Tana zaune a farfajiyar gidan rike da littafi a hannu tana karatu. Harde hannu a kirji yana kallonta yana murmushi, bai ki ya tabbata a haka cikin kallon kyakkyawar fuskarta ba.
Jikinta ne ya ba ta akwai mutum tsaye a kanta, ta dan dago kai suka yi ido biyu. Ta yi saurin kawar da kai tare da fadin, “Zauna mana”.
Ta nuna masa kujera.
“Ban ji shigowarka ba”.
Yana murmushi, “kina zaune har na zo na shige na yi ciki, kin ga ke kam idan kina karatu ba kya ji ba kya gani”.
“Yaya Zaruk mun fa kusa fara jarabawa, ina son in karbi kyaututtuka a gurin Dad da Ammi, har ma da Yayata’.
Ya tafa hannu, “Da kyau yarinya mai wayo. To ki kara da tawa, zan yi miki kyautar da babu wanda zai yi miki irinta”.
Ta yi murmushi, cikin satar kallonsa.
“To, yanzu dan gaya mini kalar kyautar”.
“No, ki dai bari zan ba ki mamaki”.
“Allah ya nuna mana lokacin”.
Ta dan yi shiru tana tunanin wani abu.
“Wannan yarinya akwai magana a bakinki”.
“Yaya Zaruk inda a ce kowa zai rike kyautarsa a yi mini alkawarin auren Yaya Aazeen, zan fi jin dadin haka fiye da komai”.
“Har yanzu ba ki bar wannan zancen ba? na ce da ke shi aure lokaci ne da zarar lokacin ya zo komai zai zamo labari”.
“Amma Yaya Zaruk Yayata ba ta rasa masoya ba, girman kanta ne ya rasa masoyan nata su tarke ta. Ka sani kuma ba ta da kirki kamar ba ‘yar gidan nan ba”.
“Ki bar ni da ita, ni ne nan zan yi mata miji, kuma ko ba ta so zan sa ta aure…”
Zumbur! Kamar wadda aka tsikara, “Yayana!”
“Na’am, kanwas?”
Ta gyara zama cikin muryar rada, “Ashe kenan za ka iya taimaka mini na yi wa Yaya Aazeen miji?”
“Kina nufin ke za ki samo mata wanda za ta aura? To ta ya ya?”
“Mun hadu da shi ne ta sanadiyyar saba lamba, sau tari ina karbar wayar Yaya Aazeen na yi game ko na kira kawayena. Rannan na karbi wayar na sanya lambar kawata Hasina, ina kira aka dauki wayar, maimakon in ji muryarta sai na ji muryar namiji. Da farko na zaci yayanta ne, na ce da shi ina neman Hasina, sai ya ce ba ta nan. Hasina kawata ce sosai, sun tashi sun koma Lagos, na dade ina neman layinta tun daga ranar na dinga bibiyar layin mutumin, ya iya magana, ba shi da wulakanci, yana da tsananin hakuri”.
Kawai Zaruk ya dinga binta da kallo.
“Mutumin da ba ki sani ba, ta ya ya ki ka iya dorar da halayyarsa?”
“Saboda a lokacin da na fahimci raina min hankali yake yi raina ya baci, na kasa tankwara zuciyata, na yi ta jifarsa da magana”.
Zaruk ya watsa mata harara.
“Ke din har wani iya magana ki ka yi? Yaushe ne ma ki ka koyi magana?”
“Allah da gaske nake yi, ita magana zuwa ta ke yi. Ya ci gaba da hadiye duk wasu kalamaina, sannu a hankali muka fara sabawa da shi, idan ban kira shi ba na kan dinga jin kamar na rasa wani abu muhimmi. Bana son a ce zumuncinmu ya sha ruwa, ina ji a jikina yayata za ta so shi da zarar sun hadu sai dai idan na tuna ba shi ne irin mijin da ta ke mafarkin samu ba, ina jin tsoro, domin na fahimci shi din ba wani mai karfi ba ne”.
Gaba daya ta dage sai zuba ta ke yi, tunda suke da ita bai taba sanin tana da magana haka ba, maganganunta yana jin zubarsu tamkar yayyafin wuta. Kullum idan ya yi magana sai a ce masa nawa ta ke? Ga shi ya yi sake har son wani ya shige ta. Ya sauke ajiyar zuciya.
“To ta ya ya za ki hada wannan soyayyar?”
“Ina son tafiyata da shi ta sauya salo”.
“Ban fahimta ba”.
“Na ce da shi sunana Aazeen, ina amfani da komai na Yayata a zuwan ni din Aazeen ce, hakan ya yi?”
Kawai jinjina mata kai yake yi.
“Amma ya ya Zaruk ka san me? Ya ki cewa yana sona, ina son in tursasa masa furta hakan”.
“To idan ya ki fa?”
“Yanzu Yaya Zaruk koya min za ka yi”.
