Skip to content
Part 4 of 25 in the Series Labarin Asiya by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Shiru ta yi a cikin keken, so take ta daidaita natsuwarta kafin ta isa gidan Zainab.

Ta rasa wane irin kallo ko hukunci za ta yanke a kan Hassan.

Idan ta ce ta rabu da shi, ba cinya ba kafar baya, don kuwa idan har ya tabbata tana da wannan cutar ba mai auranta.

Idan kuma ta ci gaba da zama da shi kullum za ta kasance cikin bakin ciki ne, don idan har za ta daga ido ta kalli fuskarsa, sannan ta tuna cutar da ke jikinta, za ta ji kamar zuciyarta za ta fashe.

Wani irin malolo ne ke tsaya mata a wuyanta, hade da wani dunkulalen abu ne ke tsaya mata a kirji.

Tana sonshi, kuma ko yanzu ma tana sonshi amma kuma ba za ta iya daina jin haushinsa ba.

Ganin an shiga layin su Zainab ne ya sa ta kuma kara daidaita natsuwarta a kokarinta na boye damuwarta.

A can bangaren Hassan tun bayan fitar Asiya ya ci gaba da zagaye falon cikin wani irin kunci, duk yadda ya kai ga daurewa sai da hawaye suka zubo mishi, ya ci gaba da daukesu cike da kunar zuciya, daga karshe ya janye hannunsa daga kan kuncin nasa, tare da ba hawayen damar sauka yadda suke so, zuciyarsa kuma ji yake kamar za ta fashe saboda matsewar da ta yi.

A hankali sautin kukansa ya fara fita, har zuwa lokacin da ya durkushe kan gwiwarsa hade da dora goshinsa kasa. Cikin muryar kuka kuma a zahiri yake fadin
“Ya Allah! Ya Allah!! Ya Allah!!! Ba ni da kowa sai kai, kai ne gatana, kai ne mai mai shaidata, Ya Allah kana ganin halin da gidana yake ciki, Allah ka dube ni ka, kawo min karshen wannan tashin hankalin. Allah ka bayyana mana gaskiya, ka tafiyar da kuncin da ke zuciyoyinmu… “

Ya kasa karasa addu’ar, saboda kukan da ya ci karfinsa, haka ya rika kuka kamar karamin yaro ba tare da ya dago da halin sujjadar da yake ciki ba.

*****

Bari mu koma gidan Aunty Zee.

Rumgume Asiya ta yi sosai cike da farin cikin ganinta, lokaci daya kuma ta shiga kokarin cire hijabin jikin Asiyar, don dama tuni ta kwance nikabin

“Wai lafiya kike kuwa, ko tsirara za ki yi mun?” Asiya ta yi maganar hade kokarin rike hijabinta

Amma duk da haka sai da Aunty Zee ta cire hijabin hade da fadin “Kokarin yayana zan gani dalla.”

Suka tuntsire da dariya a tare, kafin Asiya ta kai mata duka “Allah ya shiryaki wallahi ba ki da kunya.”

“Kin gan ki kuwa sister, kin yi kyau, kin kara wani fresh, kin zama wata yar duma-duma, wallahi yayana ya iya kiwo.” cewar Aunty Zee tana karewa Asiyar kallo sama da kasa.

Murmushi kawai Asiya ta yi hade da raɓata ta wuce zuwa falo.

“Woww! Yayana yana more kallo fa.”

Sosai Asiya ta yi dariya a lokacin da take zama a daya daga cikin kujerun dakin kafin ta ce

“Wato ke har yanzu bakinki na nan a sake ko? Kin ki ki sanya mishi linzami duk irin kunyar da kike sha ta dalilinsa.”

Tare suka tuntsire da dariya gami da tafawa

“Aunty Asee wato kin tuno zuwanmu gidan ƙawa Farida kenan.”

Suka kuma tuntsirewa da dariya a tare hade da tafawa, wanda ke nuna sun tuna wani abu a baya.

