Skip to content
Part 9 of 25 in the Series Labarin Asiya by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Wannan shi ne tubalin ginin soyayyar Asiya da Hassan, wacce ta yi karfin da ta kai su rayuwa a karkashin inuwar ma’aurata, babu wata wata matsala da suka samu a bangaren soyayyarsu, ko wane bangare yana goyon bayan soyayyar tasu, shi ya sa suka kasance cikin farin ciki har zuwa ranar da suka hada shimfidar aure.

A zamantakewarsu ta aure ma tsawon wata shida ba zasu ce ga ranar da suka wuni ko kwana da bacin ran juna ba, kowa na kokarin sauke nauyin dan’uwansa da ke kansa.

Sam Hassan ba shi da ra’ayin aikin gwamnati sai kasuwanci, amma hakan bai hana ya rika baiwa Asiya duk wata gudunmuwa da ta shafi aikinta ba, yana karfafa mata gwiwa da taimakonta a ko wane fanni na rayuwa.

Tashin hankalin ya ziyarci gidansu ne bayan da aka tabbatar da Asiya na dauke da ƙaramin ciki na wata uku, daga bisani kuma gwajin da aka yi mata ya tabbatar da tana dauke da cuta mai karya garkuwar jiki.

Da karfi ta runtse idonta, tana jin wani daci a zuciyarta, ta bude idon nata a kan Hassan da yake kwance yana bacci, da alama yana jin dadin baccin nasa.

Ta kasa gasgata shi har yanzu, ta ya ma za a ce wai ita ce macen da ya fara kusanta, to ita kuwa ta wace hanya za ta hadu da ciwon bare har ta sanya mishi, idan ita din ce ta sanya mishi.

Ta sauke ajiyar zuciya mai kauri, ya zama dole ta binciki abokan karatunshi mata ma fi kusanci da shi, sannan daga yanzu za ta sanya wa duk wani motsin shi ido, ba mamaki ta samu wani abu na kamawa.

Wayar da ke can side drower ta dauka, hade da cire pin din, call history ta fara shiga, bakin lambobi ne suka fi yawa, sai kuma abokan kasuwanci, wadanda tana jin sunansu a bakinsa.

Ta koma text message, nan ma na kasuwancin ne suka fi yawa.

Ta juya zuwa whatsapp top messages din duk na abokan kasuwancinshi ne da customers na shi.

Shiru ta yi cikin nazari, kafin daga bisani ta yi searching din sunan Cynthia, sai kuwa ga sunan ya bayyana, cikin sauri ta shiga chat nasu, babu wani abun kamawa da zai bude mata kofar zargi, kawai gaisuwa ce suke yi irin dai ta abokan da suka rayuwa a wuri daya.

Ko Facebook da ta duba ba komai, bai ma faye chat a Facebook din ba.
Ko da Cynthiar maganarsu babu wani yawa.

Amma kuma Cynthia ita ce ma fi kusanci da shi fiye da kowa a lokacin da yake service.

Wayar ta ajiye kan drower ta kuma dakko tata wayar, Facebook ta hau, hade searching din sunan Cynthia, sai kuwa sunan ya bayyana, hotunan da ke kan wall din ta, ya tabbatar mata da yanzu ma’aikaciyar banki ce, haka ta rika scrolling cikin wall din har zuwa kan hotunansu ita da Hassan, wanda da yawansu suna sanye da kayan bautar kasa ne, haka tai ta kallon hotunan.

Daga bisani ta sauka, sannan ta yi creating new accounts hade da turawa Cynthia friend request. Sauke ajiyar zuciya ta yi hade da aje wayar a kasan filo.

Sakkowa ta yi daga gadon, toilet ta shiga wanka ta yi hade da dauro alwalla ta hau kan sallaya domin mikawa mahaliccinta kukanta, a kan ya sanyaya mata zuciyarta ya sa wannan abu duk ya zama labarin gizo da koki ne.

Wanshekare da safe tana hawan Facebook din da sabon account din ta ta ga Cynthia ta yi accepting din ta.

