Skip to content
Part 6 of 10 in the Series Kyautar Zuciya by Bilkisu h muhd

Ya ci gaba da sambatunsa kamar wani tababbe ko karamin yaro.

Idan ta tuno hirarsu da Aazeen duk sai dadi ya kamata, yanzu ta ina za ta fara? Ta yi shiru cikin tunani. Ta yi murmushi, me ya sa ta damu da yawa? Me ya sa zuciyarta ta nace da son hada dangantaka da Adamu?

Ta gyara zamanta, “Kila shi ne sanadin gyaruwarta, sai kun hadu zai gane wace ke na sani, ba zai guje ki ba a lokacin da ya san halayyarki, don haka nake son in kama zuciyarsa da zummar ke ce, kuma ai ni ma mace ce, zan iya har ma sai na jira Yaya Zaruk ya koyar da ni, mutumin da yake ta faman ja min rai? Zan ba shi mamaki, sai dai kawai ya ji ana yi”.

Ta mike tsaye ta shiga zaryar yadda za a yi ta sato wayar Aazeen.

Da sauri ta yi sitroom inda ta riski Aazeen zaune sanye da wasu makalallun kaya, ta dora kafa daya kan daya cikin duba nobel book.

“Yayata, ko za ki ba ni wayarki zan kira Aisha?”

Ba ta yi magana ba, kawai ta yi mata nuni da wayar. Da sauri ta dauka ta koma daki. Sai da ta kulle ta murda key ta koma ta zauna a kan gado.

“Ke ce kuwa?”

“Mai ka gani?”

“Ba ki saba kira a irin wannan lokacin ba shi ya sa nake jin kamar ba ke ba ce”.

“Ni kaina ban san lokacin da na kira ba, kawai ina wasa da wayar na ga kawai hannuna ya kai ga lambarka’.

“Amma kuma kin taba ce min ba ki yi sabing ba…”

“Uhum”. Kawai ta yi.

“Lallai na kara matsayi, na ji dadin haka kanwata”.

“Ai da ma kana da matsayi”.

“Ok, yanzu ba ni labari”.

Ta dan yi jim kamar ba ta kan wayar.

“Labari sai dai kai, ni da kullum ke kulle a cikin gida… amma dai yanzu gaya min yaushe zan ganka?”

Ya yi ajiyar zuciya, “Saura kiris na zo, to amma idan na zo gurin wa zan ce na zo in na tura kiranki, ke kuma wa za ki ce ya zo?”

Ta yi shiru.

“Sai ki ce abokinki ne?”

“Kai ai namiji ne, ba zai yiwu ba’.

“Ok, to za ki ce saurayinki ne ya zo?”

Nan ma ba ta iya magana ba. kokarin share caftar ya yi, ta yi saurin dawo da zancen.

“Da gaske ni din budurwarka ce, kana sona kenan?”

Ya yi murmushi yana jin dadin yadda yake zolayarta.

“Ina sonki mana”.

Da sauri ta katse wayar ta yi ciki da shi. Ta yi rigingine a gado hadi da runtse ido kawai, kunyar kanta ta ke ji. Ji ta ke yi kamar ta aikata babban zunubi, amma a can karkashin zuciyarta wani irin nishadi ta ke ji, ko me hakan ke nufi?

*** *** ***

“Ji yadda duk ki ka tada hankali kamar wadda ki ka aiki jaririya, wai ke ba kya ganin yadda hadari ya hado, ga gari ya yi bakikirin? Ni ba abin da ke tayar min da hankali irin iskar da ke tasowa, kin san Nurat da tsoro, na sani duk inda ta ke tana cikin rudu. Na kira Hajiya Fati ta ce tun dazu ta fita a gidan, sai yanzu nake jin haushin rashin waya a hannunta, da sai mu kira ta”.

Shewa Aazeen ta yi ta karaso gaban Amminta tare da rungumo ta ta baya.

“Dube ki don Allah, inda a ce ni ce da yanzu kina nan hankalinki a kwance, da yanzu ma kina bacci, amma dai ki kwantar da hankalinki ‘yarki na da wayo, za ta dawo lafiya kin ji Amminmu, kuma na yi miki alkawari da kaina zan siya mata waya”.

Daga can bangaren Nurat hankalinta ya yi kololuwar tashi, musamman yadda ta ji ana ta tsawa gaba daya a kankame ta ke tafiya, cikin sharar kwalla duk motar da ta tsayar kko kallonta ba su yi. Tasowar iska ya tsananta sanadiyyar haka aka dauke wuta, gari ya soma duhu, jama’a sai gudu ake. Cikin lokaci kankani ruwan sama mai karfi ya sauko hadi da walkiya.

