Skip to content
Part 2 of 9 in the Series Labarinsu by Salma Ahmad Isah

A hasale Uncle ɗin ya cillar da littafin da ke hannunsa, ya ɗauki wata cane ya yi kanta, yana ƙarasawa kusa da ita ya ɗaga bulalar sama zai zabga mata ta kai hannunta ta riƙe bulallar.

“Babban kuskuren da za ka yi shi ne duka na da wannan bulalar, dan Wallahil Azim ka kuskura ka dakeni sai na rama”

Ta ƙarashe tana wancakalar da bulalar, Uncle ya haɗiye wani abu a maƙoshinsa, yana ci gaba da kallon yarinyar, Ba ƙaramin jajircewa ya yi ba da har ya iya yunƙurin dukan yarinyar, dan malamai da dama na yawan bada labarin yarinyar a staffroom, wasu da ga cikinsu ma kan ce wata ƙila aljana ce, dan normal ɗan adam ba zai iya abin da yarinyar nan ke yi ba.

Ta addabi kowa a makarantar, watan da ya wuce har wani malami ta mara, ɗalibai kuwa kullum sai an samu wanda zai kawo ƙararta.

Sai da ta aika masa harara, sannan ta aje jakaarta a kan desk, ta zauna tana baza ƙwayoyin idonta a cikin ajin, hakan yasa kowa ya shiga taitayinsa.

Sai da ta yi ƙwafa sannan ta buɗe jakarta ta ɗauko littafi ta gyara zamata ta shiga kwafar note ɗin da uncle ɗi ya ci gaba da yi.

“Wai me yasa ke bakya azumi kamar ‘yan uwanki musulmai”

Muryar Angelica yarinyar Mishal ta faɗi a sanda aka fito break, dan sai dai a kirata da yarinyarta, saboda duk wani aike ko bautar Mishal ɗin ita Angelican ce ke yi. Kuma kaf makarantar Mishal bata da ƙawa ko ɗaya, ita ma Angelican ita ta cuso kanta gareta. Mishal ta ture flask ɗin gabanta tana miƙe ƙafa.

“Saboda bana san wahala, bazan iya haɗa azumi da zuwa makaranta ba”

Ta bata amsa cikin harshen turanci, kamar yanda itama Angelican ta mata maganar cikin harshen turancin, kasancewarta baturiyar Engiland. Aiki ne ya kawo mahaifinta zama a nigeria.

“Amma su Rashida su na yi”

“Baki ji me nace ba ?”

Sai Angelica ta girgiza kai, tana kai loma bakinta.

“Kai ka ga wata balarabiya”

Wani sabon ɗalibi da ya fara zuwa makarantar ya faɗi yana kallon Mishal da ga nesa, abokin nasa da ake nunawa Mishal ɗin ya juyo ya kalli wurin, kuma a lokaci guda idonsa ya zare cike da tsoro da kuma mamaki.

“Kai!!, karfa kace min santa kake!”

Sabon ɗalibin me suna Abdul ya yi murmushi.

“Ka jika da wani zance, waye zai ga wannan kyakyawar ya ce ba ya so, Allah da da na ganta na ɗauka balarabiyace”

Abokin ya haɗiye wani abu.

“Abdul da ka je ka ce kana san wannan, gwara ka samu Madam Joke (Malamarsu ta Math) ka ce kana santa”

Abdul ya ƙyaƙyale da dariya.

“Kai ana gabar kana yamma, me zan yi da wata Joke arniya kuma tsohuwa, ga kyakkyawar baby a nan”

“Idan za ka ka bar jirana, tun da na haneka baka ji ba, idan ka je ita zata maka bayani….”

Kuma yana kaiwa nan ya fita da gudu ya bar wurin zaman cin abincin nasu. Abdul ya bi bayansa da kallo yana dariya, ya gyara tie ɗin wuyansa, sannan ya gyara stocking ɗin wandonsa, ya nufi wurin da kyakkyawarsa take.

“Ke rabu da assignment ɗin nan, wallahi bazan yi ba, in yaso idan mun haɗu da python ya kasheni” Cewar Mishal

Pytho shi ne sunan da suke kiran malamin math ɗinsu da shi, kuma sunan ya samo asaline tun sanda suna jss3, lokacin da ya koyar da su Pythagoras rule.

“Ke idan ki ka ƙi yi ba damuwa, ni fa ?, wata ƙila ya karyani, gwara na je na yi”

Angelica ta ƙarashe tana miƙewa tare da barin wurin.

Mishal ta gyara zamanta tana aika lomar abincinta baki, kafin wata murya ta daki dodon kunnuwansa.

“Salam!”

