Skip to content
Part 12 of 25 in the Series Labarin Asiya by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Jiki a mace Hassan ya shigo gidan, gabanshi na wani bugu kamar gidan yawa sun sami turmin tsakar gida. 

Tun jiya ya fahimci kamar akwai damuwa, kuma Asiya ta hana shi ganin ta, shi ya sa ma tun safe ya yi sammakon fita.

Asiya akwai daru idan ta so, amma tabbas tana da saukin kai. 

Yadda ya same su a falon kamar sun tasa gawa sai jikinsa ya kara mutuwa likis.

A can gefe ya tsugunna, sai dai kafin ya yi magana Jamila ta shigo dauke da Baby da yake kuka.

Addah ce ta karbe shi, yayin da Aunty Muna ta hada mishi madararsa, a nutse Addah ta shayar da shi, bayan ta fahimci ya koshi a kan kafadarta ta dora shi hade da shafa bayansa har ya yi gyatsa, daga bisani kuma bacci ya dauke shi. Har a lokacin bayan gaisuwar da suka amsa ta Hassan babu wanda ya kara cewa komai. .

“Hassan!” Addah ta kira sunansa a hankali.

Kai ya dago a hankali yana dubanta ba tare da ya amsa ba.

“Ban san sunan da ya kamata in kiraka da shi ba, amma kai butulu ne, mai mayar da alkairi da sharri, yanzu ka manta irin tarin alkairan Hadiza gare ka, duk matakin da ka taka yanzu ita ce tsani, amma…”

“Addah, me ye kawo wannan kuma, Me ya sa za ki tasa shi gaba kina yi mishi maganganu masu kama da gori? Na kasa fahimtar me kike son cewa” Hajjah ta yi saurin katse Addah.

Sosai Asiya ba ta ji dadi ba, ta so Hajjah ta bar Addah ta fada mishi irin butulci da ya yi masu.

“Ba gori ba ne. Ina tuna mishi ne, kuma so nake in sanar mishi ke ba ki cancanci wannan sakayyar a wurin shi ba, wallahi ya ba ni kunya wannan yaron, na dauki yarda dari bisa dari na dora a kanshi, amma ace wai neman matan yaron nan har ya kai matakin da zai dakko muguwar cuta ya sanyawa yarinyar nan, ta killace kanta shi kuma ya wofintar da na shi a waje. Shi ya sa zina ba ta da dadi, illar ta yawa ne da ita, sai ta shafi wanda bai ji ba, kuma bai gani ba. ni dai ba zan yafe ma wannan abun ba. Ba irin tarbiyar da na ba ka kenan ba, Allah kai shaida ne ban wofintar da tarbiyarsu ba, Allah kar ka hukunta ni a kan laifin dayansu.” cikin kuka Adda ta karasa maganar.

Har yanzu kan Hassan a duke kuma uffan bai ce ba.

Yana dai jin wani irin daci musamman yadda mahaifiyarsa ke zubar da kwalla saboda shi, sai kuma yadda aka tattare alhakin laifin duka a kansa, bayan shi ya san bai yi komai ba.

“Wai me ya sa kike kokarin dora mishi laifi ne shi kadai? Namiji ne kawai ke bin mata ko aikata zina? Mace kam ba ta zina ne Addah?”

Sosai Hassan ya ji dadin kalaman Hajjah, duk da ya san karfin hali kawai take yi. Amma ko ba komai ta fadi abin da ya kamata Addah ta duba.

“Asiya ba za ta fita da auranta ta aikata zina ba.”

“To irin wannan shaidar ma ya kamata ki yi wa Hassan, idan har kina da tabbaci a kan Asiya to Hassan ma akwai tabbaci a kansa.”

“Don Allah Hadiza ki bar irin wannan maganar, ke kanki kin san Asiya ba za ta iya aikata wannan ba.” 

