Skip to content
Part 11 of 25 in the Series Labarin Asiya by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Hajja zaune a kasa tana hada turaren wutar da za a kaiwa Asiya da safe kiran Zainab ya shigo.

Jin muryar Zainab a cikin kuka kuma tana fada mata ta zo yanzu, hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali ya yi ba.

Ko motarta ba ta saurara ba tsabar rudewa sai ta fita ta tare napep.

Shi ma ji take yi sam ba ya sauri, ta kosa ta isa don sanin me ke faruwa a gidan, da Zainab ta yi mata irin wannan kiran, kuma tana kuka.

Lokacin da mai napep din ya tsaya kofar gidan Asiya, Hajjah takardar dubu daya ta ba shi, ba ta jira canji ba ta fada gidan.

A kidime ta shiga falon inda ta iske su Zee jugum-jugum fuska jike da hawaye.

“Me ya faru?” ta jefo musu tambayar tun ba ta zauna ba, kafin kuma su ba ta amsa ta yi hanyar bedroom din, damuwarta kawai ta yi arba da Asiya.

Tun lokacin da ta Zee ta kira ta tana kuka, wani mafarkin ya fado mata, lokacin da take ta haihuwa yaran na mutuwa, tana da cikin Asiya sai ta yi mafarkin wasu mutane masu siffar laarabawa su biyu, sun same ta tana kuka, sai daya ya tambaye ta kukan me take yi, ta ce mishi ciki gare ta, tsoro take ji kar ta haihu, abin da ta haifar shi ma ya rasu kamar sauran.

Sai daya mutumin ya ce mata, ta biyo su, haka ta bisu har zuwa wani fili da ya kasance ba kowa sai wani kabari guda daya, sai dayan ya ce ta tone kabarin, haka tai ta tona kabarin har ta iske wani mutum kyakkyawa fari sol a kwance kamar yana bacci, shi ne daya ya ce ta roki duk abin da take so, sai ta ce ita bukatarta kawai Allah Ya raya mata abin da za ta haifa.

Sai dayan ya ce mata, za ki haifi mace, za ta rayu har ki ga auranta har sai kin dauki yarta ko danta da hannunki, koda za ta mutu.

Tuna wannan mafarkin ya sa hankalinta ya kasa kwanciya, ji take Asiyar kodai mutuwar ta yi, tun dai kaf abin da ta gani a mafarkin ya faru, Asiya ta rayu, ta yi aure, ta kuma haihu har ma ta dauki danta. Kar dai abin da ya rage ba ta gani din ba shi ne take shirin gani.

Shi ya sa ba ta saurari amsarsu ba ta fada badroom din kai tsaye, musamman da ta ke jiyo kukan Asiya wanda ke nuna tana cikin matsananciyar damuwa.

Ganin Hajja kuwa sai ta mike hade da fadawa jikinta ta kuma rushewa da wani sabon kuka ma tsuma zuciya .

Hajja jikinta rawa kawai yake yi, a cikin yanayin ta rumgume Asiya tsami a kirjinta, tamkar za ta tura ta ciki.

Rarrashinta take yi, ta hanyar bubbuga bayanta, lokaci daya kuma tana tambayarta me ya faru.

“Natsu ki fada min Asiya, hankalina a tashe yake, wani wuri ne ke miki ciwo?”
Cewar Hajja cikin tashin hankali.

“Hajjah! Hajjah!! Hajjah!!!” abin da Asiya ke iya fada kenan cikin kuka.

Hakan sai ya kara tadawa Hajja hankali, ta matsu ta ji me ke damun yarta ta, da har ta fita hankalinta haka.

“Zan mutu Hajjah, Hajjah zan mutu, mutuwa zan yi.” Asiya ta kuma fada cikin tashin hankali mai cin rai

Daga kanta Hajjah ta yi, hade da share mata hawayen da ke kan fuskarta.

Ta tattaro duk wani kuzari na ta ta ce
“Ki natsu Asiya, nutsu ki fada min abin da ke damunki,, fada min ko menene daina kuka kin ji.”
Cikin sigar lallashi ta karasa maganar.

Wani sabon kukan Asiya ta kuma fashewa da shi, don ji ta yi tausayin kanta ya kara kamata, cikin kukan ta ce “Wallahi! Billahi Hajjah ni ban taba zina ba.”

“Wani ya ce kin yi zina?” Hajja ta yi saurin tambaya, tana kallon idanun Asiya da suka kumbura saboda kuka

Girgiza kai ta yi, fuska jike da hawaye. Amma ba ta ce komai ba.

“To me ye ya faru?” Hajja ta kuma tambaya har lokacin idonta zube a kan Asiya.

Maimakon ta ba ta amsa sai ta kuma rushewa da kuka hade da kwantawa a jikinta sosai.

