Skip to content
Part 25 of 25 in the Series Labarin Asiya by Khadija S. Moh'd (Matar J)

A cikin shekaru biyar abubuwa da yawa sun faru, kamar yadda abubuwa da yawa suka canja.

A lokacin Asiya ba za ta iya kirga irin dumbin nasarorin da ta samu ba, daga ita har Hassan.

Hausawa sun yi gaskiya da suka ce nakasa ba kasawa ba, kuma ta gamsu da bayanin likita da ya ce, rashin kulawa, rashin shan magani, tsangwama na daya daga cikin abin da ke sanya cutar H.I.V yin tasiri a jikin mai ita, shi ya sa ko wane lokaci ba ta mance yan’uwanta a cikin addu’arta, saboda muhimmiyar rawar da suka taka mata, sun kula da ita hade da taimaka mata a duk wani abu da ta sanya gaba.

Ba sa kyamatarta ko nisanta kansu da ita saboda halin da take ciki, babban abun farin ciki shi ne yadda suka lullube mata sirrinta, ba kowa ne ya san tana dauke da cutar H. I. V ba, musamman yaran da suka taso daga baya.

Lallai ta yarda cutar H. I. V cuta ce mai sauki kulawa kamar yadda likita ya fada mata, cutar ba ta hana ta komai ba, tana zuwa aiki, tana aikin kungiya tana kula da yaranta, a takaice dai mai cutar zai iya yin duk wani abu da mara ita zai iya yi, ma’ana zai yi aure, zai haihu, zai nemi ilmi, zai bayar da ilmi, zai yi kasuwanci, zai kuma yi aikin gwamnati. Zai yi farin ciki kamar yadda kowa ke farin ciki.

A tsawon shekaru biyar din da ta baro baya, farin cikinta ya ninka bacin ranta yawa, cikin abubuwan da suka sanyata farin ciki har da auran da Zulaihat, wacce ta kammala Diploma, a halin yanzu kuma take karatun HND a gidan mijinta.

Sai Zee wacce ta kammala karatun degree a wannan shekarar yayin da Abdallah yake a shekarar karshe, Nour kuma school of midwifery ita ma tana shekarar karshe.

Affan da Afnan da su kuma suna SS 2.

Yanzu kuma bikin bude babbar cibiyarsu ne a gabanta, cibiyar dai ta lashe miliyoyin kudi yayin gina ta, shi ya sa ita ma ta dauki tsawon shekaru lokaci ba tare da kaddamar da ita ba.

Tun da satin bikin budewar ya kama Asiya da Hassan basu zauna ba, Kubrah ma dole ta zo nan domin ganin komai ya tafi yadda ake so.

Misalin karfe biyar na yamma Asiya ta yi horn, Baba Labo (maigadi) ya bude mata gate, ta Parker motar daidai inda ta saba parkerwa, ku san tare suka fito da Kubrah, ko wannensu da alamar gajiya a tare da shi, basu jima wajen knocking ba Ahmad (yaron Jamila) ya bude musu, lokaci daya kuma ya shiga gaishe su.

Suka amsa Asiya na tambayar Ina za shi.

“Zan je wani wuri ne.” ya amsata lokacin da yake fita.

Kamar ko wane lokaci falon gyare yake tsab, Sai kamshi mai dadi wanda ya hade da sanyin A.C.

Abdallah ne ya fito daga corridorn da zai sadasu da dakunan gidan. Sanye yake cikin kananun kaya masu kyau wadanda suka dace da jikinsa.

Kallo daya za ka yi mishi ka ga kamanni Hassan a jikinsa, Ya zabge sosai ya zama saurayi, babu mai cewa Asiya ce ta haife shi.

Shi ne ya fara gaishe su, lokaci daya kuma yana mika hannu da zummar karbar kamar jakar Kubrah.

“Ba ka yi askin ba dai.” cewar Asiya tana kallon shi.

Ya Kai hannu hade da shafa tarin sumar shi da ta ci kudi sannan ya ce “Zan yi.”

“Karya ba” cewar Asiya tana kokarin wuce shi.

