Let’s never forget, it’s you and me vs problem, not me vs you…
KULIYA POV.
Tsaye yake a harabar wani wurin saida motoci, yayin da ɗaya daga cikin ma’aikatan wurin ke ta nuna masa kalar motocin da suke da su a wurin.
“Wannan fa?”
Ya faɗi a yayin da ya nuna wata Audi RSQ. Ma’aikacin ya kalleshi.
“Ranka ya daɗe wannan fa tana da tsada sosai”
Nan take Kuliya ya hango kansa a cikin zuciyarsa yana kashe sauraye a fuskar mutumin. Kuma ba tare da wani tunani ba yace.
“Ka ga na maka kama da wanda ba zai iya siyan motar ba ne ko me ?”
“Haƙuri ranka ya daɗe, ba haka nake nufi ba…”
Kuliya ya masa baza ya juya ya nufi hanyar fita, da gudu mutumin ya bi bayansa yana bashi haƙuri, amma haka ya ƙi ko kallonsa bare ya amsa, ya riga ya yi zuciya, ba zai siyi mota a wurinsu ba.
Haka ya fita daga wurin, ya nufi wani wurin da ban, a inda ya je ɗin ne ya siyi wata baƙar Honda Breeze. Sannan kai tsaye ya wuce wurin aiki. Ƙarfe biyu dot, ya tashi don ya je ya ɗauko Mishal, ba wai don lokacin tashin aikinsa ya yi ba, sai don yasan babu wanda zai ɗauko ta idan ba shi ba, shi ɗin da a yanzu yake amsa sunan mijinta!.
A harabar makarantar ya yi parking, ya na raba idonsa a kan ɗaliban dake ta tunkuɗowa daga cikin makarantar. Ya kwashe kusan minti goma zaune cikin motar, kafin ya hangota tana tafiya ita da wasu mutum biyu, be damu da kallon waɗanda take tare da su ba, tun da Allah ya sa ya ganta ai shikenan.
Ya san ba gane shi za ta yi ba, tun da ba waccan motar da ya kawota ba ce, shi yasa ya fito daga cikin motar, ya fara takawa zuwa wurin da suke. Zuwa lokacin ɗayar ta tafi, saura su biyu.
A tare Rabi da Mishal dabkuma Angelica suka fito daga cikin makatarantar, kafin Angelica ta musu sallama ta tafi, suna tafiyar ne kuma suka ga mutum tsaye a gabansu.
Kusan a lokaci guda suka kalleshi, gaban Rabi ne ya yi wata mummunar bugawa, ganin wani mutum, wani sak… sak Raja, nan take ƙwaƙwalwarta ta wasto mata hoton ranar da ta tsinci wallet ɗinsa, har ta buɗe taga hotonsu su biyu, tabbas wannan ɗan uwansa ne, ɗan uwansa dake matuƙar kama da ita da kuma shi Rajan kansa.
Mishal kuwa kallonsa ta shiga yi, daga ta kalli Rabi, sai shi ma ta kalleshi, sai a lokacin ya kalli wadda suke tare. Allah ne kaɗai yasan cikin wani irin shock ya shiga, wata fuska yake gani, wadda zai iya cewa ta Mommansa ce, fuskar sak ta Zaid ɗinsa, Zaid ɗin da ya rabu da shi na tsayon shekaru masu tarin yawa, wannan fuskar da kammaninta ke kwance a kan tasa fuskar. Ƙwaƙwalwarsa ce ta hautsina, sannan ta kuma hautsunawa, tunaninsa ya birkice, ya kasa gane shin mafarki yake, ko kuma zahiri ne?. Bakinsa yana rawa ya kalleta tun daga sama har ƙasa. Zuciyarsa na bugawa da sauri.
“Ka santa ne?”
Mishal ta faɗi tana dubansa, me makon ya bata amsa, sai ya kalleta kawai, sannan ya haɗiye duk wani mamakin da yake ciki, ya ɗaga kafaɗarasa ta dama.
“Zo mu tafi!”
