Skip to content
Part 19 of 25 in the Series Labarin Asiya by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Kasancewar yau ma shirin rana gare ta, shi ya sa ta shirya da wuri da niyyar bin Hassan asibiti, so take a yi komai a gabanta, daren jiya bacci gagararta ya yi. Saboda fargaba

A corridor suka ci karo ya fito daga dakinsa sanye cikin shadda light blue, sosai ya yi kyau, musamman yadda ya murje ya yi kiba mai kyau, ya kara zama cikakken namiji, ba wanda zai kalle shi ya ce yana dauke da cutar H. I. V.

“Kin yi kyau fa” ya yi saurin fada idonsa a kanta yana murmushi.

Ita ma murmushin hade da karewa kwalliyar tata kallo, sanye take da atamfa orange, Sai manyan pattern red,dinkin riga da siket ne da zauna jikinta cas, duk da ba ta yi kwalliya ba, hakan bai hana fuskarta fita fes ba, cikin farar powder da ta shafa hade da lipsticks “Amma ai ban kaika ba. Yanmata nawa ke rushing naka a rana daya irin kyan nan” ta yi maganar lokacin da take sanya dogon farin hijab din ta.

“Basu da yawa sosai, a kalla kamar goma daga customer sai biyar daga waje.”

Murmushi ta yi lokacin da take bude store din da suke ajiye kayan tallafi ba tare da ta ce komai ba.

Ya bi bayanta yana fadin “Akwai baki ne yau?”

“Eh akwai wadanda suka kira ni dazu suna bukatar madara da garin kunun Dr Brown, kuma ina expecting madara da magungunnan da muke ajiyewa a asibiti sun kusa karewa. Shi ne zan tafi da wasu asibitin.”

Tare suka ware magunguna da madarar da zasu kai asibitin.

Sannan suka kuma ware ta mutanen da suka kira ta a wayar.

Shi ya zuba kayan a bayan mota, a daidai lokacin da Asiya ke kulle kofar gidan nasu.

Cikin kwarewa yake tuki yayin da hirarsu ta karkarta a kan Umar da kuma Zee har zuwa lokacin da suka isa gida.

Bangaren Addah suka fara shiga, ba ta ciki hakan ya sa suka wuce bangaren Hajja, saboda sun san bangaren su Umma ba kowa suna wajen aiki.

A main falo suka ci karo da Adda tana fitowa daga falon Hajja.

Tare suka duka cikin girmamawa suka gaishe ta.

Daga duken Hassan ke magana “Mun shiga ciki bamu same ki ba.”

“Eh na zo duba jikin Zee ne?”

“Ya jikin nata?” Asiya ta tambaya tana kallon Addah har yanzu tana a duke.

“Alhamdulillahi jiki ya yi sauki.”

“Ma sha Allah!”

“Ku shiga suna ciki ai.” Addah ta yi maganar lokaci daya kuma ta nufi kofar fita.

Dalilin da ya sa suka mike zuwa falon Hajja.

Shigarsu ke da wuya Zee ta taso da gudu ta rungume Hassan fuskarta cike da daukin ganin sa.

Haka shi ma a na shi bangaren dagata ya yi tare da zaunar da ita a kan cinyarsa yana tambayarta ya jikinta.

Asiya ta bi su da kallon.

“Wai me kake ba yarinyar nan ne take sonka haka? Ka ga dai ku san kullum sai ta ganni, to ba ta taba rugowa ta tarbe ni ba, idan na yi sa a ta ce min sannu da zuwa to na more.”

Murmushi yake yayin da yake kallon Zee da ta boye fuskarta a kirjinsa tana dariya kasa-kasa.

Hannu ya kai hade da dago fuskar tata, ta rufe idonta tana dariya” Wai haka Zee.”

Fitowar Hajja ne ya sanya su mayar da hankalinsu a kanta.

Lokaci daya kuma suka zame hade da gaisheta da tambayar ya mai jiki.

