A hankali Mishal ta shiga matsa gurin tana masa tausa, idonsa a lumshe ya ɗaga kannsa sama, hakan ya sa kansa ya karu da jikinta, ita ma idon nata ta lumshe, dan ta ji sak wannan yanayin da ta taɓa ji a sanda ya rungumeta. Ci gaba ta yi da masa tausar, kafin muryarta ta fito a hankali, kuma har lokacin idonta a lumshe yake, kamar yanda nasa suke a lumshe.
“A duk sanda za ka yi fushi. To wannan kake buƙata!”
Kafaɗar tasa ya motsa, hakan yasa ta buɗe idonta.
“Shin za ki kasance tare da ni a duk sanda zan yi gushi?”
Wani abu me kama da farin ciki ya motsa a ƙirjin Mishal. Hakan ya sa ta kuma lumshe idonta tana danna masa kafaɗar.
“Insha-Allah”
Allah ne kaɗai ya san yanda abun da take masa yake sanyaya zuciyarsa, ya ji duk wata damuwa da ɓacin ransa sun bi iska.
A hankali ya buɗe idonsa, sannan ya janye kansa daga jikinta, hakan yasa ita ma ta buɗe idonta, sai ta ga ya na janyowa littafinta.
A kan idonta ya buɗe littafin, sannan ya tsaya nazartar problem ɗin, kafin ya shiga mata solving. Cikin abun da bai fi minti uku ba, ya gama mata, kuma har lokacin tana masa tausar.
“Nagode”
Ta faɗi a saitin kunnensa, ya ɗaga hannunsa na dama ya ɗora a kan nata dake kan kafaɗarsa. Hakan ya sa Mishal jin wani abu me kama da shock ɗin wutar nepa ya ratsa fatar hannunta.
“You are welcome!”
T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja
10:00 PM
RAJA POV.
“Zaid”
Rhoda ta kira sunansa, hakan ya sa ya ɗaga haɓarsa daga hannunsa da ya yi tagumi, ya juyo ya kalleta, zaune yake a kan kujerar dake ɗakinsa, gaba ɗaya tunani ya hana shi sukuni, ya kasa gane abun da ya kamata ya yi. Kallon Rhodan ya yi na ‘yan wasu sakkani, sanye take da pyjamas iri na jikinsa, hannunta a dama riƙe da trayn abinci. Sai kuma ya juya ya ci gaba da kalon ƙofar bathroom, kamar me jiran fitowar wani daga ciki.
Rhoda ta girgiza kanta ta tako har gabansa, zama ta yi a kusa da shi, sannan ta aje taryn hannunta a kan coffee table, ta dafa kafarsa ta dama tana kallon gefen fuskarsa.
“Me cece damuwar?”
Hannunsa ya sa ya shafa gaba ɗayan fuskarsa, sannan ya sosa kansa.
“Wani tunani kike ga Ammata za ta yi a kaina?”
Rhoda ta yi murmushi.
“Dude! Babu macen da ta isa ta ce bata sanka, baka da wani aibu, look at your self Bro, you are dazzling, smart, athletic, stylish, chaming and elegant!”
“Ummm!, Yaushe ƙanwata ta girma haka?”
Ya tamabaya yana wani murmushi ɗan guntun murmushi, Rhoda ta yi murmushi tana kwantar da kanta a kafaɗarsa. Sun ɗan ɗau lokaci a haka, kafin ta ɗago da kanta ta na ɗaukar trayn dake ɗauke da abinci.
“Yanzu dai ka ci abinci”
Ita da kanta ta shiga bashi a baki yana ci, don zuwan nata ya sauƙa-ƙa masa ruhi, saɓanin da da komai ya jagule masa. Maganarta ta ba shi ƙwarin gwiwa sosai, kuma ya ji cewar tabbas, babu abin da zai hana rabi’a ta so shi.
Brickhall school, Kaura District, Abuja
RABI’A POV.
“…Seesee!”
Mishal ta kirata, ganin gaba ɗaya hankalinta ba ya kanta, tun ɗazu take ta famar mata hira, amma ba ta amsa mata, hakan ne ya ankarar da ita cewar Adawiyyan ba ta cikin hayyacinta. Firgi-git Rabi ta kalleta.
“Ummm”
Ta amsa tana kallon Mishal ɗin, Mishal ta kalleta cikin nazari.
“Ba ki da lafiya ne?”
Rabi’a ta girgiza kanta.
“Lafiya ta ƙalau.Tun rannan na ce miki ki riƙa ɗaura ɗankwali ko hula. Me ya sa bakya sakawa?”
Ta faɗi cikin son bagarar da wancan zancen, don Mishal ba za ta iya mata maganin damuwar da take ciki ba, ga shi yau monday, tarradaddinta shi ne yanda za ayi ta haɗu da Raja, ta na son ganinsa, amma kuma wani ɓangare na zuciyarta ba ya maraba da hakan.
