بسم الله الرحمن الرحيم
Unguwar Madalla, Suleja, Niger state
06:00am
“RABI’A! Na san cewa bayan na mutu za ki koma gidan mahaifinki… ADAWIYYA ina da tabbacin bayan kin koma cikin ‘yan uwanki da zama za ki sha wahala, na san cewa za ki shiga taskun rayuwa kala-kala, na san cewa Habiba ba ta sona, bare kuma ‘ya’yana, na san cewa ba za ta taɓa barinki ki huta ba… Amma ki riƙe addu’a, ki riƙe addu’a a ko wani irin yanayi kika tsinci kanki. Ki yi haƙuri, domin na san cewa ƙaddarorinki yanzu suka fara. Yanzu LABARINKI zai soma…”
Zubar ruwan da ya cika bokitin da ta saka a famfo ne ya jawo hankalinta daga duniyar tunanin da ta faɗa.
Kanta ta ɗan ɗaga sama ta kalli sararin samaniya, har yanzu garin akwai sauran duhun asuba, gashi kuma yanayin garin akwai zafi, kasancewar ana tsakiyar kwanki goma na ƙarshen watan azumi ne, dan bai fi saura kwana huɗu sallah ba.
Kanta ta sauƙe ƙasa ta kalli bokitin da ya cika har ruwan ciki na zuba, ta tsugunna zata janye bokitin, wata murya ta daka mata tsawa cikin faɗin.
“Uban me kike ne wai Rabi?! Tun ɗazu bokitin ya cika har yana zuba amma ba za ki ɗauke ba?,Saboda baƙin halli da kika gada a wurin uwr ki ko? To ki ci gaba da tsayuwa a wurin, idan ƙarar ruwan nan ya tada min yara sai na ci uwr ki Wallahi!….”.
Rabi ta ɗago da kanta ta kalli inda matar ke tsaye, hasken wutar nepar dake haske tsakar gidan ya haska mata fuskar matar, matar babanta ce, Habiba, matar da a kodayaushe burinta ta ga ta lalata mata rayuwa.
Kuma bata tsaya iyaka nan ba, har cikin garin Abuja take turata aikatau, yau shekarunta biyar a gidan, tun bayan rasuwar mahaifiyarta, mahaifinta ya je har garinsu mahaifiyarta ya ɗaukota, ya dawo da ita cikin gidansa, gidan da ita zata iya kiransa da kurkuku. Domin ko da da sakan ɗaya bata taɓa jin daɗin zaman gidan ba.
Babu wanda take jin daɗin zama da shi a gidan sai Saratu, ‘yar Habiban ta biyu, a wasu lokutan ma idan Habiban na mata faɗa har baki take sakawa.
Tun a shekararta ta farko a gidan ta fara ganin uƙuba irin ta matar uba, da ta saba jin hakan a labarai, labarin yanda matan uba kan ƙuntatawa ‘ya’yan mazanjensu, ko da wasa bata taɓa hasaso cewa rayuwarta zata fuskanci abu makamancin wannan ba. Sai gata tsundum cikin wannan hali.
Kuma ƙalubalen nata ya fara ne tun daga sanda ta nemi da Babanta ya maida ta makaranta, yace ai ta gama karatu, shi ba zai iya wahalar da kansa wurin sakata a makaranta ba. Ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba a lokacin, dan Allah ya sani tana san karatu, kuma burin mahaifiyarta ne ta yi karatu.
Bayan wannan sai ta koma baiwa kuma jakar aikin gidan, ‘ya’yan Habiba ko tsinke basa ɗaukewa a gidan sai de ita ta yi. Duka wannan bai ishi Habiba ta gama da rayuwarta ba sai da ta fara turata aikatau.
Kullum iƙirari take kan cewar ba zata ciyar da ita a banza ba, tun da ubnta bashi da aikin yi, ita take riƙe da gidan, kuma kusan hakan ne, dan Mahaifin nasu ba shi da wani aikin yi, kasancewar an koreshi a wurin aikinsa.