Kubrah kuma ta dora da “Don Allah ki bar shi, gayu yake da a bar shi.”

Sororo ta yi ganin Nour rabe kofar kitchen tana share kwalla, alamun kuka take yi “Me ka yi mata?” ta yi tambayar hade da kallon Abdallah da ke latsa wayarshi.

“Ah-ah! Me ya sa shi?” Kubrah ta tambaya a kokarinta na kare Abdallah.

“Saboda na san shi ne, Nour ba ta kuka a gidan nan Sai Idan akwai Abdallah, kuma ya rantse ba shi ba ne.”

Cikin siririyar dariya ya ce “Ni fa ban mata komai ba, kawai don ta yi mopping na taka da takalmi. Kuma kin santa ita ko kallonta ma aka yi Idan ba ta gamsu ba kuka take yi.”

“Shi ne kuma kake yi.” ta yi maganar lokaci daya tana aika mishi da harara.

Kai ya sunne kasa hade da dariya a hankali.

Daki ta wuce ta bar su da Kubrah tana musu fada.

Kai tsaye toilet ta wuce, wanka ta yi hade da dauro alwalar magriba.

Lokacin da ta fito gefen gado ta samu Nour din zaune tana wasa da dogayen yatsunta.

“Me ya faru?” Asiya ta tambaya bayan ta hade mata fuska.

Cikin sanyinta ta ce “Dama cewa zan yi, yanzu za a kawo miki abincin ko sai Dady ya dawo.”

Ido ta kafe ta da shi kamar ba za ta yi magana ba, Sai kuma ta ce “Sau nawa zan fada miki ki dainawa Abdallah kuka, wannan sanyin naki ya yi yawa Nour, komai kuka, ba ki da karfin zuciya ko kadan.”

Hannu ta kai hade da dauke wani hawayen sannan ta ce “Shi ne sai yay ta min abin da ban so.”

“Ke kuma ba za ki iya magana ba.”

“To Mommy ko na yi baya dainawa, Idan kuma na ce zan yi fada sai ya ce zai dake ni.”

“Kaico!” cewar Asiya cike da takaicin Nour.

Kubrah ta turo kofar a hankali ta shigo

“Lafiya?”
Ta yi tambayar idonta a kan Nour.

“Lafiya kalau, kawai na tambaye ta me Abdallah ya yi mata dazu shi ne take kuka.”

Murmushi Kubrah ta yi tare da ta ce komai ba.

Hakan ya sa Nour mikewa ta nufi kofar fita.

Bayan fitarta ne Kubrah ta ce “Tausayi take ba ni wlh, sanyinta ya yi yawa, ina tsoron wa za ta aura kar ya je yay ta cutarta wlh, ba ta magana ita.”

“Bari in yi sallah dai, ke Shehu ya roka muku.”

Dariya Kubrah ta yi lokaci daya kuma ta fice daga dakin, ba jimawa ta dawo dauke faranti, wanda Nour ta jera musu abinci, tuwon shinkafa miyar wake da ta ji aleyahu da naman rago.

Lokacin da ta shigo dakin Asiya ta idar da sallah, a tsakar dakin Kubrah ta aje musu faranti, a nutse suka fara cin abinci, lokaci daya kuma suna taba hira.

Asiya ce ta ce “Dazu kina magana a kan mijin da Nour za ta aura ko?”

Kafin Kubrah ta ce wani abu Asiya ta dora “Kin ga wannan abun da shi nake kwana, nake kuma tashi. Ba na son abin da zai taba yarinyar nan, wlh Ina sonta fiye da yaran da na haifa, sanyinta da rauninta yana karamin tausayinta. Kubrah yadda nake jin Nour a zuciyata, wlh zan iya kare duk abin da na mallaka don ganin farin cikinta. Ina jin tsoron ta auri wani a waje a yi suruka mara dattako, sabo dai zan iya saba gyalena in je in taso yarinyata bayan na ci mutumcin duk wanda ya tabata. “

Dariya sosai Kubrah ta yi hade da fadin” Ki ce za a yi tsohuwar kawai.”