Kuma kafin ta ɗago da kanta ta amsa sallamar, har wanda ya yi sallamar ya ja kujerar da Angelica ta tashi ya zauna. Mishal ta ɗan kalleshi na wasu sakkani. Bata taɓa ganinsa a makarantar ba, hakan kenuna mata cewar sabon zuwa ne, dan in ba baka ba,babu yaron da ya isa ya yi gigin mata magana kaf brickhall.

“Ba kya azumi ne na ga kina cin abinci?…”

Bata amsa shi ba, sai kallonsa da ta ci gaba da yi da olive green color eyes ɗinta.

“A wani class kike ?”

Yanzu ma bata amsa shi ba, hakan yasa Abdul tunanin ko de bata jin hausa,sai de kuma farin fatarta baya kama da na larabawa, farace, fara kuma sosai, sai dai ba irin farin fatar larabawa da turawa ba.

Kyan fuskarta, idanuwanta da kuma gashin kanta sune suke kama da na larabawan, idan zai iya sakata a jerin mutanen nigeria, sai dai a danganta ta da jinin shuwa arab.

Mishal ta zuƙi taliyar indomien da ke bakinta,sannan ta ci gaba da kallonsa.

“Can’t you speak hausa ?”

“Me kake buƙata ?”

Ta tambaya da hausa tana kallonsa.

“Ashe dai kina ji….”

“Na ce me kake buƙata ?”

Abdul ya ɗan shafa kansa sannan ya ce.

“Idan ba zaki damu ba, shin zamu iya yin soyyaya”

Sai ta yi murmushi, wanda ya bayyana ƙarafunan braces ɗin dake saman haƙwaranta, wanda Abdul ya ɗauke shi a matsayin amasar tambayarsa, sai shi ma ya yi murmushin.

Mishal ta rufe flask ɗinta a karo na biyu, sannan ta miƙe ta zagayo ta ɓarin da Abdul yake.

“Miƙe pls”

Yana murmushi ya miƙe tsaye. Tashi ɗaya Abdul ya ga yanayin fuskarta ya sauya zuwa fushi mabayyani.

Sannan ba ta yi wata-wata ba, ta ɗaga hannunta na dama ta ɗauke shi da maruka uku kyawawa.

Tsaye suke a office ɗin principal ita da Abdul ɗin da ta fasawa baki da marin da ta masa, bayan shi Abdul ɗin ya kawo ƙararta office ɗin principal ɗin.

Principal ɗin nasu ya kalleta da kyau, bayan da Abdul ya gana tsara masa aabin da ya faru, kuma ko musu ba ta yi ba, ta amsa lefinta, shi a rayuwarsa bai taɓa ganin yarinya irin wannan Hafsat ɗin ba. Kullum cikin kawo ƙararta ake, ba ga malamai ba, ba ga ɗalibai ba, kuma shi yarasa yanda zai yi da yarinyar. Shi dai ba zai iya korarta daga makarantar ba, saboda tana da ƙoƙari, tana ɗaya daga cikin ɗaliban da suke alfahari da su a makarantar.

“Hafsat, me yasa kika mare shi?”

Mishal ta wani juya idonta a cikin office ɗin, sannan ta ɗan sosa hannunta.

“Zuwa ya yi yace wai yana so na…”

“Kuma da ga cewa yana sanki sai ki mareshi ?”

“Ai dokar makaranta ya karya, shi yasa na mareshi, ya godewa Allah ma da ban karya masa hannu ba”

Principal ya ci gaba da kallon yarinyar, ba wai da wasa take faɗar hakan ba, a bakin gaskiyarta take faɗin zata karya shin, dan ta karya ɗalibai biyu a makarantar, kuma tun daga junior ta fara makarantar, sannan tun da ga lokacin kullum sai an kawo ƙararta.

Wani lokacin ma a ajinsu na koyon kung fu take dukan ‘ya’yan mutane, hakan yasa shi da kansa yace ta fita da ga anjin koyon kung fu ɗin, amma yarinyar fir taƙi, kuma taƙi ɗaukar ko wani sport sai kung fu ɗin.

“Ga wannan takardar, ki kaiwa yayanki”

Hannu ta kai ta karɓi takardar, sannan ta sa kai ta fice, ba wannan ne karo na farko da suka taɓa bata takardar suka ce ta kai masa ba, dan idan da sabo ma yayan nata ya saba zuwa makarantar a kan matsalarta.

A kusa da staffroom ɗin malamai mata ta ga wannan yarinyar….wannan yarinyar da ke tsananin bata tausayi. Sai kawai ta tsaya da tafiyar da take, ta nufi wurin yarinyar, dan tana so tai mata magana.

“Sanu da aiki!”

Yarinyar da ke sharar ta yi saurin ɗagowa ta kalleta, ita ma yarinyar ta gane Mishal ɗin, tana yawan ganinta a makarantar.

