“Oh God! Nabila bana son cutar da rayuwarki shi ya sa nake ta jan lokaci, ke mace ce wadda ba za ki iya rayuwa ba tare da mijinki na nuna miki soyayya ba, ni duk irin wannan abubuwan ban sansu ba. Ban taso a gaban iyayena na ga hakan ba, na taso cikin tsangwama da kyama, Ummina ba ta tare da Babana, ni ban iya ba ban san ya zan yi ba”.
Duk sai ya dinga ba ta tausayi, kalaminsa sun taba mata zuciya, abin da ya tsana dai shi ta yi, ta dora hannunta a kan nashi.
“Yaya Deedat na fahimce ka, ka daina tuno da abubuwan da suka wuce, ni zan iya zama da kai, zan koya maka yadda za ka kula da ni, zan rayu da kai a yadda ka ke. Kada ka damu ni ina sonka”.
“No, Nabila kina bukatar miji jarumi wanda zai dinga kulawa da ke. Na ji mutane na cewa ci da sha ba shi kadai ake bukata cikin rayuwar aure ba. ana bukatar kulawa, kin ga ni kuma ban da isasshen lokaci, asalima ni din ba mazauni ba ne yadda al’amuranki suka nuna kin fi son ko da yaushe kina tare da mijinki”.
“Sai dai ko rayuwa da ni ne ba ka son yi, amma ni zan rayu da kai a hakan’.
“No Nabila, akwai abin da ya rage da nake son gaya miki. Amma sai na komo gida, wannan shi ne zai zamo maganarmu ta karshe da ke, idan ki ka amince za a iya yin bikin a duk lokacin da ki ka shirya kin ji?”
“Me ya sa ba za mu yi maganar yanzu ba?”
“Dare ya riga ya yi, ina jin barci saboda gobe da wuri zan fita, ki bari kwana biyar kacal zan yi, ina komawa gida zan gaya miki”.
Washegari da sassafe ya sallame ta bayan sun gama karin kumallo.
ANNUR INTERNATIONAL SCHOOL makaranta ce wadda ke tashe, ta yi ma makarantu da yawa zarra, sam babu ragon Malamai, duk cikin malaman makarantar da yawancinsu a waje suka yi karatunsu, haka yawancin daliban ciki Deedat na daukar nauyinsu su fita karatu waje, kudin makarantar bai cika tsada ba, sai dai duk da haka masu hannu da shuni suna barin tsadaddun makarantu su kawo su wannan, saboda karatun da ake yi a cikinta. Wannan makaranta sunanta ya kewaye gida da waje, ba wani ne mamallakin Annur International School ba face Ahmad Deedat.
Karfe bakwai da rabi Deedat ya isa makarantar kamar yadda Maigadi ya sani, shi din abokin principal ne, gurinsa yake zuwa don haka yana yin parking din Lipan maigadi ya karasa gare shi yana yi masa sannu da zuwa.
“Ai kuwa Principal yanzun nan ya fita, sai dai na san ba nisa ya yi ba”. Maigadi ya fada.
“Okey bari na jira shi”.
“Ko a kawo maka abin zama?”
“A’a kada ka damu”.
Ya koma bakin aikinsa, shi kuma Deedat ya koma gindin wata bishiya ya tsaya yana kallon daliban da ke shigowa. Hankalinsa ya kai ga Nurat wadda ke ta faman sauri hade da waiwaye, abin da ya ja hankalinsa ke nan, ya san duban abin da ta ke waiwaye. Idanunsa suka kai ga wasu samari. Da alama ita din suke bi.
“Na gaya maka in dai Nurat ce kun yi kun gama ba ‘yar hannu ba ce. Ita din muguwar bagidajiya ce, sam ba ta waye ba saboda gidadanci, ko ‘yar kwalliyar nan ba ta yi”.
“Na ce ku sanya min ido duk gidadancinta sai na wayar da ita, zan ba ku mamaki, ni ne fa, kwana uku kawai za ku ba ni duk abin da ta ke takama da shi sai na sauke mata shi, na yi alkawari sai na sauya mata tunani”.
Gaba daya suka sa shewa.
