Once you taste a true love, ordinary will never do...
No. 213, Naf belly Estate, Asokoro, Abuja
A fusace Anna ta shigo cikin gidan, ta ja ta tsaya tana kallon Siyama dake zaune a falo, ita ta ma manta da Siyaman, wadda ta zo gidan a daren jiya. A yau da safe su na karin kummalo wayar Kuliya ta sameta, hakan yasa ba shiri ta tafi asibitin.
Siyama 'ya ce a wurin ƙanwarta, wadda ta rasu, su biyu ne yaran ƙanwar tata, Siyaman da yayarta Karima. Siyama ta zauna a wurinta tsawon shekaru, kafin zamanta ya koma gidan. . .