Tun da ya iso asibitin, Asiya ta shaida mishi likita na son ganinsa, shi ya sa bayan ya duba su, ya zarce ofishin likitan.
Zaune yake a karamar kujerar da ke fuskantar likitan, yayin da likitan ya zubawa file din da ke gabansa ido, sai dai ya sauke boyayyar ajiyar zuciya sannan ya ce
“Matarka ce?” tambaya ta farko da ya jefowa Hassan.
“Eh matata ce.” shi ma ya ba shi amsa kai tsaye
“Wane asibiti take zuwa antenatal (awo)?”
Ido Hassan ya zubawa likitan, kamar wanda yake jiran amsar tambayar daga bakinshi,
Ganin tsawon lokaci Hassan bai ce komai ba, ya sa likitan ya fahimci Asiya ba ta zuwa awo.
“Kun taba yin test ne kafin auranku? Ina nufin ko wane test.”
Gaban Hassan ya yi wata mummunar faduwa da alama yau ce ranar tonon asirinsu ranar da kullum yake gudun zuwanta, saboda yadda mutane da yawa zasu fada cikin damuwa, za ta katsewa mutane farin cikinsu, ranar da su kuma zasu zama abun kyama a cikin dangi.
Tun lokacin da likitan da ya karbi haihuwar Asiya ya ce yana bukatar a yi ma tests din hankalina Hassan ya kasa kwanciya, don kuwa yana ji a jikinsa allura za ta iya tono garma.
“Da alama ka san matsalarku kai da matarka, amma me ya hanaku zuwa asibiti, musamman cibiyoyin da aka ware domin kula da masu cuta irin taku?”
Hassan dai ido kawai yake bin likitan da shi, dalilin da ya sa kenan likitan ya fahimci Hassan na cikin tashin hankali.
A hankali ya sassauta murya” Bai kamata ku ki ziyartar asibiti ba, yanzu an waye an ci gaba, ba irin da ba ne, da idan mutum yana da cuta ya rika boyonta. Ban san me ya sa mutane suke kunyar ko nuna tashin hankalinsu idan aka ce suna H. I. V fiye da ko wace cuta ba. Bayan akwai cututtukan ma da suka fi ta hatsari.”
Ya zubawa Hassan ido hade da nazarin yanayinsa.
“Yanzu ba ka taba jin cewa cutar sikila ta fi kanjamau hatsari ba?”
Ya yi tambayar hade da kallon fuskar Hassan, ganin bai yi alamun ba shi amsa ba ya sa ya ci gaba
“Cutar sikila ta fi kanjamau hatsari, musamman wanda yake a rukunin SS, kana kallon yadda suke shiga matsalolin rayuwa saboda ko auransu ba a cika yi ba. Amma masu cuta irin taku muddin suna shan magani zasu rayu kamar kowa, ba ma wanda zai fahimci suna da cutar sai idan sune suka fada, zasu yi aure su kuma haihu, sannan akwai matakan da likitoci ke bi wajen kare jaririn da za a haifa daga cutar.”
Har yanzu Hassan idonsa a kan likitan.
Fuskar likitan ta canja zuwa wani yanayin da Hassan ya kasa fassarawa.
A hankali yake bubbuga teburin da ke gabansa, zuwa can kuma ya mike tsaye hade da dafa teburin gabansa da duka hannayensa
“Sakamakon rashin zuwa asibitin da kuka yi, ina mai bakin cikin sanar maka da cewa jaririnku ya kamu da irin cutarku.”
Fadin halin da Hassan yake ciki ma bata lokaci ne, iyakar tashin hankali ya shiga, ya kasa furta komai, a hankali hawaye masu zafi suka shiga gangaro mishi.
Shi ma mikewa tsaye ya yi hade da kallon likitan
“Why Doctor? Why?” cikin kuka yake maganar, shi kansa likitan jikinsa ya mutu, sosai yake jin ba dadi dangane da abin da ya same su.
“Likita, ni da matata bamu taba zina ba wallahi, an shaida mana muna dauke da wannan cutar tun cikin matata na wata uku, gidanmu ya shiga tashin hankali da rudani sakamakon wannan batu. Daga karshe na shawo kanta da kyar muka daidaita.” kukan da yake yi a yayin maganar ya ci karfinsa, dole ya yi shiru a kokarinsa na daidaita muryarsa.
“Na so mu koma asibiti, amma matata ta ki, wai ba ta son a kara tayar mata da hankali, dole na hakura na kyaleta. Likita me ya sa haka ya same ni? Ni ban taba zina ba a rayuwata.”