“Na fa ji kunya ranar sister, ba ki ga zuwana ba, na wuce simi-simi kamar na yi karya an gano ni, wallahi ban san angon na cikin dakin ba. Ita ma da yake munafuka ce ta bar ni nai ta barin baki. Kai! Aunty Asee bana son tunawa, ko yanzu ji nake kamar yana kallona. “cewar Aunty Zee da jikinta ya nuna alamun abin da ta fada.

” Ai kuma har yanzu kina nan ba ki canja ba.”

“Ai ɓarin baki gaba muka ba shi ba baya ba, ya zama jininmu. Kuma idan ba ma a wuri har cigiyarmu ake yi, wurin ma baya armashi, mune muke kayata wuri.”

“Dalla ina alalar da kika ce za ki yi min, ko karyar da kika saba ce kika yi min , don alalar nan fa na fasa zuwa gaisar da uwata yau na ce sai Friday.” cewar Asiya lokacin da take kallon Zee.

“Ban san munafurci, ke ma kin san karya ba halina ba ne, ga ta can a kitchen ba ta karasa ba, kuma ranar fridayn ba sai mu hadu a can ba.”

“ki rantse da Allah yaya bai ba ki komai ki kawo min ba?”Zee ta yi saurin fada lokacin da take lalube a jakar Asiya.

“Bai ba ni ba, yanzu komawa zan yi?”

“Allah ya kara maku lafiya ke da yayan nawa.” Aunty Zee ta fada a lokacin da take kokarin kiran wata lamba a wayarta.

Hassan na halin sujada ya ji karar wayarsa, jiki a sanyaye ya nufi inda wayar take ganin sunan Zainab ya sa gabansa ya yi wata irin faduwa, tsoro ya bayyana a kan fuskarsa, har kiran ya yanke bai daga ba.

Ganin kiran ya kara shigowa ne ya sa shi saurin dauka, bai yi magana ba sai dai ya kanga a kunne, yana jin surutansu da dariyarsu wannan ya tabbatar mishi da babu wata matsala.

“Yaya!” Daga can bangaren Zainab ta kira sunansa

“Kanwata” shi ma ya amsa

“Yaya yaushe ka zama haka?”

Gabansa ya yi wata mummunar faduwa, hantar cikinsa ta kada, lokaci daya mararsa ta yi wata irin kartawa, kansa ya Sara wuta ta dauke masa gabadaya.

“Yayana!” Daga can bangaren Zainab ta kuma fada don jin shirun ya yi yawa.

“Ina jin ki, me na yi?”

“Shi ne Aunty Asee za ta zo, ba ka bayar da komai an kawo min ba?” cikin muryar shagwaba ta yi maganar.

Ba Zainab ba, hatta Asiya da ke zaune a tsakiyar falon tana cin alale ta ji sautin ajiyar zuciyarsa, har sai da ta daga kai ta kalli inda Zainab din take tsaye, da alama Zainab din ba ta fahimci komai gami da nannauyar ajiyar zuciyar tasa ba, don kuwa wayar take yi da dan’uwan nata hankali kwance, wanda ke nuna tsantsar kauna da kuma shakuwar da ke tsakaninsu.

Asiya ita shaida ce a kan soyayyar da ke tsakanin Hassan da Zainab, kamar ita ce kadai kanwarsa, kila ko don ta fi kama da shi, da ace ita din namiji ce babu abin da zai hana ba ace ita ce Hussaininsa ba.

Komai nata irin nashi ne hatta yatsun kafarsu dana hannu iri daya ne babu wani bambanci.

“Kallon me kike yi min ne kamar za ki cinye ni?” cewar Zainab tana duban Asiya a lokacin da ta sauke wayar.

Tsoki Asiya ta ja, gami da mayar da hankalinta a kan alalar da take ci ba tare da ta ce komai ba.

Ba za ta iya fada mata abin da ke zuciyarta ba.

