KULIYA POV.
“Abu Aswad. Magungunana sun ƙare, please ka siyomin idan ka fita”.
Abun da ta faɗa masa kenan da safe, kuma a lokacin sai ya aje mug ɗin hannunsa wanda yake ɗauke da coffee me zafi, ya kalleta, sannan ya kalli takardar hannunta, hannunsa ya kai ya karɓi takardar, kafin ya karanta, sunayen magunguna ne guda biyu kacal, kansa ya ɗan karkatar gefe yana kallonta. A gefe guda kuma ya na shaƙar ƙamshin ƙwan da ta gama soyawa a kitchen, wanda ta haɗa sandwich da shi, sai da ta masa bismillahr sandwich ɗin, amma ya. . .