No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja
MISHAL POV.
Zaune take a falon gisansu, ta na rubuta assignment ɗin da aka basu yau, yayin da Daala ke zaune a gefenta, ta na yi ta na ɗan yiwa Daalan hira.
Takun da ta ji daga kan stairs yasa ta kalli wurin, ganin Hajjara ce yasa ta sakar mata murmushin mugunta, irin wanda take mata a duk sanda za su haɗa ido a kwanakin nan.
Sannan ta ci gaba da rubutunta. Wani malolon baƙin ciki ya tokare maƙoshin Hajjara, tun bayan ranar da suka dawo daga asibitin nan Abubakar ya. . .