Hajja ta dan nisa kadan

“Hassan ya rantse da girman Alqur’an bai taba zina ba Addah, Asiya ma ta rantse da hakan, kin ga kuwa dukkansu abun tuhuma ne ba wai Hassan kadai ba. Gasu a gabanmu yanzu, kowa yana da damar da zai yi magana da zamu fahimta, abin da ya gagaremu fahimta kuma mu bar wa Allah wannan shi ne tamu kaddara.”

Addah ta zubawa Hassan ido, saboda har cikin ranta ba ta yarda da shi ba.

Ganin haka ne ya sanya shi dago kai yana kallonsu daga bisani kuma ya ce “Allah ya sani kuma ya gani, wallahi ban taba yin zina ba, kuma idan har nine na sanyawa Asiya wannan cutar to ban san ina da ita ba, kuma gaskiya ba ta hanyar zina na same ta ba.”

Duk wanda ya kalle sa a lokacin ya san gaskiya yake fada babu karya a maganar tasa, kila dalilin da ya sa kenan falon ya kara yin shiru da alama kowa da abin da yake tunani.

“Ni ma wallahi idan ina da wannan cutar to ban san ina da ita ba, kuma ni ma ba ta hanyar zina na same ta ba.” cewar Asiya cikin sanyin murya

“Ikon Allah!” Aunty Muna ta fada hade da rike haba, alamun mamaki ya bayyana a kan fuskarta. 

Zuwa can Adda ta mike”Ku dakko yaron nan mu tafi gida gaba dayanmu a yi maganar nan a gaban iyayen yaran nan, wannan abun ya fi karfinmu. “

Jiki a mace suka fice daga gidan zuwa babban gida.

Shiru falon ya yi, tun bayan da Addah ta zayyane abin da ke faruwa a gaban Alhaji Abdallah mahaifin Asiya Alhaji Adamu mahaifin Hassan da kuma Baffa mijinsu Aunty Amarya.

Tsawon mintuna talatin babu wanda ya ce komai, da alama kowa bai san abin da zai furta ba, to abu ne duk na gida. 

Wayar da Alhaji Adamu ke yi ce ta kara janye hankalinsu zuwa kanshi.

“Yauwa kana asibitin ne?”

Basu ji me aka ce a daya bangaren ba, sun dai ji Alhaji Adamu ya kara cewa “To ga ni nan zuwa.”

Babban asibitin suka je wato FMC, kasancewar Alhaji Adamu babban dansiyasar da ya yi fice sai basu sha wata wahala ba suka hadu da likitan.

Bayan sun gaisa, kuma likitan ya basu wurin zama, Alhaji Adamu ya ce

“So nake ka debi jinin wadannan…” ya nuna Asiya da Hassan, lokaci daya kuma ya fara waige-waigen neman jinjiri.

A bayan Aunty Muna ya hango shi “Ke kawo yaron nan” ya yi maganar idonsa a kan Aunty Muna.

“Har da na yaron nan za ka diba idan zai debu, gwajin H. I. V nake so ka yi masu.”

Likitan bai tsaya neman wani ba’asi ba, ya shiga aiwatar da aikinsa. 

Cikin kwarewa aka debi jininsu, a cikin awa daya kuma sakamakon ya fito, ba dai ta canja zane ba,, saboda sakamakon dai nunawa ya yi dukkansu suna dauke da kwayar cutar H. I. V. 

Cikin kwarewa da iya kwantar da hankalin marasa lafiya likitan ya fadawa Alhaji sakamakon su Asiya. 

A hankali sautin kukan Asiya ya rika fita, wanda ya kashe jikin mutanen wurin, Addah, Aunty muna da Hajja duk kuka suke yi, 

Alhaji Adamu ya sauke ajiyar zuciya cikin wata irin murya ya kira sunan Hassan “Ta ya haka ta faru? Me ya sa ka aikata haka?” 

“Abbah ban aikata komai ba.” 

“Ba zan yarda ba, na san daidai gwargwado na ba ka tarbiyya, na ba ka ilmi a ko wane bangare na rayuwa. Me ya sa za ka saka min da ma fi munin sakamako?” 

Zuciyar Hassan ta karye, tausayin mahaifinsa da kansa ya kama shi, me ya sa kowa shi yake zargi? me ya sa kowa yake dora masa laifi?

