Washe gari…
07:10 AM.
Mishal ta rufe lunchbox ɗinta, bayan da ta gama jera abincinta a ciki, sanye take da complete uniform ɗinta, ta juya za ta fita daga kitchen ɗin idonta ya sauƙa a kan flask ɗin abincin Kuliya.
Kuliya?!, Sunan ya maimaita kansa a cikin ranta, nan take abun da ya faru a jiya ya dawo mata. A jiyan bayan shuɗewar sakan uku, muryarsa ta katse shirun dake wanzuwa a falon.
“Na ba ki daga yanzu zuwa gobe da safe, ki yi tunani a kai”
Abun da yace kenan, kafin ya saketa a hankali, ya ɗauki plate ɗin da ya ci abinci ya nufi kitchen, hakan ya bata damar faɗawa ɗakinta da gudu, ta sakawa ƙofar sakata. har gari ya waye ta na saƙawa da kuncewa.
Ko da safe da ta tashi ayyukanta ta shiga yi cikin gaggawa, don so take ta yi sauri ta kammala abun da za ta yi don ta bar gidan kafin ya fito, hakan da ta tuna ne ya sa ta zabura za ta bar kitchen ɗin, sai dai kuma fatan ta bai cika ba, don a dai-dai lokacin ƙofar kitchen ɗin ta iyo ciki, Kuliya ya shigo, kamar kullum sanye cikin baƙaƙen kaya.
Kallonta yake cikin wata iriyar siga da Mishal ba ta san ta inda za ta mata fasarra ba, hancinta ta ja, sakamakon murar da ta kamata a jiya, ta haɗiyi yawu da ƙyar. Numfashinta ya kusa ɗaukewa a sanda ya tsaya a gabanta.
“Har kin shirya?”
Ya tambaya ya na kallon hancinta da ya yi jajir, da alama dai mura take.
“Eh”
Ta amsa masa cikin muryar me mura.
“Ba ki da lafiya?”
Ya tambaya ya na duban yanayinta, da sauri ta girgiza masa kai, sai kuma ta gyaɗa kan nata tana shaƙar ƙamshin turarensa da duk murar da take ba ta hanata jinsa ba.
Wani sauti ta ji me kama da na murmushi, hakan ya sa ta kalli fuskarsa da sauri, kuma sai ta ga da gaske ne, Kuliya ne yake mata murmushi, wani abu sabo, wani abu da za ta cewa ba ta taɓa ganinsa a zahiri ba. Kuma murmushin da ya yi sai ya ƙara bayyana mata kamarsa da Adawiyya, haka zalika murmushin nasa ya ƙara bayyana kamar da suke da ɗan uwansa…
Tunaninta ya katse a sanda ta ji sauƙar tafin hannunsa a kan fatar wuyanta, wannan sanyin ya shiga bi ta jijiyon jikinta, hakan ya sa ta ɗan ɗauke numfashinta na wasu sakkani, kafin ta dawo da shi ta na jansa da sauri-sauri.
“Har da zazzaɓi kenan?”
Ya tambaya ya na dawo da hannun nasa goshinta.
“Zan bawa Ibrahim (Drivernta) maganin mura ya kawo miki”
Da sauri ta gyaɗa masa kai tana jan hanci.
“Ban manta ba… Mecece amsata?”
Ta kalli fuskarsa, amma sai ta kasa cewa komai, bakinta ya mata nauyi, kamar wanda ta haɗiyi dutse.
A hankali Kuliya ya ƙara matsawa kusa da ita, sannan ya saka hannunsa na dama ya kewaye ƙuginta, ya haɗeta da jikinsa ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama, hakan ya sa Mishal rintse ido tana kawar da kanta, hannunsa na hagu ya sa ya kamo haɓatar ya juyo da fuskarta.
“Look at me!”
Sai ta buɗe idon nata tana kallon fuskarsa.
“Did you love me?”
Saboda abun da Mishal take ji ba ta san sanda ta shiga gyaɗa masa kanta da sauri ba kuma ta gyaɗa ya fi sau biyar.
“Kin tabbatar?”
“E… Eh!”
Kalaman sun yi wa Kuliya daɗi, hakan ya sa ya yi wani irin murmushi da sai da ya bayyana haƙoransa, kafin ta ɗauke hannunsa daga kan haɓarta, ya dawo da shi gefen fuskarta, yana shafawa a hankali.