“A kan Nour zan iya yin abin da ya fi haka Kubrah. Wannan dan karamin abun da zan iya yi ne na fada miki.”

Dariya Kubrah ta kuma yi sannan ta ce “To kin ga da Haidar na nan Sai a yi dakan daka shikar daka.”

Murmushi Asiya ta yi mai dauke da abubuwa da yawa, amma ba ta ce komai ba, sai ma mikewa da ta yi zuwa kan sallaya domin gabatar da sallahr Isha’i.

Hassan bai shigo gidan ba, Sai karfe tara, Asiya ce ta shirya mishi abinci, bayan ya gama ci ne suka shiga tattauna yadda bikin zai kasance nan da kwanaki kadan masu zuwa.

Washegari da safe babban gida dukkansu suka tafi, gidan cike kamar ana biki, yaran Kubrah maza uku duk suna gidan, Jamila ma yaranta maza biyar duk suna gidan, ga na Asiya maza biyu da mata biyu (Abdallah da Affan, Afnan da Zee, Sai kuma yanzu da suka zo tare da Nour)

Bangaren Addah suka fara shiga, suka gaishe ta, sannan suka wuce bangaren su Aunty Amarya.

Lokacin da suka shigo sashen Hajjah da yansamarinne zaune a babban falo suna kallon ball, yadda suka nutsu kamar a sahun sallah Sai abun ya ba ka mamaki, daga yadda suke zaune suka rika mikawa su Asiya gaisuwa.

Falon Hajja a gyere tsab, Sai Zee da ke kwance tana latsa wayarta, shigowarsu ce ta sanyata mikewa lokaci daya kuma ta shiga gaishesu, a kofar bedroom din Hajjah suka ci karo da Afnan.
Ita ma ta gaishe su, sannan ta yi hanyar kofar fita.

“Jikin ne Hajjah” Kubrah ta fara tambaya

“Wlh amma akwai sauki ai, Alhamdulillah.”

“To kodai asibitin za mu je?” cewar Asiya cike da kulawa

“Haba ni da nake zagaye da likitoci, ko jiya Abdallah ya debi jinina ya kai lab, da an jima ya ce zai karbo result din, kuma Zee ta sanya min ruwa jiya, sosai jikin ya yi sauki. Sannan ga wata kurmar likitan ma ta zo.”

Duk suka juya suna kallon Nour da ke tsaye jingine da kofa tana murmushi.

Hajjahn ta gaisar sannan ta fice, fuskarta dauke da murmushin tsokanar da Hajjah ke yi mata.

Bayan fitarta ne Asiya ta, ce” Har yanzu Baba bai dawo ba Hajjah, kar fa a yi bikin bude cibiyar nan ba shi.”

“Ai tun da ya ce miki da shi za a yi, na san zai yi kokarin ya zo Sha Allah.”

“To Allah Ya sa, ina son komai a yi shi a gaban idanunku.”

“Allah Ya ara mana ran da lafiya, Ya kuma kai mu lokacin.”

“Amin.” suka hada bako wajen fada, sannan suka shiga tattauna abin da ya kawo su, gaba daya dai akan shirye-shiryen bude cibiyar ne.

Asabar 10: AM

Ita ce ranar da ta kama za a yi bikin bude babbar cibiyar kula da masu cutar kanjamau, wacce Asiya, Hassan, Mukhtar da kuma Kubrah suke jagoronta.

Rana ce da su dukkansu suke dokin zuwanta, sannan kuma suka shirya mata. Rana ce da suke jin ta ta musamman a wajensu, shi ya sa suka yi kokarin ganin sun mayar da ita ta musamman ga duk wanda ya samu damar halartar taron.

Dukkansu mazan iyaye da matasan ankon babbar rigar farar shadda kal suka yi, yayin da aka yi mata aikin hannu da golden color din zare, dinkin da ya karbi ko wane daga cikinsu.

Su kuma matan ankon farin lace mai dauke da golden fulawa suka yi, sosai suke daukar ido, tamkar dai karin maganar nan ta hausawa da suke cewa “Ni ko Ke kyawawa sun hada hanya.”