A hankali ya saci kallon fuskar mahaifin nasa, damuwa ce karara kwance a kai

“Ba ka kyauta min ba Hassan, yau ka muzanta ni, ka bata zumuncin da ya ginu sama da shekaru hamsin, da wace fuska zan kalli dan’uwana da ya dauki diyarshi ya ba ka ba tare da ya yi wani bincike a kanka ba, hasalima shi ya biya ma sadaki, sannan ya karbar ma auran, mahaifiyarta ta ginaka ginin da har yanzu kana cin ribar shi. Me ya sa za ka yi haka? “

“Wallahi Abbah ban yi komai ba, ina nan a yadda ka sanni da irin tarbiyar da ka ba ni kuma, ban canja ba ko daya. ” cikin muryar tausayi Hassan ke maganar.”

“Ya za ku dora mishi laifi, ita ma abokiyar zaman shi ai abar tuhuma ce.” Cewar mahaifin Asiya.

“Wannan abu dai ya riga ya faru, maganar wane ne ya sanyawa wane ba a ita ce abun duba ba yanzu, mafita ita ce abun nema.” Cewar mijinsu Aunty amarya.

“Wannan gaskiya ne, sannan ita wannan cuta ai ba dole sai ta hanyar zina ake samun ta ba.” fadin likitan yana dubansu daya bayan daya.

“ku ba ni aron hankalinku in yi maku wani bayani don Allah.”

Babu wanda ya ce komai amma sun tattara hankalin nasu a kanshi.

“HIV tana daya daga cututtuka masu hatsari tabbas, kuma cuta ce da kan sanya mai ita cikin tashin hankali da fargabar Sanin makomarsa. 

Ba wannan ne kawai damuwar ba, babbar damuwar shi ne tunanin irin kallon da jama’a gami da kyamatar da zasu yi mishi. Kuma tana daya daga cikin cututtukan da masu ita kan ji kunyar furta suna dauke da ita ko zuwa asibiti. Wannan kuma shi ne ke sanya cutar yin tasiri a jikinsu.”

Ya kai kallonsu a kansu, su ma shi suke kallo.

“Ita dai wannan cuta… ” ya ci gaba.

“Babbar hanyar samuwarta shi ne idan mara ita ya hada shimfida da mai ita ina nufin ta hanyar auratayya ko akasin haka. Sauran hanyoyin kuma sun hada da bayar da jini, yin amfani da abu mai kaifi da mai cutar ya yi amfani da shi, shi ma fa sai an samu akasi ya ji ciwo jini ya fita. “

Dukkansu suka jinjina kai alamar gamsuwa.

“Sannan ba a daukar cutar ta hanyar cin abinci da mai ita, ko sanya tufafinsa, tari ko yin amfani da bayan gidan da ya yi amfani, sannan sauro ma baya yada cutar.”

“Alhamdulillahi! ” Addah ta fada a hankali.

“Cutar kuma tana da stage biyu, stage na farko shi ne a lokacin da take HIV, na biyu kuma sai ta koma AIDs.”

“Likita dama HIV daban Aids kuma daban?” Alhaji Adamu ya yi tambayar cike da mamaki.

“Eh haka ne, HIV ce take zama AIDs idan ba a dauki matakin shan magani ba ta hanyar zuwa asibiti. Aids ta fi HIV illa, ita ce take kashe mutane farat daya, amma mai HIV yana rayuwa kamar kowa ba tare da cutar ta yi mishi illa kamar Aids ba, masu cutar ma suna warkewa amma ba a cika samu hakan ba. “

“Doctor ta ya mutum zai gane HIV yake da ita ko Aids? ” Tambayar Hajja cikin kasalalliyar murya.

“Gwaji ne kawai zai bambance hakan. ” likitan ya fada yana kallonta

“To likita me ye alamomin cutar? ” Baffa ya tambaya.

