Skip to content
Part 7 of 10 in the Series Kyautar Zuciya by Bilkisu h muhd

Da murnarta ta danno kai hotel din har zuwa dakin da yake, yana tsaye ya juya baya da gudu ta rungumo shi ta baya, ta dade a haka ba tare da ya tanka mata ba. Ta sake shi ta zagayo gabansa, fuskar nan ta gani a daure.

“Why?”

Ya kamo hannunta suka zauna.

Ya dauki tsawon lokaci kafin ya yi magana, gaba daya ta gama kafe shi da ido, cikin son ji daga gare shi.

Ya furzar da wani huci.

“Ke ce ki ka lalata komai”.

Cike da mamaki ta dube shi.

“Ni kuma? Da na yi me?”

A kufule ya zayyane mata komai, hankalinta ya yi matukar tashi. Ta mike a zuciya, “Zan yi maganinta. Wallahi sai ta gane kurenta”.

Ta nufi hanyar fita, ya yi saurin janyonta ta zube a jikinsa, za ta yi magana ya danna harshensa cikin bakinta. Sun dade a haka, cikin wani irin salo ya janye harshen nasa, sai dai tana manne a jikinsa.

“Ina son mu bi komai a hankali kamar yada ki ka ce yarinya ce za mu bi da ita ta dabara. Ina so ki samu bayanin komai daga bakinta, ina son ki yi mata wayo har ki samo mana lambarsa, inyaso sai ki bar min ragowar aikin, ni na san yadda zan ji da komai”.

“Okey, to shi kenan, ni zan tafi”.

Ya sake kankame ta.

“me ki ke nufi, haka za ki tafi ki bar ni?”

“Na ga kai ma ya ba wannan ce ta kawo ka ba”.

Ya sanyaya murya cikin salon yaudara.

“Kin sani duk yanayin da nake ciki da zarar na ji ki a jikina na kan ji sanyi, bana iya jure rashinki, don Allah kada ki yi min dangwalilliya”.

Ta daddage ta tankada shi, “Ba za ka samu komai ba yau ko da na amince da kai babu abin da zan dorar, ni kuma ba zan yi abin da zai dada dama wani ni na kasa nishadantuwa ba”.

Ta mike yana magana ta yi saurin ficewa a dakin.

Tun daga harabar gidan ta ke faman kwalla mata kira, ba ta ji motsinta ba har ta ratsa sitroom inda ta ga Ammi zaune a kan darduma da alamun sallah ta idar. Ba tare da ta ce komai ba, kodayake matar da ba ta yi sallama ba me za ta iya cewa? Kawao ta bi ta da kallo gurin nema mata shiriya.

A can daki ta tarar da Nurat tana gyaran littattafanta, ba ta saba ganinta cikin wannan yanayin ba, don haka duk ta gama tsorata. Zama ta yi a kan kujera ta dora kafa daya kan daya tana faman hada su, wannan shi ne alamarta duk lokacin da ranta yake a bace haka ne ya sa Nurat ta kara kidimewa, ba karamin abu ne yake sanya ta haka ba. gabanta ya shiga bugawa tsawon mintina uku kamar ba za ta yi magana ba, sai faman huci ta ke.

“Ki gaya min ina son sani da wa ki ke yin waya a cikin waya dina?”

Ta ji tambayar ba-zata, tsananin rudewa ta yi, ji ta yi tamkar numfashinta zai dauke.

“Wayyo Allah”. Ta ce a zuciyarta.

Wata irin tsawa Aazeen ta daka mata.

“ke nake sauraro ki yi min bayani, ko ke kurma ce?”

“Um-um…Aa’, um daman… da man… ba…ba…”

“Wannan wace irin magana ki ke yi haka, munafuka? Za ki bude baki ko sai na yi miki dankaren duka? Shegiya lumbu-lumbu wutar kaikayi, da an yi magana Ammi ta ce ke karama ce, ko ke ustaziyya ce, nan kam ke bakar shaidaniya ce, wallahi in ba ki gaya min gaskiya ba yau sai kin raina kanki”.

