The wrong one will find you in peace and leave you in pieces. The right one will find you in pieces and lead you to peace.
Shekara ta 2000
Kano…
A hankali Zaid ya juya ya kalli ƙaninsa Aliyu, wanda har zuwa lokacin yake ta risgar kuka. awa biyar kenan da aka kashe wutar da ta kama a gidansu. Wutar da ba ta bar musu komai ba, ciki kuwa harda mahaifiyarsu. Kuma har zuwa lokacin, suna sanye da wannan uniform ɗin islamiyyar, yayin da ƙonnaniyar gawarbmahaifiyarsu ke rufe a gabansu.
Zaune suke a ɗakin da aka ajeta bayan da aka samu aka kawota asibiti, kuma tun kafin su kawo asibitin jama’ar da suka ɗaukota ke faɗin ai ta cika.
Shi ma kansa Zaid ɗin so yake ya yi kukan, amma ya kasa. Bai san ina za su je ba, bai san ina za su koma ba, bai san kowa nasu ba, kuma Momman nasu ko ƙawa ba ta da ita, bare su ce za su je wurinta.
Hatta da asalinsu basu sani ba, bayan ce musu da ta yi ita ‘yar haɗejia ce, ba ta ƙara ce musu komai a kan asalinsu ba.
“Aliyu…”
A hankali nitsataiyar muryarsa me cike da kamewa ta kira sunan, yayin da lumaassun idanuwasa masu ɗauke da gray ƙwaya suke kallon Aliyu.
Aliyun ya juyo ya kalli yayansa. Kuma har a lokacin kuka yake. Lokacin ƙarfe takwais na dare da ɗorariya, jama’ar da suka kawo su asibitin ma tafiyarsu suka yi bayan an tabbatar musu da rasuwarta.
“Ba mu yi sallar magrib ba… Ga isha ta kawo kai”
Da ƙyar sautin muryar tasa ke fita, don mai sauraro ma zai iya tsintar ɗacin da muryar tasa ke ɗauke da shi, ba zai ce ya gama mallakar hankalinsa ba, amma ya san cewa duk wanda ya mutu ba ya dawowa.
Ya san cewa yanzu su da ganin Mommansu wata ƙila sai a lahira, sun zama marayu, yanzu su marayu ne waɗanda basu da kowa sai junansu. Babu wanda zai taya su kukan rashin da suka yi.
Ba tare da Aliyun yace komai ba ya miƙe tsaye, shi ma Zaid ɗin miƙewar ya yi, ya dafa kafaɗarsa suka fara tafiya zuwa waje.
Kuma har lokacin Aliyun na kuka, shi kuma Zaid ɗin sai rarrashinsa yake. A masallacin asibitin suka yi sallah. Sannan suka fita wajen asibitin.
Dan Zaid ɗin ya tuna da ɗari biyun da Momman ta basu a yammacin ranar, tace da su; su siyi wani abun idan sun je islamiyya.
Awara ya sai musu da ita, sannan suka dawo cikin ɗakin da aka kwantar da ita. Suna kallon gawar suna cin awarar. Kuma bayan sun gama suka ci gaba da zama a ɗakin, har zuwa lokacin da dare ya tsala. Aliyu ne ya samu ya yi bacci, shi kuwa Zaid kwana ya yi yana gadin su su duka biyun.
Washe gari Zaid ɗin ne da kansa ya bazama cikin asibitin, kafin ya nemo inda mahaifiyarsu ta yi aiki a da. Ya faɗawa abokan aikin nata rasuwarta.
Kuma su ne suka zo suka yi Duk wani abu na sutura. Har aka mata sallah, kafin aka binneta a maƙabartar asibitin.
Har kowa ya watse da ga maƙabarar, Zaid da Aliyu na tsugunne a kan kabarin. A wannan karon shi ma Zaid ɗin sai da ya yi kuka. Kukan rashin sanin madafar da za su dafa a yanzu, mutuwa irin wadda mahaifiyarsu ta yi akwai raɗaɗi.
