Zaune take cikin shiri zuwa aiki, lokaci zuwa lokaci takan daga kai zuwa agogon da ke manne da bango. Umar take jira, tun dazu Hassan ya ce zai zo ta ba shi key din mota ya karbo mishi sako, Sai dai har zuwa lokacin da ta gama shiryawa Umar din bai zo ba.
Kamar daga sama kuma ta ji sallamar Umar din, dalilin da ya sanyata daukar mayafinta laptop din ta, sai kuma karamar jaka, ta nufi babban falon.
Zaune ta iske shi ganinta ya sanya shi zamewa kasa hade da gaishe ta, har kunyar irin respect din da Umar yake ba ta take yi.
Ta yi – ta yi ya bari amma ya ki.
“Bismillahi ga abinci can ka ci kafin ka wuce.”
Ya daga kai hade da kallon dinning “Aunty na koshi fa.” cikin murmushi ya karasa maganar
Ita ma murmushin ta yi hade mika mishi key din motar Hassan.
“Ke ma za ki fita ne?” Umar ya tambayi Asiya bayan da ya sa hannu biyu ya karbi key din da ta mika mishi.
“Eh. Ina da aiki 12:30pm, sannan yanzu zan je tasha ne matar Mukhtar ta aiko da wasu sako zan karba in kai asibiti. A asibitin ma akwai wasu sabbin patient da aka samu suna son a yi masu register. Ka ga kuwa dole in fita da wuri.”
Kai ya jinjina kafin ya ce” To mu je mana ko tashar in kai ki. “
Ido ta zaro hade da juyowa tana kallon shi a lokacin da take rufe kofar falon ta.
“Cewa fa ya yi ka yi sauri.”
“Ba zai damu ba idan ya ji na tsaya aikin ki ne.”
Shi ne ya matsa har sai da Asiyar ta shiga, ya rufe gate din bayan ya fita da motar, cikin kwarewa yake tuki suka nufi tasha yayin da suke tattauna abubuwan da ya shafe su.
A cikin hirar ce kuma Umar ke sanar mata Rukayya ba ta jin dadi amma sun je asibiti.
Cikin jimami Asiya ta ce “Ban sani ba, amma sha Allah yau zan zo in duba ta, Allah ya ba ta lafiya”
“Amin” ya amsa, sannan suka ci gaba da hirarsu, musamman a kan cuta mai karya garkuwar jiki.
Umar bai tafi karbo sakon ba har sai da ya sauke Asiya a harabar gidan radion da take aiki, bayan ta gama da asibitin.
“Aunty ya fa kamata ki sayi motar nan ke ma.” Cikin zolaya ya yi maganar daidai tana fita.
Ita ma dariya ta yi mai sauti “Zan saya Umar idan kun dafa min, sannan hannun nawa ne har yanzu bai fada ba, kuma ga shi ba lokacin koyon tukin ayyuka sun yi yawa.”
“Haka nan za ki cire lokaci gaskiya ki koya, mun gaji da ganinki a napep, hannunki yana fadawa kuma zamu saya miki motar, don na san oga zai iya.”
Dariya take yi sosai lokacin da ta dauki hanyar da za ta sada ta da offishinta ba tare da ta ce komai ba.
Shi ma ficewa ya yi daga harabar asibitin don karbo sakon Hassan.
******
Lokacin da ta shi Karfe shidda saura mai napep ya aje ta a kofar gidansu.
Kamar kullum sashen Addah ta nufa.
Ba kowa a falon sai Baaba da yake kwance a kan 2 sitter, ganinta ya sanya shi tashi da gudu ya nufo ta.
“Me ya faru ba ka je islamiya ba?” ta yi tambayar hade da shafa kansa tana kallon shi.
“Ba ni da lafiya.”
Hannu ta kai hade da taba jikinshi
“Jikinka ba zafi Babana.”
