Yau da wuri ta baro wurin aiki, abinci take son shiryawa na alfarma saboda zuwan bakon Hassan.
Dama an ce wai aiki da mai goyo da mai ciki sam baya sauri, don kuwa wasa-wasa Asiya ba ta kammala komai ba sai wajen biyar saura
A lokacin ta samu damar yin wanka inda ta sanya tsaddaden lace mai kalar (purple) simple dinki ne riga da zane (normal) amma sosai kayan suka karbeta duk da fuskarta babu heavy makeup.
Zaune take tana ba Zee kununta lokacin da sakon Hassan ya shigo inda yake tabbatar mata nan da mintuna biyar zasu iso shi.
Dalilin da ya sa kenan ta hanzarta ba Zee kunun hade da gyara mata jiki, a buga kofar ya yi daidai da gama jona turaren wutar da ta yi , hakan ya sa ta yi saurin saba Zee a kafadarta, lokaci daya kuma ta nufi kofar.
Suka shigo hannun Hassan rike da karamar jakar Mukhtar ta matafiya, fuskokinsu sun bayyana irin farin cikin da suke ciki, ita ma sai ta shiga taya su farin cikin, ta hanyar fadada fara’arta.
A babban falon gidan suka yi masauki, yayin da Asiya ta shiga jera musu abinci a kan dinning,Sai da ta kammala ne sannan ta zauna, suka shiga gaisawa ita da Mukhtar.
Hirar su Hassan suke yi sosai, hirar da ta rika jefa su cikin nishadi, basu kadai ba, hatta Asiya da ke sauraronsu, wani lokacin ba ta sanin lokacin da take darawa.
Zee kam ta ki yarda bakon ya dauke ta, ta ma ki barin jikin mamanta bare ya san ran za ta zo wajen sa, ga shi ya nace da son daukar tata.
Bayan taba hirar tasu ce suka, was Asiya ta yi musu jagora zuwa dinning, ita ce ta yi saving nasu da fried rice, cos low, da kuma Pepechikens.
Dispenser ta janyo gabansu inda ta coconut juice, hade da aje musu kananun cups.
Wani irin sanyin dadi na fita kunya Hassan yake ji a can kasan zuciyarsa, domin iya fita kunya kam Asiya ta gama fitar da shi kunya, ya san dai babu ta inda abokin nashi zai kalubalance shi, mace dirarra kyakkyawa, mai ilmi, tsafta ga iya girki, t
Eh gaskiyar Hassan, saboda tuni Mukhtar ya dorawa rayuwar gidan abokin nasa excellent, sun burger shi matuka, ya ji kamar su yi ma canjen rayuwa, ya dade yana irin wannan mafarkin sai dai har yanzu ya kasa zame masa zahiri.
Amma ga Hassan da alama ya cika duk wani buri nasa, ba shi da wata damuwa yana zaune cikin iyalansa yana rayuwar farin ciki.
Daidai tana jera masu snack Jamila ta turo kofa hade da sallama
A guje Haidar ya karaso yana fadin “Momy sauke mun ƙanwa (haka yake kiran Zee) na sawo mata yar Baby mai magana.”
Ita ma Zee din tun da ta gan su zillo kawai take kamar za ta kwance zanen goyon ta sakko.
Dole Asiya ta sauke ta kasa,, Haidar ya aje mata babyn.
Jamila kuma ta shiga gaishe da su Hassan cike da girmamawa, kafin ta mayar da hankalinta kansu Haidar da suka cika wurin da hayaniyarsu da karar baby.
“Haidar ba ka ga mutane ba ne, ba gaisuwa?” A natse Jamila ke maganar lokaci daya kuma tana daukar Zee
Amma Zee din ta rika zukewa alamar ba ta son daukar.
“Ki ji yarinyar nan fa Aunty, wallahi don ita na biyo gidan nan amma kalli wulakancin da take min.”
Dukkansu suka yi dariya har da Mukhtar da yake wasa da Haidar tun bayan da ya amsa gaisuwar Haidar din ya janye shi jikinsa,, haka nan ya ji yaron ya shiga ransa,, yana son yara sosai, shi ya sa baya gajiya da kallon mace idan ta yi goyo.
