“Na kasa samun nutsuwa, farin cikin rayuwata na fushi da ni”.
Nurat ta dube ta don gaskata abin da kunnuwanta ke jiyo mata.
Aazeen ta dafe kuncin Nurat da hannu biyu ta dago fuskarta.
“Ko ba haka ba ne kanwar?”
Nurat ta yi murmushi, har kumatunta na lotsawa.
“Okey yanzu na amince da zabin abar kaunata, shi ke nan?”
Nurat ta buga tsalle.
“Yayata da gaske ki ke yi?”
“Eh ana”.
Ta rasa inda za ta tsoma ranta saboda tsananin farin ciki.
“Saura kawai na ganshi. Allah ya sa dai kanwata ta iya zabe”.
Cike da farin ciki, “Yayata, dole a ya yi miki. Ya dace da ke. Na gode yaya Aazeen”.
“No, kafin ki yi min godiya, ki fara jin sharadina. Akwai wanda nake son aure ke ma kin san da wannan shi ne burina. Ina son ya zamo mallakina yana da kudi, ni kuma ina matukar kaunar kudi, bana son hada hanya da talauci muddin na hadu da mutumin nan zan janye naki mijin da ki ka yi min,saidaiidan ke ki aure shi”.
Har ta sa Nurat dariya.
“Yaya ni aure kuma? Hmm har kin sa na ji kunya. To amma shi wancan din idan bai ce yana sonki ba fa?”
Dariya ta dinga yi har da tafa hannu, ta tsagaita dariyarta cikin duban Nurat.
“Ke a tunaninki har akwai namijin da zai iya cewa ban yi ishi ba? Ki ma daina wannan tunanin, ni na yarda da kaina, kodayake ba za ki fahimci abin da nake nufi ba. Za mu fita da su Zee idan mun dawo za ki hada ni da shi, kin ji?”
Ta mike ta yi waje.
Nurat ta yi ajiyar zuciya, wani irin farin ciki ya ci gaba da lullube mata zuciya.
*** *** ***
“Ba ka isa ka ce za ka juya wa Nabila baya ba, wannan karon dole ne a yi wannan aure inyaso kabarta a gidan nan, ka sani kullum ina jin nauyin mutanen nan, karo na uku kenan mahaifinta na yi mini maganar yaushe za a saka ranar auren nan, don haka yau ba za ka bar gidan nan ba sai ka sanar da ni. Ba ka san cewar cikar kamalar dan Adam shi ne aure ba?”
Mikewa ya yi tsaye, tare da juya mata baya.
“Ummita, kin sani ba ni da wata kamala, don Allah ki yi hakuri ki kyale wannan maganar”.
Da sauri ta zago gabansa, a can karkashin zuciyarta ji ta ke yi tamkar ta sa kuka da kalamansa mai narkar mata da zuciya.
A zahiri kuma ta daure fuska, “Na sani kada ka yaudare ni na san dalilin janye-janyen nan naka. Ita Nabila ai ko ma ya ta ke bai kamata ka duba haka ba, karamcin iyayenta gare mu za ka duba ko da kuwa a ce tana zaman kanta ne”.
Ya sanyaya murya, “Ummita, idan na ce zan aure ta ba kya ganin abin zai yi min yawa haka? Rayuwata da ta yarana za ta kara lalacewa, abin da ya faru a kaina ba ni na dora wa kaina ba, sai dai ba zan so a ce ni ina ganin kuskure in take saboda kawai wata alaka. Don girman Allah Ummita ki kyale ni, ba zan iya ba, ba kya ajiye min kara na tsallake sai dai wannan karon ki yi min afuwa”.
Yana gama fadin haka ya juya zai fita.
Kuka ne ya kwace mata, ta durkusa kamar karamar yarinya, dole ya juyo a rude ya karasa gare ta. Dago ta ya yi yana goge mata kwalla.
“No Ummita, don Allah kada ki yi min haka, kin san matsayin hawayenki kuwa a gurina? Shin kina son na lalace?”
Da sauri ta girgiza kai.
Ya jawo hannunta ya zaunar da ita, ya koma ya bude firij ya tsiyayi ruwan Faro a glass cup, da kansa ya ba ta a baki. Ta sha ya ajiye kofin.
“An yi an gama Ummita, ki bari na hadu yau da Nabila sai mu yanke hukunci, kin ji ko?”
Dadi ya kama ta.
“Allah ya yi maka albarka Babana, Allah ba zai tozarta ka ba insha Allah”.
