Turo kofar da ya yi ne bayan ya dawo masallaci, shi ya kuma tayar da Asiya daga nannauyan baccin da take yi a karo na biyu tun bayan kiran sallahr asuba.
Da hannayenta biyu ta yi tagumi bayan ta ziro kafafunta kasan gadon lokacin da ta mike zaune.
Mamakin irin baccin da ta yi take yi, kamar ba ta a cikin matsala, kuma har zuwa yanzu da take zaune baccin take ji.
Da kyar! Ta mike zuwa toilet, yayin da Hassan ya zauna a inda ta tashi, shi ma hannayensa biyun ya zuba tagumi dasu. . .
Yanzu su ina suka kwaso ciwon nan fisabilillahi