Yanzu kuma kallon sa gabadaya ya koma kan Jamila ko bai tambaya ba ya san kanwar Asiya ce, saboda kamarta da Asiya har ta yi yawa.
Ya kasa dauke idonsa akansu, haka nan yake ta murmushi komansu burge shi yake.
Bai ji dadin yadda suka bar wajen ba, kamar ya ce ku dawo ku ci gaba da hirarku.
Bayan tafiyarsu ne Hassan ke shaidawa Mukhtar Haidar ma ɗansa ne.
Sosai ya yi mamaki don bai yi tunanin Hassan na da wani yaron ba kuma, duk da akwai kamanni Hassan din sosai a tare da Haidar.
Fitowar su Asiya ce ta katse masu hirar da suke yi
“Malam ka zo ku tafi, ko za ka kwana a nan!” Asiya ta yi maganar tana kallon Haidar da ke zaune a kan cinyar Mukhtar
“Kin kira shi da sunan da ya fi so” Jamila ta fada cikin murmushi
Asiya ma murmushin ta mayar mata kafin ta ce
“Ai sai ya dage, zama Malam ba hawa cinyar Addah da Hajjah ba ne”
Wannan karon sautin dariyarsu ta fita sosai dalilin da ya sa Jamila saurin bude kofa kenan ta fice sabe da Zee
Asiya ma ta bi bayanta hannunta rike da na Haidar.
Q
Yau kam ba ta tsaya jiran Hassan ba, tana gama kominta na al’adar kwanciya sai kawai ta yi kwanciyarta, saboda yadda take jiyo hirarsu bai yi alamar akwai bacci a idanunsu ba.
A can bangaren kuwa Mukhtar ne ya gyara zama alamun wannan karon maganar tasa akwai muhimmanci.
“Abokina maganar gaskiya family naka ya burgeni ma sha Allah, na tayaka murna.”
Dariyar jin dadi ya yi kafin ya ce “Na gode sosai abokina, tun dazu kake ta fadar maganar nan.”
“Ba kuma zan daina ba har sai na bar gidan nan, a waya ma haka zan rika damunka, ba za ka gane baiwar da Allah ya yi maka ba ne saboda kana tare da baiwar, amma mu da bamu da ita kuma ta yi mana wuyar samu mune zamu fada ma Allah ya yi maka baiwa. Ka gara gode mishi, a duniya kam Allah ya bar ka da imaninka, sannan ya ba ka lafiya da iyali da arziki to gaskiya ka gode mishi a ko wace Sujjada ta ka, don kuwa ya yi maka abin da mutane da yawa suke nema.”
Mukhtar ya kai karshen maganar tasa da duban Hassan da ya yi fakare da kunnuwa yana saurare hade da nazarin maganar.
” Za ka yarda da ni idan ka dubi rayuwar wasu,, wasu ga kudin sai Allah ya karbe lafiyar, kudin kuma su ki amfanarsu wajen samun lafiyar, wasu ga lafiya da kudin Allah sai ya hanasu haihuwa, wasu ga lafiya ga zuri’a amma kuma basu da abin da zasu ciyar da zuri’a. “
” Gaskiya ne abokina na gamsu da wannan bayani naka. Alhamdulillah mun godewa Allah. Amma kai ma kai ne ba ka so yin aure ba, saboda Allah ya ba ka komai da za ka iya rike mata.” cewar Hassan yana kallon Mukhtar.
Murmushi Mukhtar ya yi kafin ya ce” A can gida ma fa haka suke damuna kullum yanzu kam cewa ma suke yi wai aljana ce ta aure ni saboda ni ban nemo mata ba kuma sun ba ni naki karba”
Hassan ya tare karshen maganar tasa da dariya, kafin ya ce
“Dole su fadi haka mana, tun da dai ai ka kai munzalin ma ka rike mata biyu. Kodai har yanzun ba ka ga wacce kake so ba ne?” Hassan ya rufe maganar tasa da tambayar Mukhtar
“Haba duk matan nan, na samu mana ko yau ma na kara samun wata, wacce tun da nake duniya ban taba jin naso wata mace kamar ita ba.”