Ba ta san sa’adda ta sa kuka ba, cikin shessheka, “Ni ban aikata komai ba, ban yi komai ba”.

“To gaya min yadda aka yi ki ke bin maza a cikin wayata, har kina amfani da sunana ki yi min magana”.

Ta ce cikin daga murya.

‘Wayyo Allah na shiga uku Yayata kada ki yi mini mummunan fahimta. Kada ki zarge ni, don Allah ba zan aikata ba daidai ba, ki yarda da ni”.

“Idan kina son in rufa miki asiri, ki bude baki ki gaya min gaskiya, in ba haka ba sai kin gane shayi ruwa ne”.

Hankalin Nurat ya sake tashi, duk lalacewar Aazeen hakan bai sa Nurat ta raina ta ba, Amminsu ta koyar da ita yadda za ta girmamata. Tana tsoron Aazeen ba ta ajiye mata kara ta tsallake, tana matukar tsoron bacin ranta. Wadannan abubuwa su ke kara dasa wa Aazeen kaunarta, haka ne ya sa ba ta cika takura ta ba, wani fannin tana sane ta ke biye mata su yi ta shirme, duk kuwa da cewar ta bata shekaru takwas.

“Wato soyayya ki ke yi ko? Gaya min me ki ka sani game da so?”

Ta shiga rantse-rantsen cewar ba haka ba ne.

“Ba soyayya ki ke ba, me ki ke yi?”

Gaba daya ta rasa kalmar da za ta kare kanta da shi.

“Okey, to me ki ke yi?”

“Da gaske nake Yaya, ban san me ki ke nufi ba, ban san me soyayyar ba. Ban taba ganinsa ba, ban san yadda ake yi ba, ki yarda da ni kawai dai na saba da shi ne saboda ke…” Ta karasa zancen cikin shakakkiyar murya mai tattare da tsoro cikin kallon Aazeen din.

“Okey, wato kina nufin ke ce za ki aurar da ni kenan?”

Ta shiga sintiri, ta koma ta tsaya.

“Oh ni yanzu kin gama zubda min mutunci kenan?”

Ta kai mata hauri da kafa. Jikin Nurat na krayma.

“Ki yi hakuri, na tuba ba zan sake ba”.

“Sai kin gaya min ta yadda ki ka sanshi, idan ki ka yi min karya sai na gaya wa Ammi na ke wadda kullum ke yi miki kallon yarinya mara wayo”.

Ta sake kidimewa, cikin sarkewar murya ta soma magana.

“Na saba da shi ne ta dalilin mistake din lambar Anisa kawata wadda suka koma Lagos, ta ba ni lambarta shi ne kiran ya shiga wayarsa. Hakan ne ya sa muka saba da shi a dalilin ya ce shi yayanta ne. Na kan kira shi akai-akai ina tambayarsa labarinta, a haka muka saba, sai daga baya ya ce da ni bai ma santa ba. Yana da kirki haka ya sa muka ci gaba da gaisawa…”

“To me ya sa lokacin da ya ce da ke bai santa ba ki ka ci gaba da bibiyarshi? Kuma na duba na ga kaf ke ce kadai ki ke kiranshi, tabbacin shi talakan talas ne?”

Ta runtse ido ta bude, wasu zafafan hawaye suka sulalo kan kuncinta.

“Ban san dalilin da ya sa na ci gaba da kiranshi ba, kuma ban sanshi ba, bai taba ganina ba, sau daya na tura masa da hotonki ta facebook…”

“What? Oh ni! Na shiga uku, ki ce duk kin gama tallata ni, shin Nurat kin gaji da ni? Kin tsane ni ko shi ya sa ki ke son na bar gida ko?”

“Ba haka ba ne, ki yi hakuri. Ina sonki, kada ki yi min mummunar fahimta, na tuba”.

‘To bari ki ji, daga yau kada in sake ganin wayata a hannunki”.

Ta yi waje tana faman huci.

