Karamar jakar da ke hannunsa ya mika mata, har yanzu kallon shi take a tsorace ba tare da amshi jakar ba.
Da ido ya yi ma ta alamar ta amsa.
A tsora ce ta mika hannun hade da amsae jakar har zuwa lokacin ba ta dauke idonta a kan fuskarsa ba. Gani take da zarar ta dauke idon, abu mara kyau zai faru da ita.
Suka zubawa juna ido bayan ta karbi jakar na yan sakanni.
“Kudinku da muka dauka, duba kika gani sun cika?”
Ido ta kuma warowa cike da matsanan cin mamaki tana kallonsa.
Da ido ya kara yi mata alamar da gaske yake yi
Kafafuwanta da tun dazu suke neman kasa daukata ta ja a hankali zuwa kan kujera ta zauna, lokaci daya kuma ta bude jakar, kudin ne kuwa kwance a ciki.
“Ki kirga.” ya katse mata kallon da take masa da maganarshi.
“Ban san ko nawa kuka dauka ba ai.” muryarta akwai alamun tsoro sosai.
Ya dan nisa kadan, hade da rumgume hannayensa a kan kirjinsa yana kallonta kafin ya ce
“Sunana Umar, an haifeni a wani kauye ne, a nan kuma na taso, aji uku kawai na iya yi a makarantar gaba da primary na aje karatun saboda yadda ilmin ya yi tsada, abin takaicin kuma shi ne yadda ba a bayar da shi yadda ya kamata. Mu biyu ne a wurin mahaifiyata daga ni sai kanwata Saratu.”
Ya dakata hade da kallon Asiya, ita ma shi take kallo har zuwa lokacin akwai tsoro a kan fuskarta.
“Na yi fadi tashi sosai a rayuwa har zuwa lokacin da na tafi wata jaha a kudu, inda Allah ya tarfa wa garina nono, na samu aiki a gidan gonar wata mata, gaskiyata da aikina tukuru ya sa na zama daya daga cikin manyan yaranta. Sosai nake samun kudi a harkar wanda dasu na rika tallafawa yan’uwa da kuma mahaifiyata da kanwata.
Kasancewar mahaifinmu ya rasu, nine na dauki dawainiyar bikin kanwata,l.
Idan na zo gida zo ki ga yadda ‘yan’ uwa da mutanen gari ke layi zuwa gaishe ni, saboda basu tafiya hannu banza, yan’uwana da muka hada uba daya dasu basu da abokin shawara sai ni, ko me na fada ya zauna. “
Ya kuma kallon Asiya Wacce wannan karon take kallon sa a nutse .
“Kwatsam! Sai uwar dakina ta rasu sakamakon wani fadan kabilanci da ya barke a yankin, suka kuma kone gidan gonarta. Daga nan na fara shiga wani yanayi mara dadi, na yi ta kame-kame. Har zuwa lokacin da wani ya ba ni mashin purchase. Sosai na mayar da hankalina wajen ganin na biyashi kudinshi, mashin ya zama nawa. Sai da na biya kashi biyu bisa uku na kudin, batagari suka tare ni, suka kwace mashin din bayan sun yayyanke ni da wuka. Kin san me ya faru daga nan? ” Ya yi maganar cikin murmushin da yake nuna irin dacin da yake ji a lokacin.
Asiya ta girgiza kai alamar a’a yayin da idanunta ke zube a kansa.
“Mai mashin din ya ce bai yarda ba, karya nake yi wai sun san irinmu da muke hada baki da wasu, a karbe mana mashin, was bayan kura ta lafa Sai mu sayar da mashin din mu sayi wani.
Abokan sana’ata sun shiga sun fita wajen ganin sun daidaita komai, amma sai da mutumin nan ya aikani gidan yari. Duk kuwa da sun ce zasu hada mishi kudin, ya ce idan an hada sai a sako ni. A lokacin ne kuma kanwata ta rasu wurin haihuwa, labari ya taras da mahaifiyata an kulle ni, ga mutuwar kanwata, haka ita ma ta samu bugawar zuciya ta rasu. Dangina da mutanen gari ba wanda ya zo duba halin da nake ciki, duk kuwa da irin taimakonsu da nake yi a lokacin da nake da wadata
Bayan shigata gidan yarin ne na hadu da mutane kala-kala, har na kwanta ma wani yaron mai kudi a rai, wanda a lokacin saura kwana uku ya fita, ya kuma daukar min alkawarin zai sa Ogan shi ya biya kudin a sake ni. Hakan ne kuma ya faru, ana sakina ya wuce da ni zuwa inda suke harkalla. “
Jinjina kai Asiya take a lokacin da yake kallonta bayan ya diga aya.