Fuska ya tabe alamun zai yi kuka, a dai dai lokacin kuma Addah ta bude kofar ta shigo.
“Yaushe kika zo?” Addah ta fara tambaya cike da mamakin ganin Asiyar.
“Zuwana kenan. Ina wuni?” ta duka cike da girmamawa ta gaishe da Addah.
“Wai Baba ba shi da lafiya?” ta yi ma Addah tambayar daidai tana zama akan kujera.
“Karya yake, lafiyarsa kalau, ya tsani zuwa makaranta wannan yaron ba bokon ba ba ta mahammadiyyar ba kin gan shi nan. Yau da safe sai da na yi ta ihu sannan ya tafi, yana dawowa ya ce ba zai je islamiya ba wai ba shi da lafiya, kuma jikinshi babu wani zafi fa.
Kakanshi ya ce a kyale shi tun da ya ce bai da lafiya. “
Tun Addah ta fara magana Baaba ya yi kicin-kicin da fuskarsa, yayin da Asiya ta zuba mishi ido tana kallon shi.
“Wallahi wannan yaron bai biyo Haidar ba sam, ga shi nan dai ya kusa shekara bakwai amma bana jin ko hizif biyu zai iya. “
Ido Asiya ta zaro kafin ta ce “Ki ce asarar kudinmu kawai muke yi Addah. Aiko to zan tafi da shi wajena akwai makarantu acan in saka shi, ba zai kara zuwa nan ba.”
Take ya fara kuka ya tsani ace zai je wajen Asiya, saboda ba yara abokan wasa,, nan kuwa gasu nan kullum su wuni kiriniya.
“To idan har ba ka son zuwa wajenta ka rika zuwa makaranta, don ni da kaina zan saba gyalena in kaika wajen mamar taka wallahi.”
Cewar Addah cikin kurari.
Daga Asiya har Addah fada da nasiha kawai suke wa Baba hade da tsoratar da shi da abun da baya so.
Jikinsa kuwa ya mutu likis.
Da haka Asiya ta baro sashen Addah, ta nufi na su Aunty Amarya nan ma gaishe su ta yi hade da karbar abincin da Umma ta sanya mata ta nufo bangaren Hajjah.
A nan ta samu Baba kwance yayin da Jamila ke ba Haidar nono.
Cike da sha’awa take kallon kanwar tata, abun har burgeta yake idon ta ga mace na shayar da yaronta.
Ta karasa kusa da Jamilar suna murmushi
“kin ga yadda kika yi kyau kuwa kanwata, wallahi sosai shayarwa ta karbe ki.”
Murmushi kawai Jamila ke yi ba tare da ta ce komai ba ta mikawa Asiya Haidar.
“Ki bar shi ya sha ya koshi mana.”
“Aunty wuni fa yake yi, baya son ya ji bakinshi shiru.”
Dariya Asiya take yi hade da kallon Haidar da ya yi bul-bul gwanin sha’awa gaskiya ba ta yadda za a yi a hada breastfeeding da bottlefedding, ita yaranta basa irin wannan fresh din.
“Kin ga yadda yaron nan ya yi kyau kuwa a cikin sati daya da ban gan shi ba?”
Kafin jamila ta yi magana Zee ta shigo sanye da uniform alamun daga islamiya ta dawo.
Tana ganin Asiya ta fadada murmushinta hade da rufe fuskarta da hannayenta biyu, ta dan duka” Mommy ina wuni? “
“Lafiya kalau. Sannunku da dawowa.”
“Wai me Addah ta yi wa Baba ne, na gan shi some how haka dai? ” Jamila ta yi maganar lokaci daya Kuma hankalinta na kan Baba.
Ita ma Asiya ta mayar da hankalin nata a kanshi, hade da tabe baki
“Kin gan shi nan bai yo halin dan’uwansa ba, baya son karatu ko kadan, bar shi a wasa dai. Don an yi mishi fada ne fa yake ta kunci.”