A hankali yake tafiya saboda kada ya haifarwa kansa matsala, lokaci daya ya dallaro fitila ya yi arba da fuskar Nurat. Dam! Ya ji gabansa ya buga, sauran kiris ya saki sitiyari. Ya sake rage gudu, ya san rasa mota ta yi a daidai gabanta ya yi parking, bai fito ba bai kuma kashe motar ba, tunaninsa za ta doso shi don neman taimako, maimakon haka gani ya yi tana neman kwasa da gudu, haka ne ya sa ya tada motar. Gabanta ya sha ya sake tsayawa, ta yi saurin kauce wa motar. Bai sake mamaki ba in ya yi la’akari a abin da ya faru a makaranta, dole ya yanke shawarar yi mata magana. Kashe motar ya yi ya fito cikin sauri ya karasa ya sha gabanta. Ta tsaya kyam kanta a kasa, jikinta na rawa.

“Ki shigo mota in kai ki”.

Ta yi saurin kada kai cikin tunanin inda ta san wannan muryar.

A hankali ta dago kaiza ta saci kallonsa, aka yi sa;a gari ya haska da walkiya idanunsu suka gauraya da juna. Gaba daya Deedat ya kidime wani irin bugawa gabansa ke yi, shin wace irin yarinya ce wannan wadda yake jin abin da bai taba ji ga wata mace ba a yayin da ya dora ido a kanta, ko da kuwa a hoto ne tana yi masa kwarjini, ji yake yi ma kamar yana tsoronta, ita ma din ta gane shi.

Abokin Principal din sune sai dai haka ba zai sa ta shiga motarsa ba, ko da hakan na nufin za ta kwana tana tafe a kasa ne.

Ya sanyaya murya, “Ke fa dalibar abokina ce, na san kin gane ni, ba zan cutar da ke ba”.

“Ka yi hakuri na gode”.

Yadda ya lura da ita ya sani ba za ta taba shiga ba, ga dare na dada yi, ya dan kausasa murya wai ko da za ta ji tsoro.

‘Ki shiga na ce!”

Ta raunana murya kamar za ta rushe da kuka.

“Allah ba zan shiga ba”.

Takaici ya sanya ya shige motar, ya murda key, amman ya kasa tafiya. Wayarsa ya dauko ya shiga kiran daya daga cikin masu adaidaita sahunsa tare da yi masa kwatancen inda ta ke.

Bai bar gurin ba, har sai da ya tabbatar an dauke ta tukunna ya samu nutsuwa.

*****

“Ammi ga ‘yar mitsilanki nan ta dawo ba a cinye ta ba”.

“Za ki ci gidanku, ce miki na yi ba za ta dawo ba?”

Aazeen tana dariya, “Kin ga wannan Umman taki gaba daya ta sukurkurce kamar ce mata aka yi an sace ki”.

“Ai ko ba don wani abokin Principal ya yi gadina ba da yanzu na sume a gurin, don ba kowa a gurin, ya yi ta nacin in shiga motar ya kawo ni, na ki shiga, har sai da na samu adaidaita”.

“Kin yi daidai”.

“Ammi, haka ne daidai? Inda ba ta samu abin hawa ba fa?”

“Na ma san Allah ba zai sa hakan ta faru ba”.

Yana gaisawa da Hajiya Rahma idanunsa na yawo, yana tsammanin ganin Nurat. Ya numfasa, “Ba kowa a gidan ne sai ke kadai?”

“Mutuniyarka na daki bacci ta ke yi, ba ta da lafiya, ita kuma Aazeen na shashenta”.

Ya mike, “Bari in je mu gaisa”.

“To”. Ta ce da shi.

Ta mike a doguwar kujera tana jin kida.

Ta fadada fara’arta, “Yanzu nake shirin kiranka”.

“Kirana? Kina da magana kenan?”

Ta kada kai, ‘Kawai kewarka na ke yi”.

“Sai ga ni na zo ba, amma ni ma tawa ce ta kawo ni’.

Ta mike zaune cingam ta dauka a kan table ta bare tare da cillawa a baki, ta tauna, ta yi kwai hade da yin kas-kas ta koma ta tattara hankalinta kanshi.

“Ina sauraronka”.

Ya zauna kusa da ita, ya marairace kamar mai shirin yin kuka.

