Ba ta san lokacin da ta koma yar gidan jiya ba, ba za ta iya jurewa share shi ba, zuciyarta ta kasa yi mata biyayya.
Addu’a kawai ta dage da ita, wajen neman zabi daga makagin da ya samar da ita daga babu.
A lokacin ta fahimci tasirin addu’a, ƙasa da watanni biyu da ta dage da addu’ar sai ga Hassan na replying na sakon ta.
Duk dai ba ya wuce “Thanks ko Amin” hakan ba karamin faranta ranta yake yi ba, ranar da ya fara maido mata da amsa, ta yi tsalle ta rawa, har da sujudusshukur ta yi.
Ta kuma dagewa da addu’a, sai ga Hassan yana mayar mata da text din happy Friday, duk juma’a zai tura mata sakon, ji take yi kamar ta fi kowa sa a, a duk lokacin da ta ga sakon Hassan ya shigo wayarta.
Ita kam ya zame mata kamar farilla, kiransa da kuma tura masa sako.
Yau ma kamar yadda ta saba, misalin karfe takwas ta kira wayarsa.
Gabanta ya yi wata irin faduwa, wannan shi ne karo na uku da ta kira wayarsa mace ta daga, karon farko da ta kira ta ce mata ta yi mai wayar baya kusa, wayar na caji.
A karo na biyu ma haka ta fada mata, yau ma da ta daga ce mata ta yi mai wayar ya fita, idan ya dawo za a fada mishi ta kira.
Ta sauke wayar a hankali ba tare da ta ce komai ba, abun tambayar shi ne
“Wacece mai daga wayar?”
“Me ye alakar Hassan da ita?”
“Me ya kai wayar Hassan din hannunta?”
“Me ya sa take daga kiran wayar kai tsaye? “
Wadannan sune tambayoyin da take bukatar amsarsu, sai dai ba ta san a ina za ta same ta ba
Idan har ya kasance mai daga wayar budurwarsa ce lallai yana sonta, tun da har bai shata mata layi da wayarsa ba, idan zai fita ma ita yake ba wayar ya kuma ba ta iznin daga kiran kowa.
Ta zubama wayarta ido, shi ne yake kira, karo na farko da ta ji kiran nasa bai burge ta ba, ba ta son jin muryarsa, gab kiran zai yanke ta daga.
“Kin kira bana kusa”
Abin da ya fara fada kenan.
“Uh.” ta ba shi amsa
Suka dan yi shiru, maimakon da idan da ta kira tana mishi hira sosai cikin nishadi.
A jikinsa ya ji kamar dai akwai wani abu ba daidai ba
“Me ke damunki?” ya tambaye ta cikin kulawa
Shiru ba ta ba shi amsa ba
Ya kuma maimaita tambayar, maimakon ta amsa sai shesshekar kukanta ya ji.
Karo na farko da ya ji zuciyarsa ta buga ta dalilinta
Ci gaba da tambayarta ya yi, amma maimakon amsa sai sautin kukanta ne kawai ke dukan dodon kunnesa, daga karshe take yanke kiran, hade da kashe wayar gabadaya.
Dalilin da ya sa kenan ya shiga damuwa, yay ta kiran layin duk da ana fada mishi a kashe ne amma haka yay ta gwadawa, sai daga baya ne hankalinsa ya dawo jikinsa, dalilin da ya sanya shi kiran layin Zee
“Kina tare da Asiya ne?” cikin sauri ya tambaya ba tare da ya amsa sallamarta ba
“A’a tana daki, ni kuma ina nan muna group Assignment.”
“Ki je yanzu ki kai mata wayarki, ina son yin magana da ita.”
“Lafiya kuwa Yaya”
“Ki je ki yi abun da na ce kuma kina tambayata wane abu ne haka?” cikin I tsawa ya yi maganar, hakan ya sanyata mikewa a hanzarce ta nufi dakin nasu.
Cike da mamakin me yake faruwa da Asiyar to? Lafiya kalau ta baro ta, kuma ina wayar Asiyar da ya kira layinta?”
Me ya sa ma ya damu haka, kodai akwai matsala a gida ne?