Babu abinda yake sai zaman baza, zuciyarsa ta riga ta gama mutuwa, babu abinda yake sai caca da bin matan banza. Haka Habiban za ta saka shi a gaba tana tsigeshi, kamar wani ɗan da ta haifa, amma ko tari ba ya iya mata, saboda yasan ba shi da gaskiya.
Babu yanda Rabin za ta iya, haka ta yarda ta fara zuwa aikatau ɗin, da ko wani ƙalubale dake fuskantar rayuwarta, Kalaman mahaifiyarta na ƙarashe su ne ke yawo a kanta.
A sanda take mata maganganun, gani take kamar zafin ciwo ne ke nuƙurƙusarta, gani take kamar kawai sambatun ciwo mahaifiyar tata take, dan waɗanan kalaman nata sune maganarta da ta ƙarshe, bata sake magana ba har ta koma ga ubangijinta.
Sai a yanzun take ganin duk abunda take faɗa mata, duk abinda ta ce mata zasu faru gareta su take gani. Dan yanzu haka a wata makaranta dake cikin garin abuja take aikin goge-goge da share-share.
Bata da wani buri a yanzu, bata da wani fata, bata da wani abin da take san cimmawa, dan a ganinta kamar rayuwartace ta zo ƙarahe, kamar LABARINTA ne ya ƙare, babu wani abu da ya yi saura.
Ƙwara ma kawai ta zauna ta rungumi ƙaddararta da ta zo mata a haka, tun da Allah yasa a bautawa wasu rayuwarta za ta ƙare to ta amshi hakan……
Ƙarar turowa ƙofar gidan nasu ce tasa ta juyawa takalli ƙofar. Mama ce ta shigo, ‘yar Habiban ta uku. Amma kuma ba wai hakan ne yasa Rabi mamaki ba, mamaki take na san sanin sanda Maman ta fita ta daga gidan.
Ta san cewa jiya daddare tare suka kwanta, tun da ɗakinsu ɗaya, amma ko da asuba bata ganta ba, fitar tata a daren ba wani abun mamaki ba ne, dan ta saba kwana a waje ma, ta saba bin samarinta su tafi yawon banza.
Sunan ‘karuwa’ da Habiba ta saba kiranta da shi ne ya dawo cikin kanta. Sai kawai ta juya ta ɗauki bokitin da ta juye ruwan cikinsa a randa, ta koma bakin famfo ta kunna famfon ta ci gaba da tsaiwa a wurin tana jiran ya cika. Dan Habiba na gama masifar tata ta koma ɗakinta.
A rayuwar gidansu ta tabbatar da karin maganar nan da hausawa ke faɗin ‘Laifi tudu ne, ka take naka ka hangi na wani’, ita zata bada shaidar wannan, domin duk abinda Maman ke yi da sanin Habiba, dan idan ta samo kuɗi ko kayan kwaɗayin da samarinta kan bata Habiban take kawowa. Ita abun haushinta a nan shi ne; ganin cikin watan azumin Allah ta ala ma bata bar abinda ta saba ba. Sai ta girgiza kanta a fili tana kashe famfon da ruwansa ya cika bokitin gabanta.
“Uban miye kike wani girgiza kai ?!”
Maman ta tambaya cike da masifa, dan in dai ruwan bala’i ne, to kaf cikin yaran Habiba babu wanda ya gado shi kamar Maman, dan bata da mutunci, Rabi ta kalleta, sannan ta girgiza kanta.
“Babu komai”
Sai da ta ɗan tsaya na wasu sakanni tana aikawa Rabin harara, sannan ta juya kanta ta shige ɗakinsu.
Rabi ta kuma jijjiga kanta a sanda ta juye bokiti na ƙarshe a cikin randar. Share gidan ta shiga, ta share tsakar gidan tas, kana ta shiga ɗakinsu, dan ɗaukan kayan da za ta sa, saboda wankan da za ta yi.
Tana ɗage labulen da harar Mama ta fara cin karo, sannan ta bi ɗakin duka da kallo, Saratu ce zaune tana guga, sai Fatima ƙaramar ƙanwarsu tana kwance a kan katifarta, sai sharar bacci take.
Bata cewa kowa komai ba, ta ƙarasa shiga cikin ɗakin tana nufar inda take aje jakarta ta Ghana must go.