Dakin taron ya hada manyan yansiyasa, masu kudi, da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

Duk wani abu da ake bukata wajen ganin dakin taron ya kawatar to an tanade shi.

Da farko dai an bude taron da addu’a kafin daga bisani, fitaccen mawaki mai ci a lokacin ya fito hade da nishadantar da mahalarta taron, da wakokin da suka tsuma yan kallo, musamman Asiya da ake ta wake ta, ita da zuriyarta, dalilin da ya sa ta rika barin kudi ba tare da ta sani ba.

Sai da wuri ya natsa ne, MC ya gabatar da sunan Hassan a matsayin uban kungiya, kuma shi ne zai yi bayanin godiya ga mahalarta taron, Mukhtar kuma a matsayin shi na ma’aji, sannan mai tattara bayanai (Pro) ya gabatar da sunayen, wadanda duk suka bayar da tallafinsu wajen ganin wannan cibiya ta tsayu da kafafunta.

Kubrah ce ta yi jawabin godiya a matsayinta na mai sanin shige da ficen kungiya hade da gabatar da sunayen kungiyoyin da suke bayar da tallafinsu ga wannan cibiya da kuma hanyar da tallafin ke zuwa.

Daga nan ta mika abun magana wajen Asiya domin yin jawabin ayyukan wannan kungiya a takaice.

Bayan gabatar da kanta ne ta fara da ” Kamar yadda aka ce a takaice, to a taikacen dai wannan kungiya mun kafata ne domin taimakon masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato (H. I. V) ta hanyar taimaka musu da magunguna kyauta, yin test kyauta, abinci kyauta musamman madarar jarirai.

Ba iya nan wannan kungiya ta tsaya ba, har da hada aure ga masu dauke da cutar muna yi, da kuma daukar nauyin karatun wasu daga cikinsu musamman masu karamin karfi.
Yanzu kuma wannan kungiya ta fadada ayyukanta ta hanyar bude ma’aikata mai zaman kanta, wacce aka tanadi dakin awo, dakin karbar magunguna da kuma dakin yin aiki (tiyata) ga masu juna biyu.”

Ta dan tsahirta kadan kafin ta dora” Daga lokacin da muka kafa wannan kungiya zuwa yanzu babu abin da za mu ce sai Alhamdulillah, saboda mun cimma abubuwa da yawa, wadanda ba mu yi tunanin cewa za mu iya cimma su ba.

Na san mutane da yawa za su so, su ji dalilinmu na bude wannan kungiya, kuma da abin da ya sa muka karkata hankalinmu a wannan bangare.

Cutar kanjamau na daya daga cikin cututtukan da masu dauke da su suke kunyar bayyanawa, kila ko don yadda al’umma suke yi wa masu cutar kallon mazinata, da kuma yadda ake tsangwama hade da kyamatar masu cutar.

Wannan dalilin ya sa mu ka bude wannan kungiya, inda muke wayarwa da masu cutar kai ta hanyar kwararrun likitoci, mu ka basu shawarwarin yadda zasu rayuwa, hade da basu kwarin gwiwar cewa zasu rayu kamar kowa. Zasu yi aure, zasu haihu, zasu yi karatu, za su zama duk abin da suke son zama. Alhamdulillah daga lokacin da muka fara wannan fafutuka zuwa yanzu muna da ma aurata sama da talatin, sannan akwai yaran da aka haifa karkashin kulawar wannan kungiya sama da hamsin, wadanda likitoci suka tabbatar basu dauke da wannan cuta.

Zan yi amfani da wannan damar domin mika sako ga al’umma cewa, akwai cututtuka masu dama da suka fi cutar H.I.V hatsari, misali, hanta, ciwon sugar da kuma sikila.

Cutar H. I. V ba a gadonta, sannan ba a daukarta hanyar sanya kayan mara lafiya, yin amfani da cokali, plate da kuma cup din da mara lafiyar ya sha ruwa, ba a daukarta ta hanyar hada bayan gida da mai cutar, kamar yadda sauro baya yadata, ba a daukar cutar H.I.V ta hanyar tari ko hada numfashi da mai cutar.