Ji ya yi kamar ya tsinka mata mari, dole ya danne zuciyarsa, murya sama-sama, ‘Ke din fa mace ce”.
Da sauri ta katse shi, “No, cewa za ka yi ita din fa mace ce”.
Tilas ya bi yadda ta ke so.
“Ok, na ji ita din fa mace ce, duk inda mace ta ke ana son ta darajja kanta, ki ci gaba da bi da shi a hankali, zai yi yadda ki ke so din. Amma ya kamata ki ba ni lambarsa…”
Da sauri ta katse shi, “No, ba yanzu ba, idan komai ya yi daidai kai kanka sai ka fi samun kwarin gwiwar kiransa”.
Mikewa ya yi, “Ok, ba matsala”.
Ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba, wannan yanayi da ya shiga ya kamata ta iya fahimta, sai dai ko kadan ba ta kawo komai ba, asalima dadi ta ke ji tana ganin kamar ya ba ta kwarin gwiwa ne.
A wannan dare Zaruk ya kasa bacci, yana ta juye-juye a gado, son Nurat kullum karuwa yake yi a ransa, musamman yanzu da komai nata ya bayyana. Nurat yarinya ce mai sanyin hali da son mutane, tana da shiga rai, tana da surutu amma ga wadanda ta saba da su, domin sam ba ta da saurin sabo, idan ta ga dama sai ka rantse ba ta magana saboda yanayinta mai sanyi ne. Akwai ta da tsoro, daya daga cikin abin da ta tsana shi ne mu’amala da maza, duk yadda suke da namiji ta kan yi dari-dari da shi.
Nurat mai kyau ce, sai dai ba kowa ke gane hakan ba, dalilin kwalliya ba ta dame ta ba, ba ta saka damammun kaya kullum cikin hijabi, ko da a gida ne in ta yi wanka ko hoda ba ta damu da ta saka ba, ballantana kwalli. Ba za a kira ta da baka ba, ba kuma za a ce da ita fara tas ba, idan ta tsaya a kusa da bakin mutum lokaci daya za ka iya ce mata fara, sai dai idan ta tsaya a kusa da fari. Kalarta na daukar hankali, ita ba golden ba, ita ba choculate ba, abin da ya fi komai daukar hankali a tare da ita shi ne diri, duk yadda ake son mace ta kai, tana da wushirya, muryarta a dan dashe ta ke, dambareren bakin da ke kwance a goshinta, wanda ake wa lakabi da tabon sallah ya yi matukar kara mata kwarjini da kyau. Idanunta manya farare kwal, gashin girarta a hade da dan uwansa. Abin da Nurat ta fi so a rayuwarta shi ne, Aazeen, tana matukar kaunar ‘yar uwar tata.
Ya mike zaune, “Kina kaunar Yayarki, da ita za mu yake ki. Aazeen tawa ce, sai yadda na tsara mata”.
*** *** ***
“Yaya Aazeen ana kiranki a waya fa”.
Sai da ta maimaita fada kusan sau uku, sannan Aazeen ta yi firgigt.
“Mtsew! Kyale su”.
“Yaya Aazeen ba ki da lafiya ne?”
“Ina cikin damuwa ne kawai Nurat, tunanina da hankali gaba daya sun koma ga mutumin nan, ina ji a jikina tamkar zai kusanto ni. Ina ji tamkar shi ne mijina, ban san shi ba amma kullum sai ya zo min cikin mafarkina. Wannan karon ne kadai wani abun ke neman fin karfina, amma ban taba neman abu na rasa ba, sai ya zamo mallakina ko da hakan zai zamo sanadiyyar rasa komai nawa”.
“Yaya Aazeen komai naki fa ki ka ce?”
“Eh mana, ban da abinki idan na rasa komai shi ne zai dawo min da ninkinsa. Ba ki san matsayinsa ba ne, har ma fa ya fi shugaban kasa kudi”.
“To idan bai zama yadda ki ke so ba fa?”
“Kin ga Nurat, muddin yana da kudi ko ya dai yake zan yi maleji, ai ba daure shi zan yi a kafa ina yawo da shi ba”.
“To idan ki ka samu wanda ki ke so ba”.
Ta kai mata dukan wasa, “Allah ba zai sa in kamu da soyayyar wani ba, wannan zuciyar ba ta san so ba sai jin dadi da holewa, gwara ma idan na samu mai kyau na dinga kare yawa in mayar da shi fulawa kawai”.
“Yayata kina son mai kyau’.
“Eh mana, shi ya sa nake matukar sonki”.
Nurat ta yi dariya.
“Yanzu idan ki ka hadu da mai kyau za ki so shi?”
“Mai zai hana?”
Wani dadi ya kama Nurat, tabbas hakanta zai cimma ruwa, ta fara samun yadda za ta billowa lamarin, ba za ta bari shakuwa da Adamu ya tashi a banza ba, sai sun zamo daya.
Ji ta yi an zunguro ta. Ido biyu ta yi da Aazeen, Aazeen ta kanne mata ido daya.