“Yanzu a nan zamu kwana?”
Aliyu ya tambayi Zaid ɗin, a sanda suka dawo gidansu. Wanda wuta ta gama ƙonawa, ko ina ya yi baƙi, babu abinda ya rage sai rufin gidan.
“Bamu da inda ya wuce nan… Aliyu”
Zaid ɗin ya faɗi yana ƙoƙarin sama musu inda za su zauna. Har ya gama kwashe kayan da wuta ta bari Aliyun na binsa da kallo.
Zaid ɗin da kansa ya share ko ina, ya fitar da tokar abinda ya rage, sannan da ƙyar a cikin kayan ya samu wani bargo wanda bai ƙone ba. Asalin bargon a kan gadon Mommansu take shimfiɗawa. Sai guntuwar katifar Zaid ɗin da ita ma kaɗan ne ta ƙone. Sai wasu kwanuka irin na silver wanda suka yi baƙi. Kuma a cikin tarkacen kayan, Zaid ya samo wani hotonsu guda ɗaya da rage.
Zaid ya fita can banɗakin gidan na waje, ya duba randar cikinsa ya ga akwai ruwa, ya zuba a cikin bokitin da ya samu a banɗakin, sannan ya koma ya kira Aliyu kan ya zo ya yi wanka.
“Zaid wani kaya za mu sa?”
Aliyun ya tambaya a sanda ya fito daga banɗakin, bayan ya yi wanka.
“Babu Aliyu, ba mu da wasu sauran kaya, komai kana ganin yanda ya ƙone, wutar nan bata bar mana komai ba sai ran mu”
“To ni yunwa nake ji!”
Aliyu ya faɗa yana ɗaga kafaɗarsa ta dama. Zaid ya yi shiru yana tunanin ta inda zai samawa ƙaninsa abinci, bai san ta ina zai fara ba, ba shi ma da wata dabarar sanin inda zai samu ko da kuɗin sai masa abincin ne. Shi ba ya ta kansa, ta ƙaninsa da ƙaddara ta bar masa yake.
“Ka zauna, bari na je gidansu Naufal na roƙar mana Mamansu, ƙila ta bamu ko da sauran ne”
ya ƙarshe yana ɗaga kafaɗaraa ta dama. Aliyunya gyaɗa kansa a hankali, a yayin da yake zama a bakin baƙar katifarsu. Zaid ya fita daga gidan ya shiga gidan dake maƙotansu.
Matar gidan ya fara gaisarwa, ta amsa shi da ‘yar fara’ar da yake da tabbacin ba ta kai zuci ba.
“Ashe kuma mamarku ta rasu?”
Maman Naufal ɗin ta tambaya a sigar gulma, kan Zaid a ƙasa ya gyaɗa mata, don da ma shi yaro ne mai ladabi, ba kamar Aliyun ba.
“To Allah ji ƙanta!”
“Amin… Da ma Aliyu ne yake jin yunwa, kuma wutar ba ta bar mana komai ba, shi ne na ce ko za mu samu wani abun, da zan bashi ya ci…”
Ya ƙarashe maganar, zuciyarsa na masa tuƙuƙi, wai yau su ne suke roƙon abinci, su ɗin da abinci sai dai su yi sadakarsa, wai aka ce rayuwa juyi-juyi.
“Eh, akwai wani guntu, amma iyaka na cin mutum ɗaya ne”
Kitchen ta shiga, sannan ta fito hannunta riƙe da wani ƙaramin kwano, ta miƙa masa ya sa hannu ya karɓa yana miƙewa tsaye.
“Na ce kuma wai ku baku da wasu ‘yan uwa ?”
Tun ba yau ba da ma yasan halin matar, kuma halinta na san jin ƙwaƙwaf yasa Mommansu ba ta shiri da ita. Sai kawai ya girgiza mata kai, yana ɗaga kafaɗarasa ta dama.