Allahu ƙadirun ala man ya sha’u, hatta da muryarsa sak irin ta Raja ce, sai dai akwai wani abu ɗaya da ya banbanta muryoyin nasu; muryar Raja na fita cikin sanyi da taushi ne, ta wannan kuwa ba ta da wannan sanyin, sanna babu innocent a cikin muryarsa.
Da sauri ya juya ya nufi motarsa, ba tare da ya jira Mishal ɗin ba.
“Seesee kin san shi ne?”
Mishal ta tambaya tana kallon Rabi’a, wadda ta bi bayan Kuliya da kallo.
“Ba shi na sani ba, wani ne da ban!… Ki je ya na jiranki”
Cewar Rabi’a, bayan da ta gama tabbatar da cewa duk yanda aka yi wannan me kama da Rajan shi ne mijin Mishal ɗin. Ba tare da Mishal ta ce komai a kan maganar Rabi ta farko ba, ta gyaɗa mata kai, tare da mata sallama ta nufi motar ta shiga, kuma ba jira Kuliya ya figi motar a guje kamar yanda ya saba, suka bar cikin makarantar.
Kamar yanda Mishal ta saba ganinsa haka yau ma ta ganshi, jingine jikin gate ɗin wannan estate ɗin dake tsalleken makarnatarsu, ba shiri ta juyo ta kalli wanda ke zaune a gefenta, sannan ta juya ta kalli na jikin gate ɗin a lokacin da suka wuce layin.
Kanta ya kulle, saboda sau a yau ta gano banbancin da suke da shi, wancan na jikin gate ɗin yana da zaje da kuma ɗan gemu kaɗan, wannan na zaune a gefen nata kuma, ba shi da gemu ko kaɗan, sannan ƙwayar idon wancan gray ce, yayin da wannan tasa take baƙa.
To me yake faruwa?, shin su ‘yan biyi ne ko me ?, sun san da zaman junansu ?, ta ina suka haɗa alaƙa da Seeseenta?. Gaba ɗaya tambayoyin su ne suka cika kanta fal!, ta kasa banbance fari da baƙi, har hakan ya sa ba ta lura da irin gudun da Kuliya ke shararawa da su ba.
Ba ita kaɗai ba ce kanta yake a kulle, hatta da Kuliyan shi ma kansa a kulle yake, ya kasa ganewa abun da yake shirin faruwa, rayuwarsa ta baya da yake ta kokawar mantawa da ita, ita ce ke dawo masa bayan ganin wannan fusakar, wacece ita?, me yasa take kama da su?, a ina Mishal ta santa?, don kayan jikinta ba kalar na ‘yan makarantar ba ne, bare yace makarantarsu ce ɗaya. Ya rasa takamemen tunanin da zai kama. Tunaninsa da nutsuwarsa suka sake dugunzuma fiye da da.
Ruɗani da cukurkuɗaɗɗun zantunka da tunanika suka yi wa ƙwaƙwalwarsa tsinkaye, ya kasa tantance meke shirin faru, wata ƙaddara ce za ta haɗa shi da wannan yarinyar?, wadda ke ɗauke da kammanin fuskarsa da ta Momma da kuma Zaid.
Har suka kai gidan babu wannda ya samu amsa ɗaya daga cikin tarin tambayoyin dake kawunansu, parking ya yi a harabar gidan, kuma kusan a tare suka fito,amma shi ya rigata shiga cikin gidan.
Me aikin da ke masa aikin shara da goge-goge ce kawai a gidan, da can ba wai shi takewa aikin ba, ‘yar aikin gidan Anna ce, kuma Annan ce ta sakata ta riƙa zuwa gidan nasa duk sati tana masa shara. Kuma shi kullum ba ya dawowa gidan sai bayan sallahr isha’i, ha kan ya da ko kalarta bai sani ba sai yau.
Ita ma a ruɗe ta shiga dubansu su duka, don ba ta taɓa ganinsa ba sai yau, kullum haka za ta zo ta yi aikinta ta fi, ko a gidan Amman ba haɗuwa suke ba, yau kuma sai ga shi ya dawo gidan a lokacin da ba ta taɓa zata ba, kuma ba shi kaɗai ya dawo ba, harda wata yarinya tare da shi.
