Kullum aikinta shi ne tura sako a kaikace zuwa ga Hassan, amma ko sau daya bai taba fahimtarta ba.
Lokuta da dama bata lokaci take yi wajen girka masa abin da ya fi so, tabbas zai yaba hade da godiya amma ba irin yadda take bukata ba, lokaci ma fi dadi a wurinta shi ne wanda Hajja za ta hadasu tare don yin wani abu, sam ba ta son lokacin ya wuce.
Idan ba ya gida duk sai ta ji gidan ya gundure ta, idan kuwa yana nan ta kan ji farin ciki koda basu cewa juna komai.
Shi ya sa lokacin da sunansa ya fito zuwa Imo don yin service ta fi kowa shiga damuwa.
Ji take yi duniyarta ta zama ba kowa.
Ranar da ya tafi kukan da ta yi har zazzabi ya sanya ta, musamman da ya kasance ba ta ga tafiyarsa ba.
Haka ta kasance cikin kadaici, ta kasa sabawa da yanayin, wani lokaci sai ta saci key din dakinsa ba tare da sanin Hajjah, haka za ta shiga ta yi ta kallon hotunansa da wasu daga cikin kayansa. Maimakon hakan ya kwantar mata da hankali sai ma ya kara tayar mata da shi, ta wuni ba dadi.
Ba ta faye kiransa a waya ba, amma a wannan lokacin kasa daurewa ta yi, haka take dan kiransa lokaci zuwa lokaci.
Wani lokaci da ta kasa bacci dole ta kira shi da misalin goma na dare.
A lokacin kuwa ya fara baccin gajiyar training din da suke fita tun asuba, shi ya sa cikin yanayin bacci ya daga kiran.
“Asiya!” ya kira sunanta da muryar bacci, ganin tun da ya daga ba ta ce komai ba.
“Ta amsa a hankali, kafin ta ce dama na gwada kira ne na dauka ba ka yi bacci ba?” a karon farko ta janyo maganar can kasan makoshinta.
“na yi. Me kike yi ke har yanzu ba ki yi bacci ba?”
“Ba komai.” ta ba shi amsa a takaice.
“Ok ki kwanta to, sai Allah ya kai mu zan kira ki.”
Bai jira amsarta ba ya yanke kiran.
Ajiyar zuciya ta sauke hade da lumshe ido, muryarsa ta yi mata dadi hade da kashe mata jiki, kamar ya yi ta mata magana har zuwa lokacin da bacci zai dauketa.
Record din muryarsa ta sanya tana sauraro har bacci ya dauketa.
Wani abu da yake mata ba ta so shi ne, da zarar ta kira zai katse ta da fadin sorry mun fita zuwa Training idan na yi free zan kira, kiran da ba zai yi ba kenan, har sai idan ita ce ta sake kiran sa, kuma wani lokaci sai ya kara kawo mata wan uzurin. Sosai ranta ke baci, hade da jefa a, damuwar kodai ya gaji da yawan kiran da take yi masa ne.
Akwai lokacin da ta kira ya ce mata zasu karbi abinci, zai kira, amma sai da kwana hudu bai kira ba.
Abin da ya sanyata wuni da ciwon kai, haka tai ta dirkar maganin da Hajjah ke matsa mata ta sha, amma ba wani sauki da take ji gami da abin da ke kirjinta
A ranar na biyar kam kasa jurewa ta yi, dole ta tura mishisakon kar ta kwana.
Bayan tura sakon ido ta zubawa wayar ko ta ga reply amma shiru wai malam ya ci shirwa, tsawon awanni babu amsa.
Hakan ya kuma jefa ta cikin damuwa.
Tun tana sanya ran amsarsa idan ta tura mishi sako har ta cire ranta, idan kawai ta ji kewarsa sai ta tura mishi ƙaramin sako mai nuna alamun gaisuwa da kulawa.
Kiran ma haka nan take daurewa ta kira duk bayan kwana biyu ko uku.
Ta samu sauki ne kawai lokacin da suka samu admission suka wuce school ita da Zee, yawan lecture da karatu ya rika dauke mata hankali, duk da hakan baya mantar da ita tura mishi sako a kullum amma dai ya rage mata lokacin da take batawa wajen tunanin shi.
Ko Zee ba ta taba bari ta fahimci halin da take ciki ba, duk da ba ta gajiya da jin labarinsa a bakin Zee din. Hirarsu tana tsawo ne idan ya kasance a kan Hassan ne
Kamar ko wane lokaci sai da ta kammala shirin kwanciya baccin ta ne sannan ta turawa mahaifinta sakon sai da safe, shi ba ta faye kiransa a irin wannan lokacin ba, saboda yanayin aikinsa. Bayan ta tura mishi sakon ne ta kira layin Hajja don yi mata sai da safe kamar yadda ta saba dai.
A can kasa take jin kamar muryarsa, gabanta ya yi wata irin faduwar da yake yi ko wane lokaci muddin za ta gan shi ko jin muryarsa.
Ko hotonsa ta gani sai gabanta ya yi wata irin faduwa.
