Ranar da aka yi addu’ar uku, da yawan mutane sun tafi, sai ma fi kusanci kawai aka bari, Hajjah har zuwa lokacin tana asibiti Addah ce a wurinta.
Asiya kwance kan kujera,, jikinta sanye da zumbulelen hijabi, hannunta rike da casbaha. Ita kadai ta san ciwon da kuma dacin da take ji a zuciyarta, gani take kamar mafarki wai Aliyunta ya rasu. Mutuwa akwai zafi, musamman ta mukusanci, wanda aka yi ma wa ne kawai zai shaida irin zafin.
Ta mayar da dubanta zuwa tsakiyar falon, in da kunnenta ke dakko mata hirar su Aunty Muna,, Zee, Jamila Kubra dasu Sadiya.
Labarin rasuwar Haidar Jamila ke basu cike da jimami “Wallahi Aunty, ni dai na dawo daga rakiyar Aunty Asiya nan na wuce shi kan Kujera a kwance ringingine bayan ya bude Kur’ani ya rufe fuskarsa,, sai wayar Adda da yake sauraron karatun kur’ani,, ban yi magana ba na wuce .”
Ta dan tsaya don hadiye yawu.
“Sai bayan da na yi sallah na fito zan zuba abinci a kitchen sai na kuma ganin shi kwance kamar dai yadda na bar shi. Nai ta kiran sunansa na ji bai amsa na yi tunanin ko bacci yake, sai na matsa ina taba shi sai na ga ya fado, na tsorata sosai, dalilin da ya sa na kira Hajjah kenan, tana ganin sa na ji tana ta salallami wai ya rasu. “
“Allahu Akhbar! Allah ya jikansa. “Dukkansu suka fada, idan ka dauke Asiya da ba ta ce komai ba illa ta goge sabbin hawayen da ke bin kuncinta, ba ta san ranar da za ta daina kukan mutuwar Haidar ba, ji take kamar ba za ta kara farin ciki ba a duniya.
Mamakin yadda mutane ke cin abinci a kwanakin nan take yi, tamkar gidan biki haka ake dorawa gami da saukewa. Amma da an sauke sai a nemi abincin a rasa.
Da me mutum zai ji ne, da mutuwar da aka yi masa koda maganar dora abinci.
Ita kadai take jin abin da take ji, gani take sauran duk basu damu ba, don kuwa abincinsu suke ci suna hirarrakinsu har da dariya.
Sai an jima kuma suka fara jimami, ita surutansu damunta yake yi, ba ta son a yi mata magana ko kadan, kuma ba ta son wasu suna yi a gabanta.
A yanzu ma surutun nasu ne ya ishe ta,, hakan ya sa ta mike tsaye, a hankali take takawa saboda jirin da take gani idan ta mike, ta san kuma rashin cin abinci ne da bacci, to ko ta dauki abincin da zummar ci ba ta iyawa. Sai ta ji shi kamar kasa.
Tsakar gidan ta fita tana takawa a hankali asibiti take son zuwa ta ga Hajjah don kuwa tun da aka kai ta asibitin ba ta samu ta je ba.
Tun daga nesa Hassan da ke zaune a cikin rumfa tare da yan amsar gaisuwa ya hangota, tafiya take tana hada hanya.
Cikin sauri ya tare ta gami da jan ta gefe guda.
Tun da aka yi rasuwar sai yau ne suka kebe da shi, kuma yau ne ta kare masa kallo,, ya yi mugun zubewa har tsoro ya ba ta.
“Ina za ki je?” ya tambaye ta, hade da lasar busassun labbansa.
“Zan dubo Hajja ne.” ta ba shi amsa hade da dukawa ji take kamar za ta fadi.
“Mu je to in kai ki.”
A motar ma shiru ne ya biyo baya har suka isa asibitin babu wanda ya yi magana.
Har mamakin irin rama da halin damuwar da Hassan yake ciki take yi, saboda ganin ta kamar Hassan bai shaku da Aliyu sosai ba.
Kasancewar ba a wurinsu Aliyu yake ba, shi kuma Hassan yana kwana biyu bai shiga gidan ba, sometimes ma lokacin da zai je Haidar na makaranta.