“Jiki Alhamdulillahi, ai ta ji sauki sosai sai dai rashin kwarin jiki.”

Kunun gyada Hajja ta aje masu, suka tsiyaya a cup suna sha hade da hira a hankali.

A cikin hirar tasu ne Hassan ya shigar da maganar kai Zee asibiti don sake mata gwajin HIV.

Sosai gaban Hajja ya fadi, ta zuba masu ido, ta tsani jin sunan cutar nan, bare a danganta da wani nata.

“Muna son cire kokonto ne, da mu zauna a haka muna jin tsoron kar mu je asibiti mu ji mummuna labari, gara mu je shi ne zai tsayar da hankalinmu waje daya, kar mu yi sakaci abu mara dadi.”

“Shi kenan, ta dakko hijabinta ku tafi, tun da yanzu aka yi mata wanka, Allah ya tabbatar mana da alkairi.”

Daga jin yadda Hajja ke maganar za ka tabbatar hankalinta a tashe yake yayin da jikinta ya mutu.

******

Lokacin da suka isa asibitin, Hassan ne ya wuce da Zee wajen test, yayin da Asiya ta yi bangaren da suke bayar da tallafi da samun rahoto a kan masu cutar da kuma ganawa da masu ita, ko akwai masu neman taimaka ko register da kungiyarsu.

Duk da yadda ta kasance busy a bangaren hakan bai sanya ta manta dasu Hassan da suke bangaren gwaji ba, minti-minti take tuno su hade da fargabar Allah ya sa ba cutar ce a jikin Zee ba.

Wasa-wasa sai da ta shafe awa daya a bangaren, saboda tattaunawar da ta yi da wasu sabbin dauke da cutar.

Tare suka fito da ma’aikatan jinyar asibitin inda ta bude masu boot suka kwashe kayan ciki zuwa wurin ajiya

Tana kokarin rufe boot din ne ta hango Hassan rike da hannun Zee suna fitowa.

Gabanta ya yi wani irin luguden faduwa, a hankali ta furta “Innalillahi wa’inna Ilaihir raji’un” har zuwa lokacin da suka iso gun ta, ba ta daina furta kalmar ba, yayin da gabanta ke ci gaba da faduwa a duk tako daya na Hassan da Zee.

“Na shiga ciki ban ganki ba” ya yi maganar daidai yana budewa Zee kofar baya.

“Eh. Yanzu kuma na fito.”

“Haka Doctor ya ce min.”

“An samu sabbin members ne?” ya yi maganar a lokacin da yake karbar littafin da suke rubuta sabbin membobin da suka samu.

“Eh. Mutane biyar ne. Kuma duk mata ne.” Ta yi maganar daidai tana shiga motar.

Shi ma ya zagayo ya zauna.

“Ko kin lura mata ne suka fi ziyartar asibiti idan suna da cutar nan?”

Ya yi maganar daidai yana yi wa motar key.

“Na lura sosai, saboda ko a cikin registernmu maza basu fi goma ba, amma muna da mata wajen 25.”

Duk suka yi shiru a lokacin da Hassan ke kokarin saita motarshi a hanya.

“Kina ganin akwai abin da ke kawo haka?”

“Kila suna shan magani ne a boye, ba sa son kowa ya sani. Ba wannan ba, me ye matsayar Zee?”

“Alhamdulillah! Lafiyarta kalau.”

Lumshe ido ta yi hade fadin “Alhamdulillahi” ta janyo numfashi mai karfi hade da fitar da wata iska mai zafi.

“Daman can ban yi tunanin akwai ba, amma dai test din yana da kyau a yi.”

“Ni ma hankalina ya kasa kwanciya ne, ta cika yawan ciwo ba kamar Haidar ba.”

Asiya ta dan yi murmushi kadan “Haidar kam yana jimawa bai yi ciwo ba, kuma ka ga shi ne ma mai cutar.”

