No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja.
MISHAL POV.
“A gidan Ubn wa aka ɗaurawa jikar tawa aure?… Tukunna ma ubn waye ya aurar da ita?!”
Jadda kakarsu ce ke magana cike da masifa, a sa’ilin da Ammu Musa ke sannar musu da batun ɗaurin auren Mishal da aka yi, tare da faɗin wai ga mijinta nan ya zo ɗaukanta su tafi.
Yau kwana takwas kenan da rasuwa Abubakar, gaba ɗaya ahalinsu na Maiduguri babu wanda bai zo gidan ba, haka aka yi zaman makoki aka share a jiya, sannan kowa ya koma Maidugurin, ban da Jaddan da ta ce ba za ta koma yanzu ba, sai Nimra wadda gidanta ke cikin garin Abuja. To yau ma ita da yaranta gaba ɗaya suna gidan.
Mishal dake kwance a kan doguwar kujera ta miƙe zaune, ta na jin wani zance da ba shi da ƙafa bare kai, aure ?, wa aka yi wa auren wai ?, wai ita?, ita akawa aure?, ta na cikin sallalamin rasuwar ɗan uwanta za’a wani zo mata da batun aure?. Duk da ba wani sosai take shiri da yayan nata ba, amma tasan da cewa ya na santa, kuma yana yin duk wata hidima da za ta faranta mata, ba ta yi kuka ba a rasuwar tasa, amma ta shiga cikin ƙinci mara misaltuwa, don ko makaranta ba ta zuwa.
Ammu Musa ya sunkuyar fa kansa a gaban matar kawunsu, sannan yace.
“Aure Jadda, Abubakar da kansa ya bayar da auren Hafsat ga abokinsa Aliyu! Kuma wannan ɗaurin auren shi ne abu na ƙarshe da Abubakar ɗin ya nema kafin Allah ya amshi ransa!”
Ba Jadda kawai ba, hatta da Nimra da kuma Hajjara sai da suka yi mamaki, amma me yasa babu wanda suka faɗawa batun auren har tsawon kwana takwas?.
Tun da bakin Ammu Musa ya ambaci sunan Aliyu, zuciyar Mishal ta hasko mata fuskarsa, wannan fuskar me kama da ta Adawiyya, kazalika irin wannan fuskar da take ganin mamallakinta na yawan tsayawa a tsallaken makarantarsu, kenan shi aka aura mata ?, wai tsaya ma, ita Mishal akai wa aure ?, wai har nawa ma take ?, da za’a mata aure, aure fa?.
“To Wallahi ba Abubakar ba, ko Muhammad ubn Abubakar ne zai dawo duniya yau ba ku isa ba, nawa ma yarinyar take ?, duka-duka fa bata fi shekaru 16 ba, shi ne za ku cuci rayuwarta ku mata aure?”
Anna ta faɗi tana miƙewa, kamar ta kaiwa Ammu musa bugu haka take ji.
“A’a Anna, kin san dai Ammu ba zai miki ƙarya ba, dan haka batun auren nan an riga an ɗaura, kawai dai mu yi wa Mushal fatan alkari, tare da danƙata a hamnun mijinta, kinsan dai Abubakar ba zai taɓa aurawa Mishal mijin da bai dace ba”
Cewar Nimar ta na miƙewa tsaye, Jadda ta juyo ta kalleta tare da wurga mata harara.
“Ba ke ba, ko Fatima kakarki ba ta isa ta faɗa min haka ba! Kar ki ga ina sakar miki fuska, ki ɗuka cewar za ki iya kawo min raini Falmata, Wallahi ina iya ɓatawa da ubn kowa a kan jikokina!…”
Daga nan Jadda ta shiga buɗe musu wutar bala’i, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, masifa kwando-kwando haka ta riƙa sauƙewa.
Sai da Nimra ta kira escort ɗinta, waɗanda gomnati ta bata dan kariya, a matsayinta na general, kasancewar a waje suke suna jiranta ba ɓata lokaci suka shigo, cikin su har da yaranta biyu, Ijaz da Arman.
Su suka saka bakin Jaddan yin shiru, ba dan ta na so ba a gaban idonta Nimra da ‘yarta Iqra suka shiga ɗakin Mishal suka haɗo mata kayanta kaf. Sai da suka so shiryata ma, amma da suka duba kayan nata suka ga babu na arziƙi sai suka barta haka, dan Mishal ba atamfa ko leshi take sawa ba, ita dai barta da ƙanun kaya.