Ya kuma gyara zaman hannunsa da ya goya bayansa
“Daniel danjagaliya ne, dan 419, sayar da hodar iblis da sauran muggan ayyuka a hannunsa na zama abin da na zama yanzu. Sosai na goge da ta addacin, na zama babban yaronsa saboda yadda nake da himma, Kudi nake samu a harkar ba na wasa ba. A hankali na koyi shaye-shaye bin matan banza, zuciyata ta bushe babu digon tausayi ko kadan a cikinta kashe mutum baya min wahala. ” Ya kuma tsagaitawa, ba tare da ya kalli Asiya ba ya dora
“A wajen bin matana ne na hadu da cutar kanjamau. Kin san me ya faru? “
Girgiza kai ta yi hade da kallon shi.
“Sai da na kashe duk ‘yanmatana biyar da nake hulda dasu a lokacin da aka fada min ina da cutar da wannan hannun nawa.” ya karasa maganar yana kallon hannunsa da yake a murde alamun karfi.
Asiya ta rika kallonshi a tsorace, musamman yadda yanayinsa ya canja, kamar a lokacin ne yake kisan. Ya katse ta da fadin
“Kin san hausawa sun ce (Rana dubu ta barawo daya ta mai kaya.) hakan ne ya faru damu, yansanda suka tarwatsa dabarmu, na gudu da kaya masu nauyi zuwa kauyenmu. Sai ga shi ‘yan’ uwa sun kara rufa min baya, duk kuwa da irin canji da suka gani a tare da ni, kallo daya za su yi min su tabbatar ba Umar din da suka sani baya ba ne. “
“Kudin da na zo dasu suka kare na fara tsilla-tsilla, ga ciwo yana cina a hankali, wasu irin kuraje suka feso min a jikina ga yawan tari, dandanan die mutane suka fara janye jikinsu da ni, kauye ya dauka kanjamau nake da, kowa ya kyamace ni, ko abinci na je saye a leda ake sanya mi.
Zaman garin dai ya zama ba dadi, Sai kawai na bi dare hade da die sace wasu kadarori nasu na gudu zuwa wata jahar.”
Asiya dai kallonsa kawai take yi.
“Neman kalata bai yi min wahala ba, na zama dilan kayan maye, lokaci kankane harka ta bude, na fara yin suna wajen manyan mutane musamman yansiyasa. Kudi suka rika shigowa, yayin da zuciyata ke ta kara kekashewa. “
“Amma kin san me ye burina a duniya? “
Girgiza kai ta yi alamar a’a
“Shi ne in yi aure in haihu in ganni cikin iyalina. Sai dai na san wannan burin nawa ba zai cika ba, saboda Ina dauke da cuta, duk lokacin da na zo wannan gabar a tunanina sai zuciyata ta yi daci, in ji kamar in kashe kowa ma? “
Ya nisa yayin da yanayin fuskarsa ya canja zuwa kunci da halin damuwa
“Shi ya sa kawai na fi mayar da hankalina a kan harkallata tun da dai na san burina na tara iyali ba zai yiwu ba.”
“Ranar da muka zo nan gidan yin aiki ne, na ji kamar Allah ya kawo ma rayuwata mafita saboda bayanin da kika yi min, tun da na koma nake wasi-wasi, karshe dai na yanke shawarar kawo maku kudinku, tare da neman taimakonki, idan har kika taimakeni na cika wannan burin, na yi miki alkawarin wallahi tallahi zan canja hali zuwa mutumin kirki, zan daukeki a matsayin dangina, ba zan ketare dukkan maganarki ba.”
Shiru ya ratsa wajen bayan ya kai karshen maganarsa.
Nazari take sosai a maganarsa, kokarin gano hakikanin gaskiyar abin da ya fada a cikin kwayar idonsa take yi, amma ba ta ga alamun karya ko wasa ba, sannan akwai wasu abubuwan ma da suke kara tabbatar mata gaskiyar abin da ya fada din.
Agogon da ke falon ta kalla, saura mintuna talatin ta shiga dakin gabatar da shirye-shirye, ba lokacin da zasu yi magana.
Mikewa ta yi hade da aje jakar kudin a kan kujerar da ta tashi, a sanyaye take magana.
“Labarinka ya taba min zuciya sosai, jikina ya mutu da jin waye kai, amma kuma na yi farin ciki da jin kalamanka na karshe, ni kuma na yi alkawarin taimaka maka muddin da gaske kake yi, amma akwai sharudda, sharuddan kuma lokaci ba zai ba ni damar fadinsu ba, nan da mintuna ashirin da biyar ya kamata in kasance a wajen aikina. Sannan lamarinka na bukatar tunani mai zurfi, idan ba damuwa nan da kwana uku ka dawo mu tattauna.”
“Ba damuwa. Na gode da saurarata da kika yi.” yana fadin hakan ya juya da zumar fita.
“Dakata!” Asiya ta yi saurin fada,, bai juyo ba amma ya yi kamar yadda ta bukata.