“I love you Teddy Bear!”
Ya na kaiwa ƙarshen maganar, ya raba leɓensa biyu, sannan ya sa nata na ƙasa a tsakiya, kafin ya haɗe bakinsa da nata gaba ɗaya.
Abun da ya yi ya sa Mishal ɗaga ƙafarta sama, sannan ta dunƙule hannayenta a kan ƙirjinsa. Ba ta san ma me yake faruwa ba, ba ta san me ake yi a duniyar ba, ba ta san me yake wakana a kitchen ɗin ba, abu ɗaya ta sani, shi ne ita ce riƙe a hannun Kuliya, yayin da hannunsa na hagu ke riƙe da gefen fuskartsa na dama, bakinsa kuma cikin nata, ya na aika mata da wani laffiyayyen kiss.
A lokacin ne aka ƙwanƙwasa ƙofar falon ta can compound, sannan muryar Ibrahim ta biyo baya.
“Ranki ya daɗe lokaci na ƙurewa, ki fito kar mu makara!”.
Time moves slower when you miss somebody.
T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja
RAJA POV.
Yau zaune yake a tsakar gidan, ya na kallon yanda iska ke busawa ta na kaɗa bishiyoyin farfajiyar gidan, a zahiri kenan, amma a baɗini sam ba su yake kallo ba, tunaninsa na can wata uwa duniya, yayin da shi kuma yake wannan duniyar, sati uku kenan rabonsa da farin ciki, sati uku kenan rabonsa da walwala, sati uku kenan rabon da wani abu na fara’a ya gifta a fuskarsa, sati uku kenan da shigar yaruwarsa cikin yanayin tashin hankali da zullumi, sati uku kenan da komai na rayuwarsa ya yi juyin waina a tanda, kuma a cikin wannan satin ukun ne rayuwarsa ta shiga kwale-kwalen katako, wanda ke tangal-tangal a cikin kogin da ke cike da yunwatattun kadogi, a cikin sati ukun nan komai ya cakuɗe masa.
Kuma duk hakan ya samo asali ne ta sana diyyar ɓatan Rabi’a, don zuwa yanzu ya na da tabbacin Rabi’ar ba kawai makarantar ta dena zuwa ba, ɓata ta yi, amma abun tambayar a nan shi ne, ina ta je?, ta na ina ?, shin ta na hannu na gari?, ko a’a, idan ya yi zurfi a tunani irin wannan sai kansa ya kulle, kamar wata ƙofar da aka garƙame da makulli.
“Raja!”
Ya ji muryar Jagwado na kiran sunansa, amma sai ya ƙi juyawa bare ya amsa.
“Raja!”
A wannan karon muryar Alandi ce ta yi kiran, kuma a yanzun ma bai amsa ba.
Kusan a tare suka zauna a kusa da shi, Zuzu a ɓangaren dama, Alandi a kusa da Zuzu ɗin, Rhoda ta zauna a gefensa na hagu, yayin da Jagwado ya zauna a ƙasa ya na kallonsa, kai kace me shirin ɗaukan karatu ne, kansa ya juyo ya kallesu gaba ɗaya, sannan ya ɗauke kai ya ci gaba da kallon bishiyoyin.
“Ka da ka damu Raj. Ka gane ko?. Rhoda ta ce eh… Za ta gano maka ‘yar shilarka. Dan haka kawai ka share”
Kalon Alandin dake wannan batun kawai ya yi, ya kuma ɗauke kai, shi da za su tashi su bar shi shi ɗaya ma da abun zai fi masa sauƙi, dan duniyar ma kanta ji yake kamar babu kowa sai shi kaɗai, kamar a duniyar babu wanda ya kai shi kaɗaici, kamar ma kwanakin ba sa sauri, gani yake kamar a jiya ne Rabi ta ganshi ya na harbin wannan mutumin.
“Zaid!”
Juyowa ya yi ya kalli Rhoda da ta kira sunansa.