Mishal ta kalli matar a sanda take gaisheta, amsawa ta yi tana maida mata martanin gaisuwar, hanyar corridor ta kama, amma sai muryarsa ta dakatar da ita.
“Zan koma wajen aiki, anjima kaɗan za’a kawo miki abinci…”
Daga haka ya juya ya fice, Mishal ta bi bayansa da kallo.
Ba tare da tace komai ba, ta nufi ɗakinta, tunani da yawa birgit a ranta, wanka ta yi, ta sauya kaya zuwa wani distressed jeans, da wata peach long sleeves tees, ta saka sliders ɗinta ta fito, kanta ko ɗankwali babu, sai band ɗin da ta saka a tsakiyarsa. A parlo ta zauna tana kallo, har zuwa lokacin da me aikin ta gama aikinta.
“Ranki ya daɗe ni zan wuce”.
Mishal ta janyo idonta daga kan Tv ta kalleta.
“Ina za ki je?”
Matar ta ɗan sosa ƙeya tana faɗin.
“Gidan Anna zan koma, ai da ma nan ɗin shara kawai nake zuwa na yi”
Mishal ta gyara zamanta.
“Wacece Anna kuma?”
Mamaki ya kama matar me suna Rahila, ta ya za ta auri ɗan mata, kuma tace ba ta santa ba.
“Ita ce babar me gidan naki”
Babarsa?, kenan ya na da ‘yan uwa, to duk yanda aka yi ya san da zaman wannan ɗan uwan nasa. Kuma kafin ta ƙara cewa komai, aka ƙwanƙwasa ƙofar falo, ita ce ta bada izini, me gadin gidan Ilu ya shigo, hannunsa riƙe da ledojin abincin da aka kawo daga restaurant ɗin da suka saba kawowa Kuliya abinci. Har cikin falon ya shigo, ya aje mata abincin a gabanta, sannan ta sallame shi.
“Ki zauna mu ci abinci, sai ki wuce”
Ba musu Rahila ta amince, ta zauna har Mishal ta miƙo mata abincin, ita kuma Mishal ɗin ta miƙe, ta shiga neman Ayra, har ta samota a kitchen, ba ta fita ba sai da ta bi kitchen ɗin da kallo, babu komai a ciki sai coffee maker da kuma stove, sai kayan shayi. Ko da ta buɗe firdge ma duka kayan gwangwami ne a ciki.
Ba tare da ta taɓa komai ba, ta fito ta dawo falo ta shiga cin abincinta tana bawa Ayra.
Rahila sai satar kallonta take, wato kowa da kalar yarintarsa, ita kuma wannan kalar tata kenan.
Sai ƙarfe 09:00 dai-dai Kuliya ya kamo hanyar barin headquarter, kuma kai tsaye gidan Anna ya nufa.
“Ɗazu Rahila take faɗa min cewar yarinyar tana da kirki, dan bata barta ta dawo ba ma sai da suka ci abinci”
Cewar Annan, bayan ya isa gidan. Girar Kuliya ta haɗe guri guda, alamun kokwanto.
“Wacece Rahila?”
Anna ta yi ‘yar dariya.
“Me aikina”
“Oh na gane”
Kafin kuma ya sake cewa komai, Siyama wadda ta dawo gidan Anna a yau da safe ta bayyana a falon, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai, dan sai a yanzu ma maganar da ya saurara tsakaninta da yayarta ta faɗo masa a rai.
Anna ma binta da kallo ta yi, tana mamakin irin halin Siyaman, zuwa yanzu ya kamata a ce ta cire Kuliyan a ranta, tun da ta riga da ta ji cewar ya yi aure, amma duk da haka ba ta haƙura ba, neman wata hanyar da za ta cusa kanta gareshi ma take.