Ba mamaki idan ta fada mata suna dauke da cutar Kanjamau wacce basu san daga ina suka samota ba, kila sai ta suma, dan cikin da ke jikinta ya ɓare, saboda ita kanta ba ta tsammaci cikin nata zai kawo yanzu ba, musamman yadda mararta ke ta ciwo a kwanaki ukun nan.

Ganin Asiyar ta yi shiru cin alalarta kawai take yi, ya sanya Zainab dukawa kusa da ita hade da dafa cinyoyinta.

“Sister akwai magana a bakinki fa. “

“Ba komai Asiya.” ta fada ba tare da ta dago kai ta kalli Zee ba, saboda idonta gab yake da kawo ruwa.

“Akwai, kina dai boye min ne, ba kya so in sani, a tunaninki ban fahimci haka ba tun da kika shigo?”

Uffan dai Asiya ba ta ce ba.

Wani murmushi Zee ta yi,, wanda Asiya ta kasa fassarawa, ta katse shirun nasu da cewa .

“Wai kin manta ya muka taso Sister? Ko a haihuwa an ce kwana uku kacal kika ba ni, kin ga kuwa tserayyar ba wata mai yawa ba ce da za ki iya layance min, sannan tare mu ka yi primary, secondary wurin zama daya, wurin kwanciya daya, haka makarantar gaba da secondary department ne kawai ya rabamu amma komai tare muke yi. A gida ma wurin Kwananmu daya, sai idan mun yi fada ne muke raba wurin kwana. Duk wani motsinki ina fahimta ko ba ki fada ba, sai dai ko in yi kamar ban gani ba Aunty Asee.”

Ta yi shiru hadi da duban Asiya da ta tsame hannunta a cikin alalar da take ci tana sauraronta.

Ganin babu niyyar za ta yi magana ya sa Zee ci gaba.

“Ba zan matsa sai na ji ba, tabbas yanzu na san akwai abin da sirrinku ne, na gode Allah da yayana ya same ki a matsayin mata, duk irin amintarmu hakan bai sa kin tona min wani sirrinku ba, na tabbata a duniya dai babu wanda zai ji wannan sirrin ciki kuwa har da Hajja. “

Asiya ta yi saurin dago kai, jin Zainab ta ambaci sunan mahaifiyarta.

” Yes! Na san halinki, wallahi ba za ki iya fada mata ba, ki gwada zuwa da niyyar fada mata ki ga ko za ki iya. “

Harara ta aika mata” Ke fa ba ki da hankali uwata ce fa. “

“Amma dai ai kin san na san hakan ko ba sai kin fada min ba. Abu nawa muka tona rami muka rufe ba tare da saninta ba.” Cikin hararar wasa Zee ta yi maganar.

Asiya ta canja hirar da fadin “Zan yi sallah”

Tana kan sallaya ne bayan ta idar da sallah. Zee ta shigo hade da fadawa saman gado tana amsa kiran angonta.

Hankalin Asiya ya koma kanta, cike da sha’awa. Kamar su ma basu yi irin wannan rayuwar ba. Rayuwarsu ta baya ita da Hassan rayuwa ce mai dadi hade da gardi. Basu taba tsammanin lokaci kankane rayuwa za ta canja zuwa yadda take yanzu ba

Haka take shiga irin wannan shaukin idan ya kirata, ta kan manta da kowa da komai ta ji kamar sune kawai suka rage a duniyar.

Shi ya sa ba hukunci ma fi muni da yake mata irin ya rufe wayarsa bayan sun sami sabani, sai duniyar ta yi mata kunci, bacci ya kauracewa idanunta, komai ya ki mata dadi har sai ta ji muryarsa.

Wata shida kacal da kasancewarsu a Inuwar ma’aurata komai ya canja, mummuna labarin ya ratsa kunnuwansu, wanda ya yi sanadiyyar wargaza duk wani farin ciki nasu da walwalarsu, zaman masoya ya yi ƙaura a gidan nasu, nisan da ba ta san ranar dawowarsa ba.