“Baban nawa Aunty. Ai kuma yana da kokari makarantar ce dai bai son zuwa, amma da an fadi karatu yana riƙewa wallahi. Zo nan Babana.” cewar Jamila tana kallon Baba.
Fuska a narke ya taso hade da fadawa jikin Jamila kamar zai yi kuka. Ita dai Asiya kallon su take yi.
“Fada min ba ka son makarantar ne a canja ma wata?”
Girgiza kai ya yi
“To me ya sa ba ka son zuwa?”
“Ya Ustaz ne yake dukana.” ya yi maganar hade da share guntun hawayenshi.
“Ba zai dokeka a banza ba, me ka yi?”
“Wai don ban iya karatu ba, kuma bannan aka yi.”
“You see! Idan har kana zuwa ba za a kara yin karatu ba ka iya ba, kullum ka rika zuwa, promise you zan siya ma keke mai kyau babban wanda kake da shi.”
Baki ya washe ba tare da ya ce komai ba.
“Yes!” ta kuma karfafa maganar tata tana dariya.
Waje ya yi a guje yana murna, Asiya ma ta bi shi da murmushi.
Daidai lokacin Zee ta fito daga dakin Addah ta canja kaya.
“Kin san matsalar wannan ita kuma. Wallahi ban san me ye a kanta ba, sam ba ta ganewa, kullum tana bin hanyar zuwa makaranta amma kafin ta dawo abin da aka koya mata ya bi iska, ya barbade a kan hanya.”
Asiya ta saki baki tana kallon Zee
“Ita kuma haka take?”
“Haka kuwa take”
“Ba lafiya.” cewar Asiya tana kokarin cin abincin da Umma ta ba ta.
“Sai addu’a kam.” in ji Jamila.
“Wai Hajja na gidan rasuwar ne?”
“Eh tana can, a can ma za ta kwana gobe ne addu’ar uku.”
“To Allah ya jikanta.”
“amin” Jamila ta fada.
Daga nan suka shiga wata hirar, har zuwa lokacin da Asiya ta mike don tafiya.
“Zan rubuto miki wata addu’a a rika tofawa a ruwa ana ba Zee. Sannan kin ga damuna za ta kama very soon, ruwan farko a tara a tofa mata ayatul-kursiyyu kafa hamsin a ba ta tasha.”
Asiya ta yi maganar daidai tana fita daga falon.
“In sha Allah.”
Sai da ta kuma biyawa sashen Adda suka yi sallama sannan ta wuce gida.
Yau Juma’a da misalin karfe hudu suka fito gida ita da Hassan don zuwa duba jikin Rukayya, tun da ta samu cikin har zuwa yanzu da ya tsufa Rukayya cikin laulayi take.
Tafe suke suna hirarsu cikin nishadi musamman da ya kasance a kafa suke tafiya sai abun ya basu nishadi sosai, sun rabu da kasancewa a haka.
Umar na kokarin fita su kuma suka shiga hakan ya sa ya koma yana fadin “Sannunku da zuwa.”
Rukayya ma ta fito falon sanye da hijabi yayin da cikinta ya fito sosai.
Har kas ta duka hade da gaishe su, kafin daga bisani ta koma ta zauna.
Su ma su Asiyar zaman suka yi, yayin da hira ta barke a tsakaninsu cike da nishadi.
A cikin hirar ne Hassan ya ce ” Umar ya kamata fa ka je kauye idan matarka ta haihu, so that ta ga garinku da ‘yan’ uwanku.”
Shiru Umar ya yi kai a kasa.
“Gaskiya ne kam ya kamata ka kai matarka asalinka saboda tsaro.” Asiya ma ta karfafa maganar Hassan.
“In sha Allah idan ta haihu lafiya zan yi hakan.”
“To Allah ya rabasu lafiya” cewar Asiya
“Amin” dukkansu suka amsa.
