Da gudu motar Kuliya ke tafiya a kan titi, yayin da Mishal ke zaune a gefensa, kayan da suke jikinta ɗazu su ne a yanzu ma, sai dai wani baƙin gyale da ta ɗora a kanta, hanya kawai take kallo tana tuna abun da ya faru ɗazu, yanda Kuliya ya matseta a cikin jikinsa, da yanda damuwa a kulawa suka bayyana ƙarara a cikin muryarsa, abun ya burgeta ya kuma bata mamaki, ba ta taɓa ɗaukan cewa Kuliya na ɗaya daga cikin irin waɗanan mutanen ba.
Kuliya ya juyo ya kalli side ɗinta a hankali, akwai wani. . .