Zainab kamar ita ke tsarawa kanta rayuwa, komanta daidai yake tafiya, kalli rayuwarta gwanin sha’awa, hankalinta kwance.

Da irin wannan tunanin Asiya ta share tsawon wuni a gidan Zainab.

Amma ko da wasa ba ta fada mata tana dauke da kwayar cutar Kanjamau ba.

Lokacin da keke ya sauke ta kofar gida ana kiran sallahr magariba, a falo ta ci karo da Hassan da alama masallaci za shi.

A hankali ta motsa bakinta alamar sallama.

Ya amsa a hankali hade da karewa yanayinta kallo, tana nan dai ba kuka ba guda.

“Sannu da dawowa.” ya fada lokacin da take kokarin wuce sa.

Ba zai iya gane ta amsa ko ba ta amsa ba. Saboda ta gota shi sosai.

Bai dawo gidan ba sai da aka yi sallahr isha’i.

Kitchen ya same ta zaune da cup din tea a gabanta amma ba ta sha ba.

Goye da hannunsa yake kallon ta, yayin da ta kasa da idonta hawaye na diga.

Ya tsani ganinta a irin wannan yanayin, da ace akwai hanyar da zai bi wajen dawo da walwalarta da ya bi, sai dai ya san yanzu abu daya ne zai sanyata cikin nishadi shi ne ace ba ta dauke da wannan cutar.

Ganin ta mike za ta fice, sai ya yi saurin tare kofar ta yadda ba za ta iya wucewa ba.

Zuwa lokacin sautin kukanta ya fita sosai. Ya janyota jikinsa duk da irin turjewar da take yi, cikin dakusassan murya ya ce “Sorry Rabin Raina, don Allah ki yi hak’uri wlh ba ni da hannu a wannan matsalar ban san yadda aka yi hakan ta faru ba.”

Idan akwai abin da ke kara bata mata rai shi ne ya ce bai san abin ya faru ba, wanda ta san karya yake yi, fatanta Allah ya saka mata cutar da ya yi mata cikin gaggawa.

Duk yadda ya so ya hana ta fita kitchen din sai da ta fice, inda ta ruga da gudu zuwa cikin dakinta hade da danna key.

Haka ta fada gado ta ci gaba da rera kukanta har bacci ya dauke ta.

Da safe kwai ta soya hade da tea ta karya, saboda Hassan din bai dawo ba, dama ta ji sanarwar zasu je gyaran makabarta ta san ya je. Ba mamaki ma inda za a rufesu ya je ya gyara musu, tun da dai an ce wannan cutar sunanta kabari salamu alaikum.

Lokacin da ya dawo tana jin shi yana taba kofarta ta ki budewa, dalilin da ya san ya shi komawa falon ya kwanta kan kujera, ba tare da ya dauraye ko jikinsa ba.

A yadda yake ji, bai ki ace makabartar kai shi aka yi ba shi ne ya kai kansa ba. A wannan yanayin mutuwa kawai yake fata.

Ba zai iya cewa ga lokacin da bacci ya daukesa ba.

A cikin bacci ne ya ji kamshin turarenta dalilin da ya sanya shi bude ido a hankali, daga bisani kuma ya yi saurin tashi, saboda yadda ya ganta cikin kwalliya kuma tana kokarin fita.

Yau Friday ya san ba ta da aiki har sai ranar Monday to ina za ta je da sassafe cikin kwalliya.

“Ina za ki je?” ya yi saurin tambaya ganin har ta kusa ficewa daga falon.

“Gida.” ta ba shi amsa a takaice. Saboda ba ta son ya tsayar da ita.

Kafin kuma ya yi wata magana tuni ta fice daga falon, hakan ya sa ya bi bayanta ransa a bace.