Falonta ta koma hade da bude possernta ta kirgo kudi 10k ta nufo main falon.
Har zuwa lokacin yana a yadda yake.
“Karbi”
Ya juyo yana kallonta hade da kallon abin da take mika mishi.
Hannu biyu ya sanya wajen karba, hade da godiya, ya murda key din kofar ya fice.
Jiki a sabule Asiya ta isa wajen aiki, kwakwalwarta a cunkushe, juya zancenta da Umar kawai take yi, yayin da take ganin abun kamar wani mafarki.
Karfe biyar da rabi ta fito daga gidan radion ta tare napep zuwa gida don ganin Zee da aka sallamo daga asibiti.
Bangaren Adda ta fara shiga suka gaisa sannan ta wuce nasu Umma daga bisani ta dire ana su bangaren.
Zee din zaune jikin Hajja tana shan tea Asiya ta yi sallama.
Hajja ta amsa sallamar tana kallonta.
“Ke da mijinki ya yi waya ya ce in tun safe za ki zo sai yanzu ake ganinki.”
Asiya ta yi murmushi daidai lokacin da take aje laptop nata da karamar jakarta a kan kujera.
“Hajja ke ma kin sanni da hidimomi, har na shirya zan fito na yi baki. Ya jikin Zee din?”
Ta yi maganar a lokacin da take taba kafafuwan Zee da duk suka yi tauri.
“Da sauki. Ya naki jikin ke ma?”
“Da sauki ga shi har na je wajen aiki ma.”
“Allah ya karo sauki mai dorewa. Sai ki je ki dubo yar’uwarki tun da kin ji sauki.”
“Sha Allah zan je gobe kafin in tafi aiki” cewar Asiya a lokacin da ta nufi kitchen.
Rice and stew ne ta zubo a plate sai nama manyan yanka guda biyu, ta zauna a kasa ta fara ci suna hirar ciwon Zee da Hajja.
Sai da ta yi magriba sannan ta wuce gida,, tana isa kuma ta yi isha’i sannan ta shiga kitchen don tukama Hassan Semo don tana da miya a fridge.
Har zuwa lokacin maganar Umar na makale a zuciyarta juyata kawai take yi tare da kokarin samo hanyar da za ta bi wajen gane gaskiyarsa, kar ta yi kitso da kwarkwata.
Karfe tara na dare ta shiga dakin Hassan hannunta rike da jakar da Umar ya ba ta, Hassan da ya fito daga wanka a lokacin ya saki baki yana kallonta, har ta karaso ta zauna a gefen gado.
“Jakar me ye kuma wannan?” ya yi tambayar a lokacin da yake kara goge ruwan jikinshi.
“Gajen hakuri shi ya kawo wane me ka shuka a gonarka.”
Murmushi ya yi daidai lokacin da yake sanya kayan baccinsa, turare ya fesa sannan ya zauna a gefenta yana murmushi.
“Ina jin ki.”
Jakar ta mika masa tana fadin “Duba ka gani.”
Ba musu ya bude jakar, kudi ne kwance a ciki, ya mayar ya rufe, kafin ya ce “Na menene?”
“Kudinka ne da aka sace kwanaki biyar baya, sune aka maido.”
Kallon rashin fahimta yake mata.
“Abin da ka ji dai shi nake nufi” ta fada fuskarta da guntun murmushi.
“Ni ban san irin ki ba fa, idan kina da fault to taurin kai ne, idan kika sanya kanki abu babu wanda ya isa ya hanaki sai kin yi. Da na ce kada ki yi reporting sai da kika yi kenan? To sai ki dauki kudin ni bana so.” ya yi maganar fuskarsa bacin rai kwance, lokaci daya kuma yana tura mata jakar kudin.
Ido ta zuba mishi, duk yadda ta kai da son kan ranta ya baci ta kasa aiwatar da hakan.
Mikewa ta yi jiki a mace tana kallonsa kafin ta ce” Allah sarki, dama Hausawa sun ce abun arziki bai gaji kare ba, ko ya yi ma dukansa ake yi.
Ni i didn’t report anyone to police. Sannan ban fada ma kowa abin da ya same mu ba kamar yadda ka bukata, shi da kansa wanda ya saci kudin ne ya kawo min dazu. “
Tana kaiwa nan ta mike ta nufi kofa ba tare da ta kara kallonsa ba.
Ya zubawa kofar da ta fita ido hade juya maganarta cike da mamaki.
Ya kasa gasgata maganar tata,, jakar kudin ya dauka ya bude, tabbas kudin ne.
Ajiyar zuciya ya yi hade da daukar jakar ya bi bayanta.
A lokacin kwance take lamo kamar ta yi bacci, shigowarsa ba ta sa ta juyo ba.