“Menene sunan ki”

Mishal ta tambaya fuskarta ɗauke da murmushi. Sai da yarinyar ta haɗiye wani abu, sannan ta amsa mata da.

“Rabi’a”

Mishal ta gyaɗa kanta.

“Me yasa kike aikin shara a nan?…”

Rabi ta gyara ruƙon tsintsiyar dake hannunta, to me yasa take mata waɗanan tambayoyin ?, amma kuma abun yaso ya bata mamaki, dan gaba ɗaya ɗaliban makarantar babu wanda ma yake kallonta da kima ko mutunci, kallon banza suke mata, ga wahalar da suke bata, wasu ma har tsokanarta suke.

“Am….Imm…ummm”

Ta kafa inda-inda, dan bata santa ba, batama san me za ta ce mata ba.

“Is it personal issue?”

Kuma tun kafin Mishal ɗin ta yi tunanin cewa ba lalle ace tana jin turanci ba Rabi ta amsa mata da sauri.

“Yeah, it’s personal”

Mamaki ya kama Mishal, duk da dama yarinyar bata mata kama da irin villegers ɗin nan ba, ta fi kama da waɗanda ke cikin ƙuncin rayuwa, duk da ba a walaƙance take ba, amma kana ganinta zaka ga hakan, sai dai kuma yanayinta na wayyayun ‘yan mata ne.

Sai kawai ta gyaɗa kanta.

“Gobe za ayi hutu, inaso ki min siffa, kin iya ?”

Girar Rabi ta haɗe wuri guda alamun kokwanto.

“Menene siffa ?”

Mishal ta ɗan daki gaban goshinta.

“Lalle nake nufi, kin iya?”

Sai Rabi ta yi murmushi, a shekaru zata iya girmewa yarinyar, amma da alama yarinyar tana da kirki.

“Na iya, kina so na miki ne?”

Da sauri Mishal ta gyaɗa mata kai, kuma da gaske tana buƙatar amata siffar, dan sallar azumin ba a Abuja zasu yi ba, a mahaifarsu zasu yi, wato Maiduguri.

“Wanne kike so, ɗan gam ko ɗan zane ?”

“Ni dai baƙa nake so, kuma a hannu za ki min”

Sai Rabi ta gyaɗa kanta.

“A ina zan miki ?”

Mishal ta juya tana kallon inda suke, to a ina da suka haɗu ?, a makaranta suka haɗu, to a ina zata mata da ya wuce makarantar ?.

“A nan mana”

Rabi ta zaro ido tana jinjina yarintar yarinyar.

“Makaranta ce fa”

“To sai me?, kin ga kawai zan sa a siyo min lallen, gobe zaki min, sunana Mishal”

Rabi ta kuma gyaɗa kanta….kafin wata murya ta yi magan da ga ƙofar staffroom ɗin malamai mata.

“Ke!, da kika tara wannan sharar a nan ubnki ne zai kwashe!”

Rabi ta zabura za ta koma ta ci gaba da sharar da take.

“Kawai sai ki zagi ubnta, me ta miki ?”

Muryar Mishal ta katse mata hanzari, da sauri Rabi ta juyo ta kalli Mishal ɗin, wadda ta wani haɗe rai, tana kallon malamar.

“Ke ba na ciki da rashin kunya, ki bar ganin sauran malamai su na ƙyaleki, wallahi ni ubnki zan ci….”

“Ahir ɗinki Abu, ubana ya fi ƙarfinki, wallahi ki fita sabgata, in ba haka ba yanzu zan nuna miki kalar nawa rashin hankalin, kuma ki musa ki gani”

Mishal ta katseta tun kafin ta rufe bakinta, kuma cike da rashin kunya take maganar, tana yi tana nuna malamar da ɗan yatsa.

“Bamu taɓa haɗuwa da ke ba ne, dan kina malamar art ba shi zai hana na bi ta kan mutuncinki da kika zubar na wuce ba, dan haka ki kula, kuma sharar ba zata kwashe ba, ki yi abinda kike ganin zaki iya…”

No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja

06:00pm

Me gidan Abubakar Muhammad Auwal, tare da matarsa Hajjara, sai yaransu guda biyu, Hammad wanda ya ci sunan kakansa da kuma fahima, ‘yar jaririyar da bata wuce wata biyar ba. Su ne zaune a kan danning table. Wanda ke shaƙe da kayan buɗe baki kala-kala.Da alama jiran kiran sallah suke, dan ƙiris ya rage a kira sallahr.

Ƙofar ɗaya daga cikin ɗakunan falon ce ta buɗe, farko keken guragu ne ya fara bayyana, zaune a kan keken kuma, wata matashiyar yarinya ce, wadda ba za ta wuce 9yrs ba. Kallo ɗaya zaka mata ka ga nakasarta, dan bata da hannaye gaba ɗaya, sannan kanta a langwaɓe gefe guda, bakinta nazubar da yawu.