Hajjah cikin karfin hali ta ci gaba da bubbuga bayan Asiyar tana fadin “Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un! Ya Allah koma menene ya sa ya zama mai sauki ne a garemu.”

Tsawon mintuna suna a, haka, sannan Asiya ta mike tsaye da kyar tana kallon Hajjah, daga bisani ta cije lebenta alamun abu mai daci yana damunta.

Sai da ta kara janye jikinta da na Hajja hade da saka idanunta a cikin na Hajja sannan ta ce” Cutar Kanjamau gare ni.”

Kai karshen maganar tata ya yi daidai da komawarta gefen gado ta zauna hade share sabbin hawayen da ke bin kuncinta.

Hajja dai tsaye ta yi kamar gunki tana kallon Asiya wacce ke ta aikin share hawaye.

Aunty Amarya ce ta shigo dakin tare da fadin” Me Asiya ke cewa Hajja?”

Hajja dai kamar zane haka ta zama, dalilin da ya sa Zee ta mayar da tambayar Aunty amarya kan Asiya, kai tsaye kuma Asiyar ta amsa da kalma mafi muni a kunnensu.

Ba ki bude ido waje mutanen dakin ke bin junansu da kallo da ke nuna kamar basu fahimci me Asiya ta fada ba kila shi ya sa Aunty Amarya ta ce

” Ke! Kin yi hauka ne? Kin san me kike fada kuwa?”

“Da gaske nake yi Aunty, ina da cutar H. I. V kuma yanzu haka na ba yarona ita, shi ya sa likita ya ce kar in ba shi Nono.”

Cewar Asiya cikin muryar tausayi.

“H. I. V! Kanjamau fa kenan?” Cewar Zee cikin tashin hankali.

“Koma dai menene ina da shi” Asiya ta amsata cikin kuka.

Zee ta juya da niyyar ficewa daga dakin, sai dai take kafafuwanta suka ki bin umurninta, wannan ne ya yi sanadiyyar faduwarta, duk sai suka nufe ta cikin tashin hankali.

Ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba ganin jini na bin kafafun Zee din, sannan babu alamun numfashi a tare da ita.

Take suka manta da batun Asiya suka koma na Zee, Aunty Amarya ce ta fita samo napep, ba jimawa ta dawo suka dauki Zee din zuwa asibiti.

Isarsu asibitin ke da wuya suka shiga kiran duk wanda ya dace suna sanar mishi, ba jimawa asibitin ya fara cika da ƴan’uwan Zee.

Zuwa yanzu dai kowa da abin da yake damun shi, ita dai Adda yadda yarinyarta ke a dakin tiyata a raye ko a mace shi ke damunta.

Aunty Amarya kuwa abu biyu ne ke damunta, halin da Zainab take ciki da kuma maganar Asiya wacce ke neman tarwatsa mata kwana. H. I. V kuma kamar a wani film, me ye hadin kifi da kaska, har yanzu kallon zautacciyya Aunty Amarya ke yi wa Asiya.

Hajja kuwa fadin halin da take ciki ma ba zai misiltu ba, musamman yadda ta bar Asiya a gida daga ita sai Jamila, so take yi ta koma su yi magana da yar tata, amma kuma ba dama, saboda Zee na kwance rai hannun Allah bai kamata ta tafi ba. Amma tabbas tana cikin tashin hankali, jin maganar Asiyar take yi kamar mafarki koma dai ba ta ji daidai ba.

Idan har ya kasance Asiya na da HIV to kuwa da Hassan ya gama cutarta, yadda ta yarda da shi, ta dauki amanar yarta ta ba shi, ta yi mishi kusan komai a rayuwa amma ya rasa da abin da zai saka mata sai ya mannawa yarta cutar da kowa zai kyamace ta.

Wace irin sakayya ce Hassan din ya yi mata?

Wane hali Asiya za ta kasance ita da yaronta?

Ta ya za ta bi wa yarta hakkinta?

Wadannan sune tambayoyin da Hajja ta kasa samun amsarsu har zuwa lokacin da gari ya waye masu a asibitin.

A lokacin kuwa tuni Zainab ta farfado daga aikin da aka yi mata, inda aka cire mata sambaleliyar yarinyarta kyakkyawa.

Misalin takwas Aunty Muna ta shigo asibitin wanda ya ba Hajja damar zuwa gida don kintsawa, saboda dama ita da Aunty Amarya ne suka kwana, kuma Auntyn ta tafi da safe.

Gidan Asiya ta yi wa tsinke, kamar yadda ta yi tsammani haka ta same su.

Sosai Asiya ta kode ta zube lokaci daya, ganin Hajjahn ne ya sanyata saurin dakatawa da madarar da take ba jaririn.

“Ya jikin Aunty Zee din? ” Shi ne abin da ta fara tambaya.