Zip ɗin jakar ta buɗe, idonta ya sauƙa a kan kayan da suke a saman jakar, kayanta ne, kayan da ta zo gidan da su tun shekaru biyar da suka wuce, dan tun bayan zuwanta gidan ba’a ƙara mata sabon ɗinki ba. Kuma a halin yanzu kayan sun mata kaɗan, ba wai dan ta ƙara ƙiba ba, sai dan girma da shekaru suka ƙara mata.
A yanzu ba ma ta saka kayan, kayan yayarta Baby da ta rasu su takesakawa, dan a sanda Babyn ta rasu ba zata wuce shekarunta ba, duk da Babyn na fama da cutar sickler.
Baby?!, sunan ya maimaita kansa a cikin ranta, a sanda ta ɗago wata doguwar riga sama, rigar ta Babyn ce, kuma ba wannan ne yasa ta tsaya ta ci gaba da kallon rigar ba, sai dan tunawa da ta yi da yanda Babyn ke matuƙar san rigar.
“Umma ki ce ta ba ni…”
Muryar Rabi’an ta faɗi a wancan lokacin, mahaifiyarsu dake zaune a kan sofa tana duba wasu takardu ta juyo ta kallesu, sannan ta kalli rigar da suke kokawa a kanta.
“To wai ke Adawiyya me za ki yi da wannan rigar ?, in ce de ta miki yawa”
Rab’ia ta turo baki gaba tana wata shagwaɓa irin tata ta autanci.
“Wallahi Umma ina san rigar”
Baby ta fisge rigar daga hannun Rab’ia tana hararta.
“Ai ko ba zan baki ba…”
“Yayar ummanta Adawiyyan Umma, rabu da ita, zan sai miki sabuwa, wadda ta ma fi tata kyau…”
Sai kawai ta ninke rigar ta maida ta cikin jakar, Allah ya sani sam bata san tuno LABARINTA na baya, dan hakan sam bai da amfani a ganinta, saboda wannan wata rayuwace da ta shuɗe a baya, sannan rayuwace wadda ta tafi da abubuwa da dama.
Ciki kuwa harda ita kanta, saboda gani take kamar wannan ba waccan Rabi’ar data sani ba ce, wannan wata baiwa ce dake aikatau a gidan mahaifinta, ba kamar waccan Rabi’ar ba, me rayuwa cikin gata da kulawa, autar ummanta, ƙanwar yayarta, jika mafi soyuwa a wurin kakkaninta.
Wata doguwar riga wadda Saratu ta bata kunce ta ɗauko, ta haɗa da hijabin Baby, sannan ta zuge jakar tana miƙewa. Bayan da ta aje hijabin a kan jakar, hannunta kuma tiƙe da rigar da ta ɗauko ɗin.
“Rabi dan Allah yaushe za ki min ƙunshin ?”
Saratu ta tambaya tana aje rigar da ta gama gogewa. Rabi ta ɗan dakata da tafiyar da take, sannan ta juyo ta kalli Saratun dake kallonta ita ma.
“Saura kwana nawa ne sallar ?”
Saratu ta amsa mata da “Ehhh to!, gaskiya ba na ce ba, amma jiya na ji Umma (wato Habiba, dan haka suke kiranta) na faɗin saura kwana huɗu ne ko uku?…”
“Gobe za ayi hutu a makarantar yarana nan, sai na miki goben, nima ina so ki min kalaba”
Ta ƙarashe tana ɗan dukan kanta da ke ɗauke da manyan kalaba guda huɗu, dan bata kitso, kuma ba komai ya ja hakan ba sai santsi da tsayin da gashin nata ke da shi. tun mahaifiyarta na da rai bata kitso, sai dai Ummar tasu ta kaisu wurin gyaran kai.
Amma yanzu fa ?, gashin nata ma ya fara raguwa saboda rashin gyara, kalabar da Saratun ke mata ita kaɗai kan nata ke samu.
Saratu ta gyaɗa kanta sannan ta ce.
“Allah kai mu goben”
Har Rabi zata fita da ga ɗakin sai ta juyo.