Cike da so da ƙauna Siyama ke kallon Kuliya, don ba za ta iya kwatanta yanda zuciyarta ke fama da ciwon sansa ba, a koda yaushe cikin raunata zuciyarta yake, amma hakan ba ya hana sansa ƙara ninkuwa a zuciyar tata, a duk sanda zai yi wani abu don ya bata haushi, to a lokacin yake ƙara burgeta.
Kanta a ƙasa ta kama hanyar shiga kitchen, ba wai dan akwai abun da za ta yi a can ɗin ba, sai dan kawai ta shiga kitchen ɗin ta laɓe, ko za ta samu damar sauraron muryar sahibin ranta.
Kuliya ya kamo hannun Anna ya matse, a sanda ya tabbatar da Siyama ta bar falon, jin hakan yasa Anna ta tattara gaba ɗaya hankalinta kansa. Ya ɗaga kafaɗarsa, sannan yace.
“Anna… Yau na ga wata me kama da Mommana, me kama da Zaid ɗina, kuma me kama da ni!”
Wani irin shiru ne ya ratsa falon, yayin da babu ƙarar abun da ke tashi sai na tv dake a kunne, sai kuma ƙarar acn dake fita a hankali, kuma da a ce Kuliya ya kasa kunne sosai, da ya ji sautin bugun zuciyar Anna, yanda take kallonsa kawai shi ne zai shaida masa kalar tashin hankali da mamakin da take ciki.
Siyama dake kitchen ta ɗora hannunta a kan bakinta, yayin da zuciyarta ke tambayarta; shin da ma Kuliya na da wasu ‘yan uwan bayan Anna?, ita dai haka ta taso ta ganshi a gidan Anna, kuma ce mata aka yi maraya ne da Annan ta samoshi a tsohon gidan marayun da ta taɓa aiki.
Shekarata 2000
Aliyu ne zaune kan wani benci da ke Garden ɗin gidan marayun da aka kaishi, matar da ya saba da ita cikin kwana uku kacal me suna Rahama na aikin share garden ɗin, jifa-jifa Rahaman da tace ya riƙa kiranta da Annan ke masa hira.
Sai dai shi kuma gaba ɗaya hankalinsa ba ya kanta, hankalinsa ya karkarta kan ɗan uwansa da ya shafe kwana uku ba tare da shi ba.
Babu kowa a garden ɗin, daga Annan sai shi, saboda gaba ɗaya yaran gidan na ajin ɗaukar karatun Alkur’ani.
Wata iriyar ƙara da ta cika wurin ce ta sa Anna da Aliyu firgita, a kiɗime suka dubi ginin wurin. Wanda ke taci da wuta.
Wata kalar ƙara haɗe da salati Anna ta saki, tunawar da ta yi kowa na gidan na cikin ginin, babu kowa a waje sai ita da. Wannan ɗan marayan Allahn.
A dugunzume ta ja hannun yaron suka yi waje, sannan ta shiga neman ɗauke, har aka samu wanda ya kira ‘yan kwana-kwana, aka zo aka kashe wutar, amma babu wanda ya tsira a cikin gidan, tun daga kan yaran gidan har ma’aikatan.
Ba Anna kaɗai ba, hatta da Aliyu da bai jima da zuwa gidan ba sai da abun ya taɓashi, haka gwamnati da sauran masu faɗa a ji suka riƙa sintiri a gidan marayun, kafin daga bisani aka rufe shi.
Tun bayan faruwar lamarin Anna ta ɗauki Aliyu suka koma gidan wata ƙawarta a nan garin Kano, kasancewar da ma da ta zo garin a nan ta sauƙa.
Bayan da ta gama haɗa kuɗaɗenta na mota ta ɗauki Aliyu suka koma mahaifarta Abuja, inda mijinta da ‘yan uwanta suke.
Da ma can nemawa mijinta kuɗin da za’a masa tiyata ne ya sa ta zo garin kano neman aiki, har Allah yasa ta samu a wannan gidan marayun.