“Bamu da kowa”
Sai ta jinjina kai tana gaskata abun da mutane kan faɗa a kan Rabi’ar, na cewa wataƙila cikin shege ta je ta yi a garinsu, shi ne ta gudo nan ta zo ta kafa sabuwar rayuwa.
(Kai jama’a, duniya ina za ki da mu?!, Baiwar Allah ta rasu, maimakon ai mata addu’a, sai dai a ci gaba da cin namanta. Wanda kuma hakan sam ba dai-dai ba ne).
“Ga wata jallof ɗin taliya, ka ta shi ka ci”
Zaid ya faɗi a sanda ya dawo gidan, Aliyu da ke kwance a kan katifar ya miƙe zaune, sannan ya kai hannu ya karɓi ‘yar robar. Kafaɗarsa ya ɗaga yana kallon taliyar.
Abincin duka bai fi loma biyar ba, kuma ko shi Aliyun kaɗai ba ya jin abincin zai isheshi, bare ace shi ma ya zauna ya ci.
“Kai ba za ka ci ba?”
“Ba na jin yunwa”
A sanda ya kai ƙarshen maganar cikinsa, a lokacin ya wani irin ƙulle, saboda yunwar. Amma sai ya dake ya ɗaga kafaɗarsa, sannan ya ce.
“Bari na je na watsa ruwa”
Kuma daga haka ya fice daga ɗakin. Wankan ya je ya yi, ya dawo ya tarar da Aliyu ya raba taliyar biyu, ya ci rabi sannan ya bar masa rabi.
“Me yasa ba ka cin ye ba?,ko ba daɗi ?”
Ya jero masa tambayoyin yana ɗaga kafaɗarsa ta dama, tare da juya rigar uniform ɗin islamiyyarsa dai-dai.
“A’a, akwai daɗi mana, na ga kai ma ba ka ci ba, ka daure ka ci wannan ɗin”
Wata ƙwalla ta taru a idon Zaid. A hankali ya zauna kusa da ɗan uwan nasa yana kallonsa. Wannan karon kusan a tare suka ɗaga kafaɗunsu na dama.
“Aliyu… Yanzu babu Momma, da ga ni sai kai… Babu wani mai temakon mu sai Allah… Yanzu rayuwa za ta mana wahala, ban san ya za mu ci gaba da rayuwa ba, Aliyu ban san ma mecece rayuwar ba, kawai dai nasan akwai ƙalubale, kuma shi ne abinda za mu tunkara a yanzu!…”
Shi kansa ba ya ce waɗanan kalama nasa ba ne, bai san da ga ina suke zuwa ba, jin su kawai yake suna fita daga bakinsa. Bai taɓa sanin ya iya su ba ma.
Haka kawai ya ji wani nauyin kula da ƙaninsa ya hau kansa, ya na jin zai iya komai dan ganin ya sa ƙaninsa farin ciki, yana jin zai iya sadaukar da komai don ɗaukar nauyin ƙanin nasa…
Present day……
T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja
RAJA POV.
A hankali ya zauna a bakin gadon ɗakin da yake a matsayin nasa. Yanzun nan suka gama zaga gidan, dan ganin abinda za su buƙata. Har yanzu abinda ya faru ɗazu ya ƙi sakin ransa, gani yake kamar mafarki yake, abun akwai ɗaure kai.
“Raja me ke faru wai ?”
Muryar Rhoda ta katse musu kallon-kallon da suke a ɗazun. Kuma maganar tata ce ta sa ya kalli hannun yarinyar dake zubar jini.
Ba tare da ya amsawa Rhodan da ta tsaya tana kallon ikon Allah ba, ya sa hannusa a aljihunsa ya zaro handkerchief, sannan ya ɗaure hannun yarinyar.
Ya lura da ita ma tun ɗazun kallonsa take, sannan irin mamakin da ke kan fuskarsa shi ne sak a kan tata fuskar.