“Wani kala zan miki ?”
“Ɗan gama nake so”
Da ga haka bata ƙara cewa komai ba ta gyaɗa kanta, sannan ta fita da ga ɗakin, wanka ta je ta yi, ta fito bayan da ta gama wankan, saboda yanzu ana cikin azumi shi yasa ayyukanta suka ragu a gidan.
Dan idan baki buɗe ne, sai ta kai niƙan alkamar da Habiba ke yin finkason safe, idan kuwa a week end ne ita ce ma da kanta take suyar finkason. Kuma ta hanyar kuɗin da take samu a finkason, da albashi da ake bawa Rabin a wurin aikinta, Habiban ke iya kula da gidan, dan komai na gidan ita ce ke yi.
Bayan ta shiga ɗakin, mai kawai ta shafa, sannan ta ɗauki hijabin da ta fitar ta saka, ta yiwa Saratu sallama, ta fita.
“…..Kin ji matsalata da ke, dan Allah Habiba yanzu idan baki rufa min asiri ba waye zai rufa min?….”
Rabi ta ja ta tsaya a sanda ta ɗora idonta a kan mahaifinsu tsaye yana ƙanƙan da kansa a gaban Habiba,wadda ta wani ɗaga kai sama tana shirin zazzago buhun masifa.
“Wallahi Ɗan Lami baka isa ba, a kan me zan ɗauki kuɗi na baka?, bacin na san caca za ka je ka yi da su……”
Rabi bata tsaya ta gama jin abinda take faɗi ba ta sa kai ta fita. Kuma abinda Habiban ta faɗi gaskiya ne, dan baban nasu babu wani aiki da yake face cacar, duk kuɗin da zai samu a caca suke ƙarewa.
Sai da ta ɗan tsaya a ƙofar gidansu, ta ɗan ɗaga kai saka, da ga nan inda take tana iya hango dutsen zuma rock, dubanta ya kai kan tarin bolar dake tsallaken ƙofar gidansu.
Bolar har tsiri take dan tsabar yawanta, da sauri ta ɗauke kanta da ga barin duban bolar, dan Allah ya sani idan ma takalleta zuciyarta har wani tashi take, dan ta tsani ƙazanta a rayuwarta.
Haka ta ci gaba da tafiya a cikin ƙazamin layin nasu, wanda kwatanni da datti suka masa ƙawa.
Akasarin mazauna unguwar ta Madalla masu magana da harshen gwari da baagi ne, sannan akwai hausawa sai nufawa, da wasu sauran yarukan, sannan a cikinsu akwai musulmai da cristian.
“…..Rabi!”
Ta juyo saboda jin an kiran sunanta, gamin wanda ke kiran nata yasa ta yi murmushi tana juyowa gaba ɗaya, Zara ce, mutum ɗaya da za ta iya ɗagawa ta kira da ƙawarta.
“Aikin za’a je?”
“Eh mana, keda kika sani”
Suka ɗan yi dariya.
“Kunu kika siyo ?”
Rabi ta tambaya yayin da idonta ya sauƙa kan jug ɗin dake hannun Zaran.
“Eh wallahi, bari na wuce, kafin Umma ta soma faɗan na daɗe….”
Kuma daga haka suka yi sallama, bakin titi ta fita, a titin ma sai da ta yi wata doguwar tafiya a ƙafa, kafin ta iso Ɗan kogi motor park.
Inda ta saba hawa mota, ta biya kuɗin da ta saba biya a kullum, wanda Habiba ke bata dan yin kuɗin motar, saboda da ga gidan nasu zuwa makarantar da take aikin akwai nisa. Tafiyar kusan minti 40 ce.
Sun yi doguwar tafiya a motar, kafin suka isa Joy Emodi CI inda za’a sauƙeta, daga nan ta soma tafiya a ƙafa, wadda ta ɗauketa tsawon lokaci, kafin ta iso makarantar da take zuwa aikin shara.
Brickhall School, Kaura district, Abuja
A hankali wata farar mota ƙirar Corolla hybrid ta yi parking a harabar makarantar. ko minti ɗaya ba ta yi da parking ba, ƙofar gidan baya na motar ta buɗe.