Nurat ta kwanta lamo tana maida numfashi, gaba daya ta dinga jin haushin kanta. Me ya sa ta aikata haka ba ta yi tunani ba? Ba za ta sake ba, ta daina! Daga yau ta tsinke alaka da Adamu, babu ita babu shi, sai dai a kan kanta ta karyata kanta, tana ji ba za ta iya ba.

“Dole ma in iya”. Ta fada a fili, “Ai daman ban sanshi ba, dole ne na cire shi a rayuwarmu”.

Karfe goma sha biyu da rabi na dare tana faman juye-juye a kan gado, tana faman kasa da warwara, ta mike zaune ta rafka tagumi.

“Ko da mutuwa aka yi sabo ake wa kuka, na saba da kai sosai, na dauka komai zai zo da sauki ashe ba haka yake ba? ina ji kamar na rasa abu mai muhimmanci a rayuwa ta, to idan ya daina jina ya zai yi? Na tabbata zai yi kewata, to ya zan yi?”

Ta mike tsaye zumbur.

“Kai ba zan iya ba, ba zan iya tsinke wannan alakar ba, duk me hakan ke nufi? Ba kya jin kunya, to inda a ce Yaya Aazeen ta amince haka za ki ji kenan?” Zuciyarta ke raya mata hakan ta cije lebe a bayyane kamar wata tababbiya, ta budi aki, “Ba don ni nake yi ba, babu shi a raina, kawai ina kaunar kasancewarsu da Yayata. Ina jin tausayinsa, na yi masa alkawarin Yayata za ta kasance da shi ko da kuwa me ye zai faru sai na cika wannan alkawarin, ta ya ya?”

Zuciyarta ta tambaye ta, “Yaya Zaruk! Shi ne ya fado mata a rai, da sauri ta yi waje.

Lokacin da ta isa kofar dakin Ammi sai ta shiga sanda, a hankali ta bude kofar. Ta yi sa’a Ammi na dakin Dad, ta hangi wayarta a kan gado. Ta dauka wuf! Ta yi waje kamar mara gaskiya.

A can cikin daki ta murda key tare da lalubo lambar Zaruk.

Shi ma Zaruk tunanin Nurat ya hana shi sukuni, ya ji wayarsa na ruri. Waye zai kira shi a irin wannan lokacin? Kamar ba zai daga wayar ba, ya dai mika hannu ya daga.

Lambar Ammi ya gani, cike da mamaki ya kara a kunne. Muryar Nurat ta ratsa kunnensa, ya saki ajiyar zuciya.

“Me ya hana ki bacci?” Kai tsaye ya tambaya.

A gaggauce ta soma fadin, “Yayata ta juyan baya, ta ki amincewa da Adamu, ban san ya zan yi ba”.

“Wayyo Allah”. Ya ce a ransa kamar zai yi kuka.

‘Nurat me ya sa ba za ki mance wannan mutumin bab? Aazeen ba ta rasa komai ba, don me ya sa za ki tsananta? Tunda ta nuna ba ta so ki hakura, muddin kuma ba ke ce ki ke son nasa ba”.

“Yaya Zaruk me ya sa za ka ce haka?”

“A’a to, in ba haka ba, tunda ba ta ra’ayi kurum ki hakura’.

Za ta yi magana ya katse ta.

“Kin ga, in har ba haka ba ne, ki yi min alkawarin za ki fita harkarsa”.

Ta raunana murya.

“Ba zan iya ba, na riga na yi mishi alkawarin zan aure shi…”

“What? Kin san me ki ke cewa? Nurat mutumin nan ko dai aljani ne? za ki aure shi fa ki ka ce?”

“Ina nufin za ta aure shi”.

“Saboda ita din kaza ce, ko saboda ‘yarki ce, ke ce ki ke da ikon aurar da ita? Me ta tsare miki haka?” Ya fada cikin daga murya.

“Haba Yaya Zaruk, in ba ka fahimci ni ba, bana ganin akwai wanda zai iya fahimtata kuma”.

‘Ba zan taba fahimtar taki ba har abada, mahaukaciya kawai. Yanzu ki gaya mini za ki fita a rayuwarsa ko kuwa?”

Ya soma kular da ita, duf! Ta katse wayar.