Wani dadi ya kume ta, da alama za ta samu abin da take so cikin sauki.

Shi ya sa ta aje mata gaisuwa. Ga mamakinta sai ga Cynthiar ta yi reply alamun tana online.

Da gaisuwar suka fara hade da gabatar da kansu wa juna a matsayin sabbin abokai.

Daga nan Asiyar ta sauka, ba ta son Cynthia ta harbo jirginta da wuri, dole ta iya takunta.

*****

A kwanakin zaman gidan sai ya zama ba kuka ba guda, kowa na kokarin nunawa dan’uwansa ba komai a ransa.

Amma a badini ba haka ba ne, kullum zuciyoyinsu cikin fargaba da tashin hankali suke, ga tarin tambayoyin da ba mai basu amsarsu.

Hassan ya dan zube kadan, amma Asiya kullum kara hawa take yi, kamar Fulawar da aka sanyawa yeast ta samu rana mai zafi.

Kila hakan baya rasa nasaba da cikin jikinta, don kullum kara girma yake yi, yanzu kam kallo daya za ka yi mata ka fahimci tana da ciki.

Juyin duniya Hassan ya yi a kan ta rika zuwa awo amma ta ki, magunguna kawai take saye irin wadanda ya dace da mace mai juna biyu, sai kuma zuwa scanning da take yi duk bayan wata biyu, domin duba mata lafiyar cikin nata.

Dole ya hakura shi ma ya biye mata, duk inda wani kwararren likita yake to Hassan na makale da wajen don nemarwa matarsa da jaririn cikinta abin da zai inganta lafiyarsu.

Yayin da bangaren Asiya ta kutsa sosai jikin Cynthia, a wata hirarsu ce Cynthia ke fada mata ita yar Abakalike ce, kuma a can take aiki yanzu.

Hakan ya ba Asiya damar fada mata garinta, sannan ta rufe da tambayarta ko ta taba zuwa.

Cynthiar ta amsa ba ta taba zuwa ba, but sun yi zaman camp tare da wani dan garin.

Dadi ya mamaye kirjin Asiya, jin cikin sauki za ta samu abin da take so. Shi ya sa ta ce mata ya sunanshi.

Cynthia ta amsa mata da Hassan.

A wannan karon gabanta ne ya fadi, faduwar da ta rasa dalilinta.

Sai da ta sauke tagwayen ajiyar zuciya ta ce mata yaushe za ta kawo masa ziyara.

Cynthia ta aje emoji na dariya kafin ta ce, ba yanzu ba, ta so dai zuwa lokacin auran shi amma yanayin aikinta ba zai bari ba.

Daga haka Asiya ta yanke hirar tasu, duk da akwai abubuwan da take son ji, amma ba ta son ta rika yi wa abun ci daya kumburin ciki.
Dole ne ta bi a hankali, shi ya sa tun daga ranar ma ba ta kara hawa Facebook din ba da new account din ta.
So take ta dan bayar da kafa.

Yau kam zaune ya sameta a falo, ta mike kafarta, laptop nata a gabanta, wasan kwaikwayon da ta rubutawa gidan radion nasu take tacewa da kuma daidaita shi.

Kafafunta ya matsa cike da kulawa.

“An ce kumburin mai ciki akwai matsala rabin raina, please ko don wannan ki je asibiti.”

Duban kafafun nata ta yi “Ba sai na je ba, ni fa na tsani asibiti Rabin Raina, na riga na yi magana da wata likita ta ce idan zan kwanta in rinka sanya filo a kafar maimakon a kaina.”

Ya kuma jan yatsun nata a hankali “Shi kenan zan kara tambayar wani likitan ma akan hakan.”

“Na gode da kulawarka.”

“Aikina ne yin hakan.”

“Yaushe ne za ki dauki hutun wai, ko sai kin haihu a hanya ne?”

Dariya ta yi kadan “Akwai fa sauran wajen wata biyu, na dauki hutu ai sai in gaji da zama haihuwar ba ta zo ba.”