Bayan ya yi parking, shi ne ya bude mata kofar hade da tambayar za ta iya tafiya.
Kai ta gyada alamar eh
Bayanta ya bi suna tafiya a hankali har suka karasa dakin da Hajja ke kwance.
Ba ƙaramin tsorata ta yi da yadda ta ga Hajjah ba, ta wani kode ta rame sai fata,, tsufanta ya bayyana sosai.
Dukawa Asiya ta yi gaban gadon da Hajjah ke kwance, ta saki kuka a hankali, wanda ya sanya Hajjah ta shi zaune hade shafa kan Asiyar alamar lallashi
“Hajjah don Allah kar ki tafi ke ma ki bar mu, kin ga yadda kika zama Hajja,, idan kika tafi ni ma mutuwa zan yi”
Duk da Hajja ba ta jin wani karfi, hakan bai hana ta janyo Asiya jikinta ba hade da bubbuga bayanta.
Yayin da hawaye ke kwaranya a idonta,, ita kadai ta san yadda mutuwar Aliyu ta doki kirjinta,, ko yaranta da take haihuwa a baya suna mutuwa ba ta taba jin mutuwarsu irin yadda ta ji ta Aliyu ba, sunan kawai Asiya ta haifeshi ne, amma tana yi mishi wani so fiye da yadda take jin son Asiya a kirjinta.
Shigowar likita ne ya sa Hajjah ta saki Asiya hade da share hawayenta.
“Wacece ke?” likitan ya tambaya yana yiwa Asiya wani kallo
“Ƴata ce” Hajja ta ba shi amsa.
“Amma Hajiya mun fada miki bama son abin da zai kara sanya ki a damuwa ko? Don haka ta fita, kar kuma ta kara dawowa sai kin koma gida kwa hadu”
Asiya ba ta son yin magana amma kam da can baya ne bai isa ba.
Hajja ta zubawa ido tana kallon ta cikin maraicewa
“Ta shi ki je, duk lokacin da kika kara samun dama ki dawo. Don Allah ki rika cin abinci Asiya kwana uku duk kin rame,, ke da Hassan din ban san wa ya fi wani rama ba”
Asiya ta share hawayenta gami da fadin “Sai kin dawo gida,, ina kallonki a gabana zan iya ci, amma a yanzu ba zan iya ba.”
Murmushin karfin hali Hajjah ta yi kafin ta ce “I will be back soon my daughter”
Duk suka yi murmushi sannan Asiyar ta fita zuwa inda Adda take zaune da Hassan.
Nasiha sosai take masu da karfafa masu gwiwa da kafa masu misalan da zasu rage masu damuwarsu.
A zuciyar Asiya kuwa fadi take “Irin su Addah sune abokan zama idan an yi ma mutuwa, sune zasu rika kwantar ma da hankali, ba masu cika baki da abinci ba suna dorawa da ruwa suna cewa Allah ya bada hakuri. Wasu hirarsu ma ba ta tashi sai sun zo gidan mutuwa har da gulma, don kuwa a kwanaki ukun nan labaran da Asiya ta ji sun yi yawa kuma wai daga bakin yan gaisuwa”
Wannan karon da kwarin gwiwa ta baro asibitin, Hassan yana aje ta dakin Addah ta shiga ta yi kwanciyarta don ba ta son hayaniyarsu, kara mata damuwa take yi.
Ranar da aka yi bakwai ranar kowa ya watse, su Kubrah ma ranar suka koma, Aunty Zee ce kawai ta rage a cikin bakin da suka zo daga nesa sai Alhaji Abdallah mahaifin Asiya, a ranar kuma aka sallamo Hajja zuwa gida,, ba laifi jikin nata ya dan yi kwari, amma da ta shigo gidan sai mutuwar Haidar ta dawo mata sabuwa,, musamman da ta kalli kofar dakin Addah, sai ta tuna watarana da ta fita ba tare da shi ba, har da kukansa sai ya bi ta, amma ta ki zuwa da shi.
Lokacin da ta dawo a nan kofar flat din Hajja ta same shi da sauran yara suna wasa.