Ya kasa gaskata abin da iska ya debo wa kunnuwansa. Ras! Ras!! Ya ji gabansa na bugawa, hankalinsa ya yi mugun tashi. Yana son gano yaran sai dai ya kasa tantance su. Tuni suka bace ma ganinsa, daga can nesa ya sake hangensu sun sha gabanta yana kallo ta ja da baya, ta kuma fada wani ajin, su kuma suka dauki wata hanyar.
“Ta ya ya aka samu irin wadannan yaran a cikin makarantar nan? Wannan babban kuskure ne, ba za mu laminci haka ba, duk inda yaran nan suke dole ne a zakulo su, ba za su bata mana sunan makaranta ba. Ba zai yiwu ba, wannan ba abu ne wanda za a bari ya wuce ba”.
Duk yadda suke da Principal, wato Zaid bai iya daga masa kafa ba. hankalin Zaid ya yi matukar tashi.
“Dole ne za mu nemo su, za mu je ajin da yarinyar ta shiga, hakan zai taimaka mu gano su”.
Karfe goma sha daya aka fito break, haka ne ya ba wa Deedat da Principal damar zaga ajujuwan don ganin abubuwan da suke bukatar gyara ko sakewa.
A can aji Nurat na zaune tana nazarin littafinta na English, Faisal Nura da Abdul suka kutso kai cikin ajin. Ba ta yi aune ba ji ta yi kawai an wafce littafin, a tsorace ta dago kai lokacin da ta lura da su ne jikinta ya hau bari.
“Ke ba ki ji ba, magana fa ake yi miki’.
Tamkar ba da ita suke ba, hakan ne ya sa su gaba daya suka katange ta, babu ta inda za ta iya guduwa. Faisal ya sa hannu yana shafar kuncinta, kawai ta nade hannayenta cikin hijabi ta kuma runtse ido, kwalla suka soma tsinkawa a idanunta.
“Me ye a hannun naki da ki ke boyewa?” Abdul ya fada.
“Ni kuma sai na sumbaci hannun”. In ji Faisal.
“Don Allah ku yi hakuri”.
Hakan bai sa sun fasa kudirinsu ba, Faisal ya kai hannu ya damko hannunta. Ta kwalla ihun kuka, daidai lokacin Principal da Deedat suka kunno kai. Da sauri ya saki hannun, gaba daya suka yi tsuru-tsuru.
Wata uwar tsawa Principal ya daka musu, ta sake rushewa da kuka, Principal ya yi matukar tsorata a yadda ya ga kamannin Deedat sun sauya.
“Ina iyakacin kokarina ban san ta ya ya ake samun irin haka ba. ban taba cin karo da wannan matsalar ba, dole ne ku cancanci hukunci mai tsauri. Sai kun gwammace ba ku taba yin makaranta ba”.
Deedat hankalinsa na ga Nurat, tabbas ita ce yarinyar dazu, duk ya ji tausayinta.
Principal ya kira Displine master a waya, ba a wuce minti biyu ba sai ga shi. Ya umarce su da ya yi ofis da su Abdul ya yi musu horon da ba a taba yi wa wani dalibi ba. daga nan ya sanar da assambly din gaggawa. A nan din ma a hukunta su, daga nan a kore su ga iyayensu, kora na har abada.
Su Faisal sun isa cikin samari amma hakan bai hana su kokawa ba, tare da ban hakuri, musamman yadda suka rigaya suka san muguntar Displine master a lafiya ma yana mugunta ballantana wannan ganga-gangan laifin. Yau ne karo na farko da suka taba yin da na sani a irin kura-kuran da suke tafkawa, shi kam deedat duk hakan bai burge shi ba, ya fusata sosai, inda ya danganta laifin ga Principal.
Fuu! Ya yi waje, da sauri ya rufa masa baya cike da zullumi.
Can cikin ofis Deedat ya rikicewa Principal, ta inda yake tuhumarsa. Rantsuwa ya dinga yi yana yi masa magiya da ban hakuri, gaba daya ya gama jikewa sharkaf da gumi.