Murmushi ya yi kadan kafin ya ce “Zan je kasuwa, kin san kayan can har yanzu basu iso ba wallahi, masu zanga-zanga sun tare hanyar.”

Ido ta fitar waje kadan “Har yanzu?”

“Eh mana, amma dai ana kan sansatawa.”

“To Allah ya kyauta”

“Amin” Ya amsa kafin ta yi magana ya ce

“Kar ki manta da shan maganinki, kuma dai ina kara jaddada miki sakon Aunty Zee ta ce ki aika mata.”

“Don Allah raba ni da maganar Zee din nan, tun daga nan zan yi mata wata yargullisuwa har Calabar, ba ta kusa dawowa haihuwa ba, idan ta zo ta ci.”

“Kun fi kusa.” ya yi maganar daidai yana ficewa daga falon.

Fitarsa ke da wuya ta janyo wayarta, inda ta hau sabon account din ta, post din farko da ta fara cin kara da shi, shi ne samun aikin Cynthia a babban banki kasa reshen jaharsu, sai ta tsinci kanta da ji mata, dadi, shi ya sa ta shiga comments section tana karanta comments din mutane, a nan ta ga na Hassan inda ya ce “Congratulations Dear.”

Ta zubawa comment din ido, hade da tambayar kanta me ya sa ya ce mata dear, kodai akwai wata boyayyar alaka ne a tsakaninsu kamar yadda take zargi.

Ya kamata ta lalubo wannan amsar, da gudu ta garzaya inbox din Cynthia hade da yi mata congratulations, sai dai Cynthiar ba ta online, dalilin da ya sanya sauka ita ma.

*****

Yau Hassan ne ya ajiyeta a wurin aiki, kasancewar bai fita kasuwa da wuri ba.

Grace ta fara haduwa da ita a harabar gidan radion da alama fita za ta yi.

Tun daga nesa kuwa Grace din ke aiko mata da murmushi, ita ce macen da ta fi shakuwa da ita a kaf ma’aikatan da ke gidan radion, duk da akwai bambanci addini a tsakaninsu, amma Grace macece mai amana, hankali da zurfin tunani.

Abu da yake kara burge Asiya game da ita shi ne tana da jajircewa a bangaren aiki ba ta da girman kai ko kadan wajen tambayar abin da ba ta sani ba.

Rumgume Asiya ta yi kadan hade da fadin “Amarya sai yanzu?”

Murmushi Asiya ta yi kafin ta ce “Wai ke amarcin baya karewa ne?”

“Ina sai anyo wata ai, kuma ba ma fata, daga ke an rufe kofa.” cikin dariya ta yi maganar

“Allah ya sa hakan ne.” Asiya ma ta yi maganar cikin dariya. Saboda kishiya na daya daga cikin abubuwan da ta tsana, ko can baya fadansu da Hassan to a kan kishi ya fi yawa.

Hannu Grace ta kai a kan fuskar Asiya tana shafa kurajen da suka fito mata “Wannan kurajen suna son bata mana fuska fa”

Ajiyar zuciya Asiya ta sauke, ita kanta kurajen sun fara damunta, ba damunta kawai ba, tsoro ma suke ba ta, don kuwa ta sha jin ana fadin kuraje na daya daga cikin alamun cutar kanjamau.

Idan har ya kasance sune suka fara bayyana, kenan mutane zasu fara gudun ta, da kauracewa mu’amala da ita.

Tana jin tsoron zuwan wannan rana, ranar da za a ware mata kwanon abincinta, dakinta da duk wani abun amfani na yau da kullum.

Wannan kadai ya isa ya kasheta ba tare da ta shiryawa mutuwar ba.

“Ciki ne fa, kina haihuwa za ki neme su ki rasa.” cewar Grace hade da kallon Asiya da take ta shafa fuskarta ba tare da ta san abin da za ta fada ba.

“Da gaske?” cikin sauri ta tambaya

“Sosai ma kuwa,, haka ya faru da Auntyna tana haihuwa kafin ta yi arba’in sun bata” cewar Grace cike da kwarin gwiwa.