Ana daukar cutar ne kawai ta hanyar haduwar jinin mai dauke da cutar da kuma mara ita, Sai kuma yin jima’i kai tsaye ba tare da abun kariya ba. “

Ta bi mutanen wajen taron da kallo tana ganin yadda suke sauraronta a nutse, yayin da yan jarida na gidan talbijin, da talbijin suke daukar rahoto.

” Da wannan muke kira gara al’umma (ta ci gaba) da su taimaki masu wannan cuta ta hanyar karfafa musu gwiwar ci gaba da rayuwa, su daina kyamata hade da tsangwamarsu, su tallafa musu da abinci mai gina jiki, su daina bazantar dasu da nuna musu kamar babu wani amfani da zasu yi wa al’umma. Sannan kofar wannan cibiya kullum a bude take, wajen karbar masu irin wannan cuta, ba zabe muke ba, mu na kowa ne, kuma kowa ma namu ne, da wannan nake fatan kowa zai koma gidansa lafiya. “

Ta kai karshen maganar hade da mikawa Mc din abin magana.

Wurin taron ya kaure da surutan mutane, inda suke tattaunawa a kan abin Asiya ta fada.

Abu na gaba da aka yi, shi ne daura mutane goma masu dauke da cutar, inda kungiyar ta dauki nauyin kayan dakinsu tare da jarin da zasu rika juyawa.

Haka dai aka rika gabatarda abubuwan da suka shafi taron cike da burgewa,har zuwa lokacin aka rufe taro da addu’a bayan samun kyaututtuka daga mahalarta taro zuwa ga kungiya.

Daga haka taro ya tashi cike da burgewa da kuma nishadantarwa.

Sai da su Asiya suka bi gidan amaren daya bayan daya, a kokarinsu na ganin komai ya tafi daidai.

Dalilin da ya sa basu dawo gida ba sai wajen karfe bakwai na dare, a lokacin da yawan masallatai sun fito sallahr magariba.

Bangaren Addah suka fara nufa, ganin tana sallah kai tsaye suka wuce bangaren Hajjah.

Duk yaran suna babban falo, yan matan da kuma samarin, Sai hayaniya suke kamar gidan biki(kodayake gidan ya fi na bikin ma)

Take hayaniyar ta kara yawa, inda ko wannen su ya shiga bayyanawa su s Asiya abin da ya burge shi a taron, da kyar suka kwace zuwa falon Hajja, nan ma dai hirar abin da ya faru suka iske Hajjah da Alhaji Abdallah na yi, lokacin da yake cin abinci.

A gidan suka yi sallahr isha’i hade da cin abinci sannan suka wuce gida.

Ba ta samu kebewa da Hassan ba kasancewar yana tare da baki.

Bayan kwana biyu da taro su Kubrah suka koma, har a lokacin kuma basu daina samun bakin yan jarida na ciki da wajen ba.

Kamar wasa sai da suka kwashe sati sannan komansu ya koma daidai.

Zuwa lokacin Asiya cike take da farin cikin ganin yadda suka daukaka ta hanyar samarwa da wasu mutane farin ciki, zuwa yanzu kungiyarsu da cibiyarsu ta yi nisan da ba ta yi tsammani ba.

Fatan Allah Ya sa a samu mutanen da zasu yi koyi dasu.

Zuwa yanzu dai za ta iya cewa auran Zee, Nour da kuma Abdallah ne kawai ya rage mata ta gani, wanda take fatan a yi nan ba da jimawa ba.

Da dare ne Hassan ya zo mata da albishir din ya biya musu Umra su biyar, Zee, Abdallah, Nour, ita da kuma shi.

Wannan albishir ya faranta ran Asiya sosai tare da sauran yaran.

Sati biyu komai ya kammala suka daga zuwa umra.

Fatanmu aje lafiya, a kuma dawo lafiya.

Karshe.

<< Labarin Asiya 24

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×