“Yaya ne ya zo Hajja?” ta yi tambayar a hankali
“Eh. Bai jima da isowa ba.”
“Ki ba shi wayar.”
“Kanwata, har yanzu ba ki yi bacci ba.” ya fada bayan ya daga wayar.
“zan yi baccin kenan, shi ne za ka zo ba ka fada mana ba?”
“Na fada mana, Zee ta manta kenan ba ta sanar miki ba.”
“Shi kenan za mu zo kwance jaka gobe sha Allah”
“Allah ya kaimu.”
“Kar fa mu zo ba ka nan.”
“Za ku same ni sha Allah.”
Cike da farin ciki ta yanke kiran lokaci daya kuma ta taba zee da ke gefen ta
“Ashe Yaya ya zo Sister?” Asiya ta tambayi Zee da ta fara bacci bayan ta yanke kiran.
“Wane Yaya?” cikin bacci Zee ta yi tambayar
Asiya ta ba ta amsa da “Yaya Hassan?”
“Oh! Na sha kin san ya zo ai.” cikin muryar bacci hade da juyi Zee ta ba ta amsa.
Bacci ya kauracewa idonta yayin da dare ya yi mata tsawo, wani irin doki da murna take yi, almost wata biyu ba ta sanya shi a idonta, shi ya take jin goben kamar ranar sallahrta.
Shiryawa gami da tsara yadda za ta tare shi kawai take yi.
Shi ya sa tana idar da sallahr asuba, ta kwaba lalle hade da yin design mai kyau a yatsunta.
Zuwa tara na safe ta wanke, ma sha Allah yatsun nata kuwa sun yi kyau sosai ta yadda take ganin tabbas zasu ja hankalinsa.
Misalin goma na safe suka gama shirinsu cikin atamfa mai kalar ja da ratsin fari.
Dinkin riga da sicket ne ya zauna a jikinsu das, sansanyan kamshi mai ratsa zuciyar mai shakarsa yana fita daga jikinsu.
Abun takaici ga Asiya shi ne, tun da ta isa gidan take ware ido ta ga ta inda farin cikin zuciyarta zai bullo amma tsawon awa biyu da zuwan su gidan ko kamshin turarensa ba ta shaka ba.
Ta kuma kasa tambayar kowa yana ina, sai dai kuma ba ta jin dadin komai, ko hirar da suke yi da Mamanta a kan kannenta ba sosai take fahimtar komai ba.
Zee kuwa ko a jikinta harkokinta kawai take cike da farin cikin ganinta cikin yan’uwanta.
Tana kan sallayar da ta idar da Sallahr azhar ne Hajja ke tambayarta yaushe zasu tafi.
Ta dan bata fuska kadan “Sai gobe”
“Me zai sanya sai gobe, ni kam boarding kuke ne ko Day? Ina tun farko kune kuka zabi boarding, yanzu kuma kun kasa zama, duk sati kuna gida. Ba za ku kwana ba, karfe biyar na yi za ku koma. Ni na rasa ma me ya kawo ku gidan.”
Ta kuma zumbura baki ba tare da ta ce komai ba.
“kuna da bukatar wani abu ne? Don ni fita zan yi”
“Ba komai.” ta ba ta amsa a hankali.
5k ta aje mata a gefen sallayar “Kar ki bari in dawo in same ku a gidan nan.”
Ajiyar zuciya Asiya ta ajiye bayan fitar Hajja, lokaci daya kuma ta dakko wayarta, lambarsa ta latsa da niyyar kira duk da ba ta so hakan ba.
Amma ba za ta iya tafiya ba tare da ta gan shi ba.
“Yaya mun zo ba ka nan ga shi har zamu tafi bamu amshi tsaraba ba. ” abin da ta fara fada kenan bayan ya daga wayar.
“Sorry! Wallahi na manta kin ce mun za ku zo, kuma na yi nisa sosai, idan kwana za ku yi zamu hadu da safe idan kuma ba kwana za ku yi ba, zan shigo school din naku gobe sha Allah.”
Jikinta ya mutu, bakinta ya yi nauyi sosai wajen ba shi amsa.
Wani kunci ya ziyarce ta hakan ya sa ta yanke kiran ba tare da ta ce komai ba.
Ido ta zuba ma wayar, daga bisani kuma ta yi jifa da ita, hade da fashewa da kuka mai sauti. Babu abun mai wahala irin kana son mutum bai sani ba, dama-dama wanda ya ce bai sonka, ko na komai ka san matsayinka, amma kana so ba a sani ba akwai wahalarwa.
Zuciyarta ta fara sarewa, da gaske Hassan bai san son shi take yi ba, har yanzu kallon kanwa yake mata.
Babu yadda ta iya misalin karfe biyar na yamma suka bar gidan, amma wani irin kunci take ji, ga ciwon kan da duk lokacin da za ta shiga irin wannan yanayin sai ya yi mata ciwo.
Ranar Lahadi tun misalin karfe 9 na safe Asiya ke zuba ido ta ji Zee ta fada mata Hassan na hanya, ko shi ya kira ta amma shiru.