Haka tai ta tambayar kanta, har ta isa dakin.
Kwance ta same ta fuskarta jagab da hawaye, abin da ya yi matukar daga hankalin Zee kenan.
Zama ta yi gefenta, kafin ta yi magana kiran Hassan ya shigo
“Kin zo ne?” ya tambaya bayan da ta daga kiran
“Eh.”
“Ba ta wayar.” ya yi saurin fada don kuwa burinshi shi ne ya ji muryarta
Yana jin yadda Zee ke fama da ita ta daga wayar amma fir ta ki karbar wayar sai ma kukanta da yake karuwa, kuka ne na abubuwa da yawa, kishi gami da tausayin kanta, ba tun yau ganin Hassan tare da wata ke azabtar da ruhinta ba, shi ya sa yau ta hada duk kukan take yi, ko ba komai zuciyarta za ta yi sanyi.
Haka ya gaji ya yanke kiran Asiya ba ta daga ba.
Abin da ya kara jefa shi cikin damuwa kenan. Karon farko da bacci ya kauracewa idanunsa ta dalilinta. Shi kansa ya rasa dalili amma tabbas ya san damuwarta ce ta hana shi bacci
Hotunanta da sakonninta sune suka taya shi hira a wannan dare.
Sai a lokacin ne ya rika ganin gwala-gwalan kalmomin da take amfani dasu a sakon da take tura mishi.
Bibiyar chat nasu ya rika yi, wanda bai sanin lokacin da murmushi ke subuce masa idan ya kalli wasu maganganun nata.
Da gari ya waye ma aikin da ya wuni yi kenan, neman layin Asiya, amma a kashe.
Har zuwa dare dalilin da ya haddasa mishi ciwon kai mai tsanani kenan, sannan ya ji babu abun da yake bukata da ya wuce ganin Asiya.
Ko hirar da suke haduwa suna yi bai samu ya fita an yi da shi ba.
Shi ya sa Yusuf abokinsa ya shigo yana tambayar sa lafiya, saboda ya lura duk yau baya cikin walwala.
Bayan ya gama sauraron maganar Hassan kan abin da yake damun shi, murmushi Yusuf ya yi tare da fadin”Yarinyar nan sonka take yi abokina, saboda ina, hasashen kishi ne ya sanya ta kin daga kiranka, don kuwa kishi ne kawai ke jefa mace a irin halin da ka ba ni labari take ciki.”
Hassan ya yi sauri ta tashi zaune “So kuma?” cike da mamaki ya yi tambayar
“Kwarai ma kuwa idan na canka daidai.” cewar Yusuf cike da kwarin gwiwa
Komawa ya yi ya, kwanta yana mamakin maganar Yusuf din . “Kenan tun yaushe Asiya ke son shi, kuma ya aka yi bai gane hakan ba, har sai da wani ya yi masa tafinta, kodai hasashen Yusuf ne kawai, amma ta ya za ace Asiya na son shi, yarinyar da yake mata kallon kamar Zee kanwarsa, bai taba kawo ma ransa zai zo Asiya ko ita ta so shi ba. A hankali ya rika tunano yadda take kula da lamarinshi da duk wani abu da ya shafe shi, a da, bai dauki hakan komai ba, sai yanzu ne yake ganin tabbas sako take turawa, shi kuma ya kasa fahimta. “
Haka yay ta jujjuyawa maganar Yusuf hade da tattaro hujjoji daga bangaren Asiya wanda zasu gasgata hasashen Yusuf din.
Kasa hakura ya yi, da sassafe ya baro Imo zuwa gida.
A bangaren Asiya kuwa har ramar dole ta yi, saboda ita kawai ta san irin tarin kaunar da take wa Hassan, idan har ya kasance ya mallaka ma wata zuciyarsa lallai za ta kasance cikin tashin hankalin da ba za ta iya misilta shi ba, ta ya ma za ta fara kallon ana bikin Hassan da wata.