“Hmmm! Allah dai ya jikansa, wani lokaci ina ganin rasuwarsa masalaharsa ce, a kan kalubalen da zai fuskanta a gaba”
Cewar Hassan da wani irin yanayi a kan fuskarta.

“Ni kaina ina wannan tunanin fa.” Asiya ma ta yi maganar hade da juyawa tana kallon Zee da take wasanninta

“Ni ma fa cutar nan masalaha ce a wajena.”

Hassan ya yi saurin juyowa mamaki kwance a kan fuskarsa “Saboda me?”

“Saboda ko ba komai na huta da maganar kishiya.”

Tare suka yi dariya mai sauti

“Ba ki da dama fa.”

Suka kuma yin dariya a tare.

Haka suka ci gaba da hira, har zuwa lokacin da suka isa wurin aikin Asiya, ya sauke ta, sannan ya wuce da Zee gida.

Ita ma daga wajen aikin gidan Jamila ta wuce ta yi mata sannu sannan ta wuce gida.

Tun safe gabanta ke yawaita faduwa saboda zuwan Umar, har ji take kamar ana buga mata kofa tsabar yadda ta sanya abun a ranta.

Amma har shadaya na safe shiru, har ta fara jin dama kawai ta tafi wajen aikinta,, kila ba zai zo ba.

Main falo ta fito ta fara editing shirye – shiryenta.

Ba jimawa aka buga kofar, gabanta ya kuma yin irin wata faduwa,, hijabin da ke gefenta ta sanya hade da nufar kofar tana karanta “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un.”

Da bismillah ta bude, ta yi saurin ja baya kadan tana dubansa.

Sanye yake cikin kananun kaya jar riga da kuma bakin wando, sai facing cap ja, hanya ta ba shi ya wuce cikin falon. Bai zauna ba har sai da ta ce “Bismillah”

Zama ya yi hade da janye facing cap din shi “Ya aiki?”

“Alhamdulillahi!” ta fada a lokacin da take turawa Hassan sakon isowar Umar.

Dining ta nufa, tea ta hada mishi mai kauri hade da debar mishi soyayyan irish da kwai.

“Bismillah” ta kuma fada tana kallon shi.

Ba musu ya hau kan dining din, hakan ya sa ta ba shi wuri don ya samu damar sakewa ya ci abincin sosai.

Mintuna goma Hassan ya iso, ya nufi Umar fuska a sake suka gaisa, lokacin kuma Asiya ta kuma fitowa har lokacin sanye take da hijabin dazu.

Dukkansu a kan dining din suka yi masauki, kuma gaisawa aka yi kafin Hassan ya ce

“Matata ta sanar min da abun da ya faru a tsakaninku, idan har gaske ne na yi farin ciki malam Umar, Allah yana son masu tuba, muddin ba tuban muzuru da nama a baki ba. Amma dai ina son ji daga bakinka.”

Nisawa Umar ya yi kafin ya ce “Duk abin da ta fada ma shi ne gaskiyar abin da ke cikin zuciyata, dama dole ta sanya ni shiga wannan harkar ba don ina so ba. Idan har zaku taimakeni koda sana’a ne zan bar wancan harkar.”

Tare suka kalli juna, kafin Hassan ya yi saurin dauke kai ya mayar kan Umar.

“Zamu taimakeka, amma ka ji tsoron Allah kada ka zalumcemu.”

Murmushi Umar ya yi, “Haba ba wannan a zuciyata Oga, idan akwai shi ba zan maido maku kudinku ba, saboda sun ishe ni in ja jari, amma bana son in yi da haram ne.”

“Shi kenan. Kamar yadda matata ta sanar maka suna da kungiyar irin ta masu lalurarku ta hakan ne, amma akwai wasu sharudda da ake cikawa kafin samun matar aure ko mijin aure kamar yadda kai kake bukata.”

Yanzu zamu je asibiti ne mu ga likitanmu.”