“Na ƙara tsananta bincike, ka roƙi Allah ya temakemu mu samota”
A hankali ya sauƙe ajiyar zuciya, kafin a hankali wani damshi ya sauƙo daga idonsa har zuwa ƙasan kuncinsa, wani abu ruwa, wani abu da ba zai iya tuna rabon da su fito daga idonsa ba, amma yau sai ga su a idonsa, yau shi ne yake hawaye saboda wani ɗan adam da ba Rhoda ba, a da ya ɗauka cewa duniyarsa ta mutu gaba ɗaya, bayan Rhoda ba shi da wani abun damuwa, ba shi da wani wanda yake damuwa da shi bayan ita, ba shi da wanda zai bawa kula sai ita, amma yau a kan Rabi sai ga shi ya na hawaye, hawayen da yake san ya yi su tsawon lokaci, amma ya na dannewa.
Gaba ɗayansu suka ci gaba da kallonsa cike da tausayawa, don har wata rama ya yi, ga ɗan duhu da faratrsa ta yi, tsabar tashin hankali, saboda shi gani yake koma miye ya samu Rabi’a shi ne sila.
Rhoda ta dafa shi, kuma kafin ta faɗi abun da ke bakinta ya kwanta a jikinta ya na rungumarta, tare da sakin kuka a hankali, kuka yake sosai, amma kuma ba sauti, sai jijjigar da jikinsa ke yi tare da na Rhoda da ya runguma.
Rhoda da jikinta ya yi sanyi, ta shafa kansa ita ma hawayen na sauƙo mata, tun suna yara sun riga da sun saba da ko kuka tare suke yi, hakan ya sa za ta taya shi jimamin halin da yake ciki. Su Alandi ma gaba ɗaya jikinsu ya yi sanyi ƙalau, kamar wanda suka kwana a cikin fridge.
“Rhoda ki temaka ki nemota…. Rhoda ba zan iya ɗaukar wannan ciwon ba, ba zan iya ba!”
Cikin muryar kuka ya yi furicin kuma a lokaci guda ya na sakin Rhodan, Rhoda ta shafa sumar kansa ta na girgiza masa kai.
“Na maka alƙawarin samo maka ita, ko ina ta shiga a garin Abuja, ka yarda da ƙanwarka ko?”
Ya gyaɗa mata kai.
“To ƙanwarka ba za ta barka ka faɗi ƙasa ba. Zan tabbatar da na nemo maka ita a ko ina take kuwa”
Ƙara rungumarta ya yi ya na sakin wani kukan.
“Rhoda Ina san Ammata, ina santa… Ina santa….. I na… I na…. Santa!”
Rhoda ta shafa bayansa tana gyaɗa masa kai.
“Na sani, na san ka na santa, kuma za ka aureta, da yardar yesu zaka aureta!”
No.181, Guzape, Abuja
10:04pm
KULIYA POV.
A hankali hannunsa ya tura ƙofar shiga falon gidan zuwa ciki, sai da ƙofar ta buɗe gaba ɗaya, sannan ya saka ƙafafunsa ciki, shiga ya yi ya na baza idanuwansa a falon a yunkurinsa na neman ta inda zai hangota, idan ma ta na falon kenan.
A kan kujera 3 seeter ya hangota, ta yi rashe-rashe ta na bacci, ganinta kawai da ya yi a yanzu ya tuna masa da safiyar yau, a lokacinda ya tsinci kansa cikin duniyarta, yanda ya sumbaceta a yau da safe ba ƙaramin saka shi cikin nishaɗi ya yi ba. Sai tunanin abun da ya katse masa nishaɗin safiyar ya dawo masa.
Wannan maganar ta Ibrahim ce ta sa ya saki bakinta a hankali, sai dai kuma bai raba fuskarsa da tata ba, ya na kallon murfin idonta da ta lumshe, a hankali ya janye hannunsa dake kan ƙugunta ya kama fuskarta, sannan ya sumbaci gaban goshinta, kuma sumbatar ce ta sa ta buɗe idonta.
“Ki je Ibrahim ya na jiranki”
Ya furta mata a hankali, kuma ita ma sai ta gyaɗa masa kai kawai, ta na fita daga hannayensa, ta ɗauki lunchbox ɗinta za ta fiti ya kamo hannunta, sannan ya rungumeta sosai a jikinsa, yana jin yanda jikinta ya yi karkarwa a lokacin. Kafin ya saketa ya bata damar tafiya.
Mamaki ne ya kama shi ganin maganin mura da na zazzaɓin da ya aiko mata ɗazu, hannunsa ya kai ya ɗaki kwalar maganin muran dake kan coffee table, idanuwansa a waje yake kallonta daga kwancen da take, ganin abun da ke cikin kwalbar saura rabi.