“A ina kenan ka gan ta?” Hassan ya kuma, jefa mishi tambaya hankalinsa a kansa.
“A gidan nan”
“Kana nufin Jamila?” tambayar Hassan cikin zakuwa
“Idan sunanta kenan to tabbas ita.”
“Kai Ma sha Allah, gaskiya na yi farin ciki, Jamila kanwar matata ce uwa daya uba daya, sannan kuma kanwata ce, ba ta da matsala ba don tana yar ‘uwata ba, zan shige ma gaba sha Allah idan akwai alkairi a ciki za ka aureta.” Hassan ya rufe maganar tasa yana kallon Mukhtar da ya yi shiru kamar akwai wani abu da yake tunani daban.
“Ai babu wanda zai ki son hada zuri’a da kai,, don zaman da muka yi na fahimci kai mutumin kirki ne, kana da duk wasu qualities da ko wane uba zai so aura maka yarsa.”
Girgiza kai Mukhtar ya shiga yi, yayin da fuskarsa ta canja zuwa tsantsar damuwa.
“Ina da matsala Hassan wacce za ta hana ko wane uba ba ni auran yarsa”
Shiru Hassan ya yi yana kallon Mukhtar, baya son tsanantawa amma tabbas da ya tambaye sa wace matsala ce.
“Akwai sirrin da nake boyewa, wanda na ki fadawa kowa ciki kuwa har da iyayena, saboda ban san ya zasu dauki abun ba. Wannan abun da nake boyewa shi ne ya hanani aure duk kuwa da ina tsananin bukatar sa.”
Shiru ya ratsa wajen kafin daga bisani suka sauke ajiyar zuciya a tare mai nauyi.
“Hassan! ” Mukhtar ya kira sunan a hankali
Bai sami damar amsawa ba illa dai ya zubawa Mukhtar ido.
“Allah ne ya kama ni, ya nuna mini kuskurena na saba mishi, na san za ka girgiza sosai idan na fada ma ina da cutar Kanjamau.”
Wani irin dummm! Hassan ya ji a zuciyarsa, duk kuwa da yana dauke da cutar hakan bai hana shi firgita ba. Dalilin da ya sa kenan ya kasa cewa komai sai ido da ya zubawa Mukhtar.
Cikin raunannar murya Mukhtar ya ce” A duk duniya babu wanda ya san wannan zancen daga ni sai kai, sai likitan da ya tabbatar min da hakan da kuma inda na samu cutar. Ka sha taimakona lokacin da muna tare ban sani ba ko a wannan gabar ma akwai taimakon da za ka yi min. “
Ajiyar zuciya Hassan ya yi kafin ya ce” Na tausaya ma sosai kuma na ji ba dadi, ina rokon Allah da ya bamu lafiya ba ki dayanmu.”
“Amin” cewar Mukhtar cikin sanyin murya.
“Amma kana shan magani dai ko?”
“Bana sha, ina jin kunya da tsoron a ganni bangaren masu cutar ina karbar magani, ka san kuwa irin kimata da mutumcina a yankinmu?”
Siririn murmushi Hassan ya yi “Hakan ba zai hana kuma ka nemi lafiyarka ba, cutar nan tana da illa sosai amma shan magani kan ruguza tasirinta. Kuma fa kin zuwa asibitin kan sanya ta rikide ta zama Aids. Ya kamata ma ka je asibiti a tantance ma H. I. V ce ko Aids din.”
Shiru Mukhtar ya yi ba tare ya ce komai ba.
“Wannan fa ba abin damuwa ba ne, mutane masu dauke da cutar suna nan suna rayuwa kamar sauran mutane,, suna aure, suna haihuwa suna kuma auraswa.”
“Suna aure fa ka ce, to waye zai aure su?” Mukhtar ya yi tambayar cike da mamaki.
“Masu irin cutarsu mana.”
“To yaran da zasu haifafa?” Mukhtar ya kuma yin wata tambayar
“Akwai matakan da likitoci kan dauka a haifi lafiyayyen yaro, ni kaina shaida ne a kan hakan.”
Zama Mukhtar ya gyara “Allah abokina, to amma ni a ina zan samu mai cutar in aura bayan kasan kowa boye ta yake yi.”