A duk lokacin da ta zo wannan gabar a tunaninta ba ta sanin lokacin da hawaye ke zubo mata. Ji take yi kamar ranar za ta zama ranar mutuwarta ne
Ta kasa fadawa Zee komai, kokari kawai take wajen nunawa Zee din ba ta da wata matsala, ranar ma kanta ne ke ciwo ba ta son daga kira, shi ya sa ta kasa amsa kiran Hassan.
Sosai Zee ta so hasaso wani abu, amma kuma sai wani dalilin ya shata mata layi.
Kamar ko wane lokaci idan zai zo gida, misalin tara saura na dare ya sauka, ji yake kamar ya nufi makarantarsu Asiya amma dare ya yi.
Sannan ma har zuwa lokacin wayarta a kashe take.
Da gari ya waye ma tun da ya gaishe da mutanen gidan ya dawo dakinsa ya kwanta aikin kiran Asiya yake yi, amma sam wayar ba ta tafiya.
Har zuwa la’asar bai samo wata mafita da zai hadu da Asiya a boye ba, dalilin da ya sanya kenan hankalinsa ya kuma tashi, ya ci gaba da laluben mafita.
Zuwa can kuma sai ya fice dakin nasa da sauri.
Dakin Hajja ya yi wa tsinke, cikin sa a ba ta falon sai karamar wayarta da ke kan stool.
Dauke wayar ya yi, cikin sanda kuma ya fice daga falon.
Layin Zee ya kira, shiru ya yi, duk kuwa da yana jin yadda take ta rangada sallama.
Zuwa can kuma sai ya ji ta ce “Sister Hajja ce ke kira, bana jin ta kuma, ki aje wayar a wajenki zan je in karbo handout din nan, idan ta kara kira sai ki daga.
Bai ji amsar da Asiyar ta bayar ba, sai dai ya san tabbas ta karbi wayar.
Dalilin da ya sa kenan ya yanke kiran, bayan wasu sakanni ya kuma kira.
“Assalamu Alaikum.”
Bai amsa sallamar ba, sai dai gabansa ya yi wata irin faduwar da sai da ya sanya hannu ya dafe kirjinsa da karfi.
“Hassan ne?” ya fada kai tsaye.
Saurin janye wayar ta yi daga kunnenta, hade da dafe kirjinta, don kuwa ita ma ji ta yi kamar zai fasa rigarta ya fito.
“Kada ki yanke min kira, ki saurare ni. Nan da 10mns zan shigo school dinku, ina son ganin ki ke kadai, ba tare da Zainab ba, ki san yadda kika yi kika fito. Sannan ki rike wayar a hannunki, zan turo miki address din inda nake.
Bai jira amsarta ba ya yanke kiran.
A hankali ya kuma yin sanda ya mayar da wayar inda take bayan ya goge kiran.
Wani irin farin ciki yake ji wanda bai taba tsintar kansa a ciki ba, koda ya koma daki kayan da ya rika sanyawa yana canjawa sun fi kala goma.
Daga karshe dai ya tsayar da kwalliyar tasa a kan yadi fari tas, mai shaka-shaka, wanda za a iya hango farar vest dinsa ciki.
Dinkin zamani ne ya zauna a jikinsa cif, turare mai kamshin ya fesa, bayan roll on din da ya sanya kala-kala.
Hula baka da bakin takalmi half cover ya sanya, ya fice a motar Hajja.
A bangaren Asiya kuwa matsakaiciyar kwalliya ta yi cikin atamta mai kalar purple riga da sicket ne da suka fito mata kirar jikinta sosai.
Duk da doguwar farin hijab din da ta sanya hakan bai hana kirjinta bayyana ba, musamman da ta sanya hannun hijabin
Agogo ta daura wanda fatarsa ta kasance fara hakan ya kara fito da hasken tsintsiyar hannunta.
Siriri farin gilashi ta sanya, hade da shafa humra mai sanyin kamshi.
A hankali take tafiya kanta a kasa yayin da kirjinta ya tsananta bugawa, dalilin da ya sa kenan ta danne shi da hannunta na dama da karfi.
Sosai yake kallon ta ta cikin gilashin motar, bai taba tsayawa ya yi wa surarta kallo irin na yau ba, duk da cikin hijabi take hakan bai hana surarta bayyana ba, kammaninta da Hajja ya kuma bayyana radau, babu inda ta baro mahaifiyar tata a bangaren halitta dai.