Tsararren katon hall din da kallo daya za ka yi masa ka yi tunanin fada ce ta shugaban kasa. Gurin ya yi matukar tsaruwa, kujerun gurin ma kadai abin kallo ne, yadda jama’a suka zazzauna a kan kujerun kadai abin burgewa ne.
Hall din ya yi shiru, sai sautin muryar Ahmad Deedat ne kawai ke tashi. Sanye yake da wasu fitinannun kananan kaya, wanda ya bi ya kwanta a fatarshi. Fuskar nan sai shekin annuri ta ke. Ya wani kara kyau. Ya dan dakata da maganarsa lokacin da ya hangi wayarsa na wuta alamar ana kira. Kanwata ya gani a kan fuskar wayar.
Mamaki ya ke yi, Aazeen a wannan lokaci? Lafiya kuwa? Dole ne ya daga wayar ya nemi su ba shi minti biyu, ya koma farfajiyar kamfanin wayar a kunne.
‘Kana can ka mance da ni ko?”
Muryarta ta ratsa dodon kunnensa.
“Da a ce ba ki kira ni yanzu ba da jimawa kadan ni zan kira ki”.
Ta yi dariya har yana jin sautin dariyar.
“Ka ji ka da kokari, ina za ka samu katin?”
“Dazun na saka dari biyu na kira Kakata, akwai bonus”.
“Na ji ka ce za ka kira ni, kana nufin kana kewata kenan?”
“Sosai ma kuwa”.
‘Okey, gaya min yaushe za ka zo?”
Ras! Gabanshi ya buga.
‘Har kin shirya ganina?”
“Eh mana, sosai ma”.
Ji ya yi an kwalla mata kira. Duf! Ya ji wayar ta katse.
Ya yi murmushi, “Ba mu taba yin sallama da ke ba”. Ya fada a bayyane cikin murmushi.
*** *** ***
“Ba wani yanayi a soyayya, so kamar rayuwa ne, ba kowane lokaci ba ne ake samun sauki kuma ba kowane lokaci ake samun farin ciki ba. Ya kamata ka koyi sona, tunda ina nan a raye bana jin zan iya rabuwa da kai Yaya Deedat. Kai ne numfashina na sani ba wata damuwa ka yi da ni ba, da zan iya da tuni na cire ka a raina. Sai dai ina ji a jikina wataran za ka so ni, zan iya jure komai a kanka. Na amince zan rayu da kai a ba ka sona din”.
Kalamanta sun karyar masa da zuciya. Duk sai ta ba shi tausayi.
“Nabila ban ce bana sonki ba, dabi’unki kawai za ki sauya”.
“To ka gaya min, me ye aibuna? Me nake yi wanda ba daidai ba?”
Ya ja wani dan karamin tsaki, matsalarta kenan ba ta amince da ba ta yin daidai, dabi’unta tana daukarsu abin burgewa.
“To shi kenan, tunda kina ganin komai daidai ne babu matsala, yanzu ki gaya ma su Papa, wata biyu na diba”.
Ta yi sororo.
“Yaya Deedat, wata biyu ba ma sati biyu ba?”
Ya ce, “Akwai tafiyar da zan yi, zan kai kusan hakan idan na dawo sai a yi bikin. Ni zan wuce”.
Ta matso kusa da shi, matsalarsa kenan, sam bai iya soyayya ba, yadda ka san mutumin da.
“Yaya Deedat shin ba ka dokina ne? Ya kamata a yi bikin nan kafin ka tafi inyaso sai mu tafi tare, please”.
“Ba zai yiwu ba, idan hakan bai yi miki ba kin iya neman wani”.
‘Uhm Yaya Deedat, ka sani ba ni da mijin da ya wuce ka. Ina son ka sani ko da za ka kai shekaru goma ina nan daram babu inda zan daga, kawai dai ka sa a ranka duk bala’i ba ka da matar da ta wuce ni”.
Ya yi wani murmushi mai ciwo.
“Allah ko? To sai ki ci gaba da jira”.
Murmushi ta yi, ta sani gaba daya Deedat ba ya sonta, bai tsara rayuwarsa da ita ba, kuma dole ne ya aure ta, ba za ta bari wata shegiya ta rabe shi ba, ba ta fatan ganinshi da wata ko da ba shi da komai, ballantana hamshaki kamarsa, ko za ta mutu babu aure za ta jira shi. Ta sani haramtaccen abu ne ya yi aure ba tare da ya aure ta ba. Ta sani dama yake nema da zarar ta ji haushi ta ce za ta auri wani zai auri wadda yake so, don haka za ta jira shi.
