Shi kam Deedat ya maida kai ga wayarsa yana tura sakonni. Bai fahimci abin da principal ke kokarin yi ba.
“Assalamu alaikum”.
Wani irin bugawa gabansa ya yi, da sauri ya dago kai idanunsu suka gauraya. Ta dauke kai, shi ma komawa ya yi yana satar kallonta. Ta durkusa cikin girmama ta gaishe su. Ta aje littattafan a kan tebur.
“In ji Malam isma’il”.
Mikewa ta yi za ta fita.
“Am.. dan dawo in dan sa ki aiki kafin na dawo, ki duba ki ware min books din kowane aji a cikin wadanda ki ka kawo da na gurin nan, ina zuwa”
Ya mike cikin sauri, “Deedat ba ni minti biyar ina zuwa”.
Ba tare d ya jira me Deedat zai ce ba ya yi saurin ficewa.
Ita kam ta dukufa ware littattafai, hakan ne ya ba shi damar kare mata kallo.
“Kina bukatar in taya ki ne?”
Bai san sanda wannan furucin ya kufce a bakinsa ba.
Ta dan dago kai cikin dubansa.
“Na gode na ma kusan gamawa”.
Ya shiga tunanin ta ya ya zai takalo hira tsakaninsa da ita. Ya nufasa.
“Kafin malam ya kira ki ya ba ni labarin kina da kokari sosai kanwata”.
Ta yi murmushi.
“Ko ba haka ba ne?”
“Ya dai fada ne, amma akwai wadanda suka fi ni”.
Ya dinga jin wani irin nishadi mara isaltuwa.
“Ya sunanki kanwata?”
Ta dan dube shi a kaikaice.
“Sunana kanwata”. Ta fada cikin murmushihar kumatunta nalotsawa.
“Kin amince ki zamokanwata?”
“Eh mana ai da ma kai din Yayana ne”.
“Na gode da wannan matsayin”.
Mamakin yadda ta biye mishi yake yi. Ita din ma haka ne, tana mamakin yadda ta kasa share shi, yau shi ne karo na farko da ta saki jiki da mutumin da ba ta san waye ba. babu alamun shashanci a tare da shi, ba mutum ne wanda za a iya rainawa ba. yana burge ta da yawa, da alama mutumin kirki ne, kuma ma ai shi din babba ne, ba za ta iya biris da shi ba.
Mikewa ta yi.
“Ya na ga kin mike?”
“Na gama”.
“Ai cewa ya yi ki jira shi, ko dai ni ne na cika ki da surutu?”
Murmushi kawai ta yi.
“To bari in jira shi”.
Zamanta ya yi daidai da shigowar Principal, “Kada dai kin gama?”
“Eh tun dazu”.
“Okey sannunki”.
Ta yi saurin nufar kofar ficewa.
“Kanwata babu sallama?”
Tsoro ya kamata, ba ta iya cewa komai ba ta yi saurin ficewa.
*** *** ***
“Haba Malam a kan yarinya karama ka ke neman lahanta rayuwarka? Tunda na shigo ka ke faman daddakar sigari, ba ka san wannan hayakin matsala ne a lafiyarka ba?”
“Faisal zuciyata ta kasa samun nutsuwa, ina ma zan san inda wannan dan iskan ya ke? Ban taba kisa ba,amma da na soma a kansa. Ya zo ya rusa min komai, wani abin takaici wai ba ta sanshi ba ma, ina ga idan tasanshi?”
“Zaruk sam rayuwa ba za ta yi daidai da ita ba, yarinyar da ta ke ‘yar kauye sam ba ta da wayewa, yarinyar da kwalliya ma ba ta dame ta ba, idan ka ce ita ce za ka aura za ka zamo kullum cikin jin kunya, don ba za ta fidda ka jin kunyar abokai ba, tunda ba ka rigaya ka furta mata ba ka nemi Aazeen ita ce daidai da kai”.