Kenan duka ita ta shanye?, tab, ai dole ta yi bacci, rabin kwalba fa?, dariya ta kama shi, hannunsa ya kai ya ɗan taɓa fuskarta, amma kamar wanda ya taɓa gawa. Hannunsa ya kai ya kamota ya na zaunar da ita, hakan ya sa ta buɗe idonta a wahalce, ta kuma lumshe idon sannan ta buɗe.
“K… kai… ka…”
Abun da take faɗi kenan, Kuliya bai san sanda ya fashe da dariya ba, maye take tuburan a fili, yau in ba shirme irin na Mishal ba, kusan rabin kwalba fa ta sha?, gaba ɗaya ta kasa zama gu ɗaya, sai layi take tana daga zaunen, ga idonta da take buɗewa ya na lumshewa da kansa.
“Tashi mu je na kaiki ɗaki…”
Ya faɗi ya na gimtse dariyarsa, a lokaci guda kuma ya na kama kafaɗunta, amma sai ta sa ragowar ƙarfinta ta ture shi.
“Kai… Ka… Ka rabu da ni… Ba… Ba ka san… S… San wa.. cece Mi… Mishal ba ko?…”
Sai ta nuna kanta da ɗan yatsa.
“Ni ce… Ce Hafsat… Haf… Hafsatun Aliyuu… hhhhhh!”
Sai ta ƙarashe da dariya, ta guntule dariyar tana nuna shi.
“Kai kuma… Wa… Waye kai?”
Kuliya na murmushi yace.
“Aliyun Hafsat”
Sai ta ƙyasta hannunta.
“Ka… ka ga mun yi ma… Match kenan… Amma me… Ne kake a nan?”
Zama ya yi a kujerar yayin da take kallonsa da lumsassun idanuwanta.
“Wata na zo nema…”
Bai ko ƙarashe ba ta fashe da dariya.
“Haka… Haka wani ma yace min a… A… A makarantarmu, wai… Wai shi ya na neman wani, amma kuma ni na san ni yake nema… Ni fa Cele… Cele ce a makarantar nan… Ko… Kowa ni yake san gani… Kai ma ka na san gani na ko ?”
Ya gyaɗa mata kai, sai ita ma ta gyaɗa nata kan.
“Amma kai… Be kamata ka… Ka ce kana so na ba”
Kuliya na ɗora hannunsa na dama a kan bakinsa yace.
“Amma me ya sa?”
“Saboda ni matar aure ce, mijina sunansa Kuliya… Kuliya… Yaro idan ka shiga hannun Kuliya ko, hmmmm”
Ya ƙara fashewa da wata dariyar.
“Me ya sa kake…. Kake dariya irin haka?”
“Ba dariya nake ba…. Kuka ne”
Sai kuma ita ma ta fashe da kuka harda hawaye.
“Yau ma yayata ba ta zo makaranta ba, ya… Yayata ta de… Dena sona, ba ta so… Sona… Kuliya ne kawai yake… Yake sona… Ka san… Ka san me ya min yau da safe?”
Ta tambaya tana share hawayen fuskarta, kansa ya girgiza mata ya na murmushi.
“A nan”
Ta nuna masa lips ɗinta.
“Annan ya sumbace ne, kamar haka; ummmuah!”
Ta ƙarashe tana furta masa sautin sumbatar da bakinta. Sai kuma ta fashe da dariya.
“Wai jiya cewa ya yi ya ba ni zuwa yau da… Yau da safe na… Na yanke shawara a kan soyayyarsa…”
Sai kuma ta ƙara fashewa da wata dariyar.
“Shashasha bai san cewa tun ba yau nake san sa ba….”
Ta kuma saka wata dariyar, sai kuma ta jingina da jikin kujera, a hankali idonta ya shiga lumshewa, bakinta na motsawa, ta na faɗar wasu kalamai da shi bai ma san ma’anarsu ba.
Ganin kamar shirmen nata ya ƙare ne ya sa shi miƙewa ya ɗauketa duka, sannan ya yi ɗakinta da ita, a kan gadonta ya kwantar da ita, sannan ya lulluɓeta ya fita.
Ɗakinsa ya koma ya yi wanka, ya sauya kayansa zuwa wanda ya saba sakawa na zaman gida a irin wannan lokacin, wato baƙin sweat trouser da kuma baƙar T-shirt.