“Babu inda kika ji ciwo?”
Wannan salihar muryar tasa ta tambaya, yayin da take kallonta da gray drunken eyes ɗinsa.
Ya lura da yarinyar ta haɗiye wani abu, sannan ta gyaɗa masa kai. Shi ma sai ya gyaɗa mata nasa kan, sannan ya miƙe a hankali, idonsa a kanta, yayin da ita take zaune a dandariyar ƙasa.
Juyawa ya yi a hankali sannan ya nufi motarsu da ke tsallake, Rhoda da Zuzu da su ma suke kallon abun mamaki suka bi bayansa, kuma da haka suka iso gidan.
Waɗanan lumsassun idanuwan nasa ya ƙara lumshewa, fuskarta na dawowa a idonsa. Sai kawai ya shafi sumar kansa dake cikin askin high fade. Sannan ya ɗaga kafaɗarsa.
Shi ya kasa ganewa, me yasa hakan ke faruwa da shi ?, wacece wannan yarinyar ?, menene LABARINTA ?, me yasa take kama da shi, Momma da Aliyunsa?.
A hankali ya buɗe rabin idon nasa kamar kullum, ya kamata a ce ya kawar da wannan tunanin, don ba abun da ya kawo shi Abuja ba kenan, ya zo ne domin cimma wani ƙudirinsa, ya zo ne domin ya kawo ƙarshen wani abu.
Dan haka dole ya jingine komai, ya fuskanci abun da ke tunkararsa, Allah ya ƙaddara haɗuwar wannan yarinyar da shi ne dan kawai tasa ya tuna rayuwarsa ta baya, kuma ya tuna ɗin, dan haka komai ya ƙare, ya ƙare daga nan.
Abun da bai sani ba shine; yanzu komai zai soma, yanzu ƙaddarar ta soma, ba ayi komai ba ma. Ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta nan da ‘yan wasu kwanaki na dab!, da faruwa, wata ƙaddara da za ta tarwartsa komai, sannan ta saita wasu lamura.
Unguwar Madallah, Suleja , Niger State
08:30pm
RABI’A POV.
Zaune take a ɗakinsu, yayin da take jera kayanta a cikin ghana most go ɗinta. Gani ta yi kayan nata sun jima ba tare da ta duba su ba, shi yasa yau ɗin ta fitar da su, dan ta sauya musu ma’aji.
Hannunta na dama ta kalla, wanda ke ɗaure sa handkerchief ɗin da wannan mutumin na ɗazu ya ɗaura mata. Wannan mutumin?!, Wannan mutumin da ta ji macen da suke tare, me kaya irin nasa ta kira shi da RAJA!. Wannan mutumin mai kama da Ummanta.
Tunaninsa ya tuna mata da wallet ɗinsa da ta tsinta a ɗazun. Don bayan ya miƙe ya shige motarsa sun bar wurin, ta shiga yunƙurin miƙewe, kuma miƙewar da za ta yi idonta ya kai kan wallet ɗin da take da tabbacin tasa ce. Hakan yasa ta tsugunna ta sa hannu ta ɗauka, kuma ba ta buɗe a lokacin ba, sai kawai ta juya ta ci gaba da tafiyar ta.
Waige-waige ta shiga yi a kan katifar Saratu, dan tana zaune ne a bakin katifar, ƙasan hijabin da ta fita da shi yau ta samo wallet ɗin.
A hankali ta ɗauketa, sannan ta jujjuyata, kafin ta saka hannu ta buɗeta, a dai-dai inda ake saka hoto, ta ga hoton mutum biyu masu kama ɗaya, kuma hatta da kayan jikinsu iri ɗaya ne.
Ba dan dariyar da ɗaya ya yi ba, da babu abun da zai hana tace duka mutum ɗaya ne, zaune suke a ƙasa, daya ya dafa ɗaya. Yau ta fara ganinsa, amma duk da haka sai da ta gano shi a cikin su biyun, saboda rabin idanuwasa da suke a lumshe, sannan akwai tsotsiyar karen da ta ga a ƙasan haƙorinsa.