“Ba damuwa zan cika ko wane irin sharudda muddin burina zai cika.” cewar Umar a ladabce.

Ba bata lokaci suka nufi asibitin, inda aka yiwa Umar gwaje-gwaje, tun daga genotype, diabeties, hanta da kuma HIV inda aka gano yana dauke da kwayar HIV wacce har ta kai matakin Aids.

Bayan nan baya da wata matsala.

Asiya ce ta shige gaba wajen nemar mishi wacce zasu dace da shi.

Yayin da Hassan ya saka shi a shagonsa da zuciya daya, sannan suka ba shi daki a wajen flat nasu da aka yi don baki.

Cin shi shan shi, kula da lafiyarsa da shige da ficen sa duk suna kula dasu.

Tun suna dari-dari da Umar har suka saki jiki da shi, mutum ne mai hazaka da jajircewa a kan abin da ya sa gaba, yana da girmama na sama da shi.

A cikin wata daya aka lalubo wacce zasu yi daidai a zaman aure.

Rukayya matashiyar budurwa ce da ita ma take dauke da cuta irin ta Umar, yanayin rayuwa ya sa duk ta watsar da makaman rashin jin maganarta ta koma ga Allah.

Koda aka yi mata tayin Umar ba ta musa ba.

Su Asiya sune suka je nema mishi aure, yayin da cikin wata daya aka yi komai amarya ta tare gidanta da Hassan ya kama masu haya a kusa dasu.

Sosai Rukayya da Umar ke girmama Asiya, yayin da Asiya ta daukesu tamkar yan’uwanta na jini.

Idan har za ta yi abun marmari to akwai sunan Rukayya a ciki, a bangaren Rukayya ma haka ne.

Hassan kuwa sosai ya rike Umar ya ja shi a jiki, a tsawon zamansu Hassan bai taba kama shi da laifin ha’intarsa ba, hakan ya sa ya kara sakin jikinshi da shi baya jin kyashin yi mishi komai.

A wannan satin sosai Asiya take busy, ga zuwa aiki, ga maganar kungiyarsu, sannan ga Jamila ta haihu namiji.

Abubuwan sun yi mata yawa don ma Rukayya na taimaka mata, ta bangare biyu, bangaren Jamila da kuma kungiya, komai ake bukata game da kungiya Rukayya kan yi bakin kokarinta.

Da yake yau ne sunan Jamila a can gidan jamila Rukayya ta kwana saboda aiki.

Asiya ma daga wurin aiki can ta wuce suka shiga hidimar suna.

Maijego kam ta fita fes rungume da yaronta da ya ci sunan Aliyu.

Sosai Asiya ta yi rawar gani musamman da ya kasance sunan Haidar aka mayar wa yaron.

Karfe goma na dare Hassan ya dakko su ita da Rukayya bayan da suka kawo Maijego dakin Hajja don yin wanka.

Gajiya ce likis a jikin Asiya shi ya sa tun da suka taho idan ka dauke hamma babu abin da take yi.

A kofar gida ya sauke Rukayya daidai lokacin kuma Umar ya fito daga gida, cike da girmamawa ya duka har kasa ya gaishe da Hassan.

“Ka baro kasuwa kenan” Hassan ya tambaye shi yana kallon shi.

Har zuwa lokacin duke yake ya amsa da “Eh dawowata kenan.”

“Wadancan mutanen dana yi ma magana sun zo ne?”

“Eh sun zo yallabai, na basu kayan ma, amma sai da suka bayar da kudin.”

“To ina kudin?”

“Na turawa Alhajin da kuka yi magana da shi a onitsha, na ga gara kawai a sallame shi.”

Jinjina kai Hassan ya yi cike da jin dadin bayanin Umar, Allah ya sani yana jin dadin tarayya da shi.

“Aunty ina wuni” murya Umar ta katse wa Hassan tunani.