“Da sauki.” Hajjah ta yi maganar daidai lokacin da take zama a kan kujera, lokaci daya kuma ta amshi jaririn ta ci gaba da ba shi madarar.

Gaisuwar Jamila ta amsa hade da tambayarsu ya suka kwana, “Lafiya kalau” Jamilar ta fada hade da shiga kitchen don kawo ma Hajjah abun kari.

Sai da ta tabbatar ya koshi har ya yi gyatsa sannan ta mikawa Jamila shi, hade da fadin “Je ki falon waje ki sanya shi ya yi bacci zan yi magana da Auntynki.”

“Ba ki ci abinci ba” Asiya ta yi maganar hade da duban abincin.

“Ana ta kai wa ke ta kaya, babu abinci a gabana. Maganar da kike fada min jiya duk ta kosar da ni, amma me ye gaskiyar ta?”

Ajiyar zuciya ta sauke mai karfi, cikin sanyin murya ta ce “Gaskiya ne Hajja.”

“Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un!” Ita ce kamar da Hajja ta rika maimaitawa.

Sai kuma ta ce “Asiya garin ya ya?”

“Shi ne ban sani ba ni ma.”Cewar Asiya cikin yanayin jimami

“Kamar ya ba ki sani ba, dole za ki sani.” Hajja ma ta fada idonta a cikin na Asiya.

“Ban sani ba da gaske Hajja, wlh ni dai ban taba hada shimfida da wani ba, bayan Yaya, shi ma kuma har qur’ani ya rantse min bai taba ba.”

“Karya ne! Cikin ku biyun wani ya yi karya.”

Asiya ta narke kamar za ta yi kuka sannan ta ce “Wlh Hajja ban taba hada shimfida da wani ba, kuma shi ma Yayan ya tabbatar da hakan.”

“Ya salam!” abin da Hajjah ta fada kenan cike da dimuwa, saboda kwakwalwarta a cushe take ta rasa yadda za ta bullo wa lamarin, abu ne dakan daka shikar daka, da ace bare ne to har kotu sai ta kai wannan batun, amma yanzu ido shi ne nata, ba za ta iya cewa komai ba.

Shiru duk suka yi, da alama kowa da abin da yake tunani.

*****

A can asibiti kuma Aunty Muna ce zaune a gefen gadon Aunty Zee tana yi mata ya jiki.

Ganin ba kowa a kusa ne ya sa Aunty Zee gyara kwanciyarta hade da ya fito Aunty Muna da hannu.

Sai ko Auntyna Muna din ta duko sosai hade aje kunnuwanta saitin bakin Zee.

“Kin san me yake faruwa kuwa Aunty?”

A tsorace ta ce “A’a. Me ya faru?”

Hannu ta sanya hade da share hawayen da ya zubo mata. Kafin ta ce

“Wai su Asiya ne ke dauke da cutar kanjamu shi ya sa ma likita ya ce kar ta ba yaronta nono.”

Zabura Aunty Muna ta yi baki bude hade zaro ido, ta ce “Wace Asiyar?”

“Asiya dai tamu.” Zee ta amsa ta

“Me kike son fada min ne.”

Kuka Aunty Zee ta fashe da shi a hankali, cikin ta cega “Wallahi Aunty da gaske nake yi.”

“Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un!” Cewar Aunty Maimuna, yayin da tashin hankali ya kwanta karara a kan fuskarta.

Shiru ya ratsa dakin idan ka dauke salalllamin Aunty Muna lokaci zuwa lokaci.

“Zainab! Mun shiga uku, to a ina ta samu kenan?” Aunty Muna ta yi karfin hallin fada.

“Ban sani ba, amma a wajen wa za ta samu idan ba wurin Yaya ba.”

“Wane Yayan?” Aunty Muna ta tambaya kamar ba ta fahimta ba.

“Ya Hassan mana.”

“Ke maganar nan ta fita bakinki, kar in kara jin ta.” Cewar Aunty Muna cikin gargadi, kafin Zee ta kara cewa wani abu kuma Aunty Muna ta ci gaba da rangada sallallaminta.

“Innalillahi! Ke Wai tsaya ma, Kenan shi ma yana da ita?”

“Har ma fa da jaririn.”

“Zainab mun shiga uku,”

Aunty Muna ta fada a kidime.

“Kuma Addah ta sani?”

“Ba ta sani ba”Zee ta ba ta amsa

Shiru ya ratsa wurin kowa da abin da yake tunani.

Can kuma sai Aunty Muna ta ce

“Zainab bari in je gida, wannan batu ba na zama ba ne.”

Ba ta jira amsar Zainab ba ta fice.

Addah ce a kitchen ke ta kiciniyar shirya abinci da za a kai asibiti, a falo suka yi kicibis da Aunty Muna.