Basu bar gidan ba sai gab magriba, su Hassan suka wuce masallaci ita kuma Asiya ta yo gida.
Sai dai ba ta jima da zama ba, Hassan ya shigo ya ce ta shirya su kai Rukayya asibiti ba ta jin dadi.
Sai da ta hada komai na haihuwa sannan suka tafi.
Isarsu ke da wuya aka ce haihuwa ce, cikin ikon Allah kuwa aka ciro mata kyakkyawar yarinyarta ta hanyar CS.
Farin ciki wajen Umar ba a magana, musamman da aka tabbatar mishi da yarinyar lafiyarta kalau.
Tun a asibitin ya yi mata huduba da sunan Asiya amma zasu kirata da Nour.
Kwana uku aka sallamo Rukayya aka ci gaba da shirin suna
Sosai Asiya ta yi rawar gani ita ce uwar miji kuma ita uwar maijego.
Su Hajja ma duk sun yi rawar gani, sune dai suka zama dangin Umar.
Ranar suna gida ya cika aka yi shagalin suna lafiya aka kare lafiya.
Tun daga lokacin da yawan dawainiyar Nour Asiya ce ke yin ta, haka nan Allah ya dora mata kaunar Nour, ji take yi kamar jininta ce.
Da ta dawo daga aiki za a kawo mata ita sai idan kuma za ta tafi aiki ta mayar da ita.
Da ta fara tafiya ma tare da ita suke zuwa wajen aikin.
Umar yana jin dadin wannan karamci na Asiya da mijinta, bai taba ganin mutane irinsu ba, da suke mayar da kowa nasu, abun hannunsu bai rufe masu ido ba.
Asiya ce ta sanyata makarantar da take kusa da gidan radion da take aiki, ko wane lokaci dai Nour na manne da Asiya gidansu sai dai ta je da yawo.
Lokuta da dama Hajja kan ce “Ikon Allah, sai a kan Nour ne kike jin dadin raino na ga ko yaranki ba ki raina kamar yadda kika raini Nour ba.”
Murmushi take yi kafin ta ce “Haka nan nake jin kaunar yarinyar nan Hajja gami da tausayinta, ban san dalili ba.”
Ita kanta Nour din ta shaku da Asiya da Hassan fiye da iyayenta.
Tun bayan da aka haifi Nour suke ta sanya ranar tafiya zuwa kauyensu Umar amma Allah bai nufa ba, har Nour din ta yi wayo basu samu sun je ba.
Sai karshen watan nan dukkansu suka shirya ma tafiya zuwa kauyen don nunawa Rukayya da Nour dangin Babanta.
Misalin karfe shidda na safe suka fito cikin shiri don zuwa kauyensu Umar.
Hassan sanye da blue voyel mai laushi gami da tsada, dinkin babbar riga ya karbi jikinsa sosai, kwarjininsa da zatinsa ya fita sosai a cikin dinkin.
Asiya ma blue lace ne a jikinta mai tsada dinkin bai kamata ba sosai amma ya zauna a jikinta das, farin mayafi takalmi da karamar farar jaka ta yi amfani dasu, ta fita kamar wata commissioner ko minister.
Nour kuwa mai kimanin shekaru biyar da Zee wacce ta tasar ma shekaru sha biyu, sanye suke cikin kayan kanti masu kyau, wandon jeans na mata da farar t-shirt mai kyau ta mata
Kafafuwansu sanye cikin bakin takalmin covershoes, kunnnuwansu manne da karamin dankunnen gold mai kyau.
Sai agogon yara, yayin da kansu ya sha kananun kitso, da yake Nour ta fi Zee ga shi sosai kan nata ya sha bead da ya kara kawata kitson nata.
Zaune suke a bayan mota yayin da Asiya ke gaba ita da Hassan, suka nufi gidan su Rukayya.
Kafin su isa ne Hassan ya dubi Asiya “Madam kina kyau fa.”
