Skip to content
Part 33 of 35 in the Series Labarinsu by Salma Ahmad Isah

She doesn’t need to be your whole world. She just wants to know that she holds a special place in it. That’s all

KULIYA POV.

“Babu zafi yanzu?”

Cewarsa ya na kallon Mishal, wadda idanuwanta suka yi jajir, saboda kukan da ta sha, kuma har zuwa lokacin ba ta dena hawaye ba, sai jan zuciya take.

Zaune take a kan wata kujera dake cikin permacyn da ya tsaya siya mata magani, bayan da suka dawo daga asibiti. Shi kuma ya ɗan sunkuya a saitin fuskarta ya na kallonta, a hankali ta gyaɗa kanta tana jan hanci, sai shi ma ya gyaɗa nasa kan.

“Then tashi mu koma gida”

Ya faɗi yana miƙewa, tare da miƙa mata hannunsa, ta kalli hannun nasa, sannan ta kalli fuskarsa, ba ta taɓa zaton cewa son Kuliya take ba sai yau! Yau ɗin da kishi ya rufe mata ido har ta aikata abun da ba ta taɓa zaton za ta iya ba. Sai ta yi ƙoƙari ture wannan tunani, ta ɗago da nata hannun, ta ɗora a kan nasa, a hankali shi kuma ya naɗe natan cikin nasa.

Mishal ta lumshe idonta, ta buɗe, saboda wani ɗumi da ya ratsata, ɗumin hannunsa ne ya ratsa har tata fatar, a hankali Kuliya ya ɗagota daga zaunen da take, sannan ya riƙe hannunta da kyau ya na jawota jikinsa, hakan ya sa Mishal riƙewa wata iska a maƙoshinta, ta juyo ta kalleshi, a sanda shi ma yake kallonta.

Idanuwansa kaɗai sun isa su bayyanar da gajiyar da yake ɗauke da ita, kuma bayan gajiyar ma da alamun yunwa. Ta haɗiye yawu, a lokacin da suka fara tafiya a tare, don rabin jikinta yana jikinsa.

Ko da suka shiga mota ma ba gida suka wuce kai tsaye ba, sai da ya tsaya a wani super market ya sai mata chocolate.

“Na gode!”

Ta faɗi cikin muryarta da ta gaji da kuka, a karo na farko tun bayan sanin Kuliya da ta yi, ta ga ya yi wani abu me kama da murmushi, dan wannan ba murmushi ba ne, kuma dai kamar murmushin. Ita ta na mamakin halinsa, ɗan uwansa sam ba haka yake ba, su na tafiya a mota, Kuliya ya jefo mata tambayar da ke ci masa rai tun bayan ganinta tare da wannan me kama da shi ɗin.

“Hafsat! Wacece wannan wadda na ganku tare da ita?”

Mishal ta yi murmushi tana ɓare ledar chocolate ɗinta.

“Yayata ce, Anti Adawiyya!”

Ƙiiiii!, kake ji ƙaran sautin birkin da Kuliya ya taka, gabansa na wani irin matsanincin bugu ya juyo ya kalleta, ita ma ta ɗa firgita, dan ta kai chocolate ɗin bakinta kenan ya taka birkin, hakan ya sa chocolate ɗin ta gogi gefen bakinta, duk da halin ruɗu da Kuliya ke ciki sai da ya yi dariya a ransa, ganin yanda chocolate ɗin ta gogu a gefen bakinta, abin dariya!.

“A ina kika santa?”

“Aikin shara take a school ɗinmu”

Kuliya ya juya ya kalli gefen titi, kamar me neman wani abu.

“Shin kin san wani abu game da ita?”

Mishal ta girgiza kanta.

“Ni kaina a sanda na fara ganinka sai da na yi mamakin kamar da kuke da ita, amma a sanda ta bani labarinta sam ban ji wani abu da ya danganceka a ciki ba”

Kuliya ya dafe kansa.