“Allah ya sa ni ma ya zama hakan, don kuwa na yi amfani da sabulai da magunguna amma shiru.”

“Kar ki damu, zasu bace.”

“Ina za ku je ne?” Asiya ta canja akalar zancen nasu

“Za mu je dakko wani rahoto ne a fadar mai martaba.”

“To sai kun dawo, bari ni ma in karasa ciki.”

Cikin kwarewa take gabatar da shirye-shiryen nata kamar dai kullum, har zuwa lokacin da ta yi sallama da masu sauraro don mika akalar gabatar da shirye-shiryen ga abokin aikinta.

Gidansu ta yiwa tsinke, kamar kullum sashen Addah ta fara shiga ta gaisheta, sannan ta wuce bangaren su Aunty Amarya, daga bisani ta shiga bangarensu, a lokacin kuwa ko minti goma Hajja ba ta yi da dawowa ba.

“Wai sai yanzu kika dawo? Ni fa na sha tun dazu kina nan, ashe da na shigo ma tun dazu da ban same ki ba.” Cewar Asiya a daidai lokacin da take zama a gefen gadon da Hajja ke zaune cike da gajiya.

Kallon Asiyar kawai take yi, don kuwa ta canja sosai, ta ce zama wata shirgegiya, ga kumburi da ta yi, musamman ma kafafunta.

” Wai ke kina zuwa awo kuwa? ” Hajja ta yi tambayar tana dubanta

“Ina zuwa mana, me kika gani?”

“Wannan kumburin naki mana, matsala ne fa mai ciki ta rika kumburi.”

Nisawa Asiya ta yi “Sun ce ba komai zai ba je, kafin haihuwa, kuma na fara sabewa ma.”

“Hakan ne kika fara sabewa? Abu ga ki I nan shim uwa rumfa”

“Kai Hajja, wai ke ma haka za ki ce? Haka Yaya ma ke damuna fa.” Cikin shagwaba ta yi maganar
I

“Ga wasu kuraje duk sun bata miki fuska, sabulun da Jamila ta kai miki ya kare ne?” Hajja ta kuma yin maganar ga mi da bin jikin Asiya da kallo

“Saura kadan dai ya kare.”
Hajjah ta tabe baki

“Ni ban taba ganin wacce ciki ya sa muni ba irinki”

Asiya ta kyabe fuska kamar za ta yi kuka.

Hakan ya ba Hajja dariya a karon farko tun bayan shigowar Asiyar.

“Shi ya sa fa ko yawo bana so, sai in ga kamar kowa ni yake kallo” Asiya ta fada da muryar shagwaba.

“To ai kin kusa saukewa dai ki huta.”

“Hajja wai Jamila ba za ta koma wajen nawa ba?”

“Sau nawa zan fada miki sai kin haihu. Ke kin cika naci uwa kuda.”

Dariya Asiya ta yi mai sauti “Wallahi har kin tuna mun Babana. Wai yaushe zai zo ne Hajja.”

Tabe baki Hajja ta yi hade da kawar da kai gefe “Wa ya sani ne to.”

Ba tun yanzu ba Asiya ta san damuwar mamanta game da aikin Babanta, don kuwa yakan kwashe har wata uku ba tare da ya zo gida ba, idan kuma ya zo sati daya ya koma.

Da Hajja ta kan bi shi, amma yanzu da girma ya kamata babu inda take zuwa sai dai shi idan ya samu lokaci ya zo.

Shi ya sa ku san komai na hidimar gida Hajja ce mai yin ta, biyan sch fees, zuwa taron iyaye, gyare-gyaren gida, komai ita ke yi, iyakarsa ya turo kudin, tun ba ta saba ba har ma ta saba.

Amma kuma wani lokaci sam ba ta jin dadin yanayin idan ta kalli wasu matan zaune a gida mazajensu ne ke zarya tsakanin matsalolinsu, sabanin ita da kullum ita ke tufkawa ta kuma warware.

Shi ya sa take tausayawa Zee da ta auri force amma kam za ta iya samun damammaki masu yawa, da ba lallai ta same su ba idan civilian ta aura.