“Kana son ka ce in zabi Aazeen ta zamo uwar ‘ya’yana? Anya kana kishina kuwa? Ta ya ya za ka ba ni shawarar haka alhalin ka riga ka san ita din wace ce? To bari ka ji, ni na tsani mazinaciya, na tsani ‘yar iska. Ba zan taba rayuwa da tantiriyar mace mai wayewa irin Aazeen ba, na fison na auri matar da ba zata zo wucewa wani namiji ya dube ta yana tuna abin da suka aikata da ita ba. Na fi son na auri macen da ko hannunta wani da namiji bai taba rikewa ba. Na fi son mai nutsuwa da kamun kai irin Nurat, ina ganin ita ce ta fi kowacce mace halin kwarai”.
Faisal baki bude yake kallonsa cike da mamaki, ya koma ya tuntsire da dariya.
“Oho da kyau, wato kana son ka ce Allah za ka yi ma wayo ko? To bari ka ji, shi Ubangiji ba haka Yake ba, ita din ta gama kauwama kanta tana tsare mutuncinta, sa’annan sai Ubangiji ya yi mata tukwici da samun miji kasurgumi kamarka? A’a ranka ya dade ba wannan zancen, lallaba kawai ka karasa rayuwarka da Aazeen din dai… kai ba ma wannan ba, ita din Aazeen ta ya ya za ta iya barin ka yi wannan kwamacalar?”
Ya kai ma kafadar Zaruk duka.
“Ka ga Malam, kawai dai ka sake tunani”.
Da karfi Zaruk ya daki table din da ke gabansu har sai da Faisal ya firgita.
“Allah ya tsine ma duk mutumin da ke kokarin shiga tsakanina da Nurat ko da bai furta ba”.
Ya fada yana huci da zaro ido.
Faisal ya daga kafada cikin yanayin ko a jikinsa.
“Ni dai na ga ka makance ne shi ya sa nake son dawo da kai kan hanya. Ka gama bin yawon matanka, sannan ka ce kana kyamarsu?” Ya fada daidai lokacin da Zaruk ya bar gurin.
“Kana tunanin za ka kubuta daga fadin Ubangiji ne, alhalin har yanzu ba ka tuba ba? kama ta dini tujani”.
Gidan ya cika da ife-ifen Aazeen da kawayenta, gaba daya suka kankame ta. Kallo daya za ka yi mata ka tabbatar tana ji da kawayen nata fiye da yadda Dad dinsu ya sake mata komi na dakinsu an yo musu odar abin da za su dinga ci, an samo ‘yar aiki daga wani hotel wanda za ta dinga kula da abincinsu zuwa lokacin da za su tafi.
Suna zaune a dinning room, hira suke yi na yaushe gamo tare da gaya mata yadda suka yi kewarta. Zainab wadda suke kira Zee ita ce wadda halayyarsu ta zo daya da Aazeen, tantiriya ce ba a haife ta da digon kunya ba, ba ta da tsoro, haka ibada ba ta dame ta ba. Ba ta da burin da ya wuce kullum ta ganta ga ta ga namiji.
Sai Mima, ita kuma tana son harkar kawance, tana daukar kowa da muhimmanci fiye da uwar da ta haife ta, duk rayuwarta tana karewa a yi ma kawaye hidima. Hakan ne ya sa ta jefa kanta a harkar less.
Sai Tina, ita din arniya ce, ba ta da addini. Ita kuma sun fi kusanci da Mima saboda kusan harkarsu daya, don haka ba su taba rabuwa. Minal ita ce mai saukin hali a cikinsu, ita dai bar ta da shaidanci, ga tsananin yaudara. Kyakkyawa ce ta gaske, kyawunta ya zame mata kadara, iyayenta talakawa ne tubus, ita ce komai nasu. Kyawunta ke burge Aazeen, don haka ta ja ta jikinta, Minal na da kirki, datausayi. Tanada son taimako, ga ta da shiga rai.
Ammi ta fito daga sashenta cikin nuna farin cikinta.
Minal ta dube ta, “Our Momcy ko?”
Hankalinsu ya karkata gare ta.