Yaran suka ruga da gudu suna mata Oyoyo, amma shi ya yi kamar bai gan ta ba.
Hakan ya sa ta ta karaso kusa da shi tana tambayar “Wai wannan ba Haidar ba ne?”
“Ni ne.” ya ba ta amsa kansa a kasa.
“Ba ka ganni ba ne na dawo?” ta kuma tambayar sa cike da mamaki.
“Na gan ki.” har yanzu kansa a kasa.
“To ba ka gane ni ba ne?”
“Na gane ki.”
“Shi ne ba za ka min Oyoyo ba?”
Baki ya zumbura, “da na ce zan bi ki b a kin yarda kika yi ba.”
A lokacin dariya ta yi, a yanzu kuma hawaye ta yi don kuwa tana kallon yadda za ta yi rayuwa ba tare da Haidar ba a wannan gida.
Nasihohi Addah ta yi mata sosai bayan ta kai ta daki.
Alhaji Abdallah ma tarasu ya yi gabadaya ya yi masu nasiha da kalaman karfafa zuciya gami da karbar ko wace kalar kaddara idan ta zo masu.
A hankali komai yake wucewa yayin da sabbin abubuwa kan zama jiki a saba dasu.
Hakan ne ko ya faru, Asiya satinta biyu a gida, shi ma Alhaji Abdallah haka, saboda yanayin jikin matarsa, amma a ranar ya ba Asiya umarnin ta koma gida, sannan ta koma kan harkokinta, hakan zai debe mata kewa,, musamman kungiyarsu da kullum takan samu baki sama da biyar masu irin cutar sun zo don yin register da kungiyarsu.
Duk da Haidar ba a wurinta yake ba, amma da ta koma gidan sai ta ji ta so lonely.
Sai da ta fara zuwa aiki ne sannan kadaici ya fara raguwa a tare da ita. Amma kullum kewar Haidar take hade da tuna abubuwan da suka faru a lokacin da yake raye.
A yanzu kam ma ta fara dakewa da mutuwar Haidar,, da ko gaisuwa aka yi mata sai ta yi kwalla, yanzu tsab take amsawa ba tare da ko digon hawaye ba.
Mutuwar Haidar da wata biyu aka sha bikin Jamila, Asiya kam ta taka rawar gani, a matsayinta na babbar ya kuma uwa.
******
Zaune take a office nata kan kujera yayin da wayarta ke hannunta, videon Haidar da hotunansu na karshe take kallo, wanda ya zamar mata kamar ibada, muddin za ta samu lokaci to sai ta kalla. Ga hawaye na zuba,, amma kuma murmushi take yi, musamman yadda Jamila ke tsalle da shi a baya suna dariya.
Wani lokaci tana ganin mutuwar Haidar rahama ce a garesa da kuma su ba ki daya, saboda duk lokacin da ya girma kuma ya fahimci yana da wannan cutar, tabbas zai ji ina ma ace ya mutu bai rayuwa har zuwa wannan lokacin ba.
Hannu ta sanya gami da share hawayen da ke bin fuskarta, ko wane lokaci addu’ar ta gare shi ne Allah ya haskaka makwancinsa,, ya sanya wannan cuta ta zama kaffara a gareshi.
A hankali ta mike hade da daukar jakarta, saboda lokacin tashinta ya yi tun dazu.
Bayan fitowarta kasuwa ta wuce, digital Qur’an ta saya da kuma Alqur’ani, daga nan ta wuce Islamiyar su Haidar, don kuwa tun 2pm ake zuwa sai 6pm suke tashi. Tun bayan rasuwar tasa taso cika mishi alkawarin, amma abubuwa su kai ta fadowa, musamman na kungiyarsu, yanzu kungiyar na daya daga cikin abin da ke zamar da ita busy.
Bayan an yi mata iso ga shugaban makarantar ta zauna, malaman makarantar suka rika shigowa daya bayan daya suna gaishe ta
Sosai ta daure wajen rike hawayenta, bayan fitarsu ne ta mikawa shugaban makarantar ledar da ke hannunta, hade da yi mishi bayani a kansu.