A waje cimmata hannunta rike da basket wanda yake dauke da food flask guda biyu, wanda sai yanzu ma ya lura da basket din

Kwamdon ya karbe daga hannunta, wanda hakan ya yi masifar tsoratata, don kuwa karba ce irin ta ba cikin dadin rai ba, kai tsaye za ta iya cewa fisgewa ya yi.

Dalilin da ya sa kenan ta yi saurin dubansa cikin ido.

” Me ye laifina ne wai Asiya? Yadda fa kike tuhuma ta ko zargina a bangarena ma haka ne gami da ke?”

“Me kake nufi?” ta yi tambayar idonta a cikin na shi.

“Abin da nake nufi shi ne, yadda kike zargina da sanya miki wannan cutar haka ni ma nake zargin ki. Yadda kike tuhuma ta haka nake tuhumar ki a kan me za ki kwashe duk zunubin ki dora bisa kaina?” Ransa a bace sosai yake maganar.

Har yanzu kallonsa take yi cikin ido, zuciyarta na wani irin kuna da daci. Murmushi mai kuna ta yi hade da dan cije lebenta na kasa sannan ta ce

” Ka fi kowa sanin a cikakkkiyar ma ce ka same ni ai… “

” Ta ya zan iya sani bayan ni ban taba kusantar wata mace ba sai ke”. Ya yi saurin katseta

Zuba mishi ido ta yi sosai, duk yadda ta, so daurewa sai ta kasa, idanuwanta suka ciko da kwalla, muryarta ta yi rauni, cikin rawar murya ta ce

“Amma kai ka zama ciki mai manta kyautar jiya, yanzu a cikin ido kake kallona kana fadin ba cikakkkiyar mace ka same ni ba. Idan na taba kwanciya da wani namiji bayan kai Hassan Allah ya saka ma cikin gaggawa.” kuka ya ci karfinta sosai, wanda hakan ke nuna lallai ta ji dacin maganar tasa.

” Haka a bangarena Asiya, ban taba hada shimfida da wata ba, idan har kika ci gaba da ganin laifina ni ma zan ci gaba da tuhumaarki. “

Girgiza kai ta shiga yi cikin zafin maganar da yake fada mata, cikin kuka sosai ta ce “Allah shi ne shaidata a kan wannan batun, amma wlh ni wani namiji bai ta kusantata ba.”

Jikinsa ya yi sanyi sosai, ganin yadda ta karasa maganar tata, zuciyarsa ta karye tausayinta game da sonta ya cika mishi kirjinsa.

Basket din da ya fisge a hannunta ya aje, hade da kama hannunta suka koma cikin falon.

Ma’ajiyar kur’aninsu ya nufa bayan ya zaunar da Asiya a kan kujera.

Durkusawa ya yi gabanta da Kur’anin.
“Idan na rantse miki da wannan na san za ki yarda. Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Asiya Ina miki rantsuwa da wannan littafi mai tsarki ban taba hada shimfida da wata mace ba sai ke.”

Kukan da take yi ya karu, lokaci daya kuma ta amshe Alqur’anin ta mayar inda yake.

Tana juyowa da zummar komawa kan kujerar ne ta fada kansa, saboda ba ta san ya biyo bayanta ba, maimakon ta yi kokarin tashi kamar yadda ya zata, ji ya yi ta kara kwanciya a jikinsa, kukanta ya ci gaba da ratsa dodon kunnensa. Yayin da bugun zuciyarsa ya canja saboda yadda yake jiyo na Asiya.

Shi ma hawayen yake yi, don Asiya tana jin saukarsu a bayanta.

Tsawon lokaci suna a haka, a hankali ya zare Asiya daga jikinsa, ya zuba mata idanunsa da suka canja launi zuwa ja. wanda rinewar sun ba ta hana ta hango tsantsar kaunarta shimfide a ciki ba.

Hannayenta du biyun ya kama.