Kai tsaye gidan mijinta ta wuce da Aliyu, kuma da isarsu ta zauna ta masa bayanin inda ta samu Aliyu, be musa mata ba, haka ya amince da zaman Aliyun tare da su, ya tiƙe Aliyu kamar ɗan da ya haifa, kasancewar Allah bai taɓa basu haihuwa ba. Haka Aliyu ya ci gaba da zama a gidan Anna. Wadda ita ce ke kula da kaf nauyin gidan nata, kasantuwar shi mijin nata ba shi da lafiya, har makaranta ta saka shi, bayan da ta samu aikin dafa abinci a wani restaurant, da albashin da suke bata take kula da kaf matsalosalun gidanta.
Anna ita ce wadda ta ƙarawa Aliyu sunan Bhici a gaban sunansa na makaranta, kasacewar mijinta hifaffen garin Bhicin jahar Kano ne. Shi kuma mijin nata shi ne yake kiran sa Kuliya, saboda yace halayensa kaf irin na wani ƙaninsa ne da ya rasu, kuma sunan kanin nasa Kuliya!.
Har zuwa lokacin Zaid na maƙale a ran Aliyu, sau tari yakan keɓe kansa ya sha ƙuncin kewar yayan nasa. Da haka har ya kwashe shekaru biyar tare da su Anna, a cikin wannan shekaru biyar da suka shuɗe, Allah ya yi wa mijin Anna rasuwa, sakamakon jinyarsa ta ciwon ƙoda da ya kasa sakun sauƙinta.
Haka Anna ta ƙara rungumar Aliyu a matsayin wanda ya rage mata, ta manta da cewar shi ba ɗanta ba ne, ta manta da cewar ba ita ta haifeshi ba, ganin bayan mijinta da ‘yar uwarta ba ta da kowa, kuma ga shi mijinta ya rasu, sai ƙanwar tata da kuma shi Aliyun.
Lura da Anna ta fara yi da yanayin damuwar da Kuliya ke ciki ne ya sa ta ritsa shi da tambayoyi, har ta samu nasara a kansa, ya bayyana mata abun da ke cin ransa.
Da haka ta masa alƙawarin za ta je har Kano tare da shi don su duba ɗan uwansa. Sai de me?!. A sanda suka isa Kano suka je gidansu Aliyu na da, basu iske kowa a cikin gidan ba, hakan ya sa Aliyu da kansa ya shiga gidansu Naufal ya tambayi Maman Naufal ɗin, shin ta san inda ɗan uwansa yake?, kuma Maman Naufal ɗin ce ta sanar masa da cewar ai rana ɗaya suka tashi suka ga babu Zaid ya gudu.
Jiki a saɓule cikin tashin hankali da sallalami Anna ta dawo Abuja da Aliyu, kuma tun daga lokacin yanayinsa na shiga ƙunci ya ƙaru fiye da da. Babu yanda Annan ba ta yi da shi ba, kan ya dawo yanda yake amma ya ƙi. Har ta haƙura ta zubawa sarataura Allah ido.
Bayan da Kuliya ya kammala secondary, Anna ta ƙuƙuta ta sa ma masa gurbin karatun diploma a wata makaranta dake cikin garin Abuja. Bayan ya kammala diplomar ne ya shiga fafutukar neman aikin da suka taso cikin burin yinsa shi da ɗan uwasan, aikin da Momma ta ƙarfafa musu gwiwa a kai, tun suna ƙananu suka yi wa kansu alƙawarin yin aikin DSS!.
Sai da ya gama shan wahalar neman aikin, kafin Allah ya sa wani ɗan uwan mijin Anna ya kawo masa offern aikin DSS ɗin. Da an ce mutum na da hannaye shida, da Kuliya ba zai yarda ba, amma a sanda aka ba shi offern zai iya cewa ya ga hannayensa sun nunku daga biyu zuwa shida wajen karɓar takardun, ya yi matuƙar farin ciki da samun aikin.
Kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga aiki gadan-gadan, bayan da aka musu training, ƙwarewarsa kan aikin da kuma gaskiya da maida hankali ne yasa shi samun nasarori da dama, tare da samun ƙarin girma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.