Ta karasa gabanshi inda suke iya jin hucin juna.
‘Zan jira ka ko da hakan zai kai mu da tsofewa, na yi alkawari ba ni da miji face kai, in ka je ka yi shekara ba ka dawo ba Mr. Man”.
Ta yi murmushi, a gurin ta barshi.
Takaici kamar zai rufe ta da duka.
“Dole ne fa ka yi yadda iyayenka ke so, kai ma ka sani tuntuni ita din zamanka ta ke yi, ba ka da hujjar da za ka guje mata”.
“Mtss! Salim ka sani bai taba sonta ba, ta ya ya zaman aure ya yiwu a haka?”
“Nawa aka yi Yaya? Iyayenmu na da suka yi ba su taba zaben mace a kan kansu ba, kai wasu ma ba za su taba sanin wace matarsu ba sai ranar da suka tare”.
‘Ok, na ji wannan, amma kuma ba ka tunanin ita din Nabila wace ce ita ba?”
“Wannan ba hujja ba ce, a koyaushe dan Adam na iya sauyawa, ballantana Nabila wadda da zarar ka aure ta soyayyarka na iya sauya ta, in fa ka aure ta za ku kasance ne tare, in ma ba ku kasance tare ba kana datse ta a gida zama za ta yi”.
Deedat ya furzar da wani huci mai zafi, kalaman Salim ba su zame masa hujja ba. ya sani babu wanda zai iya fahimtarsa, babu wanda zai hangi abin da shi yake hange.
“Kawai ka lallaba ku rabu da Ummi lafiya”. Salim ya katse shi da fadin haka.
Bai dai ce masa komai ba, ya soko wata maganar, ba ya son ci gaba da maganar Nabila.
Gaba daya rayuwar gidan ta sauya, gida ya koma tamkar ba na musulmi ba, kide-kide da raye-raye shi ne abin yi. A kullum cikin kawo maza suke, da Hajiya Rahma ta yi magana sai Aazeen ta ce abokansu ne daga ofis dinta, tana tsoro, don haka kusan kullum ta ke nemar wa Nurat inda za ta tura ta ta wuni. Tana jin tsoron kada idanunta su dinga ganin irin wadannan abubuwan.
Haka a wannan lokacin ta kara kaimi gurin kai kukanta ga Ubangiji a kan Aazeen, babu abin da ba ta ayyanawa a kan Aazeen. Tuni ta gama sallama cewar ita din tana bin maza ne, don haka ma babu aure a gabanta. Yau kam ta gama kai wa kololuwa, ko kawayenta ko ita ba za ta ci gaba da zama da su ba alhalin ba su da niyyar komawa, sun ma mike kafa, don haka ko da ya dawo ba ta doshi turakarsa ba, ba ta kuma kai mishi abinci ba.
Ya dinga kiranta a waya ta yi biris! Ya turo tedt nan ma babu amsa. Ya kulu sosai har wani huci ya dinga yi. A zafafe ya mike ya nufi shashinta, ya afka ciki. Tana zaune a kan sallaya yana huci.
“Ban san sa’adda raini ya shiga tsakanina da ke ba, ina so ki sani ba zan dauki wannan wulakancin ba, ba zan taba ba. In ban da rashin mutunci ta ya za a yi in dawo ban tarar da abinci ba, in kira wayarki ki ki dauka, wannan ai iskanci ne”.
Har ta shafa addu’a ta cire hijabi tare da ninke darduma ta ajiye a gefe, ta koma bakin gado ta zauna ba tare da ta tanka mishi ba, hakan ya sake kular da shi, hannu ya daga ya kifa mata mari.
Dafe da kunci ta dube shi da ido fal kwalla.
“A kan me za ka mare ni?”
Ya sake daga hannu zai kara mata, ta yi saurin kaucewa ta dube shi a tsakiyar ido, yayin da kwalla ta gama lullube mata ido.
“Akwai Allah”.
Ya bi ta ya shako ta.
“Ki gaya min abin da ki ke nufi”.
‘Ni ka cika ni na ce”.
Ta daddage ta kwaci kanta da kyar tana haki.
“Wallahi muddin wadannan yaran ba su bar gidan nan ba, ba za mu taba zama lafiya ba”.