Murmushi ta yi “Na kaika? Kullum kara cika kake kwarjininka na kara fita. Yanzu haka ina, tsoron kar wata ta yi mun shigar sauri.”
Dariya ya yi mai sauti” Ke kadai ce kawai, ba, wuri.”
Tabe baki ta yi ba, tare da ta ce komai ba.
“Wai Aliyun fasa zuwa da shi kika yi da kika ce tare da shi zamu. “
“Yana gidan kakarshi, ni kuma kawai na cewa Jamilar ta kyale shi.”
Isowarsu gidansu Rukayya ya katse hirar tasu.
Su ma sun shirya cikin kwalliyar shaddar dark yellow da ta sha zubi, sun fita kamar wasu amare.
Cikin tsokana Rukayya ta ce “Sannu maman biyu.”
Asiya ta harareta da wasa kafin ta ce “Don Allah ku daina kirana da sunan nan, kar mala’ikun rahma su amsa, dayan ma ya mutum ya gama da shi.”
“Kuma sha Allah biyun ne Aunty” Umar ya yi magana yana dariya.
“Ni fa cikin nan sam ban so shi ba, na riga ma na fitar da raina da sake yin wata haihuwa kuma, Baba fa shekararsa tara. Wallahi har kunya nake ji cikin nan ya fito.”
Sosai Rukayya ta tuntsire da dariya.
“Da ace maza na karbar ciki, da tuni na amshe cikin nan na huta da yawan korafin matar nan, a rana daya sai ta yi maganar cikin nan ya fi saba’in” Cewar Hassan a lokacin da yake bude bayan mota ya zauna.
Duk suka yi dariya kafin Rukayya ta ce “Fatanmu dai a haihu lafiya.”
Umar ne ya karbi tukin yayin da Asiya da Hassan suke a bayan mota da yara.
Tafiya ce ta kusan awa hudu, don haka Nour baccinta kawai take yi a jikin Asiya, Zee ma jikin Hassan ta kwanta, duk da rabi bacci rabi kuma tana kallon hanya.
A tafiyar Umar ne ke ta basu labarin yadda ya yi rayuwa a wajen da yanayin mutanen kauyen nasu, yan’uwanshi da abokan arziki.
Tun da suka shigo yankin nasu yake ba su Hassan tarihin wasu manya-manyan bishiyoyi, gonaki da dazuzzukan da ke gefen hanya.
*****
A kofar family house dinsu Umar ya yi parking yayin da yaran dake wasa a kasan bishiyar bedi (neem tree) suka yi cirko-cirko suna kallon motar.
Har zuwa lokacin da su Umar suka fito, yaran basu gane Umar ba, don basu san shi ba, bare kuma su Asiya.
Da sallama suka shiga gidan, gidan yana nan bai canja ba, sai dai wasu da suka gyara sashensu da rufin kwano da siminti.
Dakin matar yayan Babanshi Umar ya shiga, zuwa lokacin ta kara tsufa amma hakan bai sa ta kasa gane Umar ba.
“Ummaru!” ta ja sunanshi cike da mamakin ganin sa.
“Dama kana duniyar nan Ummaru?” ta kuma jefa mishi tambaya tun kafin ya gasgata maganarta ta farko.
Ba ta jira cewar sa ba tayo waje tana fadin “jama’a ku fito ga Ummarun Kaltume yau ya zo gida, ku fito matan gida.”
Kafin wani lokaci kuwa bangaren su Yaya (haka kowa a gidan ke kiranta) ya cika dam da yara da manya. Kowa cike da mamaki.
Dandanan aka aika kiran iyayensu maza, kafin wani lokaci dai gida ya cika da yan’uwa ana mamakin ganin Umar.
A hankali ya yi masu bayanin su Asiya da kuma Rukayya.
Kowa mamaki yake yadda aka ce Umar na da kanjamau, ya aka yi kuma ya yi aure har ya haihu. Kodai dama karya ake masa.