Mishal ce ta biyo baya,wadda ita ce ke turo keken, sanye take da wata farar linen tunic dress, da kaɗan rigar ta sauƙo gwiwarta, ga kuma rigar ko hannu bata da shi, kanta babu ɗankwali kamar yanda ta saba zama, gashin kanta tifke cikin braid(kalaba) guda ɗaya, ta saka hair band daga sama.

Gaba ɗayansu suka kalli wurin, kuma daga Hajjara har mijin nata basu ɗauke idonsu a kansu ba har suka ƙaraso danning area ɗin.

Kujera ɗaya Mishal ta kawar ta mayeta da keken Firdaus, wadda take kira da Daala.

Sannan ita ma ta samu kejera kusa da ita ta zauna, sai da ta ɗauki tissue ta gogewa Daalan yawun da ya zubo mata sannan ta juyo tana kallon mutanen dake kan danning ɗin.

Hajjara ta kawar da kanta tana taɓe baki, Allah ya sani, har cikin zuciyarta bata san Mishal, wata ƙila dan igiyar aurenta da ta taɓa zama sanadiyyar tsinkewa ne, ko kuma dan rashin kunyar da take mata.

Mishal ta kalli yayanta,wanda shi ma ita yake kallo, hannunta na dama ta ɗago, wanda ke riƙe da envelop, ta miƙa masa.

Abubakar ya girgiza kansa, ya san duk yanda aka yi wani laifin ta aikata, ba yau ta saba kawo takardu irin wannan ɗin ba, hasalima suna nan tili guda yana ajewa, dan sun ma fi yawan report ɗin ta na makaranta da take kawowa. Abu ɗaya ne yasa ba zai cireta daga makaranta ba kwata-kwata, hazaƙarta ce tasa hakan, dan ba ma shi ba, hatta da makarantar suna tinƙaho da ita, gashi de ba wasu shekaru ne da ita ba, amma girman jikinta ne zaisa ka zaci wata babbace.

“Me kuma kika yi ?”

Ya tambaya yana karɓar envelope ɗin, kanta ta sunkuyar, tana wasa da yatsunta.

Murmushi kawai ya yi a sanda ya buɗe ya karanta, dan bi da bi ya gama haddace kalaman da ke ciki, saboda a kullum abu iri ɗaya suke turo masa tun tana junior. Ya rasa irin abunda ke damun ta.

“Hammad yace min yau baki yi azumi ba, bayan shi ma yau yana yi”

Ta ɗago da kanta ta kalli Hammad ɗin dake gefen uwrsa, kamar yanda bata san uwar yaron shi ma haka ta tsaneshi, dan kaf halayen uwrsa babu wanda bai ɗauko ba.

“Saboda makarantar da nake zuwa ne…”

“Makaranta sai ta hanaki azumi?”

Sai kawai ta miƙe tsaye tana faɗin.

“Bari na je waje…..”

Bayanta ya bi da kallo yana mamakin halin yarinyar, du-du-du ba za ta wuce 17-16 ba, har yau yana tuna yanda ya ɗauketa da hannayensa ranar da aka haifeta, da kuma irin maganar da mahaifiyarsu ta masa a wancan lokacin.

_“Sadiq, ka kula da ita, nasan za ta tashi cikin maraici, bata da kowa sai kai, kada ka danƙa renonta a hannun kowa, ciki kuwa harda Amma (tana nufin mahaifiyarta), ka kula da ita, ka kula da ita……”_

Kuma kalamanta na ƙarshe kenan, a kan idonsa a ka shiga da ita ɗakin tiyata. sai kawai fito masa aka yi da jairiya, aka ce ta haihu, amma ta rasu sai dai babyn da ta haifa.

“Wai haka za’a zuba ido ana kallon yarinyar nan tana abinda take so?…..”

Hajjara ta faɗi a ƙufule, dan Allah ya sani ta gaji da halin yainyar, kuma da ma tun sanda ta ɗora idonta a kan yariyar ta washeta.

“Me ta yi ?”

Ya furta hakan cikin halin ko in kula, yana ninke takardar da Mishal ɗin ta bashi.

“Jiya fa na yi baƙi, baka ga rashin kunyar da ta min a gabansu ba”

“Yarinta ce take damunta, idan ta girma za ta dena”

Haushi kamar ya kashe Hajjara, dan dama abin da ya saba faɗa mata kenan, a duk sanda ta kawo masa ƙarar Mishal ɗin, yau ɗin ma tsautsayi ne yasa ta kawo ƙararta, a ranta ta yi ƙwafa, Allah ya kawo ranar da za ta ga bayan yarinyar nan.

<< Labarinsu 1Labarinsu 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×