Iko sai Allah, kenan ba ma shi kaɗai ba ne, to amma umma ta faɗa mata cewar abokiyar tagwaitakar ta wato mai sunanta Rabi’a ta rasu, kuma ta rasu, bayan rasuwarta ma aka ce su ma yaran da ta haifa sun rasu.
To su waye waɗanan ?, me yasa suke kama da Ummanta da kuma ita, dan ganin ɗaya ɗan uwan nasa yasa ta ƙara ganin kamarta a cikin fuskokinsu, duk da a lokacin yarinta aka musu hoton.
A hankali hannunta ya ci gaba da buɗa wallet ɗin, akwai kuɗaɗe a ciki, sai atm cards. Bakinta ta taɓe, sannan ta rufe wallet ɗin, wata ƙila Allah zai sa su ƙara haɗuwa, sai ta samu damar ba shi kayansa.
Aje wallet ɗin ta yi a gefe, sannan ta ci gaba da shirya kayan nata. Kuma a cikin kayan ne, hannuta ya ɗauko wata jersey, jerseyn ta Bacerlona ce. Kuma tata ce. Nan take idanuwanta suka hango mata lokacin da aka samu rigar.
“Yaya Baby, Umma ta dawo”
Muryarta ta faɗi, a sanda take kallon Umman tasu da ta dawo daga asibiti, sannan a lokaci guda ta faɗa jikin mamar tata ta rungumeta.
“Umma sannu da dawowa”
Baby ta faɗi a sanda ta leƙo daga ɗakinta. Umman tasu ta kalleta tana amsawa.
“Yayar mamarta kin san me Umma ta kawo miki ?”
Umman ta faɗi a sanda take zama a kan sofa, cike da ɗauki Adawiyya ta girgiza mata kai alamun a’a.
“Jersayn Becelona!…”
Umman ya faɗa tana fiddo da jersyn daga jakarta da ta saba fita da ita. Adawiyya ta daka tsalle ta rungume Umman tana murmushi.
“Thanks Umma”
Jin wata ƙwalla na shirin taruwa mata a ido yasa ta yi saurin cilla rigar cikin kayanta, a mafiya yawan lokuta rayuwarta ta baya ba ta faɗo mata sai a sanda ta ga wasu kayanta na da.
A da ba ta da jerseyn sakawa da ta wuce wannan, dan Barcelona shi ne favourite team ɗinta. Ba ta da burin da ya wuce idan ta girma ta fara biluga ball, har ta kai ga wata rana Barcelona su ce za su siyeta, ta tafi can ta je tana buga musu ball.
Jama’a da dama sun sha mata kallon banza a kan ball ɗin da take da burin yi, kuma ba kowa ba ne illa al’umarta, hausawa ‘yan arewa, kamar dai sauran mata, ita ma haka ake fatan ta darƙushe baiwarta ta ja bakinta ta yi shiru.
Saboda ana ganin ba za ta iya ba, a matsayinta na mace, mutane na ganin zaman gida ne ya dace da ita, ita kanta ta san da hakan, amma kuma aure ba shi zai hanata cimma burinta ba, tana san ta zama wata aba a fannin buga ball.
Wata rana ita ma a saka sunanta a jerin ƙwararru, kuma duk wanda zai kira sunan nata dole sai ya kira arewa, domin nanne tushenta, nan ne asalinta.
An sha cewa ba ta da hankali, dan kawai tana san zama ‘yar ball, a ganin mutanen arewa ball wasan maza ne, mace ba za ta iya ba.
A da Ummanta ta saka mata a ranta cewa za ta iya, ta ba ta duk wani goyon baya kan ta yi, amma kuma yanzu komai ya tsaya, komai ya wargaje tare da rasuwar Umman.