“Kin san gidansu?”

Ya tambaya ba tare da ya ɗago kansa ba, ita ma sai ta girgiza kanta.

“Ko unguwarsu ban sani ba”

Ba zai iyu ba, babu ta yanda za ayi a ce suna kama irin haka ba tare da wani dalili ba, gaskiya ne yarinyar tana kama da shi, zai iya yiwuwa ta zama ɗaya daga cikin ahalinsa, ya kamata ace ya yi wani abu a kai.

“Kuma akwai!…”

“Ya isa Hafsat, kaina ba zai iya ɗaukan wani batun ba, please!”

Ya yi saurin katseta, ya na yiwa motar key, Mishal ta taɓe bakinta cikin halin ko in kula, da ma so take ta faɗamasa cewar akwai wani me kama da shi again, amma tun da ya dakatar da ita ai shikenan, shi ya jiyo.

Kuliya na tuƙa motar ya na hasaso yadda za ta kaya tsakaninsa da su Karima, don basu ci bilis ba, sai ya ɗauki mataki a kansu.

Chikakore, Kubwa, Abuja.”

05:30 AM.

Gate ɗin ɗaya daga cikin maka-makan gidajen dake layin ne ya buɗe, me gidan ya fito, sanye cikin jallabiya, tafiya ya fara yi cikin sauri, da alama masallaci zai je. A hanya suka haɗu da maƙocinsa. Bayan sun gaisa sai suka ɗunguma zuwa masallacin duka.

Tun daga nesa suka hangi wani abu a gefen hanya, nannaɗe cikin wani abu haka kamar bargo. Tar suke iya ganin abun ta cikin hasken fitulun da suka haska layin ta ko ina.

Alhaji Bukar ne ya fara razana, lura da ya yi abun kamar gawar mutum ce a ciki.

“Ahaji Hadi! Anya kuwa wannan ba gawa ba ce”

Alhaji Hadi ya kalli Alhaji Bukar cike da tsoro, tsayawa suka yi suna kallon abun, cikinsu an rasa wa zai duba ya gani, suna cikin hakan Allah ya jefo wani moƙocin nasu, ganinsu a wurin ya sa ya tambayesu shin; lafiya?, shi ne suka bayyana masa abun da suka gani, duk kuwa da shi ma ya ga abun.

“To ai ba tsayuwa ya kamata mu yi ba, kamata ya yi mu duba mu ga mene a ciki, kafin mu san matakin ɗauka”

Da farko ba su yarda da shawarar tasa ba, amma daga baya sun amince, haka suka zagaye abun da suke da tabbacin mutum ne a ciki, da farko sai da suka ƙara tsorata, ganin jini a jikin bargon, kuma ba su ƙara tsorota ba sai da suka yi arba da abin cikin bargon.

“Innallillahi wa inna ilaihi raji’un!”

Kusan a tare suka furta hakan, sakamakon ganin gawar matashiyar yarinya, babu sitira a jikinta, ga gefen fuskarta da aka mata wani faffaɗan rauni, sai kanta da ya fashe ya na zubar da jini.

A wannan ranar:

Brickhall school, Kaura District, Game Village, Abuja.

10:40 AM.

A karo na biyu, Fu’ad ya girgiza kansa, sakamakon bayanin da Principle ɗin makarantar ke masa, game da tambayar Rabi da ya yi, ba wannan ne ya fi ɗaga masa hankali ba, abun da ya fi ɗaga masa hankali shi ne; yau da safe Saratu ta kira shi ta na ta rinjin kuka, babu yanda bai yi da ita ba, dan kwantar da hankalinta amma ta ƙi saurarensa, har cewa ta yi za ta je makarantar ta duba da kanta.

“Nagode ranka ya daɗe”

Ya na faɗin hakan ya miƙe ya fice daga office ɗin, jiki a tsaɓule ya shiga motarsa, kai tsaye ya nufi Suleja.

