da ita lokaci  gudaba dole sai yabi ahankali bazaiyi gaggawar ba tunda ita din tasa ce shi, shi kadai.

Koda gari ya waye yan buya suka koma shi kanshi tsintar kansa yayi da Jin nauyinta abinci ma basu ci tare ba  har zuwa dare sai adaki suka sake haduwa lokacin da ya sake zuwa gareta taji tsoro amman haka ta daure sabida idan tabari ya gane hakan bazai Sami nutsuwaba koda tana so haka zai hakura ta fahimci shi ba mutunne maison takurawa ba.

yau kam ta biye masa sosai ta nuna masa kwarewarta akan abinda ya koyar da ita jiya yayi mutukar samun nutsuwa da ita a inda ya janye kudirinsa na cewar zaibi a hankali bai San sa arda komi ya faruba kawai sai jin hawayenta yayi na diga a hannayensa.

“Baby na kuka kikeyi?

ta kada Kai alamar a,a

“Kiyi hakuri kinji na kasa rike kainane sannu kinji haka ya dinga lallashinta bacci ne Mai karfi yayi awon gaba da ita mikewa yayi ya janyo bargo ya lullubeta ya koma ya kunna fitila ya dawo yasakata agaba yana ta kallo kamar wata sabuwar halitta .

bayan wata daya akayi bikin zaruk da Aazeem yayin da zabe ke karatowa Alhaji munir da deedat suka tsayama Kabir Kuma da alama za aci nasara.

bayan wata uku nabila ta dawo daga kasar waje angyra mata fuska sai dai ba,a bari a kwashe duka idan ka santa ada ba lalle ka ganeta yanzuba fuskar babu yabo ba fallasa.

yanzu haka Nurat nata faman laulayi yayinda deedat ke cikin fargaba tare da Jin haushin kansa sabida rashin hakurin da yayi mai yasa bai barta ta Kara kwariba yanajin. tsoro bazata iya haihuwa da kantaba sabida zulumi har wata yar rama yayi baya tabayin nesa da ita ya sakarma Salim duk wasu aiyu kansa  lokacin da cikin ya Kai wata takwas ya hada komatsenta suka komo kano shigar dare sukayi washe gari da sassafe ya kaita asibitin dan duba lafiyarta an sakeyi mata skynin a inda aka gano yara uku take dauke dasu acikinta jiyakeyi tamkar an saukar da wahayin mutuwarta bai bari an sanar da itaba Kai tsaye ya nufi gidansu da ita a kofar get ya sauketa yace tashiga yanzu zai dawo .

Yana zaune agaban iyayensa kuka yakeyi sosai kamar wani karamin yaro Wai Nurat zata mutu ta kaici agun umminsa kamar ta bigeshi Alhaji munir ne ya dinga lallashinsa ita ko ummi ta bulbuleshi da fada Alhaji munir ya jashi harabar gidan Yana cigaba da lallashi .

“daddy Mai zai hana ayi mata aiki aciro yaran Ina tsoron kada ta rasa ranta daddy kana ganin fa tayi kankanta bazata iyaba yara uku sunyi mata yawa karama cefa shekararta Sha bakwai Ina Jin tsoro.

dubansa kawai daddy keyi yana mamakin yadda yake son matar tasa.

“Ka kwantar da hankalinka, ka mika lamuranka ga ubangiji da izininsa zata haihu lafiya kaji.

Cikin rashin kuzari ya Isa gidan nasu Nurat kwance tayi matashi da cinyar ammi tana shan agwalima Yana son sanar da ita amman yana tsoro tasani ,tanaji itama zata karaya amman ya zaiyi ya dan dubeta itakam babu abinda ya dameta.

“Deedat darefa nayi yakamata kutafi haka ko.

“ammi Wai da anan zan barta ai bai karasa maganar ba ta mike ta dauki jaka ammi tabita kawai da kallo dole haka ya tsuke baki.

Gidan su na kano kullim a gyara yake .

Acan bedroom tayi matashi da kirjinsa tana yi masa mita.

“Kada ka sake kaini wani gidan kace Wai zaka banni in kwana kasani fa bana iya bacci batare da mijina ba.

Tausayinta ya keji ya shafa gefen fuskarta.

“Kiyi hakuri bazan sakeba kinji.

wata safiye dad dinsa yayi masa Kiran gaggawar kamar jira akeyi ya tafi tafara nakuda ta godema Allah da bayanan tana Sane da firgicin tsoron da yake ciki dan haka take ta rokon Allah kada yasan da haihuwarta sai dai yadawo ya tarar da yaronsa ammi ta Kira awaya ba a dauki wani lokaciba ta karaso suka rankaya asibiti ,basuma doshi asibitin Saba gudun kada yaji labari.

basuyi cikakken awa gudaba Allah ya sauketa lafiya ta haifi yara uku rigis biyu maza daya mace macen da namijin sunyi kama sak da deedat yayin da daya namijin yayo Nurat sak dukkansu suna cikin koshin lafiya  .

Dagacan bangarensa aiyuka sun rikeshi zaruk ya Kira ya rokeshi alfarmar Aazeem taje ta zauna da Nurat kafin yadawo.

Lokacin da ta Isa gidan shidewa ne kawai batayi ba sabida dadi dawowarsu daga asibiti kenan ta shigo kamar ta cinye yaran.

Karfe goma suka iso gidan shida zaruk da niyar zai dauki Aazeem su wuce gida.

Motsin tohowarsu taji da sauri tafito ta tsaya abakin kofa ta tokare “bazaka shigaba.

ras gabanshi ya buga gaba daya ya gama kaduwa.

“Mai yasa Ina Nurat din take mai ya sameta?

Bai tsaya sauranta ba kokarin tunkude ta yakeyi tayi saurin kwucewa.

Jarirai ya gani rigis jere akan gado kamar zaiyi hauka idanunsa sun rufe baisan sa arda ya rungume Nurat yana saka mata albarka.

“baby na samunki babbar sa,ace,nagode sosai Ina mutukar sonki, ya koma ya dauki dukkan yaran yajeresu a jikinsa wani irin iska na shigarsa Mai dadi Yana jinsa babu yeshi aduniyar nan.

Ammi ko tuni ta silale dan kunya bazata iya jure ganin wannan fitsararba haka itama ya tallafota jikinsa .

“Zan kula da ku iya daidai gwargwadon iyawata kema har yanzu baby ce nagode kin bani komi kin bani farin ciki Allah ya raya min ku bisa son ma aiki.

Duk gidan rediyon da tv daka murda labarin yaran akeyi da cewar ana gayyatar kowa da kowa suna tare da alkawarin cewar deedat zai bayyana wa masoyansa kansa dan haka kowa yaci buri.

ranar suna maza da mata ta ko Ina ketowa suke an radama yara sunan Alhaji munir da mahaifin Nurat sai macen wadda taci sunan mahaifiyarta wato Nurat karama.

Anyi barin kayan masarufi da kudi tamkar ba a so, tun daga wannan rana Deedat bai sake boye kansa ba.

Alhamdulillah Ina godiya ga Allah daya bani ikon gama wannan labarin wato KYAUTAR ZUCIYA.

<< Kyautar Zuciya 33

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×