Da yake ita ma Mishal ɗin wasu lokutan ba wayo ta ci ka ba, sai ta shafa kanta, ta na sinne kan cikin alamun rashin gaskiya, saboda tun rannan Anti Adawiyyan ta ce mata ta riƙa saka hula ko ɗankwali, don a yanzu ta zama matar aure, kuma sai ba ta yi hakan ba.
“Na zo da hular fa. Ba ri na saka”
Ta faɗi ta na jan jakarta, tare da buɗeta, wata baƙar hular sanyi ta fitar daga cikin jakar, sannan ta saka a kanta.
“Ko ke fa, ai kin fi kyau a haka”
Mishal ta ɗan yi murmushi.
“Kowa a class ɗinmu ya na ta magana a kan ball ɗin da kuka yi rannan, yaushe za ku sake?”
Rabi ta ɗan yi murmushi, don ta ɗan fara samun sauƙi a ranta.
“Duk sanda kuka saka rana, amma ban da yau”
Daga haka suka shiga hirar ball, kafin ɗaya daga cikin masu aikin shara a makarantar ta zo kiran Rabi’a, kan ta zo za ta yi aiki a ɓangaren kwanan ɗalibai.
Wai hausawa suka ce rashin sani ya fi dare duhu, domin da ace ta san abun da zai iya faruwa a wannan tafiyar tata, da ba ta fara ba, domin babbar ƙaddarar rayuwata ta faru ne ta sanadiyyar wannan aikin da aka sakata a wannan lokacin.
Haka suka yi sallama, Rabi ta tafi ɓangaren kwanan ɗaliban ta fara aikin sharar, aikin yau har ya fi na kullum, don ba ita ta gama ba sai wajejen ƙarfe 5, kuma bayan ta gama da can ta dawo ɓangaren ajujuwa, zuwa lokacin an jima da tashi, haka ta bi aji bayan aji ta share ta goge, har lokaci ya ƙure mata, don ba ta gama ba sai 7.
Wani abu sabo da ba ta taɓa yinsa ba, shi ne kaiwa magariba a makarantar, duk da akwai mutane a cikin makarantar, don akwai masu kula da ɗaliban da suke makarantar kwana, ga shi gaba ɗaya ta gaji, haka ta fito a gajiye tiƙis.
Sai da ta ɗan tsaya ta kalli ƙofar estate ɗin su Raja, ta cikin hasken fitilun da aka kunna ta ko ina a layin, sannan ta kama hanyar fita zuwa babban titi.
Yanayin tafiyarta ne kaɗai zai tabbatar maka da gajiyar da ta yi, kamar daga sama ta ji ƙaran harbi a bayanta, hakan ya sa wani abu ya yi ƙulululu!, a cikinta, tsoro mara adadi ya mamayeta, idanuwanta suka zaro waje saboda tsoro, kamar kwaɗon da mota ta take shi a kan titi, haka ta juyo a tsorace ta kalli bayanta.
Wani irin bugu da zuciyarta ta yi ya sa ta dafe ƙirjinta da sauri, don ji ta yi kamar zuciyar tata za ta fashe ne lokaci guda, nan take ta ji kanta ya sara, wani gumi da ba ta san ta inda yake fita ba ya jiƙa jikinta sharkaf, ta cikin waddataccen hasken da ya haske ko ina, ta ga RAJA tsaye a kan wani mutum, hannunsa na dama riƙe da bindiga wadda ya yi pointing ɗinta kan mutumin dake yashe a ƙasa babu rai, alamun dai shi ne ya harbin, wani irin yamutsawa cikin ya yi, hakan ya sa ta rafka wani uban salati.
“Innallillahi wa inna ilaihi raji’un!”
A firgice Raja ya ɗaga kansa ya kalli setin inda ya ji salatin cikin muryar Rabi’a, hasken fitilun wurin ya haske masa fuskarta tar, saboda har ya na iya ganin gumi da hawayen da suka jiƙa fuskarta.
Karo na farko a rayuwarsa ya saki bindiga daga hannunsa, a karo na farko ya yi na damar karɓar wannan assignment ɗin, a karo na farko a rayuwarsa tsoron wanke kansa a gaban wani ya kama shi. A dai-dai lokacin Rhoda, Alandi, Jagwado da Zuzu suka iso wurin cikin gudu, su ma a tsorace suke kallon Rabi’a, wadda ke kuka tana girgiza musu kai, sai kuma ta juya da gudu tana fashewa da kuka.
“Raja ka bita ka mata bayani”
Rhoda ta faɗi hankali a tashe, cikin sanyin jiki Raja ya girgiza mata kai ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama. Ko yau ma sai da ya fito ya tsaya a ƙofar estate ɗinsu ko zai ga wucewarta, amma haka ya tsaya a wurin har na tsawon awa biyu, amma babu ita babu dalilinta, hakan ya sa ya ɗauka cewar ba ta zo ba.