“Dole ne ka zamo jajirtacce, na tsorata da al’amarin nan, idan ita yarinyar ta sanar wa da iyayenta da me za mu kare kanmu? Wannan sakacin zai iya janyowa a rufe makarantar baki daya, ka sani rufewar ba zai dame ni ba, kamar yadda talakawan da suke more za su dame ni”.
Cikin muryar lallashi Principal ke fadin, “Zan sanya idanu, hakan ba za ta sake faruwa ba”.
Malama Aisha ce ta turo kai, inda ya umarce ta da ta kira Nurat. Shi kam Deedat ya shiga kai-komo, al’amarin ya gigita shi. Shesshekar Nurat ya tabbatar masa da sun karaso.
“Principal me ke faruwa da Nurat haka, na ga yarinyar ta shiga rudani da yawa”.
Principal ya dubi Nurat.
“Ko dai sun yi miki wani abin ne bayan abin da idanunmu suka gane mana?”
Fir! Ta ki magana.
“Ita ya kamata ta jata ta tambaye ta”. Deedat ya fada, Kamar abokin naka ya san halinta, kodayake kila kanwarka ce, Nurat akwai kunya. Principal ya dan ja ta gefe ya shaida mata abin da ya faru. Malama Aisha ta nufi ofis dinsu da ita, inda ta dinga tambayarta cikin dubara.
Da kyar ta iya budar baki cikin shesshekar kuka.
“Ammina ta ce duk lokacin da na bari namiji ya taba mini hannu, ciki zan samu, in…”
Daidai lokacin Principal da Deedat suka kutso kai cikin ofis din nata. Deedat ya kasa jurewa shi ya sa ya azalzali da a biyo sahu. Ganinsu ya sa Nurat tsuke baki.
“Ke nake saurare Nurat, ba komai ki yi magana kin ji”.
Kawai Nurat ta yi kasa da kanta.
“Ummi ta ce, duk lokacin da na bari namiji ya taba min hannu zan samu ciki in haifi shege, idan na haifi shege mutuwa za ta yi, kuma su… su… sun taban hannu…”
Ta karasa cikin saka gursheken kuka.
Deedat ya harba cikin tunani, gaba daya jikinsa ya hau tsuma, wani irin tsoro ya ziyarci zuciyarsa tare da wani irin abu wanda ya kasa tantance ko me ye.
“Amma wannan zancen banza ne ta ya za a dora ki a kan wan…”
Deedat ya yi saurin dakatar da Malama Aisha, “Haka ne, Ammi ta yi gaskiya, ai na ga hannunsu bai taba naki ba sosai, yanzu za mu je asibiti in har da cikin za su gaya mana. Ki daina kuka kin ji ko”.
“Ina jin tsoro, za ta gane hakan ta faru, bana son na samu shege kowa zai tsane ni, bana son samun dan da ba shi da tsarki”.
Ba ya son jin kalamanta, da sauri ya yi waje, idanuwa sun sake rinewa, “Za mu je asibiti”. Ya fada lokacin da ya bar ofis din.
A can harabar makarantar Doctor Salim amininsa ya kira inda a takaice ya ba shi labarin abin da ke faruwa, tare da sanar da shi ga shi nan tafe, yana kuma son a yi mata duk abin da zai sa ta samu nutsuwa. Ya yi saurin katse wayar daidai lokacin da Principal ya yi parking din mota a gabanshi. A can baya ya hangi Nurat gidan gaba ya shiga, yana gano yadda hawaye suke faman tsinkowa daga idanun Nurat. Ya yi saurin kawar da ido, yayin da gabansa ya dinga dukan uku-uku, yarinya ce karama, sai dai akwai ta da kwarjini. Lokaci-lokaci ya dinga satar kallonta har suka isa asibitin.
Abin da ya bai wa Nurat mamaki, yadda sunan makarantar da na asibitin suka zamo daya.
Dr. Samir sun tsara komai da Nurse kafin su karaso, sirinji ya dauka ya yi umarnin da ta miko hannunta zai dauki jini domin gwaji. Nan fa idanunta suka yo waje, ji ta ke kamar ta sa gudu, sai ga wasu sababbin hawayen.
Dr. Samir babu wani abin da za a yi, maimakon daukar jinin?” Deedat ya fada.