” Akwai tari, ciwon kai, zazzabi,, kurajen jiki, rikicewar al’ada wa mata. Duk suna daya daga cikin alamun cutar”

“To tsawon wane lokaci take kai wa a jikin mutum kafin ta nuna wadannan alamomin?” Tambayar da Alhaji Adamu ya sake yi. 

“Eh sati biyu ne, amma wasu su kan yi shekaru ma ba tare da alamomin cutar sun bayyana a tare dasu ba.”

Kamar hadin baki duk suka aje zuciya a tare. Kafin Addah ta ce “To yanzu su wadannan yaran HIV ce ko Aids a jikinsu?”

“HIV ce” cewar Likitan yana kallon Addah.

“Alhamdulillahi! Da dan sauki.” fada cikin sauti.

“To me ya sa kuma aka ce kar Asiya ta ba yaronta nono?” Aunty Muna ta tambaya.

“Abin da ya sa aka ce kada ta ba shi nono saboda ana son a gwada yana da cutar ko a’a…”

“To yanzu Doctor kenan Asiya ba za ta kara haihuwa ba, kuma ya makomarsu take?” Hajjah ta yi saurin katse shi ta hanyar tambaya.

“Za ta haihu mana, wannan cuta masu ita zasu iya auran juna kuma su haihu ba tare da jariri ko jaririyar sun kamu ba.”

“Ta ya ya kenan?” Tambayar tambayar Alhaji Abdallah. 

“Ta hanyar zuwa asibiti, idan har masu cutar suna zuwa asibiti kuma suna amfani da magunguna da shawarwarin likitoci to ba ma kowa ne zai gane suna da cutar ba.” ya dan tsahirta

“Idan mace na da ciki akwai magunguna da za ta rika sha don kariya, sannan idan ta tashi haihuwa sai ta zo asibiti, an fi son yin aiki a lokacin haihuwa, saboda idan ta haihu normal akwai yiwuwar yaron ya dauki cutar ta hanyar haduwar jininsa da na mahaifiyarsa. Amma idan aiki ne akwai tabbacin ba zai samu cutar ba. “

Suka jinjina kai gabadaya alamun gamsuwa. 

“Sannan shayarwa ma za ta iya shayar da yaron na wata shida kacal daga nan ta ci gaba da ba shi madara. Shi ma bottle feeding din ya fi tabbas a kan shayarwa ta nono. Kodayake shayarwar akwai abubuwan da likitoci kan duba kafin yin hakan.” 

“Kenan kana nufin nan gaba Asiya kan iya haifar lafiyayyun yara?” Hajja ta kuma tambaya 

“In sha Allah! Wannan ma ya faru ne saboda sakacinta na kin zuwa asibiti. Amma yanzun zan dorata a kan magani daga ita har yaron.” 

“To Doctor za ta iya shayar da yaron yanzu?” Tambayar Aunty muna jiki a mace

“Eh za ta iya, amma wata shida kamar yadda na fada a baya.” 

Suka ka kuma jinjina kai. 

“Sannan akwai wani abu.” 

“Menene?” Alhaji Adamu ya yi saurin tambaya 

“Masu cutar suna bukatar karfafa gwiwa, lafiyayyen abinci mai gina jiki, rashin tsangwama da kulawa ta musamman. Hakan zai sa su ji kamar basu da cutar saboda ba a kyamacesu ba.” 

“Wannan ba matsala ba ce. Sha Allah zamu kula da wannan dukkanmu.”Cewar Baffah. 

“Ni kuma na yi maku alkawarin baku duk wani taimako in sha Allah. Ku dan bamu wuri idan badamuwa ina son yin magana dasu.”

Cewar likitan yana dubansu Alhaji. 

Cikin dakika office din ya koma daga likitan, Asiya da kuma Hassan. 

“Ina son ku sani wannan cutar ba tana nufin karshen rayuwarku ba, za ku rayu kamar ni da sauran yan’uwanku, muddin za ku kiyaye shan magani a kan lokaci da kuma cire damuwa. Cutar ba ta son yawan damuwa, kamar yadda na fada a baya sha Allah zan ba ku duk wani taimako da kuke bukata a bangarena.”