Haka ya koma gida cikin rashin jin daɗin zuciya, ba don ransa na so ba, suka shiga dudduba makaman da suka karɓa a wurin wannan mutumin shi da su Rhoda, kuma a lokacin kamar da aka ce ya kalli window ya hango inuwar mutum. Hakan tasa ya tashi ya fita waje don ya duba, kamar yanda ya yi zato, ɗan leƙen asiri ne aka turo musu, daren gudu suka shiga yi a layin shi da mutumin, har zuwa lokacin da Allah ya ba shi iko ya harbi mutumin, ashe rabom Rabi’a za ta gani ne.
“Duk abin da zan faɗa mata yanzu ba za ta fahimta ba. May be next time?”
Ya yi maganar cikin raunin zuciya, kuma ya na gama faɗin hakan ya juya ya fara tafiya.
Abun da be sani ba shi ne, da ace ya bi Rabi’a a wannan lokacin, da wata ƙaddarar ba ta faru ba, wata ƙaddara da za ta tarwatsa komai, ta kuma zama sanadiyyar shiryuwar wasu lamura.
Don a wannan juyawar da ya yi, wata mota ƙirar Lamborghini ta wuce ta gefensa. Har su Rhoda na tare gawar mutumin dake yashe aƙasa, gudun kada me motar ya samu danar ganin gawar.
Sosai Rabi ke kuka, zuwa lokacin ta dena gudun, tafiya kawai take, ba tare da tasan inda take cilla ƙafarta ba. Wai me ya sa ne?, me ya sa ita ba ta da sa’a a rayuwa?, me ya sa komai yake cakuɗe mata?, shin sai yaushe ne za ta saku dawamammen farin ciki?, sai yaushe?, sai yaushe?.
Ta na cikin waɗanan saƙe-saƙen nata, wata mota ta tsaya a bayanta, kuma duk da ta ji kamar tsayuwar mota a bayanta bai sa ta waiga ba.
USMAN POV.
Shi da abokansa biyar ne ke cikin sabuwar motarsa ƙirar Lamborghini, Bash, J-boy, Jaz, Bareeki sai kuma shi kansa. dawowarsu kenan daga wani club, inda suka je suka yi tatul a can, kuma yawon shaɗancin nasu ne ya biyo da su ta Joy Emodi CI.
“Guys! Kun ga wata can!”
Cewar Bareeki ya na nuna wata yarinya dake tafe a gefen titi, yanayin tafiyar yarinyar kaɗai zai sa ka fahimci cewar ba a hayyacinta take ba, Daga gidan ba ya na motar Usman ya furzar da hayaƙin shishar da ya shaƙa daga bakinsa, sannan ya furta abun da ya zama sanadiyyar faruwar ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta a cikin wannan daren.
“Sanƙamoma mana ita!”
Su duka suka kwashe da dariya, kafin Bareeki ya yi parking motar ba tare da ya kasheta ba, shi da J-boy suka fita daga motar, suka shiga bin yarinyar a baya suna dudduba layin, ko za su ga wani, sai da suka tabbatar da babu wanda ke ganinsu, kafin suka yi sauri suka suntumi yafinyar, Bareeki ya riƙe ƙafafunta, J-boy kuma ya riƙe kafaɗunta yana rufe mata baki, suka yi maza suka dannata a mota, da mugun gudu suka bar layin. Kai tsaye suka nufi gidan Usman ɗin Kubwa.
MISHAL POV.
Yau a gajiye ta dawo gida, hakan ya sa tana yin wanka ta yi sallah sannan ta kwanta don ta huta, ba tare da ta ankara ba bacci ya kwasheta. Ba ita ta farka ba sai ƙarfe huɗu, haka ta tashi jiki a mace, saboda baccin yamman da ta yi, banɗaki ta shiga ta yi brush, haɗi da alwala, ta futo ta yi sallah.
Saboda yunwar da take ji tana idar da sallahr ta wuce kitchen, ba za ta iya jira sai ta girka wani abu ba, don haka ta ɗauki youghurt da cake, ta zauna ta ci har ta bawa Ayra.
Bayan ta kammala ta tashi ta shiga share gidan, kuma tana cikin sharar falon ne ta ji an turo ƙofar falon, hakan ya sa ta ɗago daga sunkuyen da take, ta kalli ƙofar falon, mata biyu ne suka shigo, ɗayar kawai ta iya ganewa, ita ce wannan wanda Annan ta kira da ƙanwar Kuliya. Amma ba wannan ne abun dubawar ba, kallon da ɗayar ke mata ne abun tuhuma. Saboda wani irin kallo ne da ta saba samun irinsa daga wurin Hajjara, wato kallon tsana.