Sosai ya yi farin ciki hade da godiya, da kuma yi mata alkawarin sha Allah za a rika yin amfani dasu kan lokaci a kuma hanyar da ta dace, ta yadda ladan zai rika iske Haidar a makwancinshi.
Daga nan Asiya ta bukaci idan akwai abin da makarantar ke bukata ya fada mata.
Ya gyara zama “Ma sha Allah Hajiya, bamu da wata matsala sosai sai ta rashin ruwa,, solarmu ya lalace mun kira mai gyara ya fada mana za ta ci 100k, shi ya sa muka dakata mu ga abin da Allah zai yi.”
“To ba matsala, ka ban account lambarka sai na tura ma,, in ya so sai a gyara, fatana ladan ya isa wajen Haidar” cewar Asiya tana kallon malamin.
Wata godiyar ya yi hade da ba ta account lambar.
Daga nan ta fito zuwa gida.
Sai take jin wani dadi, yau ta sake nauyin Haidar, Wanda tuni taso yin hakan.
Ita ma Hajja ba ta yada alkawari ba, duk ranar Juma’a ake sauka a Islamiya, kuma dama suna yin abinci a kai wa yan sauka,, har yanzu ba ta fasa ba,, duk ranar Friday sai ta yi.
Gidansu ta biya don daukar Baba amma fir ya ki bin ta yana wajen Addah, hakan ya sa kawai ta yi masu sallama ta tafi saboda za ta yi girki.
Gab magriba ta karasa girkin nata, ta kintsa wajen hade da turare gidan nata, alwalla ta yi game da yin sallahr magriba, tana kan sallayar ne ta ji bugun kofa, wannan ya tabbatar mata da Hassan ne ya dawo.
Da hanzari ta mike zuwa kofar, cike da mamaki take kallon mutane ukun da ke bin bayan Hassan, kafin ta yi wani yunkuri tuni sun fado falon gabadayansu lokaci daya kuma daya daga cikinsu ya dannawa kofar key.
Wani irin dukan tara-tara gabanta ke yi, lokacin da daya daga cikinsu ya dora mata bindiga a goshi yana fadin “Mu je ciki”
Dakin Hassan suka shiga, guda biyu ne suka bincike dakin tas suka kwashe duk kudin da suka gani, sannan suka kuma taso su gaba zuwa dakin Asiya.
A kan hanyar wucewarsu ne suka ga wata kofa, babban cikinsu ya ce “Kai ku bude kofar nan.”
Cikin rawar murya Asiya ta ce key din yana dakina
“Kai tasa keyarta ta dakko keyn” cewar babban nasu cikin wata murya mara dadin ji.
Hannu na rawa Asiya ta bude kofar lokacin da suka dawo daga dauko key din.
Ba komai a cikin dakin sai kayan tallafin masu HIV irinsu madarar yara, magunguna, pad, da kayan abinci.
“Me ye wannan?” ogan ya tambaya yana kallon Asiya.
“Kayan tallafi ne da muke ba masu cutar HIV” cewar Asiya a tsorace.
Ogan ya zubawa kayan da Asiya idon kafin ya ce “Kai mu ware zuwa dakinta, ba za a rasa abun tabawa ba.”
Bincike dakin Asiya suka yi tas, nan ma suka kwashe kudin ciki sannan suka fice.
Bayan Asiya ta tabbatar sun fita, ta juya kan Hassan jiki a mace “A ina ka hadu da su ne wai?” ita ce tambayar farko da ta fara mishi.
Ya sauke ajiyar zuciya “na bude karamar kofar gate zan shigo in bude babbar kofa daya ya fito a cikin mota kamar zai yi min tambaya, yana zuwa kawai sai ya turo ni ciki ya gwada min bindiga, sauran ma sai suka shigo.”
Gwalo ido ta yi cike da tsoro kafin ta ce “Ba ka kula suna bin ka a baya ba ne?”
“A kofar gidansu Maman Jesica fa naga motarsu a tsaye” ya ba ta amsa hade mikewa ya fice zuwa dakinsa don sam baya son yin magana. Ji yake kamar mafarki wai barayi sun shigo gidansu sun yi sata.