“Hajja ina kayan da kika ce in zo in karba din?” Asiya ta katse mata tunani .

“Gasu can cikin wardrobe”

Asiya ta mike da kyar zuwa wurin wardrobe din ta dakko kayan.

Kaya ne masu kyau da tsada, wanda za a iya sanyawa maza da mata.

Sosai suka yi mata kyau, uwa kenan, sosai Hajja ta damu da cikin nan, kullum kira a waya ya kike ji, wani wuri na ciwo ne, ba dai wata matsala ko? Kullum sai ta yi wadannan tambayoyin ba ta ko gajiya.

Sai 8pm Hassan ya zo suka tafi gida bayan sun ci abinci sun kuma gaisa dasu Baba Alhaji, don dama sai dare suke dawowa gidan.

Sai da ta tabbatar ya yi bacci sannan, ta janyo wayarta hade da bude data ta hau Facebook.

Kai tsaye sakon Cynthia ta nufa don dama shi ne ya kawo ta.

Godiya ce kawai a kan taya ta murnar da Asiya ta yi, dalilin da ya sa Asiyar canja hirar tasu da tambayarta yaushe za su zo shan Coke.

Dariya Cynthia ta yi kafin ta ce ta san ba za ta zo ba ai.

Asiyar ma ta yi dariya kafin ta ce za ta zo tare da yayanta auto ta ya kawo ta Arewa.

Emojin mamaki Cynthia ta aje. Ba tare da ta ce komai ba.

Ko wani ya riga mu? Asiya ta tambaya, kafin Cynthia ta amsa sai ta yi sauriin cewa “Oh na manta akwai Hassan”

Emojin dariya Cynthia ta aje Sannan ta ce babu komai tsakaninsu da Hassan kawai abokinta ne

Ita bugun cikin da Asiya ta yi mata, Cynthia ba ta sauka a kan wannan layin ba, wannan ya tabbatar mata lallai babu alamar soyayya tsakanin su biyun.

Amma duk da haka ba ta hakura, za ta kuma canja ma wasan salo.
*******

Misalin sha biyu na dare ta farka ta ji a jike tamkar ta yi fitsari, hakan ya sa ta yi sauri ta shi zaune hade da haska fitilar wayarta.

Tabbas ba fitsari ba ne, amma kuma bai sirka kala ba, haka ya ci gaba da zubo mata har asuba.

Don kuwa sai da ta yi amfani da always ma.

Tun da Hassan ya tashi, ya fahimci kamar matar tasa akwai abin da ke damunta, dalilin da ya sa kenan ya kasa samun natsuwa.

Kitchen din ya bi ta, tsaye ya cimmata, hannyenta a kan kirjinta, da alama ta yi nisa cikin tunani.

Hannayen ya janye daga kan kirjin nata

“fada min matsalar Gimbiyata” ya yi maganar hade da saka idonsa a cikin nata.

Ta janyo ajiyar zuciyar da ta bayyana a hankali ta ce”Wani ruwa ne ke fitar min tun sha biyu na dare, kuma ni bana jin ciwon komai”

“Kin tabbatar ba kya jin ciwon komai?” Ya yi tambayar hankalinsa a kanta

Kai ta daga alamar Eh.

“To yanzu menene last decision naki?”

“Ba komai”

“Ba za mu je asibiti ba Rabin Raina?”

“Ni a’a.” ta kyabe fuska kamar za ta yi kuka.

Ya nisa kadan hade da janyota zuwa jikinsa “Ba tun yau nake fama da ke a kan maganar zuwa asibitin nan ba amma kin ki firr. kuma kin san bayan matsalar ciki muna da wata matsalar ma, ya kamata mu ga likita don sanin halin da muke ciki da yaronmu, amma kin ki haba Rabin Raina.”

Hannu ta sanya hade da share hawayen da ke bin fuskarta” Na fi ka damuwa da rashin zuwana asibiti, amma kuma haka shi ne kwanciyar hankalina, bana so in je su kuma fada min abin da zai kara daga min hankali.”