“Da Allah ki rika sallama, sai ki fadowa mutum yif kamar gini, kin ba ni tsoro fa.” Cewar Addah tana duban Aunty Muna.

Ajiyar zuciya Aunty Muna ta sauke hade da rungume hannayenta a kan kirji tunanin yadda za ta fadawa Addah maganar take yi.

Har Addahn ta fito daga daki hannunta rike da leda Aunty Muna na nan tsaye kamar falwaya.

“Ke wai lafiya kuwa?” Addah ta yi tambayar don kuwa yanzu ta fahimci akwai damuwa.

“Eh. Me kika gani?”

“Na gan ki ne kamar dabara ta kare miki.”

“Hassan ya shigo ne da safen nan?”

“A’a. Har yanzu bai shigo ba.” Addah ta ba ta amsa daidai tana shiga kitchen.

Hakan ya sa Aunty Muna bin bayanta.

“Addah!” ta kira sunanta cikin sanyin jiki.

Addah ta fasa sanya plates din da ta dakko cikin leda ta ci gaba da kollonta da ke nuna tana sauraronta.

“Kin san me ke faruwa kuwa?”

“A’a me ya faru?” cike da tsoro a muryarta Adda ta yi tambayar bayan ta mike tsaye sosai.

“Wai likita ne ya ce Asiya na da Kanjamau, kuma wai har ta gogowa yaronta.”

Plates din da ke hannun Addah ne suka fadi kasa tsabar rudewar da ta yi.

“Kanjamau kuma! Kin san abin da kike fada kuwa?”

Hannu ta sanya hade da goge hawayenta, “wallahi Addah shi ya sa ma likita ya ce kar ta ba yaronta nono.”

“Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un!!!” kalmar da Addah ke iya maimaitawa kenan, daga bisani ma toilet ta shige a ciki ma babu abin da ta yi haka ta karaci zamanta ta fito.

Aunty Muna zaune a kan kujera tana aikin share hawaye Addah ta fito da hajabi a hannu tana fadin tashi mu je gidan Asiyar ai ba zama an saci dan ɓarawo. “

*********

Asiya kwance a kan cinyar Hajjah tana aikin kuka, ita ma Hajjah ta kasa jurewa kukan kawai take yi, ko ba komai kila ta rage nauyin da zuciyarta ta yi mata.

Don kuwa ko wane irin hukunci za ta yankewa Hassan ba ta huce ba.

Idan ta ce raba shi da Asiya za ta yi, to Asiyar ta auri wa?

Shi ne dai ma fi kololuwar hukuncin da za ta yi mishi ta ji ta gamsu,, amma hukuncin ba zai bayar da wata ma’ana ba.

Iya dai cuta ya gama cutarta, saboda ta san ba za ta iya furta ko bakar magana ba a kan wannan lamarinki ba.

Turo kofar da aka yi hade da shigowar bai sanya sun dakata da kukan da suke yi ba.

Hakan kuwa ba ƙaramin karyarwa da Addah zuciya ya yi ba, jikinta ya kuma mutuwa lakwas, saboda yadda ta gansu, ya tabbatar mata da abun da Aunty Muna ta fada mata, wani irin tausayinsu ya lulllubeta. Ba tausayi ba har ma da kunya, idan abun nan ya kasance gaskiya da wane ido za ta kalli Hajja.

Saboda Hajjah ba ta cancanci irin wannan sakayyar daga gare su ba.

Jiki a mace suka zauna ba tare da sun ce komai ba, ganin shirun ya yi yawa ne Addah ta yi karfin halin cewa.

“Tabbas yau ita ce rana ma fi muni a rayuwata, ranar da ba zan taba mantawa ba, ban san da wace kalma ya kamata in yi amfani da ita ba wajen ba ki hakuri ba. Ba mu yi miki halacci ba, mun saka miki da sharri a kan tarin alkairorinki garemu Hadiza. Ki yi hakuri,, ki yi hakuri. Allah ya, huci zuciyarki.”

Cikin muryar kuka Addah ta karasa maganar.

“Kira min Hassan ya zo yanzun. “Cewar Addah tana kallon Aunty Muna.

Cikin sakanni Aunty Muna ta kira Hassan, a lokacin Addah kara ba Asiya hakuri take yi wanda hakan ke kara karya zuciyar Asiya,, don yana tabbatar mata da lallai a yanzu ita abun tausayi ce, kuma abin da take gudun faruwarsa ya faru.

Wato da gaske dai tana da cutar kanjamau ba tare da ta taba aikata zina ba.

Lallai Hassan ya cuceta, kuma ya rainata mata hankali da ya ce wai ba shi ne ya ba ta cutar ba, kuma tsabar rashin wayo sai ta yarda.

To idan ba shi ba waye?

<< Labarin Asiya 10Labarin Asiya 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×