Tun daga lokacin da ta taso Allah Ya dasa mata kaunar Hassan a zuciyarta,
Komin shi burge ta yake, musamman yadda baya daure musu fuska, kuma baya sake musu, kai tsaye suke tambayarsa abu, kuma kai tsayen yake yi musu idan yana da shi.
Bai faye shiga shirginsu na wasanni a gidan ba, yana da kamewa, kamewar da ke burge Asiya.
Shi ba miskili ba ne, kuma ba mai yawan magana ba ne, wani lokacin yana zaune za a ta magana amma kala ba ya cewa.
Wani abu da yake kara burge ta da shi, shi ne hustler ne, baya gajiya wurin neman na kansa, tun ya taso a karaminsa yake sana’a, har dan karamin shago da aka bude masa a kofar gida.
Yana da naciya da jure kalubale a kan duk abun da ya sa gaba.
A bangaren ɗabi’a kuwa mutum ne mai tsabta, kula da addini, yana da son zumunci sosai, ba shi da raini ko girman kai.
Yaran gidan suna girmama shi sosai, kasancewar shi ne namiji babba a gidan.
A bangaren siffa kuwa dogo ne sosai, duk da dai ba zakaka ba, amma a kallo daya za ka saka Hassan a layin dogaye. Yayin da ya debo rashin jiki a wurin Addah.
Baki ne amma bakin mai haske kamar dai jikin Addah din. kodayake ku san duk yaran gidan ma haka kalarsu take, su ba bakake ba, ba kuma farare ba.
Fuskarsa dauke take da siririn dogon hanci, da madaicin baki mai dauke da labba marasa kauri sosai, yana da yalwar gashin gira, wacce ta karawa matsakaitan idanunsa kyawu.
Asiya na daya daga cikin mutanen da Hassan ke burgewa, ba ta gajiya da kallonsa idan yana harkokinsa a tsakar gida.
Kasancewar flat nasu a jere yake, musamman take fitowa ta zauna a baranda tana kallon sa.
Yayin da duk wani abu na shi ba ta daukarsa da wasa, tun daga gyaran daki, abincinsa da duk wani abu da ya shafe sa.
Lokacin da ta kara girma ne da kanta ta fahimci tabbas sonsa take yi, irin son nan mai zafi, saboda yadda take shiga damuwa idan ba ta gan shi ba.
Ta rike lokacin fitar sa da kuma dawowarsa, lokacin yana yi za ta fito falo hade da yaye labulen window tana lekansa.
Duk da wani lokaci ya kan shigo bangarensu kafin ya fita musamman idan shi ne zai riga Hajjah fita.
Da kanta ta san iska ce wahalar da mai kayan kara, saboda ko sau daya Hassan bai taba nuna mata ya fahimci sakon da take tura masa ba,, abin da ta fahimta shi Sam, babu mace a gabansa.
Hakan bai sa gwiwarta ta sare ba, kullum cikin kyautata mishi take, hade da hidima da shi, ta kan siyo abu ta ba shi, misalin turaren ko package na kayan amfanin maza, irinsu roll on, after shaved da sauransu.
Har karyar ciwo take yi, saboda idan tana ciwon ne kawai take samun damar kasancewa da shi, ko ba komai Hajjah za ta ce ya kai ta asibiti.
Cikin murmushi ta tuna wata ranar Alhamis, a ranar ne kawai yaran gidan kan fito farfajiyar gidan su yi wasanninsu, kasancewar ba Islamiya da yamma.
Juma’a kuwa ranar ziyara ce. Yayin da Asabar da Lahadi suke wuni a tahfeez
kamar ko wace ranar Alhamis haka suka fita harabar gidan da yamma don wasanninsu, masu table tennis na yi masu vardimentone na yi.
Asiya na daya daga cikin wadanda suke yin wasan vardimentone tare da Abbas, ita din mayyar vardimentone ce, ta kware a wasan sosai, sanye take da kayan sport farare Kal, sun yi mata kyau sosai hade da fito da kyakkyawar surar jikinta.
Zainab ce alkaliyar wasan, yayin ds sauran yaran suke ba idanunsu abinci .
Irin cin da take wa Abbas ne yake sanya ta dariya, tun tana dannewa, har dariyar ta fito fili, cikin dariyar ne ta ruga aguje don taro yar kwallon da Abbas din ya jeho mata sai ta zame timm ta fadi, irin muguwar faduwar nan, da ta sanya jikin kowa sanyi, hakan ya sa duk suka taru a kanta cike da mutuwar jiki.
Hassan ma da ya shigo tsaye ya yi, sosai ya ji faduwar tata a jikinsa, dalilin da ya sa kenan ma ya kasa motsawa daga inda yake kamar an dasa shi haka yake kallonsu ba tare da ya ce komai ba.