“Dole dai sai dai jinin”.
Babu yadda ta iya haka ta runtse ido, ya shiga shirin zuko jinin, inda Deedat ya dauko wayarsa a fakaice ya shiga daukarta ta yadda babu mai lura da abin da yake yi.
Bayan an gama Nurse ta yi wani daki da jinin, sun zauna sai ga sakamako ta shigo da shi. Ta mika wa Dr. Salim, ya duba cikin gintse dariya a ciki, saboda yadda ya ga alamun tsoro karara a idanun Nurat, sai da ya dan yi ‘yan rubuce-rubuce sannan ya sake dago kai cikin dubanta. Idanun nan sun yi luhu-luhu saboda kuka, tana jin kamar ta matsi bakinsa ya yi magana, Deedat kam yana iya jin bugun zuciyarta na tsananta, da yake shi ne a kusa da ita.
“Ina taya ki murna dalibar kirki, ba ki da matsala”.
Cike da farin ciki ta sake wani irin murmushi, dukan kumatunta suka lotsa. Wani irin wushirya mai daukar hankali suka bayyana. Da sauri Deedat ya shiga daukarta.
“Doctor na gode”. Ta ce.
Ya mika mata ambulan, “Doctor na bar maka”.
Ya yi murmushi.
“Ki dai tafi da shi”.
Ta karba.
“Abu na gaba ina son kada wannan maganar ta fita ko a gida kada ki fada kin ji ko?”
“Insha Allahu babu wanda zai ji”.
Cikin farin diki ta ke magana.
Deedat ya shiga duniyar tunani, yana tunanin a inda ya san wannan muryar, sai dai duk iya yinsa haka ya hakura.
Sai da Principal ya sanya ta a mota aka maida ita makaranta, sannan ya dawo ofis din Dr. Samir inda kowa ke fadin albarkacin bakinsa a kan al’amarin Nurat.
“Hakan na da kyau, ban yi tunanin akwai irin wadannan iyaye ba. babu wadda ta burge ni sai mahaifiyarta wacce ta dora ta a wannan turba”. In ji Salim.
Principal ya karbe zancen, “Cikin class mate dinta ita ce mafi kankantar shekaru, ga su nan gandama-gandama amma babu wadda ta kai ta kokari. Kwakwalwarta tamkar computer, irinsu ake ma lakabi da gifted. Na dade ban ga yarinya kamarta ba, yadda dalibai da malamai ke kaunarta bai sa ta giggiwa ba, gaba dayanta ma tsoro ne da ita, ba ta shiga cikin mutane sosai. Ba karamin abu ne zai sa ka ji bakinta a class ba, kullum ka ganta wala’Allah a makaranta ko a gida cikin hijabinta zumbulele kamar mai shirin tafiya masallaci. Su kansu malamai mata in sun zauna hirarta suke babu wanda ya taba kawo kararta’.
Haka ya yi ta bada labarinta, har sai da Deedat ya ji a cikin zuciyarsa babu masakar tsinke, bai taba jin yadda yake ji game da ita ba a kan wata mace ba, shin me hakan ke nufi? Me ke shirin faruwa da shi?
“Ammi ta ce duk lokacin da na bari namiji ya taba min hannu zan samu cikin shege, idan na samu cikin shege mutuwa za ta yi”.
Sautin muryarta ya dinga yi masa kuwwa a kunne, ya shiga kai-komo, gaba daya ya kasa samun nutsuwa. Bathroom ya shiga, gaba dayansa ya shige cikin shaya yana jin ko hakan zai saukar masa da nutsuwa. Babu abin da ya ragu, sai ma rikicewa da ya kara yi. Doguwar riga ya saka jallabiya mai yankakken hannu, ya yi zaman dirshan a kan carpet, kuka yake yi kamar karamin yaro. Ya rike kai yana juyawa cikin tafin hannunsa.
“Sun cutar da ni, sun cuce ni”.
Wani irin zazzabi mai zafi ya rufe shi har hakoransa na gwaruwa, barci ya sace shi. A can cikin baccin nasa babu abin da yake gani sai fuskar Nurat.