“a cibiyar kula da masu cutar a nan za ka samu.”
Duk suka yi shiru alamun kowa da abin da yake tunani.
Shi dai Hassan yana tunanin yadda Allah ya nuna mishi in da ya samu wannan cuta ba tare da ya tonawa kansa asiri ba a wajen abokinsa.
Tabbas yana zargin cudanya da Mukhtar ita ta sanya shi kamuwa da wannan cutar.
Bai taba tsammanin Mukhtar zai hada hanya da cutar ba. Saboda ba kama,
Kasancewarsa mai addini hadi da riko da shi, yana da halaye masu kyau sosai shi ya sa ma ya saki jiki da shi sosai.
Lalle maganar Hausawa ta tabbata, inda suka ce wai an ce ma wani “Allah gafarta Malam” ya ce “A baka ba.”
Aka ce “a zuci fa”
Ya ce “Kai dai ga mutum”
Wannan batu kam haka yake, don haka sifa ko dabi’un mutum na zahiri kar su hana yin bincike kafin aure, don kuwa ana iya yin kitso da kwarkwata.
“Yanzu dai shawarata gare ka shi ne, kana komawa ka je asibiti ka binciki lafiyarka, duk abun da sakamakonka ya nuna to hakan zai sanya in ga ta ina zan fara taimakonka. Amma kafin sannan ka cire damuwa a ranka don Allah kada wata cutar kuma ta kara samun ka.”
Hassan ya katse musu shirun.
Kai kawai Mukhtar ya jinjina hade da share hawayen da ke sauka a fuskarsa.
“Abokina ina matukar tsanar kaina, a duk lokacin dana tuna zina ce silar da na samu cutar nan, ban taba tsammanin zan aikata zina ba, kai Subhanallah Allah ya sa mu fi karfin zukatanmu.”
“Amin” Hassan ya fada cikin dakusasshiyar murya.
mikewa ya yi hade da dafa kafadun shi.” Ya kamata mu kwanta ka ga har biyu saura na dare, ga shi gobe sammako za ka yi. “
“Ba damuwa” Mukhtar ya fada hade da mikawa Hassan hannu.
Hassan ya nuna mishi masaukinsa da Asiya ta gyare tsab hade da saka duk wani abu da zai bukata, ga kamshi mai dadi yana fita.
Bacci kuwa mai dadi Mukhtar ya yi, saboda wata natsuwa da farin cikin kalaman Hassan a gare sa
Hassan bai samu kebewa da Asiya ba, kasancewar ita ma da sassafe ta fita, shi ma kuma da safen ya fita rakiyar Mukhtar tasha.
Yanzu ma sai misalin goma na dare ya shigo dakin nata, a lokacin zaune take kan gado ta tasa laptop dinta a gaba, ganinsa ya sanya ta dago kai.
1
“Ba ki yi bacci ba?” ya yi saurin tambaya.
“Ina ni Ina bacci shugaban gida na waje.”
Zama ya yi kusa da ita hade da kwantar da kansa a kan kafadarta, a hankali yake shakar sansanyar kamshinta.
“Me kike yi ne?”
“Zaman jiran dawowarka.”
Ya saki murmushi, lokaci daya kuma yana
sauke ajiyar zuciya.
“Labaran da za a gabatar gobe ne nake tacewa.” ta yi maganar hade da rufe laptop din bayan ta yi saving aikin nata.
Ture laptop din ta yi daidai da janyo ta zuwa jikinsa, a hankali yake magana cikin muryar da ta kashe mata jiki
“Na cuceku Asiya sakacina da rashin lurata ya jefa ku cikin tsaka mai wuya, ina ma ace iya kaina abun ya tsaya. Don Allah ku yafe min. Ina tausayin Haidar sosai nan gaba, ban san da wane idon zan kalle sa ba sannan ban san ya rayuwarsa za ta kasance ba, lallai zai ji kunci fiye damu. Ga Zainab da ba ta taba dandana nononki ba a matsayinki na mahaifiyarta, ita ba ta san dadin nono ba, alhakinta kadai bai ishe ni kaya ba Rabin Raina? ” ya karasa maganarmu cike da sanyin murya
A hankali Asiya ta zame jikinta daga rungumar da ya yi mata, ita ma rungume shin ta yi hade da bubbuga bayansa alamar lallashi.
