Some people are your happy pill, no matter how sad you are...
Brickhall school, Kaura District, Abuja.
RABI'A POV.
Za ta iya!, tabbas za ta iya. Wannan shi ne abun da take faɗawa kanta, a dai-dai lokacin da take tsaye a filin ball ɗin makarantar, sanye take cikin kayan ball ɗin da Mishal ta ba ta jiya, a cikin filin kuma akwai wasu 'yan mata guda biyar, waɗanda su ma ke sanye cikin kalar nasu kayan wasan ball ɗin.
Daga can wajen ragar filin kuma, Mishal ce tsaye, ta yi ƙuri da idonta a. . .