A wannan karon kam ta yi alkawarin ba za ta kira shi ba, idan ya zo shi kenan idan kuma bai zo ba ta hakura.
Jiki a mace take yin komai, zuciyarta sam babu dadi, ko library da suka je don yin karatu littafi kawai take budawa amma ba ta fahimtar komai.
Karfe shidda suka fita daga libraryn, Abbah da ke ta bibiyarsu tun shigowarsu ya bi bayansu da sauri.
Gaban Asiya ya shiga, fuskarsa dauke da murmushi hannuwansa rungume a kan kirjinsa
“Ranki ya dade.” ya fada idonsa a cikin nata.
“Abbah!” ta ja sunansa a hankali
Shi ne namiji na farko a duk fadin makaranta da ya nuna yana sonta, kuma ya jure wa rashin kulawar da take ba sa. Yau kam sai ta ji ya ba ta tausayi, idan abin da take ji a kan Hassan haka shi ma yake ji a kanta, ya kamata ta saurare shi, ba mamaki ma Allah Ya dube ta, ya kawo mata sassauci a na ta lamarin.
Lumshe ido ya yi “Ranki shi dade”
Suka dan yi gajeran murmushi a tare, lokaci daya kuma ya mayar da idonta a kan Zee da ta dan yi nisa da tafiya.
“Yaushe za ki ban dama ne? Ina ta fama da dakon kaunarki a zuciyata, wallahi ni kawai ne na san halin da nake ciki a kanki, amma kin ki saurarata”
A wannan yanayin ba ta san doguwar magana, ta rasa dalili, maganar Hassan ce kawai take mata dadi, ita ce kawai take iya sauraro ba tare da gajiya ba. Amma sai ta tsinci kanta da sauraron shi hade da jin wani abu ya darsu a Zuciyarta gami da shi
Abbah ya hada komai da namiji zai yi takama da shi a wurin mace, to amma kuma ya ki kwanta mata a rai. Don idan cika ce
ma irin ta namiji ya fi Hassan cika ido, sai dai Hausawa sun ce abin da kake so shi kake gani
Hannu ta mika mishi “Ba ni wayar taka?”
Ba musu ya ciro ta daga aljihun rigarsa na gaba ya mika mata.
Lambarta ta sanya mishi, ba tare da ta ce komai ba ta mika mishi wayar lokaci daya kuma ta raba gefensa ta wuce.
Bai damu ba, don kuwa ya dade yana neman lambar tata bai samu ba sai yau.
Rashin zuwan Hassan ba karamin sanyayata ya yi yau ba, kowa kallon mara lafiya yake mata, kila ko don yadda take abu cike da rashin kuzari ne.
Duk irin tambayar da Zee take yi mata a kan me ya same ta, ba komai kawai take ce mata.
Don kuwa ba za ta iya fada mata son yayanta ke dawainiya hade da wahalar mata da ruhi ba.
Abin da ta sani kawai za ta yi hakuri hade da juriyar mantawa da shi, ta karbi soyayyar wasu ba mamaki hakan ya debe mata kewar Hassan da bai san tana dakon soyayyarsa a kirjinta ba.
Ba Abbah dama kuwa sai ya rage mata kaso 40 na damuwarta, yayin da karatu da harkokokin makaranta ya kwashe 30,dalilin da ya sa kenan har suka kammala jarabawar first semester tsakaninta da Hassan din baya wuce text din Happy Friday, idan ta yi status ya buda, sai gaisuwa sama-sama.
Sai dai hakan bai rage komai a son da take yi mishi ba, hasalima azabtuwa take yi sosai da yanayin.
Saboda kullum kara kyau da cika yake yi, ga ni take kamar da gayya ma kullum yake kara canjawa, yadda yake sakin zafafan hotuna cikin kayan bautar kasa na karamin rudata yake yi ba, ga shi nan kullum cikin nishadi, irin dai ba shi da damuwar nan.
Wani lokaci kuma danasanin bude status din shi take yi, saboda yadda take ganinsa tare da mata, akwai wani guntun video da ya taba dorawa kadan ya hana ta samu heart attack. Zaune a kan dutse jikin wata bishiya yana taba wayarsa, yayin da wata ke tsokanarshi, ganin yadda ya yi banza sai ta matso hade da fige hular kansa, wannan ya sa ya mike hade da bin ta, kafin ya kamata videon ya kare, ranar kam ta yi danasanin kallon Wannan video. Ciwo ta yi sosai na ku san sati daya, don har gida ta koma, kuma tsawon jinyar Hassan bai taba kiranta ba, duk da ta ji Hajjah na fada mishi ba ta da lafiya, sai dai kawai ya ce a yi mata sannu.
Wannan ya sa ta kara lallashin zuciyarta hade da tursasa mata nesanta kanta da Hassan, tun da dai ba ta ita yake yi ba.
Tun daga lokacin ta kauracewa kiransa hade da tura mishi sako, ba karamin azabtuwa take yi ba, sai dai haka nan take daurewa.