Asiya ta ja dogon sallalmi ta ajiye, mamakin abun take kamar a mafarki, sata da karfe bakwai na yamma, wannan wane irin abu ne.
Mikewa ta yi ta bi bayan Hassan. Kwance ta same shi, gefen shi ta zauna, hade da tallafe habarta shiru ta kasa cewa komai illa lokaci zuwa lokaci ta saki salati ta dora da fadin “Ikon Allah!”
Ta gaji da zamanta ta mike da niyyar fita
“Kar ki sake maganar nan ta fita” Hassan ya yi maganar a hankali.
A hanzarce ta juyo hade da zuba mishi ido “Kana nufin ba za mu yi report zuwa police station ba?”
“Idan mun yi ma ba lallai ne a kama su ba, don haka kawai ki yi shiru bana so a gida a ji, kar hankalinsu ya tashi.”
Tabe baki ta yi hade da ficewa dakin lokaci daya kuma tana mamakin maganarsa. Hade da laluben dalilinsa na kin yarda su yi report wa police bayan kuwa ba karamar sata aka yi masu ba.
Haka nan ta yi sallah cike da juya abin da ya samesu.
Samun kanta ta yi da jin tsoron kwanciya a dakinta, dalilin da ya sa kenan ta nufi dakin Hassan.
Maganganun kwantar da hankali ta rika mishi ganin yadda damuwa ta kwanta a kan fuskarsa.
Ba ta san karfin hali take yi ba sai can da dare ya yi, tsabar fargaba ya haifar mata da zazzabi, zuwa safe kuwa zazzabi mai zafi ya rufeta, ko ya ta rufe ido sai ta rika ganin mutanen tsaye da bindiga a kanta.
Wasa-wasa har ruwa ta sha, kwana hudu ko wurin aiki ba ta iya zuwa, yayin da yan dubiya suke ta faman zuwa dubata.
A rana cikon na biyar ne ta shirya don zuwa wajen aiki, kila za ta dan rage fargabar da ke damunta, don ana buga kofa sai ta ji kirjinta na laguden bugawa.
Doguwar riga (Abaya) a jikinta mai kalar baki, sai farin guntun hijab mai duwatsu da ta dora wanda ya tsaya iya kafadarta.
Fuskarta babu wata kwalliya idan ka dauke powder da man lebe sai yar ramar da ta yi wanda hakan ya sa fatarta ta yi haske.
Laptop din ta dauka, lokaci daya kuma ta dauki wayarta da kiran Hassan ke shigowa.
“Kin tafi ne? Abin da ya fara tambaya kenan bayan ta daga kiran.
“A’a. Amma dai na shirya ina shirin fitar kenan. “
“Ok dama so nake in fada miki an sallami su Zee daga asibiti kuma tana wajen Hajja ba gidan Jamila ba.”
“Ok!” ta fada hade da mayar da hankalinta a kan kofar da ake bugawa, gabanta yana faduwa ta nufi kofar,duk lokaci da aka buga kofa sai ta ji kamar zuciyar ta aka buga tsabar fargaba. Lokaci daya kuma tana cewa Hassan “Yanzu dai karfe shadaya na safe, ban sani ba ko in biya gidan Hajjar ko in bari sai na taso aiki ne ban sani ba.”
“Duk yadda kika yi dai.”
Ta bude kofar a daidai lokacin da Hassan ya yanke kiran.
Ba ta san lokacin da wayar da ke hannunta ta sullube zuwa kasa ba.
Mararta ta murda dandanan fitsari ya cika ta dam.
Mutumin ya shigo sosai hade da datse kofar ya zare key din.
Asiya ta kuma firgita sosai kallonsa kawai take a tsorace.
Fuskarsa ba za ta taba bace mata ba, saboda shi ne ya aje mata bindiga a goshi, kuma a cikin su ukun shi ne kawai fuskarsa a bude.
Tsaye take kamar zane yayin da jikinta babu inda ba ya rawa, shi ma kallonta yake a lokacin da ya cire facing cap nashi fuskarsa ta kara bayyana sosai.
Nice