A inda ya saba aje motarsa ya yi parking, wato bakin layinsu Saratun, ya fito daga motar tasa ya shiga cikin layin a ƙafa, a ƙofar gidan nasu ya tsaya, sannan ya kira Saratun ya sanar mata da zuwansa. Ko minti ɗaya ba ta ƙara ba sai ga ta ta fito a rangauce, kallo ɗaya za ka mata ka gano tashin hankalin da take ciki, yau ko Mama ce ba’a ganta ba tashin hanlalin da za ta shiga sai haka, babu abun da ya fi ɓata mata rai irin yanda Habiba ta basar da lamarin, ta shiga harkokin gabanta, don a yanzu haka ma ta na cikin gidan ta na suyar funkasonta hankali kwance , kamar tsumma a cikin randa, bayan ta tura ‘yar mutane aikatau an rasata.

“Me suka ce? Ka ga Rabin? A ina ta kwana?!…”

Ta jero masa tambayoyin a birkice, idonta kawai yake kallo, yanda ya yi jajir, ba lalle ma a ce ta yi bacci daren jiya ba.

“Sarah, ki kwantar da hankalinki…”

“Fu’ad ka faɗa min gaskiya kawai!”

Fu’ad ya haɗiye yawu, sannan ya sunkuyar da kansa ƙasa.

“Tabbas jiya Rabi ba ta bar can ba sai ƙarfe bakwai na dare, amma sun tabbatar min da bata can…”

Bai kai ga ƙarashe maganar ta sa ba, saboda kukan da Saratun ta sa kamar wanda ya watsawa ruwan asid me zafi a fuska.

KULIYA POV.

A hankali tayoyi motarsa suka tsaya a harabar makarantar Brickhall, kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya fito daga cikin motar, sai da ya tsaya ya ƙarewa gine-ginen makarantar kallo, kafin ya nufi cikin makarantar, sai da ya yi tambaya kafin aka sada shi da office ɗin principal.

“Akwai wata yarinya da take muku aiki a nan, sunanta Adawiyya, shin zan iya ganinta”

Cewarsa, yayinda yake zaune a kujerar tsallaken teburin principal ɗin, mutumin ya ɗaga kansa sama cikin tunani, sannan ya sauƙe kansa.

“Mts!, gaskiya babu me wannan sunan a cikin masu aikinmu”

Kuliya ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama ya na haɗiyar yawu.

“Rabi’a fa?”

Da sauri mutumin ya gyaɗa kansa.

“Eh, akwai Rabi’a a cikinsu, sai dai kuma yau kwata-kwata ba ta zo aiki ba, don har wani mutum daga gidansu ya zo ya ce wai suna nemanta, don tun jiya rabonta da gida!”.

Wani irin ƙara zuciyar Kukiya ta yi, da sai da ya ji a kunnuwansa, ba ta zo ba?, ana nemanta a gida?, to me hakan ke nufi?…

“Laaaa, Abu Aswad!”

Cak, ya tsaya da tafiyar da yake, jin muryarta ta ambaci sunan da ta laƙaba masa, addu’a ya yi ta yi ta kada Allah ya sa su haɗu, amma sai ga shi an samu akasi, shi a yanzu kansa na cikin wani hali, saboda abubuwa sun cakuɗe masa, ya rasa mamakamar zaren, bare har ya san ta inda zai kama don ya fara saƙa mafitar lamarin, zuwansa makarantar ma bai masa wani amfani ba. Sai temakawa da ya yi wurin ƙara dagula masa lissafi.

Juyowa ya yi a hankali ya kalleta, gani ya yi ta ƙara nutsuwa, kamar ba ita xe6 wannan yarinyar me shirinta da aka aura masa ba, yarinyar da ko hula ba ta sakawa idan za ta je makaranta, amma yanzu ya lura da kullum ta na saka hular. Sai dai kuma hular da ta saka ba ta ɓoye raunin dake goshinta ba, kamar yanda ya saba ganinta, fuskar nan a jeme, babu ko kwalli, daga gefenta kuma wata baturiya ce da a shekaru ba za ta wuceta ba.