Ita kuwa Mishal tun da aka fara wannan dambaruwa ta rasa gane kanta, ba ta ma fahimtar zancen da ake, dan zantukan nasu sun wa ƙwaƙwalwarta girma, wai yau ita aka yiwa aure, ita ɗin da take cewa ko da candy ta yi, ba za ta yi aure ba sai ta fara aiki, ga shi tun ba’a je ko ina ba har zancen ya warware.
KULIYA POV.
Tsaye yake a harabar gidan Abubakar, ya jingina da jikin motarsa, tunanika iri-iri na kai kawo a cikin kwanyarsa, shi kansa ba zai ce lafiyarsa ƙalau ba, dan yasan ba shi da lafiyar a irin halin da yake ciki. Kuma ba ya jin akwai maganin damuwarsa, komai ya masa duhu, ya kasa gane ainahin kan lamarinsa, shin farin ciki yake don ya samu wadda zuciyarsa ta gama tabbatar masa da sonta yake ?, ko kuma yana alhinin mutuwar amininsa, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wurin ceton tasa rayuwar?.
Ya kasa ganewa, ya kasa gane dai-dai da akasinta, ya kasa gane duhu da haske, ya kasa gane sarƙaƙiya da warwara. Ba ya fahimtar komai, ya na jin kamar rayuwarsa ce ke tangal-tangal a cikin kwale-kwalen katako, wanda ke tsakiyar tekun dake ambaliya…
Tunaninsa ya katse, a sanda ya hangi mutane na fitowa daga cikin gidan, sojoji ne guda huɗu a kan gaba, kowannensu riƙe da akwati, sai mata uku daga baya, sun saka ɗaya tsakiyarsa, wadda yake da tabbacin ita ce Mushal ɗin, duk da fuskarta a rufe take da gyale.
Har suka ƙaraso inda yake ya na kallonsu, ɗaya daga cikin sojojin ne yace ya buɗe musu booth, bai musa ba ya buɗe, suka saka akwatunan a ciki. Dai-dai da lokacin da mata nan biyu suka saka Mushal a cikin motar tasa a seat ɗin gaba.
Ɗaya daga cikin matan ce ya fusaknci cewa babbace, don ga shekarunta nan sun bayyana hakan, kuma sai yake ga kamar ma yasan fuskarta. Gaishe da ita ya yi cike da girmamawa.
“Kai ne Aliyu right? ”
Sai ya gyaɗa mata kai idonsa a ƙasa.
“Ba ka gane ni ba ko?”
Sai ya gyaɗa kansa yana ɗaga kafaɗa, don ya kasa ganotan.
“Mun taɓa haɗuwa sau ɗaya, General Adamu Nimra Arab”
Take fuskarta a ranar da suka fara haɗuwa ta dawo masa, tabbas ita ce, ita ce matar da ta babshi award a wani taron karramawa da ya taɓa zuwa.
“Ni uwa ce, kuma yaya a wurin Mishal, ba sai na zauna na maka dogon bayani ba, nasan ka mallaki hankalin kanka, ka kuma san hakkin mata a kan mijinta, na kuma san da ka san hakkin Maraya, don haka sai ka kiyaye!”
Maganganun nata ba su da yawa, amma baƙaramin taɓa shi suka yi ba, shi kuwa ya san maraici, ai yana jin babu wanda zai bada labarin maraici sama da shi…
RAJA POV.
Zane yake a kan kujerar dake facing Alhaji Bala, wanda ya buɗe akwatin dake cike da hodar ibilis, wadda su Rajan suka ƙwato masa a hannun waɗanda sukai haɗa kasuwanci da su. da ma haka Alhaji Bala ya saba saka su aiwatarwa tun suna garin kano.
Sai ya yi yarjejeniya da dilolin cocaine, kan yana so a kawo masa zai biya kuɗin, sai kuma ya tura ‘yan daba karɓar kayan, idan waɗanda aka aiko da kayan ba su yi gardamar hana kayan ba, ‘yan dabar Alhaji Bala za su karɓi kayan salin alin, idan kuma waɗanda aka aiko da kayan sun yi gardama, ‘yan dabar Alhaji Bala za su kashesu su ƙwaci kayan.