Saitin kanta ya zauna hade da juyo da ita, cikin sanyi murya ya ce
“Haba Rabin Raina, ke ma kin san ba ma yar haka da ke, yanzu za ki iya bacci kina fushi da ni?”
Ba ta ce komai ba, duk kuwa da idonta a cikin nashi suke suna kallon juna.
“Shi kenan ki yi hak’uri don Allah, ki huce, na tuba.”
Har yanzu ba ta nuna alamun za ta yi magana ba
“Haba uwar Haidar da Baaba, ga kuma Zee, sannan mata a gidana ni kadai, har yanzu fa na kasa hango wata irinki.”
Zumbura baki ta yi hade da kokarin juya mishi baya, hakan ya sa ya fahimci ta fara sakkowa.
Da sauri ya dawo da ita yadda take, hade da dora hannunsa a saitin zuciyarta
“Tun asali nan wajen nawa ne, wani bai taba samun damar shiga nan wajen ba, fuskarki za ta iya fushi da ni, saboda tana kallon fuskoki masu yawa, amma nan wajen baya kallon kowa sai ni, shi ba zai iya fushi da ni ba.”
“Dalilin da ya sa kenan kake yanke min hukunci ba tare da saurarena ba. Saboda ka san bana iya fushi da kai. Ba fa tun yanzun kake min irin wannan ba, don kawai ka san fushina baya tasiri a kanka.”
Murmushi ya yi hade da jan hancinta “Ba na ce ki yi hakuri ba.”
Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba
“Ba ni labarin yadda aka yi.”
Daga kwancen da take ta kwashe labarin abin da ya faru kaf ta fada mishi.
Hannushi rike da haba alamun mamaki yake kallonta a lokacin da ta kare ba shi labarin.
Zama ya gyara kafin ya ce “Rabin Raina tun da kike kuwa kin taba jin labari makamancin wannan?”
Girgiza kai ta yi alamun a’a.
“To ni ma ban taba ji ba gaskiya, wannan kuma wani iko ne daga Allah, abu indai naka ne da rabonka a ciki, to sha Allahu ko a ina ne, komai dadewa kuma sai ya zo inda kake.”
“Kin san me?”
“A’a” ta yi saurin fada hade da kallon shi
“Mutane da yawa suna farin ciki da bakin cikinka ba ka sani ba, don haka jira suke abun bakin ciki ya same ka su yi dariya, fasa maganar nan zai kai har kunnen makiyanmu, su yi Allah ya kara, wani mugun baki gare shi duk abin da ya fada sai ki ga ya faru.
Sannan koda mun yi report idan ba rabonmu ba ne wallahi ba za a same su ba.
Sannan muna iya bayar da wata kofa da wasu barayin zasu kara zuwa saboda sun huda sun ga jini.
Shi ya sa na bar wa Allah, na kai kukana a gare shi, ga shi kuwa ya ji ni, ya share min hawaye ta in da ban tsammani ba.”
Asiya ta jinjina kai cike da gamsuwa da bayanan shi, sannan ta dora nata da fadin
“Ni kaina a ko wace sujada tawa ina mika mishi kukana, a kan idan rabonmu ne Allah ya bayyana barayin, sai ga shi ya bayyanasu ta hanyar da bamu za ta ba. Maganar Umar ta zauna mun a zuciya, har yanzu ban san matsayinta a wajena ba.”
“Umar da gaske yake Rabin Raina, ki yi nazari sosai, sannan ke fa yar jarida ce za ki iya fahimtar gaskiyar maganarshi daga fuskarsa gami da yanayinshi”
“Exactly!” Asiya ta fada hade mikewa zaune
“Na fahimci gaskiyar maganarsa a kwayar idonsa, zan jira shi zuwa lokacin dana debar masa, domin gindaya mishi wasu sharudda.”
“To idan haka ne me ye abun kokonto, addu’a za mu yi Allah ya sadamu da alkairan da ke tare shi, ya nesantamu da sharrinsa.”
“Haka ne kam” Asiya ta kuma fada hade da komawa ta kwanta.
“Na biya na kara ganin jikin Zee akwai sauki sosai, amma ina son a kara yi mata gwajin HIV ta faye laulayi.”
Zumbur Asiya ta kuma mike zaune tana kallon shi,, yayin da gabanta ya tsananta faduwa.
“Look! Bana nufin komai fa, amma yana da kyau a yi hakan, duk da an yi a can baya an ce lafiyarta kalau, amma za a kara yin wani.”
Da alama Asiya bakinta ya mutu, saboda fargabar da ta lullube zuciyarta.
Tana kallonsa har ya shige toilet, ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi.
Tabbas Hassan gaskiya ya fada, yana da kyau a kara yi mata test din, sai dai tana rokon Allah ya sa ba cutar ba ce.
Jiki a mace ta koma ta kwanta yayin da baccin ya kauracewa idonta.