A hankali likitan ya dafa kafadunsa, hade da zaunar da shi a kan kujerar “Look! Ai ba dole sai a zina ne ake kamuwa da cutar ba, baban kuskure ne a kalli mai irin wannan cutar da cewa zina ya yi ya same ta. An san zina ita ce hanya babba ta kamuwa da cutar, amma akwai wasu hanyoyi ai, misali ta hanyar karin jini…”
“Ni ban taba ba kowa jini ba, kuma babu wanda ya taba ba ni, haka ma matata.” Hassan ya yi saurin katse likitan.
“To akwai aski, ta hanyar yin amfani da abu mai kaifi tare da mai cutar. Ka yi tunani da kyau ko hakan ya faru da kai.”
A yanzu dai ba zai iya yin wannan tunanin ba, dalilin da ya sa kenan ya tambayi abin da yake son sani
“Yanzu Doctor me ye matsayar yaronmu?”
“Sha Allah zai rayu, idan har aka kiyaye da kuma bin matakan da likitoci zasu tsara maku.”
“Wane matakai ne?”
“Akwai magunguna masu rage radadin ciwon da karfin cutar, sannan kar ta shayar da shi nono, saboda hakan zai kara sanyawa cutar ta yi tasiri a jikinsa.”
“Kana nufin yanzu ba za ta shayar da shi ba?” Hassan ya tambaya hankalinsa a kan likitan.
“Eh haka nake nufi, da duk sauran wasu yara ma da za ta haifa a nan gaba.”
“Wata haihuwar kuma Likita?”
“Sosai ma kuwa”
“Hmmm! Kenan mu ci gaba da haihuwar yara marasa lafiya, da su girma su rika jin haushinmu saboda mun yanke masu wani bangare na jin dadinsu.”
Murmushi likitan ya yi “Akwai hanyoyin da idan aka bi su, ba za ku haifi yara da cutar ba.”
Hassan ya nisa lokaci daya kuma ya mike tsaye, cikin yanayi mara dadi ya ce
“Likita ta ya zan fahimtar da familyna wannan matsalar? Ta ya zan fuskanci matata in fada mata yaronta yana dauke da cutar H. I. V. Zan iya rasa ta, abin da ni kuma ban shirya mishi ba yanzu. Ban son rasa matata.”
Cikin yanayin tausayi ya kuma dafa kafadunsa a kokarin sa na kwantar mishi da hankali
“idan ba damuwa, ka, hada ni da ma fi kusanci da kai, ni kuma zan tattauna dasu ta yadda zasu fahimta.”
“Doctor matata fa?”
“Matarka zamu ba ta duk wata kulawa da take bukata da kuma kai kanka, abin da nake so shi ne ka dawo cikin hankalinka, sannan ka hadani da ma fi kusanci da kai, kamar yadda na fada ma a baya.”
“A ina kenan likita?”
“Duk inda ka zaba, idan ka ce nan ba damuwa, idan kuma ka ce a gida ne, zan iya zuwa in yi masu bayanin da nake son yi masu.”
“Hankalina zai fi kwanciya idan ya kasance a gida ne, yanzu dai ina son ka sanar dasu Asiya ta dakata da ba yaro nono, ka samo dalilinka na fadin hakan.”
“Sha Allah zan yi hakan.”
Shiru ya ratsa ofishin kafin daga bisani suka fito zuwa inda Asiya ke kwance tana jiran sallama.
Ku san kowa ya yi mamakin maganar likita ta cewa kar a ba yaro nono, amma ganin likitan ya ce zai zo gidan da misalin karfe takwas na dare don kawo wasu magunguna sai hankalinsu ya dan kwanta.
Ba bata lokaci suka rankaya gida, inda yan’uwa, abokan aiki,, yan’unguwa ke ta zuwa gaishe da ta.
Aunty Amarya, Jamila da kuma Zee ne a tare da ita, suke yi mata komai duk kuwa da katon cikin da Zee ke da shi hakan bai hanata yin aiki ba.
Sosai Asiya ke son yin magana da Hassan, saboda ta fahimci akwai damuwa shimfide a kan fuskarsa, sannan hankalinta bai kwanta da maganar likita ta kar ta ba yaro nono ba, fakar ido take yi ta ba shi kuma sha yake sosai.
Tana jin lokacin da Zee ke magana da shi, hakan ya tabbatar mata da ya dawo daga sallahr isha’i, shi ya sa ta faki ido zuwa sashensa.
Zaune yake a bakin gado ya zuba tagumi da hannayensa biyu, shigowarta bai sanya ya sauke hannayen ba, ya dai dago kai ya kalle ta.
Ta zauna kan kujerar da ke fuskantar shi, bayan ta gama nazarin shi ne ta ce
“Na fahimci akwai abin da ke damunka, ka fada min menene?”
Ya nisa kadan hade da kallon agogon da ke jikin bangon dakin “zan fada miki idan na dawo, kin san zamu hadu da likitan can karfe takwas.”