Wani irin gaisuwa suke mata, kawai yake Ammi ke yi. Cikin nuna musu shariya bata ji dadin mu’amalar yarinyarta dasu ba, shigarsu gaba daya tamkar ba yaran musulmi ba. Daga gaisuwar nan ci gaba suka yi da harkokinsu. Zee ce ta kunna music a wayarta suka hau rawa daga zaune, Ammi ta kada kai kawai ta koma ciki.
Nurat ta shigo sanye dakayan makaranta, ganin fuskar Aazeen a sake ya ba tadamar karasowa ta tsugunna tana gaida baki.
“Nurat ce ta girma haka?” Minal ta fada yayin da ta kai hannu ta dago ta daga tsugunnen.
“Masha Allah, ka ga yadda yarinyar nan ta kara girma, ta yi kyau na ban mamaki”. In ji Mima.
“Zauna mu ci abinci kin ji”.
Gaba daya Nurat ta gama shige musu rai.
“Kanwata ba kya magana, ko don ba ki sanmu ba”. Zee ta fada.
“Rabonmu da ganinki tun kina ‘yar mitsitsiya, lokacin da ku ka je da Dad dinku bisiting”.
Tina ta karbe zancen, “Yanzu ga yadda ta cika har tana son ta fi sister Aazeen nonuwa”.
Aazeen ta daure fuska tamau cikin duban Nurat, “Ke je ki daki”.
Sum-sum ta mike, Mima ta kai mata duka.
“Ji ki da Allah, sai wani muzurai ki ke”.
“Na lura yarinyar akwai ta da kunya”.
Wannan kalmar ce ta tuno mata da layin da Amminsu ta dorata na cewa, in ta bari namiji ya rike mata hannu za ta samu ciki, gaba daya suka kwashe da dariya.
“Ki ce an cusa kan yarinya a ta kunta ba za ta ji dadin rayuwarta ba, ita din zubin hakan ce”. In ji Aazeen.
Suka sake shekewa da dariya.
“Haka ya fi mata”. Minal ta fada.
Horn din motar Alhaji Usman suka ji da gudu, Aazeen ta mike kanta kan ya fita har ya cimma gurin. Gaba daya ta kankame shi, shi kuma sai washe baki yake.
“Bakin namu har sun karaso kenan?”
“Sannu Dad, da fatan mun same ku lafiya?”
A daya daga cikin kujerun gurin ya zauna. Hira suke da shi sosai.
“Wai ina Amminku ne?”
Aazeen ta yatsina baki, “Tunda ta leko suka gaisa ta shige ciki ba ta sake lekowa ba”.
“Bari in karasa na gani”.
Yana barin gurin suka shiga yaba masa.
Da alama Dad ya fi yi da ke, amma fa ya burge mu, wayayye da shi. Dole ki fantama yarinya, ashe daurin gindi ki ka samu tun daga tushe?” Zee ta fada.
Suka saka wani ihun shewa, hadi da tafawa.
*****
“Ke kullum burinki ki kaskantar da Aazeen, ina amfanin haka? Kun yi baki kin wani shigo ciki kin kwanta, kina son nuna musu cewar ba ki damu da ita ba kenan ko?”
Banza ta masa tamkar ba da ita yake ba, idanunta a rufe.
‘Na sani kina jina, da ke fa nake”.
Ganin ta ki motsawa ya daka mata duka.
Ta bude ido a kufule.
“Ina magana kin maishe ni sha-ka-tafi, wai shin ba baki ku ka yi ba ne?”
Ta mike zaune.
“Kana son ne in je na zauna a cikinsu kamar yadda kai din ka yi?”
Ya saki baki yana kallonta.
“Kada dai a ce kishi ki ke yi da ‘ya’yan cikinki?”
“Uhum, Yallabai kenan. Ashe da na dade da karewa, ai ni inda sabo na saba da irin haka, ina da aikin yi”.
Ta mike za ta barshi a gurin. Ya wani figo ta ta zube a kasa.
“Ni za ki raina wa hankali, ina magana za ki fita? Yaushe ki ka dawo haka?”
“Komai koya dan Adam yake yi”.
Mamaki ya sake kashe shi, yana ji kamar ba Rahmarsa ba ce.
“Ni ki ke gaya ma magana?”