Ya bi su da kallo daya bayan daya. 

“Ku cire zargin junanku, ku dauka wannan ita ce kaddararku. Sannan ku yi nazari da kyau, ko akwai wanda kuka yi mu’amala ta hanyar hada kayan aski, shaving stick, reza da duk wani abu mai kaifi dai ko tsini.”

Sosai likitan ya rika yi masu bayanin karfafa gwiwa da ya rage musu tsoro da fargaba da suke ciki.  

Bayan ya sallame su, jiki a mace suka karaso inda su Hajja suke, suka wuce gida kowa shiru 

Idan ka dauke Alhaji Adamu da ke ta fadan duk laifinsu ne da basu sanyasu yin gwaji kafin aure ba, da duk haka ba ta faru ba. 

Cewa yake ya dauki darasi, ba zai kara hada aure, ko aurar da kowa ba, sai an yi test tun daga Genotypes, hanta da kuma H. I. V. 

A haka dai ko wane bangare suka shiga shirye-shiryen suna, Zee ma an sallamota tana gida.

Asiya ta ci gaba da shayar da jaririnta kamar yadda likita ya ce, sannan tana shan magunguna a kan lokaci haka ma tana ba yaron. Sai dai kasan zuciyarta akwai wani irin daci da take ji, musamman duk lokacin da za ta hadiyi maganin ko ba jariri, na jiririn ne ma ya fi bata mata rai. Bai san hawa ba, sai ga sauka a kanshi. 

Hassan ma yana shan magani ba ya wasa da hakan, duk da shi mamaki ne ke kama shi fiye da kuncin, wai shi ne ke hadiyar maganin H. I. V, kamar mafarki. 

Ana i gobe suna gidan Asiya cike da yan’uwa makusantanta, ita ma a lokacin zaune take ana karasa mata kitso, a bangare daya kuma tana jiran lallen da aka yi mata ya bushe.

Sosai ta fita kamar amarya lokacin da aka wanke lallen, ga jikinta danyen jego ta yi fresh da ita.

Zaune take bakin gado tana ba yaro nono Hassan ya shigo.

Kallonta yake tamkar ba ita ba, ta kara kyau haka ta cika ko ta ina ma sha Allah.

A hankali ta aje yaron kasancewar ya yi bacci.

“An yi wa yaron nan huduba kuwa?”

“A’a.” ta ba shi amsa a takaice.

“miko shi.”

Ba ta yi musu ba ta mika mishi shi, a daidai lokacin da yake zama gefen gadon.

Ya zuba mishi ido, kamar yana son gano wani kuskure a halittarshi, sai dai wani irin tausayin shi yake ji, ji yake ina wani na iya karbar ma wani cuta, da ya karbe ta shi, ya karawa kansa, koda hakan yana nufin kawo karshen numfashin shi.

“Wane suna kike so?” ya yi maganar hade da sauke ajiyar zuciya. 

“Aliyu.” ta kuma ba shi amsa a takaice.

Da Aliyun ya yi mishi huduba sannan ya aje shi hade da fuskantar ta.

“Ina so mu yi hakuri Asiya,, mu rumgumi kaddara mu gina rayuwarmu da ta yaranmu, bana son ina kallon ki a irin wannan yanayin, kuma kin san likita ya ce ba a son yawan damuwa. Don Allah ki yarda ba zan taba yin abin da zai cutar da ke ba. Wlh idan ni na sanya miki cutar nan ban san ina da ita, ki yarda ba zan cutar da ke ba. “

“Zan yi kokari sha Allah.” ta yi maganar a hankali 

“Akwai wani da muka zauna daki daya da shi a lokacin da nake service, shi ne kawai zan iya tunawa mun yi shearing din abubuwa musamman shaving stick nail cutter da Kuma Reza. amma kuma mutumin kirki ne, shi ne ma yake mana jam’in sallah. Na rasa ta ya zan fara tuhumarsa a kan wannan.”