“Wannan kaddararmu ce Rabin Raina, Allah ya fi mu sanin abun da yake nu fi da wannan, har yanzu ina sonki, wannan bai sanya na ji sonki ya ragu a zuciyata ba. Abin da nake so shi ne kawai ki natsu, ki dawo cikin hankalinki mu magance matsalar kada ta yi girman da za ta fi karfinmu. Damuwarki na daga mun hankali, kin san yadda take tarwatsa duk wata natsuwa tawa. Kin san ya zuciyata take a kanki, kin san irin raunina a kanki Rabin Raina, kada ki yi amfani da damar wajen tarwatsa rayuwata. Ki tausaya min, kin manta alkawuranki gareni? Na cewa ba za ki guje ni ba duk runtsi, me ya sa yanzu kike kokarin yin hakan? Bayan zama a inuwar ma’aurata shi ne burinmu. “

Kuka take yi sosai,, kukan da shi ne kawai ya fahimce shi, ya san yanzu sai yadda ya yi da ita.

Jikinsa ya kuma jawota a karo na biyu, ba musu kuwa ta yi yadda yake bukata, tana jin yadda zuciyarsa ke harbawa da sauri, jikinsa ya yi wani irin zafi, hakan ya tabbatar mata yana tsananin bukatarta.

Bayanta yake bugawa a hankali, har zuwa lokacin da sautin kukanta ya daina fita sai ajiyar zuciya.

Shi ma zuwa lokacin jikinsa ya daidaita, toilet ya ja hannunta bayan ya cire mata hijabin jikinta.

Da kansa ya wanke mata fuskarta, gefen gado ya ajeta, kafin ya shiga kitchen ya zo da ruwa mai sanyi, ya mika mata.

Ba musu ta karba, shi ya karbi cup din ya aje a kan durowar gado, ya zauna suna fuskantar juna.

Ganin ba za ta iya jure kallon da yake mata ba ne, ta yi saurin aje kanta kasa hade da wasa da yatsun hannunta.

“Rabin Raina.” ya ja sunanta a hankali. Ba ta amsa ba sai dai ta dago kai tana kallonsa.

“Ina fatan komai ya wuce, za ki ba ni hadin kai wajen fuskantar matsalarmu?”

Kai ta daga alamar. Eh

“Promise?”

Ta kuma daga kai.

“To fada mun wane mataki kike so mu dauka a gaba, ni dai da tunanin mu sake zuwa gwaji nake yi.”

Kai ta yi saurin girgizawa hade da fadin “Mu bar wa Allah na sa ikon kawai. Ni ba na son komawa asibiti kuma.”

Ya zuba mata idanu cike da tausayinta. Ji yake kamar ya kwashe duk damuwarta ya canja mata ita zuwa farin ciki

“Hakan ya yi miki?”

Kai ta daga alamar Eh.

Ya sauke ajiyar zuciya mai karfi, wacce ta sanya Asiya saurin daga kai tana kallonsa.

Gefe guda ya tsirawa ido kamar wanda yake kokarin karanta wani rubutu da bai gane ba.

Jin tashin Asiya ne ya sa shi dawowa dogon tunanin da yake yi.

“Rabin Raina! Wannan sirrinmu ne, don Allah kada kowa ya ji, sannan ki kiyaye mu’amala da mutane kai tsaye.”

Kai jijjiga alamar gamsuwa

Shi ne ya rike mata basket din, har bakin hanya ya rokata, sai da yaga tafiyarta sannan ya koma gida.

Yanzu sai ya ji ya fi samun natsuwar da zai fuskanci wuri daya, don Asiya ba ƙaramin tayar masa da hankali ta yi ba.

Inda ya gode Allah kawai ba ta da riko sosai, dama ya san za ta sakko sai dai bai san rana da kuma lokacin ba.

Bayan tafiyarta ne ya nemi abinci, ya yi wanka sannan ya tafi kasuwa.

<< Labarin Asiya 3Labarin Asiya 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×