“Na kasa jurewa, ba zan iya ba”.

Ta bi shi da kallo, ‘Wai me ke faruwa?”

“Ina son Nurat, lokaci ya yi da zan furta mata. Rashin furtawa a wanan lokaci zai iya haifar da komai”.

Tuntsirewa ta yi da dariya, har da kyakyatawa.

Ya kulu sosai, mikewa ya yi zai fita, ta sha gabansa ta kama hannunsa ta zaunar da shi.

“Afuwan, mu yi magana, amma ranka ya dade ka rasa wadda za ka zaba ta zame maka mata sai kwaila, kuma ma wacce ba ta waye ba? kuma wai har ma ka dubi idanuna ka ce kana son kanwata? To wai ma gaya min da me na rage ka?”

Ya watsa mata harara, “Ok, haka ki ke son na yi ta zama babu aure ko?”

“Why not, yanzun da me na rage ka ko kana son ka ce ni din na gundire ka?”

“Kin ga Rangida wannan daban ne, kin san kamalar mutum shi ne aure ko?”

“Na ji wannan, amma me ya sa ba za ka samu gogaggiya irinka ba? Ka san Nurat karama ce ba za ka samu yadda ka ke so daga gare ta ba”.

“Kin ga Rangida kada ki ce kishi ki ke da ita?”

Ta ja wani dogon tsaki.

“Matar arziki ma ban yi kishi da su ba sai wannan? Kawai dai ina tsoron alakarka da ita kada ka lalube mini ita’.

“Kin ga ki ajiye zancen wasa ju tausaya mini ki gaya min ya zan yi, ta ina zan fara?”

Ta lakuce masa hanci, “Dube shi don Allah ko kunyata ba ya ji. Ka ga shawarata ka bi a hankali, muddin ka kuskura gurin furta mata kalmar so, kai da ita, kun soma wasan buya kenan in ma ba ka yi sa’a ba kun kulla gaba kenan don haka ka bi a sannu cikin dabara za ka fahimtar da ita a aikace”.

Ya mike ya shiga zarya.

“Nurat, ban ga damar canza ta ba ne yarinyar bagidajiya ce amma ka ban lokaci, da sannu zan fahimtar da ita abin da duniya take ci….”

“Ban amince ba”. Ya yi saurin katse ta cikin gigita, “Ni rayuwarta ta yi min a haka nake son rayuwa da ita”.

Ya koma ya zauna cike da tsananin tsoro “Come down, abokina, kana tsoro ko, amman ba ka tabbatar ita din matarka ba ce ballantana ka…”

Turo kofar da a ka yi ne ya katse daga maganar da take son yi, sanye ta ke da zumbulelen hijab, Aazeen ta saci kallon Zaruk cikin muryar rada.

“Haka din yayi maka ko?”

Ya dan lumshe ido ya bude alamar hakan ya yi masa.

“Yaya Zaruk sannu da zuwa”.

“Yauwa kanwa ta gwara da Allah ya kawo ki, daman ya dame ni da surutu”.

Shigar jikinta ya sanya Nurat jin kunyar Zaruk, three kuater a jikinta na wando, sai riga plat, kan nan ya sha attach, ta lura da yadda Zaruk ke faman satar kallonta. Yana ji tamkar ya bi ta.

“Ya Zaruk me ya sa ba ka yi mata fada na ga kamar tana jin maganarka”.

Ya maida kallonsa gare ta, “A kan me fa?

“A kan me? Ba ka ganin yadda ta ari al’adar da ta saba wa addininmu na islama?”

“Kada ki damu da hakan, ra’ayinta ne haka, wataran za ta daina da zarar ta shiga daga ciki shi kenan komai zai sauya, kamar ba a yi ba, kin ji?”

A hankali ta rausayar da kai.

“Haka ne Yaya Zaruk, Allah ya nuna mana lokacin”.

Wani mayen kallo ya dinga bin ta da shi har sai da ta tsargu.

Ya yi murmushi, “Ba kya son kallo da yawa ko? Ki yi hakuri kanwata, kina da kyau da yawa. Ban gajiya da kallonki, da ma a ce mu dauwama a haka”.

Ta dan murmusa, “Yaya Zaruk ka iya zolaya”.

Ya sake rike haba cikin kallonta.

“Murmushi na yi miki kyau, ina ma kada ki daina?”

“Yau ka zo ne musamman don ka tsokane ni ko? Ka san wani abu?”