Fuskar Alhaji Balan, ɗauke take da wani irin yanayi, wanda yake cakuɗee da farin ciki da kuma mamaki, tun da ya fara safarar hodar ibilis, bai taɓa yin wadda ta kai wannan yawa ba.
Kuma masu kayan suna da matuƙar haɗari, bai ɗauka cewar su Rajan za su iya ƙwato kayan cikin sauƙi kamar haka ba, wannan aikin da suka masa yasa ya ƙara basu matsayi me girma a cikin zuciyarsa, tare da ɗaura niyyar ɗorasu a kan sauran harkokinsa, zai buɗe musu cikinsa, ya faɗa musu sauran ayyukansa da ya saba yi, don su taya shi ya tara kuɗin da yake buƙata, wajen yin campaign ɗin takararsa.
“Da kyau Zaki, aikinki na kyau! Na ji daɗin wannan aikin, Dan haka zan ƙara baku wani aikin!”
Kusan a tare Raja da Rhoda suka kalli juna, a cikin idon Raja roda ta hango ‘Ba na faɗa miki ba?’, ita ma ta idon nata ta mayar masa da ‘Na gani’. Sai kuma suka juya dubansu kan Alhaji Bala dake ta washe baki. Raja ya ɗaga kafaɗa yana faɗin.
“Wani aiki ne wannan ?”
“Safarar makamai!”
RABI’A POV.
Zaune suke ita da Zara a tsakar gida, yayin da Habiba da Mama ke ɗaki suna ƙus-ƙus ɗin da suka san na miye, wai yau suke faɗin Maman za ta yi tafiyar, kuma tun safe suke ta shirye-shirye. Anti Saratu kuma na banɗaki tana wanka, Fatima da Mahmud kuma basa ma gidan.
Fitowar Mama da Habiban ce tasa su dakatawa da hirar da suke, a tare suka kallesu.
“Allah ya tsare Mamana, Allah kare min ke gabanki da bayanki, Allah ya kauda idon maƙiya a kanki!…”
Haka Habiba ke ta faɗi har Maman ta sa kai za ta fita. A lokacin Saratu ta fito daga banɗaki, kallonsa kawai ta yi, ta kama hanyar ɗaki cike da takaici. Daga Mama har Habiba bin bayanta suka yi da harara. Har waje Habiba ta bi Mama tana ta mata addu’a. Kuma kafin ta dawo ne Anti Saratu dake ɗaki ta ƙwallawa Rabi kira.
“Gani Anti Saratu!…”
Rabin ta faɗi a sanda ta shiga ɗakin , ta iske Anti Saratu zaune a bakin gado tana shafa mai.
“Awara za ki siyomin”
“To kawo… Ki ban ɗari biyar a cikin kuɗina sai na ƙaro mana da kifi”
“To”
Anti Saratu ta amsa tana miƙewa, tare da nufar jakarta inda take aje kuɗi, kuɗin ta shiga lalubowa, kuma kafin ta gama lalubo kuɗin, wani yaro ya rangaɗa sallama daga bakin ƙofa, Zara dake tsakar gida ce ta amsa masa, abinda ya fito daga bakin yaron ne ya sanya duniyar Anti Saratu da ta Rabi girgiza, don abu ne da ba su taɓa zato na, wani abu da kaf tsawon zaman Rabi a gidan ba ta taɓa gani ko jinsa ba.
“Wai saratu ta zo in ji Fu’ad!”
Abun kamar mafarki, abun kamar wasa, wai yau wani ne ke sallama da Anti Saratu, wani abu sabo, wani abu da bai taɓa faruwa a tarihinta ba, ko da wasa ba ta taɓa yin saurayi ba, tun tasowarta babu wanda ya taɓa cewa yana sonta da soyyaya. Ko dan Allah maji roƙon bayinsa ne, kuma ma an ce wai haƙuri me tadda rabo.
No.181, Guzape, Abuja…
MISHAL POV.
Zaune take a bakin gadon da a yanzu yake amsa sunan nata. Ita fa har yanzu ba ta ganewa komai, ta kasa ganewa halin da take ciki, gani take kamar mafarki ne, kamar ba gaskiya ba ne, babu abun da ta yi kewa a gidansu sai Daala da kuma su Mama Ladi.
A karo na barkatai ta ƙara kallon ɗakin, sannan ta ja guntun tsaki a ƙasan numfashinta, miƙewa tsaye ta yi a hankali, ita ba ta saba zaman ɗaki ba, dan haka ba za ta iya zama gu ɗaya ba.