“Look Rabin Raina!” ya yi maganar hade da dago kanta yana share mata hawayen da ke bin kuncinta

“Sau daya, ki amince mu je asibitin nan please, bana son ki samu matsala ko Babynmu. Kin fahimta?”

Kai ta daga alamar Eh

“Yauwa mu yi break sai mu je ko?”

Kai ta kuma dagawa alamar Eh.

Tare suka hada breakfast din, suka karya sannan suka nufi wani private hospital don ganin likita.

Likitan ya tabbatar masu lafiya ƙalau, sannan kuma haihuwar akwai saura, amma dai ba lallai ta wuce satin ba tare da ta haihu ba.

Da kwarin gwiwa suka dawo gida, Hassan ya wuce kasuwa ita ma ta ci gaba da hidimominta na gida kasancewar ta dauki hutu.

Wanshekare kam a hankali take jin ciwo, tun tana daurewa har dai abun ya fara cin karfinta.

Unguwarsu irin sabbin unguwannin nan da kowa yana gidansa, sai kaga makoci ma bai san makoci ba, ba laifi ita suna gaisawa da makotanta, amma yanzu kam ta san duk suna wajen aiki.

Da kanta ta hada duk wani abu da ake bukata na haihuwa ta sanya a Ghana must go.

Asibitin da suka je jiya ta koma.

Labour room aka kai ta, nurses suka shiga aikinsu.

Aunty Amarya ta kira, a lokacin kuwa tana wajen aikinta, amma da sauri ta baro wurin aikin zuwa asibitin.

Tun shabiyu na rana suke asibitin amma har biyar na yamma Asiya ba ta haihu ba, zuwa lokacin tuni ta gane Allah da girma yake.

Hassan ma tuni ya zo asibitin, Aunty Muna ma da Umma duk suna asibitin.

Hajja da Addah ne kawai a gida, suma alkunya ce kawai ta hana su zuwa amma kam hankalinsu kaf yana asibitin.

Minti-minti suke kira suna tambayar ya ya ta haihu.

Zee ma da yake a ranar ta baro Calabar kosawa ta yi ta iso, haka duk bayan mintuna biyar sai ta kira tana tambayar ko Asiyar ta haihu.

Cikin ikon Allah dai ana kiran sallahr magriba Asiya ta sambalo kyakkyawan yaronta kuma lafiyayye.

Jarintaka ba ta hana a gane kamannin Hassan a tare da shi ba.

Asiya ma kalau babu wani ciwo ko karuwa ma ba ta yi ba.

Hajja kam kasa hakura ta yi a sallamesu, saboda an ce sai da safe akwai gwaje-gwajen da asibitin ke jiran results dinsu ya fita.

Har goman dare asibitin bai yanke da mutane ba, abokan aikin Asiya yan’uwa da abokan arziki. Zee ma jakarta kawai ta ajiye ta nufo asibitin.

A wannan rana dai Facebook da WhatsApp sun sha hotunan yaron Asiya.

Hassan ma da ya koma gida farin ciki hana shi bacci ya yi, kadan ya jawo waya hade da zubawa yaronsa ido mai kama da shi, idan ba Allah ba wa isa yay mishi wannan kyautar.

Yana yin sallahr asuba asalin gidansu ya wuce, bayan sun gaisa da Addah ne take fada masa ita ma yau asibitin za ta je ba za ta iya jurewa ba ta je ta ga Asiyar ba.

Misalin karfe takwas na safe kuwa asibitin ya kuma cika, wanda yake nuna lallai akwai wata yargatan dangi da ke kwance a asibitin.

Kallo daya za ka yi wa fuskokinsu ka fahimci suna cikin farin ciki mara misultuwa.

Don hatta Alhaji Abdallah da aikinsa yake hana shi yin wasu abubuwan, ya tabbatar masu da ya taso don zuwa ya ga jikansa na farko a duniya.

Sai dai kuma bayan darar akwai wata caca.

<< Labarin Asiya 8Labarin Asiya 10 >>

2 thoughts on “Labarin Asiya 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×