Da ɗaukinta ta ƙaraso gabansa, bakin nan buɗe ita a dole ta ga mijinta a makarantarsu.

“Wurina ka zo? Ai muna can baya, anti Adawiyya nake ta dubawa, don yau sam ban ganta ba!”

Dammm!, gabansa ya buga, amma sai dake, ya kasa ce mata komai, dan bakinsa ya masa nauyi, ji yake kamarya haɗiyi dutse. Kallonta kawai ya ci gaba da yi, yana saƙa da warwara a zuciyarsa.

“Ko ba wuri na ka zo ba?”

Ta tambaya, wannan fara’ar da take a ɗazu ta na shirin ɗaukewa daga kan fuskarta, sai ya girgiza kansa da sauri ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama.

“Dan ke na zo!”

Daɗi kamar ya kasheta da jin furincinsa, a jiya kawai Allah ne kaɗai ya dan adadin yanda ta kira sunansa a ranta, ita ba ta tabbatar da sonsa take ba sai a jiya, jiyan da kishinsa ya rufe mata ido har abun da ya faru tsankaninta da su Siyama, ya zo ya faru.

“Kin ci abinci?”

Da sauri ta gyaɗa masa kai, idanunta har ƙyallin murna suke, shi ma ya gyaɗa nasa kan.

“Da ma zuwa na yi na ga ya kike. Zan wuce gidan Anna”

Ya zaɓi ya mata wannan ƙaryar ne don kada ta zargi wani abun.

“Zan koma” Ya faɗin ya na shirin juyawa.

“A’a. Ka tsaya ku gaisa da Angelica, kuma ina so na nunawa sauran ‘yan ajinmu kai, rannan na ce musu an min aure, amma babu wanda ya yarda”

Har yanzu dai wannan shiriritar na nan, kuma kafin yace a’a, har ta kama hannunsa ta shiga jansa, sai ya riƙe kalamansa ya shiga bin bayanta.

“Kai shashashu! Na ce muku an min aure kun musa ko? To ga ku ga mijinawa, sai ku tambayeshi ku ji!”

Abun da ta faɗi kenan a class ɗin nasu cikin ɗaga murya, kasancewar lokacin break ne, kowa na harkar gabansa, ido ya dawo kansu gaba ɗaya, sai kallon kallo ake, wasu na mawa mijin Mishal ɗin kallon sani, don ya na musu kama da wannan me sharar, sai masu masa kallon sani, saboda kullum idan an tashi suna ganinsa tsaye a tsallaken makarantarsu, wasu kuwa ma basu san shi ba.

No. 213, Naf belly, Asokoro, Abuja.

“Wallahi Aliyu ba ni da masaniya kan abun da su Karima suka aikata!”

Anna ke faɗin hakan cikin hawaye, bayan da Kuliya ya zo ya na sanar da ita haukan da Karima da kuma Siyama suka je gidansa suka aikatawa Mishal. Kuliya ya kamo hannayenta ya riƙe. Bayan ya bar Brickhall kai tsaye gidan Annan ya nufo.

“Na sani Anna. Na san ba za ki aikasu su yi wa matata haka ba, amma ina son na sanar da ke da ki jawa kowaccensu kunne, kan kada su ƙara taka ƙafarsu cikin gidana, jiya ma girmanki da darajarki suka ci, ba dan haka ba Wallahi ba zan barsu ba”

Anna ta share hawaye.

“Ba komai Aliyu, tashi ka tafi aikinka, zuwa yanzu na san ka makara, ka je kawai, ni na san matakin da zan ɗauka!”

Ya karkatar da kansa gefe.

“Ba za ki dena kukan ba?”