Wannan shi ne tunanin da ke zuciyoyin wadanda suka san Umar na dauke da cutar.
Tsarabar da su ka kawo aka fitar daga boot, irinsu buhun shinkafa carton na taliya dasu makoroni, sabulai, omo, manja, package na lemuka da kuma fruit.
Aka shiga rabon tsaraba, makota da yan’uwa, gidan bai tsagaita da masu zuwa kallon Umar ba sai misalin sha biyu na rana.
A lokacin ne kuma aka fito da katuwar tabarma aka baje masu ita a kasan bishiyar mangoro mai yalwar ganye.
Asiya ta nade mayafinta, ta aje gefe ta ja filon da aka aje masu ta kwanta, tana sauraron hirar matan gidan da suke zaune a kasan bishiyar, sai kuma yara da suke ta kallonsu kamar tv.
Tun Asiya na jin hirarsu har bacci ya yi awon gaba da ita, kasancewar inuwar akwai sanyi ga fresh air mai dadi.
Su Hassan kuwa suna waje a barandar masallaci da iyayen Umar maza da yayyu da kuma kanensa suna ta hira cikin nishadi hade da ba, Umar labarin abubuwan da suka faru bayan bayanan.
Nour kuwa tana like da Asiya Zee ce dai ta shige cikin yaran kauyen tana kallon yadda suke wasaninsu.
Sai misalin biyu saura Asiya ta tashi daga baccin jin maganar su Hassan a kanta.
Ta bude ido a hankali tana kallon Nour da ta yankwane, wannan ya tabbatar mata da yunwa take ji, saboda duk abin da aka kawo masu babu abin da Nour ta sanya a bakinta.
Zee kuwa duk abin da ta ga iyayenta sun ci sai ta ci, an kawo masu dafaffen wake mai bawo ba ta taba ganinshi ba, amma haka nan tai ta ci, gujjiya da su rake komai Zee ci take yi.
Asiya ta idar da Sallah tana kallon Nour da ta langwatse ta son jira kawai take ta yi magana ta fara kuka, me za ta ce wa mutanen gidan, Nour ta ki cin abincinsu.
Kafin ma ta yi magana Rukayya ta shigo kiranta su je su ci abinci.
Wani daki ne aka kuma sharewa fes, aka shimfida katuwar tabarma har da kunna turaren wuta.
Tuwon dawa da ya sha kanwa da miyar busasshiyar kubewa, waina da miya, damammiyar fura da nono mai kyau, sai danwake sune aka aje wa Asiya a matsayin abincinsu
Kaf abincin babu wanda Asiya ba ta ci ba, ji take ko nama bai kaisu dadi ba.
Nour kuwa danwaken ta rika tsakura, tana ci tana hawaye, duk su kai ta mata dariya.
Basu baro kauyen ba sai karfe biyar na yamma, bayan motarsu cike da tsaraba, gyada, gujiya, dankali, rake, wake, kubewa busassa,, da danyar masarar da ba ta gama bushewa ba.
Sosai suka ji dadin ziyarar, tun da suka taho kuwa tattauna abubuwan da suka faru a kauyen suke yi, na ban dariya haushi da kuma takaici.
Hassan ya dakko wayarsa ya mikawa Asiya.
Ta zaro ido tana dariya, bidiyo ya yi mata a lokacin da take jan ko wane kwanon abinci tana ci kamar wata mayunwaciyar saniya.
Ita kuwa Rukayya Nour ta yiwa bidiyo lokacin da take cin danwake tana kuka.
Basu iso gida ba sai bakwai na dare.
Umar ya wuce da motar bayan da ya aje su Hassan sai karfe tara ya maidota kasancewar gidansu babu wurin parking.
Lokacin kuwa tuni Asiya ta yi bacci, ballantana Nour da zazzabi ya rufe ta.