Ko ina na Asiya a cike, ba ramammiya ba ce, a takaice zai iya cewa siffarta ta fi ta shi cika.
Ya sauke ajiyar zuciyar da ta bayyana a daidai lokacin da ta bude kofar motar ta zauna kusa da shi.
Hancinsa ya bude a hankali ya ci gaba da shakar kamshinta mai sanya shi natsuwa.
Ita ma kanta a kasa tana wasa da agogon da ke hannunta, tun da ta yi sallama ya amsa babu wanda ya kara cewa komai.
Kowa da abin da yake tunani a zuciyarsa.
“Ina wayarki?” ya janyo tambayar a can kasan makoshinsa, don zuwanta ya sa ya rasa duk wani wayonsa, ba ta taba mishi kwarjini irin na yau ba.
“Ga ta nan” ta yi maganar hade da saka hannunta cikin hijabinta ta dakko wayar.
“Me ya sa kika kashe tsawon wannan lokacin?”
“Ba komai.”
“Ban bata lokacina da barij aikina ba, don kawai in zo ki fada min ba komai.”
Shiru ya ratsa wajen yayin da Asiya ke kallon wani gefen.
Ya zubawa tulluwar kanta ido, wacce ta kawata kwalliyar tata a baya
“Ina jin ki fa”
“Ba komai” ta fada kamar za ta yi kuka.
“Saka idonki a nawa ki fada min ba komai.”
Maimakon ta yi hakan sai ma kara dukar da kanta kasa ta yi hade da wasa da yatsunta.
“Ban ji dadin abun da kika yi min ba gaskiya, kin tayar min da hankali, na kasa aiwatar da komai har sai da na baro wurin aikina na zo wajenki, don kawai in ji me na yi, dana cancanci wannan hukuncin?”
Ya nisa a hankali yana dubanta, har yanzu kanta a kasa.
” Koma me na yi ina son ji a yanzu, don kuwa gobe zan koma sha Allah. “
A hankali ta dago kanta da niyyar duban sa, cikin sauri kuma ta yi kasa da kanta saboda yadda idanunsu suka hadu.
” Ehen!” ya yi maganar a hankali.
Ganin ya tsareta da ido, da alama amsarsa yake jira, sai ta rasa ta ina za ta fara, duk kuwa da abin da ke ci mata zuciya kenan.
“Ke nake saurare.”
Kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa hade da tura bakinta gaba.
“Ina jin ki.” ya kuma fada idonsa a kanta
Jin yadda idanunsa ke yawo a kanta ne ya sa ta ce
“Ni bana so idan na kiraka in ji wata ta daga.” ta yi maganar cikin zumbura baki, hade da kallon gefenta.
Ya zuba mata ido yayin da murmushi ya bayyana a fuskarsa. To kodai maganar Yusuf ta tabbata ne, Asiya kishi ne ya motsa, wani dadi ya cika mishi zuciya, bai taba kawowa ransa komai a kan Asiya ba, amma da alama zai tsinci dami a kala..
“Juyo ki fada min da kyau, yaushe kika kirani wata ta daga, abun har da sharri .”
Cikin sauri ta juyo ta saka idonta a cikin nasa “Ni ba sharri na yi ma ba, sau uku ina kiran wayarka mace na dagawa.” ta karasa maganar cikin fari da ido hade murguda baki kamar tana a gaban mai daga wayar ta shi. Alamun dai har lokacin cike take da haushin abun
Tun da ta fara maganar ya zuba mata ido, sannan ya karanci abubuwa da yawa a cikin kwayar idonta a lokacin da take maganar,, ganin ta kai karshe ne, ya sake yin siririn murmushi hade da ajiyar zuciya a hankali.
“Har sau uku fa kika ce?”
Kai ta daga alamar Eh.
“To shi kenan kaina bisa wuyana, ina mai bayar da hakurin hakan.”
Shiru ba ta ce komai ba, har lokacin kuma kanta yana kasa
“Don Allah!” ya fada hade da hade hannayensa du biyun ya daga sama alamun ban hakuri.