“Haba Abban Haidar, ina mun riga mun rufe wannan babin, me ya sa kake son maido shi baya? kaddararmu ce haka dole kuma mu sanya hannu biyu mu karba. Me muka rasa Allah ya wadatamu da komai kada mu yi masa butulci mana don wannan.”
Jikinsa ya janye a hankali, lokaci daya kuma ya kama hannayenta biyu ya rike ya zuba mata ido.
“Ba ki san ya nake ji a zuciyata ba tun bayan da, Mukhtar ya shaida min yana dauke da cutar H. I.V wannan ya tabbatar min na samu cutar ne daga gare shi. “
Asiya da ta saki baki tun lokacin da ya fara magana, ta rufe bakin a hankali hade da tambayarsa “wai wane Mukhtar din?”
“Wanda ya zo jiya.”
Ta yi saurin janye hannayenta.
“Fahimtar da ni da kyau Abban Haidar?”
A natse ya zayyane mata duk abin da ya faru tsakanin sa da Mukhtar.
Maimakon ta ji tsanar Mukhtar ko haushinsa sai ta ji tausayinsa ya cika ko wane bangare na zuciyarta.
Saboda shi har yanzu bai da madafa, su kuwa suna rayuwarsu cikin dadi ba tare da matsaloli masu yawa ba
Idan har ta shiga rayuwarsa ta hanyar hada shi da Kubrah da suka hadu kasa da wata daya baya wajen amsar magani tabbas za ta taimakesu, don kuwa ita ma tana bukatar abokin rayuwa, matashiyar budurwa ce mai ilmi da hankali.
“Subhanallah! So painful Rabin Raina”
“of course, na tausaya mishi, ban san ta ya zan taimake shi ba, musamman ganin ya cika burinsa na zama uba.”
“Ni zan taimake shi idan har zai iya auran bazawara.”Asiya ta yi maganar jiki a sanyaye
Kallon karin bayani Hassan yake mata
“Akwai wata da muka hadu wajen amsar magani, duka watanta biyar da aure mijinta ya rasu, ashe yana dauke da cutar H. I. V ya aureta ba a sani ba. Yana da kudi sosai kila hakan ne ya hana a zurfafa bincike a kansa.
Yanzu haka ta kusa fita takaba, idan yana sonta zan hadasu, don sosai take ba ni tausayi.yarinya ce mai kananun shekaru, Kuma na san za ta amince da shi sha Allah.”
Kai ya jinjina kafin ya ce” Zan sanar da shi, amma wai me ya sa mutane ke kin yin gwajin cutar nan kafin aure, saboda kawai don sun yarda da dabi’un mutum ko yana da kudi, ganin laushi ai bai kamata ya hana tankade ba. “
“Kai me ya sa ba ka yi ba? ” Asiya ta mayar masa da tambayar cikin wasa.
“ki fahimta mu daban, a tunaninki idan wani daban ne a waje za ki aure sa ba tare da an yi mishi test ba?”
Kai ta girgiza alamar A’a
“You see! Wannan ma fa wani sakacin ne muke kara yi, ya kamata koma waye zai auri yarka, kanwarka to a yi test kafin aure, shi ne zai hana danasanin irin namu. Saboda ganin mu dakan daka shikar daka tankaden bakin gado za a yi, shi ya hana a karfafa maganar test din, yanzu kin ga ai ya zame mana izna.”
“Gaskiya kam,, haka haihuwa daya horon mahaifa “
Cewar Asiya lokacin da ta mike don shiga toilet.
Bayan ta fito ne ta kuma jaddadama Hassan a kan ya tuntubi Mukhtar sannan kuma ya je asibiti a tantance wace irin kwayar cutar ce a jikinsa
Idan H. I. V ce to za ta fara kokarin hada shi da Kubrah.
Da alkawarin zai yi duk yadda ta bukata Hassan ya rufe masu hirar hade da jan bargo suka yi addu’ar bacci.