Da kyar ta mike hade da kakkabe jikinta, kafarta ta ja zuwa kan plastic chair ta zauna, sai a lokacin ne masu dariya suka fara mata dariya.
Ita kuma ta daure fuska kamar za ta yi kuka.
Bai ce komai ba ya wuce su zuwa cikin gida, amma tabbas faduwar Asiyar ta tsaya masa.
Zuwa takwas na dare Asiya ta kasa bacci kafa na ciwo, tun tana daurewa har ta dangyaso kafar zuwa dakin Hajja.
A lokacin Hajjah aiki take yi a cikin laptop din ta.
Ganin Asiyar ne ya sa ta ce
“Lafiya?” a
“Kafata ke ciwo” cikin shagwaba ta yi maganar
“Garin ya ya?” cike da mamaki Hajja ta tambaya, saboda ita ba ta sa ta fadi ba
“Faduwa na yi dazu muna wasa.” cikin zumbura bakin shagwaba ta kuma fada.
“Mu gani.” Hajja ta yi maganar hade da dukawa tana duba kafar Asiyar da ta kumbura tana kuma fadin
“Wai faduwa kika yi ne?”
Kara narkewa ta yi sannan ta ce “Dazu ne na fadi a filin wasa.”
“Ahaf! Ba ga irinta ba, abu ne kun yi girma da shi amma ba za ku daina ba, wannan wasan na yara ne ai, ba irinku da kuka fara girma ba. Wannan abun duk da ban san targade ba, to gaskiya targade ne.”
Asiya ta narke fuska kamar za ta yi kuka yayin da Hajja ke kallonta.
“Shigo, bari in kira yayanki idan ya dawo ya zo ya kai ki wurin gyara. Don wallahi idan ya kwana,, hmmm, ba zan ce komai ba.
A hankali Asiya ta kuma dangyasa kafar ta karasa kan kujera ta zauna jki a mace, saboda ta ji an ce gyaran targade da zafi, ta sha gani ma ana gyara ma wasu sui ta ihu.
Tana cikin tunanin ne Hassan ya shigo sanye da jallabiya mai ruwan toka, kamshin turarensa mai dadi ya mamaye falon.
Ta lumshe ido bayan ta jefa kwayar idonta a cikin nasa.
Duk da bai da jiki, amma kuma kana kallon jikinsa kasan cewa baya tare da wahala ko yunwa, gashi luf-luf kwance a jikin nasa, musamman kafarsa da tsintsiyar hannunsa. Sannan jikinsa ko ina a cike amma kuma dai a hakan ba za a kira shi mai kiba ba.
A natse yake sauraron bayanin da Hajja ke yi, har zuwa lokacin da ta karasa, a lokacin ne kuma ya dora idonsa a kan Asiya, wacce dama shi take kallo.
“Tashi mu je” ya fada daidai yana daukar key din motar Hajja da ke kan stool
“Idan ba ta tsaya ba, ka kwakkwaɗemun ita da kyau don Allah, tun da ba ta jin magana, kullum ina mata warning a kan maganar kwallon nan ba ta ji.”
Bai yi magana ba, har ya fice, Asiya kuma ta bi shi a baya kamar jela bayan ta zumbula hijabin Hajjah.
A kofar gida suka samu mai gyaran, tsoho ne da ya ta sar ma shekara sittin.
Dalilin da ya sa kenan ya cewa Hassan “Za ka iya rike ta?”
Ya mayar da kallonsa a kan Asiya da ya fahimci sosai ta yi laushi tun kafin a taba kafar.
“Ba sai an rike ta ba za ta iya tsayawa. “
Ya yi maganar yana kallon Asiya, kallon da ke nuna alamar ta je wurin mai gyaran.
Kamar gaske kuwa ta zauna hade mika mishi kafar, yayin da Hassan ya tsaya a kanta hade da harde hannayensa a baya yana kallon yadda mai gyaran ke jan kafar Asiya a hankali hade da tofa addu’a.
A hankali kuma jan kafar ya fara canja salo, inda yake dan murzawa a hankali.
Tun tana daurewa har ta fara kuka a hankali, can da mai gyaran ya fisga, sai ta kwace kafar hade da zumduma ihun da ya janyo hankalin mutane da yawa wajen.
Lokaci daya kuma ta kwasa da gudu tana dangyasa kafarta.
Hassan da ke tsaye a bayanta yana kallo sosai abun ya ba shi dariya, har ya kasa rike dariyarsa, ya bi bayanta da nufin dawo da ita.