A wannan karon ma ba ta yi magana ba.
“Ranki ya dade! Ina ta magana fa, ko har yanzu ba ki huce ba?”
Ya yi maganar lokacin da yake kokarin lalubo kwayar idon Asiya.
Ta tura baki hade da kawar da kai, kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta ce
“Wacece ta daga?” t
“Hmmm! Cynthia ce? …”
“Wacece ita?” ta kuma tambaya wannan karon ta kalle shi kadan.
“Abokiyar aikina ce.” ya ba ta amsa yana kallonta, hade da mamakin yadda ta tsare shi da tambayoyi kuma yake ba ta amsa kamar ba shi ne Hassan yayanta ba.
“Da ta baro daga gidansu ta taho service Imo, service nata a kan daga wayarka ne?”
Ya yi saurin girgiza kai alamar a’a, yayin da murmushi ke kufce masa
” To wai me ma ya kai wayarka hannunta, har take da damar daga kiran duk wanda ya kira ka?” wannan karon idonta ta saka a cikin nashi, kuma ba ta janye ba duk kuwa da shi ma kallonta yake, har yanzu mamaki yake, wai haka Asiyar take dama.
A idonta ya kuma karantar abin da ke cikin zuciyarta, sosai ta ji haushin daga wayar da Cynthia ta yi, dalilin da ya sa kenan ya sauke muryarsa kasa.
“Ki fahimta mana, muna da matsalar wuta ne, ita kuma tana da sola, shi ne nake kai caji, amma tun da ba ki son is tana daga kiran ba za ta kara ba. Ba aikin daga kiran wayata ne ya kawota ba, sorry please.”
Baki ta tabe hade da kawar da kai gefe cikin halin ko in kula
” Ehen! Ba ki ce komai ba. “
” Na fahimta ” ta yi maganar a hankali ba tare da ta kalle sa ba.
Tare suka sauke ajiyar zuciya bayan shirun da ya ratsa wajen.
“Zan koma gida,, kin ga har an yi magriba, ina fatan wannan zai wuce?”
“Eh zai wuce idan ka so.”
“me kike nufi?”
“Nufina idan na kara kiranka wata ta daga zan daina kiranka,, koda hakan yana nufin numfashina na karshe.” karshen magana tata ya yi daidai da bude kofar motar da zummar fita a fusace.
Cikin sauri ya yi saurin riko hannunta, hakan ya sa ta yi saurin juyawa tana kallon sa, shi ma ita yake kallo, kallon da ya kashe musu jiki, dalilin da ya sa kenan ta zare hannunsa daga na ta a hankali.
Ya lumshe ido hade da sauke ajiyar zuciya “Why? Kin faye rigima”
Jin ba ta ce komai ba ya kuma cewa
“Me ya sa kike son daukar abu da zafi ne, na yi miki alkawarin hakan ba zai sake faruwa ba tun da ba kya so. So what again?”
“Shi kenan” ta fada cikin zumbura baki.
Sautin ajiyar zuciyarsa ya fita a hankali “Thanks. And I waiting your messages Kamar yadda kika sa ba.”
Kai ta daga alamar to
Ya yi murmushi a bayyane, kafin ya ce “Haka kike da rigima?”
Ita ma murmushin ta yi hade da rufe fuskarta da tafukan hannunta du biyun.
“Me za ki fadawa Zee idan kin shiga ciki da wannan ledar da zan ba ki?”
Ya yi tambayar hankalinsa a kanta, a daidai lokacin da yake dakko ledar da ke gefen sa.
“Zan ce kai ne ka kawo min .”
“No ki samu abun da za ki fada mata ban da wannan.”
Kai ta daga alamar gamsuwa
Karon farko da ya ji baya son tafiya ya bar ta, ya ji baya son ya daina jin muryarta, ya yi mamakin yadda karon farko kaunarta ta cika masa zuciya, kamar dama jiranta yake yi.
haka nan ya yi mata sallama ya tafi, ba don ya so ba, zuciyarsa cike da wani sabon yanayin da bai saba jin sa ba.