Ya yi cilli da wayar yana jin zuciyarsa tamkar ta faso kirjinsa, ga dare ya yi ballantana ya yi wani abu a kai. Tuni ya janyo kwalin taba ya kunna ya shiga zuka, ya kusan shanye kwali guda ba tare da ya samu wata nutsuwa ba. yana jin tamkar an tsawaita daren, idanuwan nan sun yi jajir ko kadan bai runtsa ba, kan safe ya yi wani zuru-zuru.

Ita kam Nurat a safiyar tunda sassafe ta shirya tsaf don tafiya makaranta.

Hajiya Rahma da Alhaji Usman zaune suna karyawa ta fito.

“Da wuri haka?” Dad ya tambaya.

“Yau muna da test”.

“Amma dai kin karya ko?”

“Ammi bana jin yunwa”.

Ba ta tsaya sake jin komai ba, za ta fice, Aazeen ta fito ita ma cikin shirinta.

“Bari na sauke ta, ni ma yau fitar wuri zan yi, muna da manyan baki a ofis”.

A gidan baya Nurat ta zauna, hakan na nufin Nurat din na fushi da ita ta fara tuki babu wanda ya kula wani har zuwa get din makarantar.

Kusan tare suka yi parking da Deedat, bai sauka a kan Bespansa ba ya hangi Nurat na kokarin fitowa a mota. Gabansa ya yi wani mugun bugawa. Da sauri ya maida ido ga motar don ganin wanda ya kawo ta, duk da bai ganta tartar ba ksancewar gilas din motar ba mai haske ba ce. Ya shiga tunanin inda ya santa. Bacewa ganinta da ya yi ya sanya ya gaza tuno komai, zai maida kallonsa ga Nurat ita ma ta bace wa ganinsa.

Ina tsantsar kaunarta ina sonta, ita kadai na taba so a rayuwa ta, ina ji tamkar ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba, kafe shi principal ya yi da ido cikin mamaki, har yana ji kamar ba Deedat dinsa ba ne.

Deedat mai kunya da aji ya kan yi hakuri a kan abin da yake so, ya danne. Tabbas al’amarin yana girmama, gane abin da yake kauna abu ne mai wahala. Sai ga shi yau ya dubi kwayar idonsa ya furta masa yana son dalibarsa.

Abin da kansa ya haramta, ya dubi Deedat cikin sauke ajiyar zuciya.

“Ina jin komai tamkar cikin mafarki, amma ina zuwa”.

Karasowa ya yi kofa ya murda key ya dawo ya zauna.

Deedat ya dube shi, wani irin duba, duban da ya sanya Principal ya sake gaskata abin da bakinsa ke furtawa.

“Dalibarka ta kasa goguwa a zuciyata, ban taba sanin haka soyayya ta ke ba, yarinya ce karama wadda ba tsarata ba, amma zuciyata ta kasa sukuni da sonta. Ban taba cin karo da abin da nake matukar kauna ba irinta. Ka gaya min ya zan yi? In ka yi la’akari da waye ni, za ka tabbatar da cewar lalacewa ta zo min, wannan shi ne jarrabawa ta. Allah ya jarrabe ni da abin da ba zan taba samu ba, ita din…”

“No, kada ka ce haka”. Principal ya yi saurin katse shi.

“Babu mahalukin da za ka so alaka da shi irin wannan, ya ce zai guje maka ko da kuwa bai sa matsayinka ba, kwarjininka da kalaman da ke shimfide a fuskarka kadai zai sa ka samu komai da kowa, ballantana idan aka gane waye kai”.

“Abin da bana so kenan, ina son samun macen da za ta so ni don Allah ba don komai nawa ba. Ina son samun soyayyar gaskiya”.

Principal ya dafa kafadarsa cikin dan bubbuga shi.

“Da yardar Allah za ka samu abin da ka ke so”.

“Ina zuwa”.

Wayarsa ya dauko ya shiga laluben wata lamba.

“Malam isma’il ka bai wa Nurat littattafan nan ta kawo min yanzu”.

<< Kyautar Zuciya 6Kyautar Zuciya 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×