Amma fir! Ta ki dawowa, tun yana lallabata har ya fara canja fuska, cikin kurari ya ce
“Wuce mu je, idan ba haka ba wallahi zan yi miki shegen duka a nan, sannan kuma in sanya a daureki kam sai an gyara”
Ba ta yi magana ba illa kukanta da take yi, kuma ba ta yi alamun za ta tafi ba..
Ganin ba ta da niyyar tafiya ne ya kuma canja fuska yana fadin “Za ki je ko sai ranki ya baci.”
Ganin da gaske yake ne ta ce “Zan je”
“To wuce.”
“Ya yi mun a hankali to” cikin kuka take maganar
Da kyar ya kuma tasa keyarta wurin mai gyaran.
Yana ja, ta kuma zabura ta ruga da gudu tana tsalle da kafa daya.
Dalilin da ya sa kenan mai gyaran ya ce sai an nemo mai rike ta, wahala za ta ba shi, shi kuma ba zai iya ba don ya tsufa.
Ita ko tana gefe hade da mitsittsikar idanu kukanta na fita a hankali.
Wani gardi mai gyaran ya kira, yayin da Hassan ya yi mata jan ido ta zo ta zauna.
Ana rike kafar kuwa ta kuma yunkurawa za ta tashi, katon nan ya yi ram da ita, ko numfashi da kyar take fitarwa saboda mugun rikon da ya yi mata, ga azabar gyara ga ta riko ga tsamin jikin gardin ya dame ta.
Ihu take yi sosai tana kiran Hassan, don shi tuni ya koma cikin mota, jin kiran nashi ya yi yawa ne ya sanya shi fitowa zuwa inda ake gyaran.
“Yaya!” ta kira sunansa cikin kuka
Bai amsa ba ta ci gaba “Ka ce ya sake ni wallahi zan tsaya, don Allah ka ce ya sake ni, ni zan tsaya a gyara mun”
Duk mutanen da ke wurin suka tuntsire da dariya idan ka dauke Hassan da shi ma bai ji dadin yadda katon ya yi cumu-cumu da ita ba.
“Za ki tsaya da gaske?”
“Eh wallahi zan tsaya” ta fada cikin kuka.
“Shi kenan sakar ta”
Ba musu kuwa ya sake ta.
Iskar yanci ta shaka, don da rikon nasa da gyaran targaden ba ta san wanne ya fi azaba ba.
Daurewa kawai take, idan ta tuna rikon gardin can sai ta ga gara ta tsaya haka ya fi mata sauki.
Amma wata matsa da aka yi wa kafar ba ta san lokacin da ta saka kara mai karfi ba, hade da kwalawa Hassan kira.
“Yayaaaaa!!!!! Wayyyo Yaya!! Ka zo za a kashe ni. Wayyyo Yaya! Hajja za a kashe ni, wayyyo Babana!”
Cikin sauri ya kuma tahowa har yana tuntube, a cikin kansa yake jin sautinta, ji yake kamar ta sanya amsakuwwa, da ya san abin da zai faru kenan da bai rako ta ba.
“Haba Asiya, wai me ye haka ne? Kalli yadda kika tara mana mutane. Ke ko kunya ma ba kya ji? ” cikin fada sosai ya yi maganar
Ta daga kai hade da kallon mutanen daya bayan daya cikin kuka ta ce
“Ni ina ruwana dasu, sun san wahala da azabar da nake sha ne? Don Allah ni dai zo ka rike ni, ni bana son wancan ya kuma rikeni, kamar zai kashe ni nake ji, kai kuwa dan’uwana ne”
Mutane wurin suka kuma kwashewa da dariya.
Ga dai kuka tana yi amma bakinta ya ki mutuwa
Haka nan Hassan ya aje gwiwowinsa kasa, sai ya rasa ta ina zai rike ta, me zai rike a jikinta? Ba zai iya yi mata irin rikon da wancan ya yi mata ba. Kafin ya ankara sai ya ji ta fada kanshi ta kwanta, a jikansa tai ta birgima har aka gama gyaran. Sosai ya yi likis kafin a gama gyaran saboda yadda ya yi ta taro ta, ko kuma ta kama shi ta kankame kamar za ta tsaga jikinsa ta shiga, abin da bai fi 15mns ba, amma ya daukesu har awa daya.
Idan ya kalleta sai ya ji dariya ta kama shi, musamman yadda ta yi wujiga-wujiga da ita.
Koda suka dawo dakinta kawai ta wuce, ta sauke gajiyarta a can.
Kuma ta yi sa a ba Zainab.
Jikinta kamshin turaren Hassan kawai yake yi, saboda haka ta ki cire kayan da su ta yi bacci tana shakar kamshin turaren da ba yake kashe mata jiki da sanya ta kasala.