‘Zancen banza, an gaya miki su irinki ne? su din suna da gurin zuwa, ke kam idan na kora ki ba ki da gurin zuwa, su da gatansu, ke ko fa? Ba ki da gatan, ke din korarriya ce, mujiya ce wadda ki ke da danbareren tabo har a gurin Allah, ke din…”
“Ya isa! Ya ishe ka haka! Ka fara tunanin makomarka kafin ka hangi tawa. Wannan fuffukar da ka ke yi a da kenan, yanzu kar nake kallonka, na san ta yadda zan bi in wanke kaina. Na san yadda zan yi shari’a ta daure ka, ita din kanta na san yadda zan bi ta dinga ganin bakinka saboda ni ce mahaifiyarta. Sanin kanka ne uwa ta fi uba soyuwa a gurin zuciyar yaransu”.
Ya saki wata dariyar takaici.
“Ni a gurina Aazeen na yi nisa! Yadda nake da Aazeen ko cewa na yi ta kashe ki na yi imanin za ta bi umarnina, kuma wallahi idan ba ki bi a sannu ba sai kin yi kuka da idanunki, sai kin zamo kaskantacciya a gurin yaranki. Sai na yi miki lambar da za ki zame musu tamkar jaba, mara mutuncin banza. Karkari kuma ki ce ba za ki ba ni abin da nake so daga gare ki ba, ki je ki rike, kawai ina zuwa ne saboda in fita hakkinki, abin naki da kike rowarsa ba ya kara ta da komai, kawai maleji nake”.
Ya yi waje, ya rufe kofar da karfi har sai da ta firgita.
“Wayyo Allah, na shiga uku!”
Ta zube a kasa tana wani irin kuka.
‘Ni na ja wa kaina, kaico! Na sani hakan za ta faru. Usman tuntuni na gama sanin waye kai, sai dai soyayyarka ce ta makantar da ni. Usman ban taba ganin mara imani irinka ba, Ubangiji ka kashe ni in har mutuwa ta za ta zamo alheri a gare ni”.
Wunin ranar ba ta iya fita ko da sitroom ba. A haka Aazeen ta riske ta, hankalinta ya yi matukar tashi, duk shaidancinta tana son mahaifiyarta, ba ta son abin da zai daga mata hankali. Da gudu ta tsugunna a gabanta.
“Ammina, waye ya taba ki? Ammi kalli yadda ki ka komo wuni daya, gaya min, Dad ne ko?”
Ta kada kai.
“To me ke damunki? Don Allah ki fada min kin ji”.
“Na ce da ke babu komai, kawai kaina ne ke yi min ciwo”.
“No Ammi, ban amince ba, tunda kawayena suka zo ki ka kasa sukuni. Za su tafi, zan sallame su, ko kuma na maida su hotel, hakan ya yi miki?”
Ba ta kula ta ba, kawai binta ta ke yi da ido har ta gama surutunta ta fice, tsananin tausayinta ta ke ji.
Ta gama ba su labarin abin da ta fahimta ga Amminta.
“Tab! Lallai Ammi tana da matsala”. In ji Tina.
“To ai shi ke nan, sai ki yi irin rayuwar da ta ke so din, saboda na ga kamar kin shiga damuwa”.
Zee ta karbi zancen, “Yanzu ke hakan ne zai sauya ki? Kin ga Hajiyata kawai injoy your life”.
Mima ta ce, “Ita wannan Ammin a haka kamar wayayyiya. Duk ta maida kanta wata ‘yarkauye, ba ta da aiki sai rike carbi, ga kyakkyawar kanwarki na kokarin kwaikwayarta, kauyancinta ya sanya an kasa gane ita din mai kyau ce. Wai shin ma idan ba ki more rayuwarki a lokacin kuruciya ba, yaushe ake son ki more shi? Sai lokaci da ta zamo yagwalgwal?” In ji Zee.
Gaba daya suka dau shewa.
“Kun ga ku daina wannan zancen kuna kada min da gaba, babu abin da na tsana irin in ji an ambaci tsufa, a hakan ma nauyin shekaruna na ke ji, don haka nake rokon in mutu kafin tsufa”.
“Shi ne aminiyas, kawai ki huta”. Minal ta ce da ita.
“Amman da har Ammi na son karya min zuciya, na ji tausayinta yau”.
“Okey, shi kenan sai ki koma zumbula hijbi, rike carbi, zama a kan darduma takura kai”.
Suka sake kwashewa da dariya.
“A duk lokacin da ta sanya karatun alkur’ani na kan ji duk na takura”. Tina ta fada, “Ban sakewa wallahi. Ki yi mata magana”.
‘No Tina, don’t cross your limit. Ki rufe bakinki haka kada ki wuce gona da iri”. Minal ta katse ta da fadin haka.
Tuni ta shiga taitayinta.