Anna ta ɗan yi murmushi tana share wani hawayen.

“Na dena, ka je kawai”

“Shikenan”

Ya faɗi ya na miƙewa, har ya fice Anna na kallonsa, ta san abun da za ta yi. Don ta zubawa su Karima ido suna ta haukansu ba wai don ba za ta iya taka musu birki ba ne, ba ta san cewa haukar tasu ta ƙamari ba, amma ba komai, Allah ya kaimu gobe, za ta yinwa tufkar hanci.

Vinca Hospital, No.12, Remkom street, Kubwa, Abuja.

Da gudu wata nurse ta fito daga wani ɗaki da aka kwantar da wata mara lafiya da ta baƙunci asibitin nasu a safiyar yau, hannunta na dama ɗore a bakinta, a ƙoƙarinta na tare kukan dake son cin ƙarfinta, ta jingina da jikin bango tana kallon ƙofar ɗakin, a hankali ta zame zuwa ƙasa, kukan da take ta yunƙurin riƙewa ya fito da ƙarfinsa.

Tun da uwarta ta kawota duniya ba ta taɓa ganin tashin hankali irin wanda ta gani yau ba, ta na jin labarin fyaɗe, amma ba ta taɓa ganin wanda aka yi wa fyaɗe ba sai yau, an ce mata idan ta fara aiki sai ta gamu da abun da zai sa ta kuka, a wancan lokacin da aka faɗa mata dariya ta yi, don ita ba ta hango yiyuwar hakan ba, sai a yau ta yarda da abun da aka faɗa mata, kuka take sosai har ta na dafe ƙirjinta.

Ƙofar ɗakin ce ta buɗe, likitan da suka shiga tare da shi ya fito ya na sharar ƙwalla, kafin ya kalli nurse ɗin, shi kansa da ya kwashi tsawon shekaru ya na aikin bai taɓa ganin abu makamancin wanda ya gani yau ba, bare ita da ta ke sabuwa a aikin.

“Ke Sakina! lafiyar ki kuwa?”

Wata ƙawarta ta tamabaya, a sanda ta biyo corridorn ta ga ƙawar tata zaune a ƙasa tana kuka kamar wadda aka yi wa mutuwa, juyawa ta yi ta kalli likitan, shi ma duk jikinsa ya yi sanyi, kansa a ƙasa kamar da aka ce shi ne ya aikata fyaɗen.

Hannunta ta kai ta kamo ƙawar tata tana miƙarta, tare da share mata hawaye, amma Sakinan sai ta ƙwace fuskarta ta na komawa gefe.

“Dan Allah Kausar ki bar ni na yi kuka. Bar ni na koka da abin da na gani. Kausar wasu mazan ba su da adalci, ba su da tausayi!”

Ta ɗaga hannunta tana nuna mata ƙofar ɗakin.

“Shi ga ki ga abun da suka yi wa wata yarinya. A shekaru dai na san yarinyar ba za ta wuce 19 ba, amma ki je ki duba ki ga yanda suka mata fyaɗe cike da rashin imani, mutum biyar Kausar, mutum biyar ko sama da haka ne suka haike mata!.Kuma ba su barta da wannan tambon ba, sai da suka ƙara mata da wasu raunuka a jikinta, gefen fuskarta da kuma kanta duk sun fasa mata, yanzu haka yarinyar ta shiga doguwar suma!”

Ita kanta Kausar ɗin sai da gabanta ya buga da mugun ƙarfi, don za ta iya cewa wannan ɗin sabo abu ne da ya shigo asibitin nasu.

“Me ya sa Kausar?. Me ya sa mu ba mu da ‘yanci?, Kowa sai ya taka mu ya wuce yanda yake so. Me ya sa wasu mazan ba sa ganin mata da kimi?. Me yasa?… Sai zuwa yaushe ne za mu tsira?, sai zuwa yaushe?!”.

<< Labarinsu 30Labarinsu 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×