“Tunanin me ki ke yi? Gaya min, ko kin kamu ne?”
Ta yi murmushi, “Haba ‘yar maniniyata, kawai kina maganar maikyau na tuna da wani, ni ban ma taba ganin mai kyawunsa ba, za ku dace da shi”.
Tsaki Aazeen ta ja daidai lokacin wayarta ta sake daukar ruri, ta mike tana fadin, “Ke kin cika shirme’. Daki ta shige.
Zuciyarsa tamkar ta faso kirji, son Nurat na neman halaka shi ta ina zai fara? Ya zai yi? Da sauri ya fito a dakinsa. Zainab matar yayansa na zaune a babban sitroom rike da waya a hannu tana game. Kawai ya zube a kujera, ta dan dube shi, yadda yake ta faman huci.
“Man, waye ya taba mana kai?”
Kansa a kasa bai ce da ita komai ba, za ta sake yin magana ya yi saurin katse ta.
“Ban san haka nake sonta ba, ta yi tasiri a zuciyata, ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba. lokaci ya yi da zan tinkari su Papa da maganar kada na mutu”.
‘Duk ita kadai? Wace wannan haka?”
Ya furzar da huci.
“Nurat! Ina sonta, ina matukar sonta. Ina jinta tamkar numfashina, ina jinta a can karkashin zuciyata’.
Ta yi murmushi cikin sigar wasa ta dungure mishi kai.
“Da Allah can, sunan wacce ka ke ihun ita ce ruhinka ka mance Aazeen za ka ce”.
“Oh God! Kina tunanin mantuwa na yi? Nurat wadda na debi shekaru ina dakon sonta, Nurat ita din dai nake nufi”.
Ido bude ta ke dubansa.
“Allah ba zai yi ma Nurat haka ba”.
A zahiri ta yi murmushi, “Haba dai, me za ka yi da wannan ‘yar mutsilar yarinyar da ba ta gama sanin ciwon kanta ba? Aazeen din dai. Aazeen ita ce wadda za ku yi matching, gogaggiya kamar kai. Amma Nurat is too younger…”
“Stop Aunt! Kawai ki fito ki ce ni din ban cancanci zama mijinta ba, saboda ni ban da kirki, ni ba na kwarai ba ne. To ina son ki sani zan sauya, zan iya yin komai a kan in mallake ta”.
Ta karyar da murya, “No, ba fa nufina kenan ba. Wai ni ina son in ce karama ce ita”.
Tsaki ya ja ya mike yana jin iya ci gaba da tsayuwa a gurinta zai iya marinta. Juyowa ya yi ya dube ta da idanun nan jajir, haka ne ya sa ta shiga hankalinta.
Ya tarar wayarsa na faman ruri, lambar Aazeen ya gani, da sauri ya dauka. Muryar Nurat din ce ta ratsa kunnuwansa, wata irin ajiyar zuciya ya sauke.
“Yaya Zaruk”. Ta kira sunansa a can bangarenta, ta kuma rasa da me za ta fara, don haka ta yi shiru.
Ya katse shirun da fadin, “Gaya min, kina son ganina ne?” Ya fada yana mai rokon Allah ya sanya ita ma ta jarabtu da sonsa.
“Nurat, gaya mini kada ki damu, kin ji?”
“Um-um… da man ce maka zan yi ina son kiran Adamu jiya mun fara hira da Yaya Aazeen, sai nake jin kamar zan dace, za ta iya amincewa”.
Ya cije lebe, ji ya yi kamar wani tsini ya soke shi. Da kyar ya danne zuciyarsa.
“Ya kamata ki fara shawo kanta kafin ki jajibo shi”.
“Ai na ce da kai ta fara amincewa”.
“To shi kenan, ki bari gobe in na zo sai mu ga ya za mu yi”.
Ta yi murmushi mai sauti. Ba ta sake jiran me zai ce ba ta yi saurin katse wayar.
Ciki ya yi da wayar ya rike kai yana faman huci.
“Zan nemo shi, ba zan amince ba. zan yi wani abu a kai, bana tsoron duk abin da zai faru. I don’t care, zan gaya ma Papana dole ne in tabbatar da za ki zamo tawa, kina wasa da rayuwa ta, ba zan taba amincewa da wannan ba, kullum ana raina min hankali da fadin ke din karama ce, da zarar na taso sai a dankwafe ni, an bar zuciyata da masifa, shekara da shekaru ina azabtuwa. Wallahi na yi alkawari ko kallonki wani ya yi da zummar so sai na batar da shi, bana tsoro, ba zan daga kafa ba, dole ne ki zamo tawa. Ni ne kadai na san muhimmancinki ba zan yarda ba, ina! Haka ba za ta taba yiwuwa ba, kai din ma sai na gano ko kai waye na sani duk da ba ka santa ba da zarar ka dora ido a kanta ba za ka barta ba”.