Ta tabe baki, kallonsa ta ke a tsakiyar ido, babu shakka a tare da ita.
“Kana mamaki ko? Muddin wadannan kananun ‘yan barikin ba su bar gidan nan yau ba, zan ba ka mamaki”.
Yadda ta yi din ya daga masa hankali, ya kasa zaune ya kasa tsaye.
“Tabbas ni din kaina ina ji a jikina irin wannan tashin hankali da ya shiga da walakin, kamar yana tsoron wani abu. Da sauri ya rufa mata baya, kai tsaye sashen su Aazeen ya yi.
Bai ji motsinta a nan ba, haka ne ya sa ya nufi bangarenta, inda ya tadda ta zaune a tsakiyar gado tana faman kuka. Gaba daya ya gama karaya, dole ya sassauta yana ganin wannan karon tsaurinsa ba zai sa ta biyu ba, dole ne sai ya hada da lallami.
Ya haye gadon tare da raunana murya.
“Kin kasa fahimtar dalilin biye mata din da nake yi, a tunani na yadda nake mata din zai sanya ki yaba mini, sai na ga sabanin hakan, in ban biye ma yaran nan ba ya ki ke so su yi? Su ne komai namu, idan ba mu biye musu ba waye za su je gurinsa da lamarinsu ya biye musu? Ki fahimce ni mana, ki duba ki gani Aazeen ta wuce munzalin da za mu takure ta. Ta mallaki hankalin kanta, ta san fari ta san baki, ba za ta aikata abin da zai cutar da rayuwarta ba, kawai abin da za mu yi shi ne addu’a, lallabawa za mu yi su tafi inyaso sai mu kiyayi gaba kin ji”.
Binsa ta ke yi kawai da kallo cike da mamakin yadda soyayyar ‘yarsa ta rufe masa idanu, har ya kasa tantance fari da baki.
“Ji yadda duk ya bi ya rude, sai faman zuba yake”.
Hannu ya kai yana share mata kwalla.
“Ki yi hakuri kin ji”.
Dole ta dinga daga kai alamar ta hakura.
Labarin da Aazeen ke ba su ya yi matukar sanya su nishadi, ita din kanta cikin nishadi ta ke ba su labarin. Minal na dariya, “Bai kamata ki yi ma Nurat haka ba, ki karbi zabinta, Hajiya ta. Sau tari abin da ake dauka wasa yakan dawo abin burgewa…”
“Babu mamaki wani alheri ne ya tunkaro ki”. Zee ta katse ta da fadin haka.
“Hajiya ta ki nemi ganinsa, ke ma za ki yaba. Hajiya alheri na tunkaro ki kina wasarere?”
Aazeen ta kai mata duka.
“Rufa min baki, alheri ko shirme?”
“Ku tsaya duk ku ji”. In ji Tina.
“Idan da ni ce ita, biye mata zan yi. Bai kamata a ce kin gwale ta ba, musamman yarinya irin Nurat”.
“Tabbas haka ya kamata ta yi”. Minal ta ce.
“Ok, kuna son ku ce in biye ma shirmenta kenan ko? Ok, zan yi yadda ku ka ce, ko ba komai na yi sabon kamu. Allah ya sa dan harka ne”.
“Good aminiyar, ashe kin gane karatun namu?”.
A wannan daren kwana suka yi cur a gindin talabijin suna faman kallon tashar fim din da addininmu ya haramta mana gani. Abin da ya jawo Mima da Tina suka kasa daga wa juna aka kebe suka yi gefe suna biya ma kansu bukata.
Ita kam Zee chating ta shiga yi da saurayinta, Minal da Aazeen hira suke yi, a haka suka kwana zur sai da aka fara kiraye-kirayen sallah, Aazeen ta dauki filo ta koma gefen su Tina.
“Ni ban ga tsiyar da za ki tsinta a wannan harka ba sai wahala”.
Ta ja tsaki ta yi waje tana faan hada hanya saboda tsananin baccin da ta ke ji. Sashen Ammi ta nufa domin tashinta. A kan dardua ta riske ta a zaune ta daga hannu tana kai kukanta ga Ubangiji.