Koda ya kasance shi daya dariyar gyaran targaden Asiyar yake yi, sai a lokacin yake jin haushi da bai yi mata bidiyo ba. Gobe kam Hajja za ta sha labari.
*Wanshekare da safe*
Kamar ko wace safiya gidan Alhaji Baba idan gari ya waye kowa hidimominsa kan sha masa kai na daga girki, gyaran gida, shirya yara zuwa makaranta da kuma shirin fita aiki.
Zuwa tara na safe gidan ya zama shiru kamar ba kowa.
A daidai lokacin ne kuma Hajja ta fito cikin shirinta, kasancewar akwai zaman majalisar jaha da za ta dakko a gidan gwamnatin jaha da misalin goma na safe.
Asiya ce kawai zaune a falon hannunta rike da ƙaramin kofin tea, gabanta kuma dankalin irish ne da kwai take ci a hankali.
“Ya kafar ta ki?”
“Da sauki. Hajja ina son zuwa wanke kai fa.”
“Kina dangyashin za ki je, komin saurin unguwar zoma ai ta jira dai a haihu. Babanki ma zai zo jibi.”
“Eh mun yi waya da shi dazu da safe.” farin ciki kwance a kan fuskar Asiya a lokacin da take maganar.
Daidai lokacin ne kuma Hassan ya shigo, cikin shigar kana nan kaya, farin jeans tas, da jar riga t-shirt wacce ta kame jikansa.
Kamshinsa mai dadi ya cika falon.
Kamshin da yake kashewa Asiya jiki da jefata cikin kasala.
Kallonta ya yi cikin murmushi yana fadin “Ya kafar ta ki?”
Baki ta zumbura hade da kawar da kai gefe ba tare da ta ce komai ba.
Hajja ma dariya ta yi hade da fadin “wai me ya faru ne a wurin gyaran?”
Hassan ya yi dariya mai sauti “Ba zan sake kai yarinyar nan wurin gyara ba, sai kin ga mutanen da ta tara min, ni fa yanzu haka ma jikina duk ciwo yake yi.”
Ido Hajja ta fitar waje hade da kallon Asiya “Wai haka?”
“Hajja kin ji azabar da na ji ne?” a shagwabe Asiya ta yi maganar.
“Ke matsa can, sai ka ce ba mace ba, haihuwa fa za ki yi watarana.”
“Idan ka shirya fita mu je, ko ba ka karya ba?” Hajja ta canja maganar tasu
“Na yi break a wurin Addah, zan je in kai wa Aunty Maimuna wasu kaya ne.”
“Ba ta ce yau za ta zo ba.”
“Ta fasa kuma, ta ce wai ba yanzu ba.”
“Ok to shi kenan mu je.”
“ki tabbatar kin gasa kafar nan kin shafa man zafin nan.” Hajja ta yi maganar daidai suna fita
Ficewarsu ke da wuya, Asiya ta sauke numfashi hade da sansanyar ajiyar zuciya.
Har yanzu falon kamshinsa yake yi.
Ta rasa hanyar da za ta bi wajen nuna mishi soyayyarta, don ba za ta iya fada mishi tana sonsa kai tsaye ba.
Shigowar Zee ce ta katse mata tunani.
Fadawa kanta ta yi hade da tuntsirewa da dariya.
“Sister ashe jiya kuka kika yi wajen gyara, na ji haushi da ba aje da ni ba.”
Asiya ma dariya ta yi kafin ta ce “Ba za ki gane ba, akwai zafi sosai fa, wani shirgegen kato aka sanya ya danne ni, saura kadan in mutu.”
Dariya Zee ta kuma tuntsirewa da ita “Na ji Yaya na fadawa Addah dazu suna ta dariya.”
“Bari in je in gyarawa Yaya daki kar in manta.” cewar Zee a lokacin da take tashi. Lokaci daya kuma ta dauki Irish din da ke gaban Asiya ta kai bakinta.
“Bari in gama zan gyara mishi”
Ido Zee ta fitar waje “Da gaske?”
“Eh mana”
“Dama yana ta cewa in gyara da kyau kamar yadda kike gyarawa, saboda ya ga yau kamar ba za ki iya ba.”
“Zan iya.”
cewar Asiya lokacin da ta Mike hade da dangyasa kafar tata zuwa dakin Hassan.
Gyara na sosai ta yi, duk da babu wani datti, amma har shirin dakin sai da ta canja, Zee taimaka mata kawai take yi, sai da suka turare dakin da turaren wutar Hajja sannan suka ja kofar.
Gab magriba ya shigo gidan, Asiya da ke zaune tana jiran Shigowarsa farin ciki ya lullubeta.
Cikin sauri yake yin komai har zuwa lokacin da ya fice sallahr magriba, sannan ita ma ta koma ciki.