Haka kawai ya ji zuciyarsa ta buga.

“Sai kin fada”.

“Ammina tana son Yayata ta yi aure, na ga kai ma ka fada idan ta yi aure za ta daina duk wadannan abubuwan shi ya sa nake ta neman taimakonka”.

“Shi ya sa na ce ki ba ni lambar mutumin nan”. Ya katse ta da fadin haja.

“Na san yadda zan bi in daidaita komai”.

“Ba ka sani ba, komai ya daidaita har na zurmo shi da bakinsa ya furta cewar yana sona”.

Lokaci daya ya firgice duk walwalar fuskarsa ta dusashe, cikin shakakkiyar murya ya soma magana, “Kina son ki ce kin zubar da kimarki gurin rokonshi ya so ki ko? Nurat kin hauka ce? Me ya sa ki ka fitini kanki da yawa a kan wannan? Ki gaya min ki ke sonsa ko? Ki gaya min gaskiya”.

Ta tsorata da sauyawarshi.

“Yaya Zaruk ni in ce ina sonsa? Wace irin magana ka ke yi haka?”

“Shiru! Na ce ki rufe min baki, ni za ki raina ma hankali? Ni za ki yi wa haka?”

A zahiri ta gama tsorata ba ta taba ganinshi cikin irin wannan yanayin ba, gani ta yi ya mike a zafafe ya fice ya turo kofa da karfi har sai da ta firgita, kawai ta bi shi da kallo, ta rasa me hakan ke nufi.

Ta sauke ajiyar zuciya, a sanyaye ta mike ta yi waje.

A harabar gidan ta samu Ammi zaune tana alwala, Aazeen na kokarin ficewa.

“A’a sai yanzu ki ka bar Ya Zaruk ya tafi?” Aazeen ta fada.

Nurat ta daure fuska.

Aazeen ta maida kallonta ga Ammi tana fadin, “Ammi da alamun tuwona maina za mu yi”.

“Ammi kina jinta ko? Wallahi za ta sa na daina kula shi”.

“Me ya yi zafi? Allah ya ba ki hakuri, ai shi din Yayanki ne”. ammi ta ce tana murmushi.

“To ai Ammi shi ma babu abin da zai yi da kwaila”.

“Eh din na ji”. Nurat ta fada a kufule kamar za ta yi kuka.

Binshi kawai ta ke da kallo, yadda ta ga yana faman dudduba ko’ina na gidan.

“Yallabai lafiya kuwa?”

“Ina duba ta inda zan fara ne”.

“Me za ka fara?”

“Rangida za ta yi manyan baki daga Jos, tana bukatar a yi wa gidan kwaskwarima”.

Ta jinjina kai cike da takaici.

Ya janyo kujera kusa da ita ya zauna, ta dube shi cikin sanyin murya, ya fahimci haka, “Da magana ne?”

“Ina ganin bai dace a ce ‘yar da muka haifa ta dinga tsara mana abin da za mu yi ba, hatta da girki sai wanda ta ke so ake yi? Ya kamata ka yi nazari watarana fa gidan wani za ta je, za ta iya rayuwa da kishiya ko uwar miji, kana ganin za su dauki wannan? Waye zai iya zama da ita da wannan dabi’un? Ya kamata ka duba ka koma ka sauke ta daga wannan layin ya kamata  Aazeen ta san rayuwa, sangartar nata ya yi yawa, rayuwa na iya juyawa a kowane lokaci bana fata, amma…”

Ya yi saurin katse ta, “Ba za ta taba ganin duhu a rayuwarta idan kina tunanin gidan aurenta ne, su kansu mazan yanzu har da iyayen nasu duniya suke bi, idan za ta ce mijinta ya durkusa ta hau bayansa ina rantse miki sai ya durkusa”.

“Shi kenan”. Ta ce da shi, ta koma ta tsuke baki.

“Kin yi shiru, ba gaskiya na fada ba ne?”

“A naka ra’ayin ka yi daidai amma don ya kamata a kalla mu koya mata mu’amala yadda za ta jeranto wa wanda ya girme mata magana”.

“Okey, gaya mini wa ya taba kawo kararta? A kunnena ina jin yadda ake yaba mata, ba ta taba yin ba daidai ba”.

Ta mike cikin kokarin barin gurin, ta dan dube shi a kufule.

“A ganinka ba…”

Kan ya kai ga magana ta yi saurin barin gurin.

*****

<< Kyautar Zuciya 5Kyautar Zuciya 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×