Wata matashiya ta fito,sanye cikin wata baƙar pleate skirt, da kaɗan skirt ɗin ta sauƙo gwiwarta, sai farar oxford shirt, wadda ta ɗora maroon suit a kai, daga gefenta suit ɗin na dama an manna symbol ɗin makarantar, wuyanta saƙale da tie, kanta babu ko ɗankwali, sai gashin kanta wanda ya ji gyara, an ɗaureshi cikin pony rail, jelar sai reto take a bayanta. Bayanta goye da backpack ɗinta me kyau, ƙafafunta sanye cikin baƙaƙen sneakers.
Kuma ba ita kaɗai ce ke sanye da irin kayan ba, dan gaba ɗaya ɗaliban dake kai kawo a harabar makarantar sanye suke da irin kayan jikin nata, maza ne kaɗai ke saka wando, kuma shi ne abinda ya banbantasu, hakan ke nuna cewa kayan shi ne uniform ɗin makarantar.
Tafiya ta fara cikin takunta na wanda ƙuriciya bata gama saki ba.
“MISHAL!, kin manta abincin ki….”
Muryar drivernta malam Ali ta faɗi da ga cikin motar.Tsayawa ta yi da tafiyar, sannan ta juyo ta kalli motar, kafin ta fara takowa zuwa wurin motar.
Ba tare da ta ce masa komai ba, ta buɗe gidan baya ta ɗauki lunchbox ɗin nata, ta rufe ƙofar motar, kana ta ɗaga masa hannu alamun bye, sannan ta yi gaba.
Malam Ali ya girgiza kai yana murmushi, a cikin ransa ya na wa Mishal ɗin fatan shiryuwa, ita duk gari ana azumi amma banda ita, zai iya cewa tun da aka fara azumin ma bai fi guda goma ta yi ba, da ya mata magana ma sai tace masa wai akwai wahala haɗa azumi da zuwa makaranta.
Duk inda ta wuce sai an bita da kallo, amma ita ko a jikinta, dan bata damu ba, saboda wannan ba shi ne karo na farko da aka saba bintada kallon ba, wasu kallonta suke cikin tsoro saboda sanin halinta, wasu kuma cike da burgewa saboda sanin jarumtarta, wasu kuma suna kallonta ne cikin jin haushi, wata ƙila saboda faɗa ya taɓaa haɗasu.
Bata ko kalli kowa ba, duk da tasan cewa kowa kallonta yake. Har ta kai ƙofar class ɗinsu, ta saka ƙafarta a cikin ajin, sai kuma ta dawo da baya, ta gyara tsaiwarta tana kallon wannan yarinyar.
Yarinyar da ke aikin shara a makarantar tasu, ba yau ne karo na farko da ta fara ganin yarinyar ba, hasalima tafi wata shida tana ganin gilmawarta a makaranta.
Ba wannan ne yasa take kallonta ba, kawai rayuwar yarinyar ce ke bata tausayi, dan da alama yarinyar na cikin halin ƙuncin rayuwa, ita kuma haka Allah ya yi ta, duk da baƙin halinta da rashin jin maganarta da wasu ke gani, Allah ya hallici zuciyarta da tausayin wanda bashi da shi, haka Allah ya saka mata tausayin yarinyar.
Duk da ba za ta iya kiranta da yarinya ba, saboda da alama ta girmeta, saide bata kai sa’ar Akinta(Yayanta) ba.
Da alama ma ita yarinyar bata lura da ita ba, dan moping ɗin floor take bil haƙƙi da gaskiya. Ba tare da ta yi komai ba, ta juya ta shiga ajin nasu.
Malamin geography ne a ciki, kuma tana shiga ajin ya yi tsit!, kallo ya dawo kanta kamar kullum. Ba tare da ta damu ba ta nufi seat ɗinta.
“Ke Hafsat Muhammad Auwal!”
Uncle ɗin geographyn ya daka mata tsawa, ta juyo ta kalle shi da sauri, idonta babu ko da ƙwayar tsoro a ciki, dan bata saba jin tsoron kowa ba, kowa gani take kai kai ɗaya yake da ita.