Asiya da ke ta hamma ta ce “Lafiya kalau Umar, ka yi hakuri fa, daga jiya zuwa yau mun rike ma mata.”

Murmushi ya yi shi ma kamar yadda ta yi yana fadin “Haba Aunty ko shekara za ta yi ba zan damu ba muddin kuna tare.”

“To mun gode Umar Allah ya saka da alkairi.”

“Amin. To sai da safenku”
Ya yi maganar daidai Hassan yana juya kan motar.

Bayan sun hau hanya ne ya ce “Rabin Raina, wani fa tunani nake yi. Kin ga babban store din cikin gidanmu na wajen can. Kawai zan fasa mishi kofa ta fito waje a gyara shi, a zuba wa Umar kaya a ciki, tun da unguwar nan ba wani babban store. Ko ya kika gani?”

Ta kai hannu hade da rufe bakinta dalilin hammar da ta yi” Gaskiya ka yi tunani mai kyau, ni dai wannan shawara ta yi min dadu, sai dai mu yi fatan alkairi kawai. Umar mutumin kirki ne, kawai bai samu wanda zasu tallafi rayuwarshi ba ne, shi ya sa ya zama yadda ya zama a baya. “

“Kwarai kuwa, kuma kin san akwai irin su da yawa a cikin garuruwanmu da unguwanninmu suna yawo, suna neman taimakonmu amma mun yi burus dasu, daga karshe su fada harkar banza, kuma mune farkon target din su, don haushinmu suke ji bamu taimakesu ba.”

“Wannan gaskiya ka duba kwanaki can baya da aka taso unguwarmu da sace-sace karshe fa duk yaran unguwar nan ne aka rika kamawa.”

Bai yi magana ba saboda fitar da ya yi don bude gate.

“To shigo da motar.” cikin tsokana ya yi mata maganar

Dariya ta yi kafin ta ce “Hidimomina ne fa suka min yawa amma da tuni na kware a tuki.”

“Gaskiya ya kamata ki iya, ba girmanki ba ne yawo a napep.”

“Zan yi kokari sha Allah zan fitar da lokaci, hannuna ya kara fadawa sai a nemi mafita.”

“Washhh! Yau fa na gaji har a bakina.” ta yi maganae lokacin da suke shiga falo

Murmushi ya yi “Dama ana gajiya a baki ne?”

“Ga shi ni dai na yi” ta yi maganar hade da kwantawa kan doguwar kujera.

Kafafuwanta ya rika matsawa “Wai rawa kuka yi ne?”

“To me ye ma bamu yi ba. Har ma kusan dambe.”

Ido ya zaro hade da dakatawa daga danna mata kafafun.

“Dambe kuma. Daga suna sai dambe?”

“Kai ma dai ka fada an yi wa ‘ya mugun miji. Ka san dangin mijin Jamila sai a hankali, a kan fa abinci ne wai mun dauke shinkafa mun bar su da tuwo. Me ye kuma shinkafa da za ta hada fada. Yau na so ace Aunty Zee na nan wallahi da ta warware min su.”

Baki Hassan ya tabe” Umm! Ku ba ku rabo da kananun maganganu, to ba sai ku basu shinkafar ba magana ta wuce.”

“Ni na hana a basu, ni fa dama haushinsu nake ji, kiri-kiri suka hana Jamila ta rike Zee dole ta koma wajen Hajja,, Hmmm ai mutanen can bakin halinsu ya yi yawa.”

“Ke kuma ba ki manta abu. Ta so mu je ki yi wanka.”

“Ni fa ba zan yi ba na gaji.” a shagwabe ta yi maganar.

Murmushi ya yi hade da dago ta.

“Ina bukatar twins ne a daren yau.”

Ido ta fitar kafin ta yi magana ya ce, “Da gaske fa.”

Shi ya taimaka mata ta yi wanka sannan suka kwanta.

<< Labarin Asiya 18Labarin Asiya 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×