Shi ma wanda ke amsa suna mijin nata bayan ya kawota gidan ya ajiye , ba ta ƙara ganinsa ba, ga shi har kusan ƙarfe tara na dare. A ƙofar ɗakin nata ta tsaya, tana kallon corridorn dake ɗauke da ƙofofo uku, wanda take da tabbacin ɗakuna ne.
Ba ta damu da buɗe ko da ƙofa ɗaya ba, ta ci gaba da takawa zuwa cikin falon, kasancewar gidan bungalow ne. A falo ta ci birki, ta shiga kalle-kalle, har idonta ya sauƙa a kan wata farar kyakkyawar mage, kwance a kan sofa. Ba ta san sanda murmushi ya suɓuce mata.
Da sauri ta yi wurin magen ta na ɗaukarta, hakan ya sa magen ta farka, sosa jikin magen ta shiga yi ta na mata wasa kamar wadda ta samu ƙarimin yaro.
Jin ana buɗe ƙofar shigowa falon ya sa ta ɗora magen a kanta ta kalli ƙofar, dai-dai da shigowar Kuliya, sanye cikin baƙaƙen ƙananun kaya. Kamar yanda take kallonsa haka shi ma yake kallonta.
Sanye take cikin wani short trouser, wanda bai rufe gwiwarta ba, sai wata half vase da bata rufe duka cikinta ba, ta ɗora falmaran ɗin wandon a saman half vase ɗin, wadda take da ɗan tsa yi, ƙafafunta sanye cikin wasu pink fluffy sliders, gashin kanta fake cikin ponytail.
Zuciyar Kuliya ta yi tsalle daga ma’ajiyarta, wani abu me kama da garwashi ya shiga bi ta kan zuciyarsa, yanda ta kafe shi da olive green eyes ɗinta kaɗai ya isa ya sa shi a uku.
Da ƙyar ya haɗiye wata iska, sannan ya fara takowa zuwa cikin falon. Mishal ba ta san wa ta kunya ba, hakan ya sa ba ta ji komai ba dan ya ganta a cikin irin wannan shigar.
“Wannan kuliyar, take ce?”
Muryarta ta fito a sake, kamar ta san shi, kamar ta saba da shi, haka ta masa maganar tana shafa bayan kuliyar. Ba tare da ya kalleta ba, ya aje ledar hannunsa a kan coffe table, ya ɗaga kafaɗarsa sannan ya ce.
“Ayra”
Mishal ta ƙyal-ƙyale da dariya, dan ta fahimci cewa sunan Kuliyar ne Ayran. Ɗagowa ya yi ya kalleta, wai ita ba ta san rashin sabo ba ne?, ji yanda ta ke, kamar wanda suka saba tsawon shekaru.
“Wato saboda kada a kirata da irin suna ka, shi ne ka yiwa Ayra star takwara, tab ɗi jam, Ayra star go sue you oo!”
Kallonta ya ci gaba da yi, yanda take maganar a sake, da yanda take shafa jikin kuliyar, da kuma yanda take abu cike da yarinta ne ke nuna masa ƙarancin shekarunta. Leda ɗaya ya miƙo mata, cikin ledojin da ya shigo da su.
“Ki ci!”
Mishal ta ɗan kalli ledar, wai shi ba ya doguwar magana ne ?. Ba tare da tace masa komai ba, ta karɓi ledar, sannan ta ɗora Ayran a kanta, tana zama a kan sofa, tare da yunƙurin buɗe ledar.
Gadan-gadan Kuliya ya ga tana shirin fara cin abicin da hannunta ba tare da ta wanke hannun nata ba. Da sauri ya dakatar da ita ta hanyar faɗin.
“You have to wash your hands first”
Sai ta dakata da shirin kai lomar da take, ta ɗago ta kalleshi, ya na tsaye a yanda yake, sai kuma ta aje take away ɗin, sannan ta sauƙe Ayran dake kanta.
Ta nufi ɗakinta dan ta wanke hannun nata. Kuliya ya bi bayanta da kallo yana mamakin irin halin da yarinyar ke ciki, Abubakar ya sha ba shi labarin irin halayenta, bai taɓa yarda ba sai yau.
Lalle akwai aiki ja a gabansa, dole ne yasan yanda zai seta yarinyar nan, saboda sam ba ta san ma mecece rayuwa ba, rayuwarta take kanta tsaye.