Shiru Asiya ta yi tana juya batun, daga bisani kuma ta ce” Mu jira a gama hudimar suna mun yi tattauna a kan batun. “

“Akwai abin da kike bukata ne? “

Girgiza kai ta yi hade da fadin” Dama mai ne ya kasa da ake yin doughnut, kuma an karo, babu wani abu da ake bukata. Gaskiya ka yi kokari Allah ya saka da mafificin alkairi.”

Karon farko da ta yabe shi tun bayan faruwar wannan badakalar. Sosai ya ji dadi, da lallausan murmushi ya kalleta” kin cancanci fiye da haka ma Rabin Raina.”

Ita ma siririn murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba.

“Kin yi kyau, na kasa hakura, waye ya yi miki lallen nan kamar ya zana da computer?”

Hannunta ta bi da kallo,” sai na ga ya fi kyau yanzu da ka yaba.”

Cikin murmushi ya janyo hannun hade da kissing na shi “Ga tukuici nan.”

Murmushi ta yi hade da janye hannunta saboda shigowar Aunty Muna.

Ita kanta ba ta san Hassan din na ciki ba, duk sai ta daburce hade da kame-kame.

Shi ma bai ce komai ba ya fice.

*****

Ranar suna yaro ya ci Aliyul-haidar

Sosai sunan ya kayatar an yi bajinta, Asiya har ta manta tana da wata damuwa saboda yadda mutane suka debe mata kewa, yan’uwa suka mantar da ita komai.

Saboda gidanta cika ya yi dam, ta sha hotuna kam, haka ta yi kwalliya ta tsadaddun kaya daga lace, shadda da atamfofi.

Ta yi kyau tamkar ranar ne aka daura auranta, ta samu kyaututtuka daga yan’uwa, kawaye, abokan arziki da na aiki.

Sosai ta rika samun kulawa a wajen su Hajjah, Addah da kuma mahaifanta maza.

Kowa kokarin nuna mata yake yana tare da ita, babu wanda yake nuna kyama a garesu, kullum kwarin gwiwa ake basu.

Hakan ya sa Asiya ta rage yawan damuwarta, musamman da ta koma aiki har mantawa take yi ma tana da cutar wani lokaci.

Aliyu ma yana samun kulawa sosai ta bangaren magunguna da abinci, shi ya sa idan ka kallesa ba ka taba cewa yana da wata cuta haka ma iyayensa.

 girmansa yake ta yi saboda yanzu ta daina ba shi nono sai madara, shi ya sa idan za ta tafi aiki sai ta kawo ma Addah shi, idan ta taso sai ta dauke shi.

Rayuwarsu dai ta komai daidai, ciwon ya zama jiki, sun daina yawan damuwa kamar da, musamman yadda likitan kullum yake kara musu kwarin gwiwa.

*****

Yau kam misalin 6pm ta shigo gidansu (family house) kamar Kullum bangaren Addah ta fara shiga, Haidar ne ke ta wasanshi cikin tafiyarsa da ba ta gama nuna ba, yana ganinta ya yo kanta cikin murna.

Ita ma da sauri ta yi wajen tararsa hade da daga shi ta manna shi a krijinta tana dariya.

Sosai take son Haidar irin son nan da baya misultuwa, ko kadan ba ta son ta ga wani abu ya same shi, idan ta ji zazzabi a jikinsa to ko abinci ba ta iya ci cikin salama.

“Oyoyo my lovely son. How are you doing?”

“Fan” ya ba ta amsa cikin maganarsa mara dadi a daidai lokacin da take zama kan kujera.

“Ina Addah?”

Sauka ya yi a kan jikinta ya ruga zuwa bedroom sai ga shi ya fito rike da hannun Addah.

“Ban ji shigowarki ba, muna waya da Zainab ne.”

“Tana lafiya ko?” Asiya ta tambaya hade da duban Addah.

“Eh. Wai tana son zuwa gida ne, ta kuma gaji da calabar din.”

“Ita kam ba za ta zauna a wuri daya ba ne? Kullum sai yawo ba ta gidan gwauro ba ta gidan mai mata.” Asiya ta yi maganar rike da haba.