“Rabin Raina akwai matsala ko?” ta yi maganar cikin sanyin murya
Ya zuba mata ido “Ba sosai ba. Ina fatan dai ba ki ba yaron nan nono ba.”
“Na ba shi fa.” kai tsaye ta fada
“Are you serious” ya fada a firgice,
“Ehen”
“Oh My God! Me ya sa ba kya ji ne ke?” rai bace ya yi maganar.
“Ta ya za ace kar in ba yaro nono, bayan kuma da ruwan nonon, kuma ya fi shan nonon ma a kan wannan madarar fa.”
Girgiza kai ya shiga yi tare da fadin “Ke fa kina da matsala, kin cika tauri kamar ganda, idan an ce miki ga yaki sai ki ce ga kura, likita kam bai san da duk wannan ba ya ce kar ki ba shi nonon. Asiya za ki kashe ni.” Rai bace yake maganar tamkar zai rufeta da duka.
“Taurin kan me kuma na yi? Ta ya za ace kar a ba yaro nono, bayan kuma yana son sha” ita ma murya a dage ta yi mishi maganar.
Dubanta yake daga sama har kasa, sannan ya ce, “Na dade ina rarrashinki a kan maganar zuwa asibiti, amma kika kafe ke ba za ki je ba.”
“Ba zan je ba kam, saboda bana son a kara tayar mun da hankali.” ta yi saurin tarar numfashinsa.
“To da ba ki je din ba, yanzu wa gari ya waya?”
“Me kake nufi?” ta yi tambayar hade da saurin tashi tsaye tana kallon sa.
Shi ma mikewa tsayen ya yi idonsa a cikin nata.
“Abin da nake nufi shi ne, a sakamakon kin zuwa asibitin da kika yi, yaronmu ya kamu da irin cutar da ke jikinmu. Dalilin da ya sa kenan likita ya ce kar ki ba shi nono, don rage tasirin cutar a jikinsa.”
“Innalillahi Wa’inna Ilaihir raji’un!”
Kalmar da Asiya ke iya furtawa kenan cikin tashin hankali.
Hassan kuwa key din mashin dinsa ya dauka zuwa waje, ba tare da ya kara cewa komai ba.
Tsawon mintuna ban da kalmar sallallami babu abin da ke fita daga bakin ta.
A hankali kuma ta fashe da kuka mai sauti wanda ba ta san ma ta sake shi ba, lokaci daya kuma ta fito zuwa dakinta.
Hankalin Aunty Amarya, Zee da kuma Jamila ba ƙaramin tashi ya yi ba, ganin yadda ta shigo hannu a kai tana furta kalmar Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un, wani lokaci kuma sai ta ce “Na shiga uku ni Asiya, wannan wace irin kaddara ce, wayyyo Allahna!”
Aunty Amarya ce ta rike ta gam tana fadin “Subhanallah! Ke me ya same ki?”
Asiya kuka take yi sosai har da faduwa, duk wanda ya kalleta tabbas ya san ba ƙaramin abu ne ya same ta ba.
“Sister me ya faru please,, don Allah ki natsu ki yi mana bayani” cikin kuka Zee take maganar
“Mutuwa zan yi sister, wallahi mutuwa zan yi, ku kai ni wajen Hajja ko ku kira min ita. Aunty Zee na shiga uku, yarona, wallahi an cuceni Aunty Zee.”
“Waye ya cuce ki Aunty Asee fada min shi” cewar Aunty Zee cikin kuka.
Maimakon ta ba ta amsa mikewa ta yi da sauri zuwa inda jaririnta ke kwance ta dauke shi hade da manna shi a kirjinta, kukanta ya tsananta sosai, ta ci gaba da fadin “Kai ba ka yi komai ba, ba ka san komai ba, za ka rayu cikin kunci da kyamata, duk wanda ya zulunceka tsakanin ni da babanka Allah ya saka maka, amma ko ka girma kada ka yafe mana, ka bari Allah ya saka maka, ni ma ban yafewa duk wanda ya cuceni ba, na san sai ka yi danasanin da muka kasance a matsayin iyayenka, saboda mun yi wa rayuwarka gibi… ” kuka ya ci karfinta, dalilin da ya sa kenan ta durkushe a wajen tana kuka.
Aunty Amarya ce ta yi saurin janye yaron hade da mikawa Jamila shi da take tsaye tana ta kuka, don kuwa gani take tamkar yar’uwar tata ta haukace.
“Rike yaron nan Jamila, ku fita zuwa falo. Ke Zainab kira min Hajja a waya da sauri.”
Inasan naganfarkon lbrn Hasiya
Ka shiga menu na Bakandamiya, sai ka shiga list of book, ka je L alphabet, za ka labarin to sai ka shiga kan labarin da ya yi blue ka danna