“Ke ma dai kya fada an yi wa ‘ya mugun miji.”

“Dazu na yi waya da ita, ta ce min Iman ba ta jin dadi, ba ta fada min tana son zuwa gidan ba ma.” cewar Asiya hankalinta na kan Haidar da ke kokarin amshe wayar da ke hannunta. 

“To ni kuma ba ta fada min Iman din ba ta da lafiya ba ma.” Addah ta fada da alamun mamaki a kan fuskarta. 

Shigowar Jamila ne ya sanyasu mayar da hankalinsu a kanta

“Yarorona!” ta fada hade da saurin cafe Haidar da ya yi kanta cike da dokin ganin ta 

Sama ta daga shi tana mishi wasa, daga bisani ta sauke shi hade da dakko Nutri milk ta mika mishi. 

A daidai lokacin ne kuma ta gaishe da su Addah 

“Wai sai yanzu kika dawo school din?” Asiya ta tambaya tana kallon Jamila 

“Eh. Lecture ne da ni 4-6.” 

Kafin su yi magana Ahmad yaron Aunty Amarya ya shigo

“Aunty yau ba ki gaishe ni ba a gidan radio.” 

Duk suka yi dariya 

“Amadi kullum sai na gaisheka?” 

“Eh mana.” ya yi maganar daidai yana mikawa Adda ƙaramin food flask. 

“Ga shi in ji Umma.” 

“To na gode” Addah ta fada a daidai lokacin da su Asiya suke ficewa falon Jamila dauke da Haidar suna ta surutu.

Hajjah na kabbara sallahr magriba suka shiga, hakan ya sa Jamila ta sauke Haidar ta wuce yin alwala.

Ita ma Asiya alwallar ta yo don gabatar da sallahr magriba

“Yaron nan ya karo wulakanci fa” Jamila ta yi maganar daidai tana daga Haidar da ya haye wuyan Asiya da ke Sujjada.

Dariya Hajja ta yi kafin ta ce “Haka yake yi wallahi. Ranar can haka ya haye min wuya wajen 5mins ina a Sujjada.”

Asiya ma ta yi dariya daidai tana nade sallaya, bayan da ta idar da sallah. 

“Haidar kam ma sha Allah akwai rashin ji, ga surutu bakin ma ba dadi.” Asiya ta fada daidai tana ajiye sallahyar

“Ranar can ya ban dariya wai yana sallah zo ki ga sujuda Aunty ” Jamila ta yi maganar lokacin da take aje masu abinci.

Tuwon shinkafa ne miyar ganye da nama, Haidar ne ke bin naman nasu yana dauka ya tauna sai ya zubar kasa.

Jamila kuma na tsincewa tana ci.

“Me ya sa kike cin wanda ya tauna ne ya zubar?” Asiya ta yi tambayar hade da kallon Jamila.

“Ai haka suke yi, shi kuma da ya ga tana ci, har nuna mata yake yi.” cewar Hajjah a lokacin da take cin tuwonta

“Amma bai kamata tana ci ba Hajja ” Asiya ta kuma fada a hankali

“Me ya sa Aunty, ba kyau ne?”

“A’a. Kin san dai ba lafiya ne da shi ba, bai kamata kina cin abin da ya tauna ba, saboda jininsa zai iya shiga ciki ba tare da an sani ba.” cewar Asiya tana kallon Jamila

Baki jamila ta tabe kafin ta ce “Manta da wannan Aunty, ni ko maganar ma bana so.”

“Ki dai kiyaye” Asiya ta kuma jaddada mata.

Hajja dai ba ta ce komai ba, illa zuciyarta da ta yi rauni, sosai take tausayin Asiya da kaddara ta fadama wa, amma kuma ta fi tausayin Haidar da bai san ma me duniya take ciki ba.

Sai a nan gaba ne na shi kalubalen zai fara.

Sai dai kullum tana addu’ar Allah ya yaye mishi cutar tun da likita ya ce ana warkewa.

<< Labarin Asiya 11Labarin Asiya 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×