Kitchen ya fara dubawa ko zai samu abinci, ya tarar da ta aje masa wanda zai iya ci, za ma ya yi ya na ci ya na murmushi a kai a kai, don shirmen nata ba ƙaramin nishaɗi ya bashi ba.
Bayan ya kammala cin abincin ya ɗan taɓa aiki a system ɗinsa, kafin ya fara jin bacci, system ɗin ya rufe, sannan ya nufi ɗakinsa dan ya kwanta, sai wata zuciyar ta raya masa da me zai hana ya je ya kwanta a ɗakinta, wata ƙila ta buƙace shi ko da cikin dare ne.
Ba tare da wani tunani ba ya nufi ɗakin nata, sai ya tarar da ta hargitsa kwanciyar da ya mata ɗazu, ba kamar. Murmushi ya yi ya na gyara mata kwanciya, sannan ya kwanta a gefenta ya na kashe musu wuta.
Janta ya yi jikinsa, sannan ya lumshe idonsa don yin bacci, ba jimawa kuwa baccin ya ɗauke shi, don a gajiye yake, amma kuma baccin nasa bai yi minti goma ba ya farka, saboda wani duka da Mishal ta masa da ƙafarta, sam ya manta da ba ta iya kwanciya ba.
Ƙafafuwan nata ya gyara mata, amma da aka jima sai ta ƙara lafta masa ƙafarta, tun ta na yi ya na gyara mata, har ya gaji ya rabu da ita, haka daren ya ƙare ta na ta bugunsa da ƙafarta.
Da asuba ya farka, hakan ya sa ya tashi ya koma ɗakinsa, ya ɗan watsa ruwa kaɗan, sannan ya sauya kaya ya fita zuwa masallaci, har ya dawo ba ta farka ba, hakan ya sa ya mata tashin duniyar nan amma ko motsi ba ta yi ba, har ruwa ya watsa mata amma kamar an mintsin kakkausa, sai ya ƙyaleta ya koma ya kwanta a gefenta.
Wajejen ƙarfe 09:00 dai-dai wayarsa ta yi ringing.
Cikin bacci ya ji ƙarar, hakan ya sa ya buɗe idonsa, hannunsa ya kai ya ɗauki wayar, sunan ‘Sharon’ ya ga ya na yawo a kan screen ɗin, sai ya ɗaga ya na wani cin magani kamar ta na gabansa.
“Lafiya yau ka makara?”
Sharon ta tambaya bayan sun gaisa, sai da ya juya ya kalli Mishal dake baccinta tsakani da Allah, hankalinta kwance, kamar tsumma a randa, sannan yace.
“Hafsat ce ba ta jin daɗi, zan kaita asibiti”
Sharon ta ƙunshe dariyarta sannan ta ce.
“Allah ya ba ta lafiya, sai yaushe kenan?”
“Gobe”
Ya bata amsa a taƙaice.
“Sai goben”
Ya na gama sauraren hakan ya katse kiran sannan ya aje wayar a inda ya ɗauketa.
“Yau Sir ya na more amarci… Dan haka ba zai fito ba”
Cewar Sharon ta na kallon su Symon, wanɗan da suka zo suka sakata a gaba kan ta kira Kiloya ta ji me ya sa yau bai zo ba. Dariya suka kwashe da ita, daga nan kuma sai aka shiga hira a kan Kuliya da Mishal.
Ya kamata ace zuwa yanzu ta tashi, Kuliya ya faɗi a ransa, ya na kaiwa hannunsa tare da ɗan tattaɓa fuskarta.
“Ummmm!”
Ta faɗi cikin muryar bacci.
“Hafsat”
Ya kira sunan a hankali ya na kallonta, yayin da yake kwance a gefenta.
“Ummmmmm!”
“Ki tashi gari ya waye”
Idonta ta buɗe a kansa, sannan ta ƙara lumshewa, ta kuma buɗewa, kuma a lokacin ne ta gano abun da ke faruwa, Kuliya ne kwance a gefenta, sannan a kan gadonta.
Ba shiri ta tashi zaune ta na waige-waige, kamar me neman wani abun, ita dai tasan bayan ta yi sallar isha, ta zauna a falo ta ci abinci, sannan ta ɗora da magungunan da ya aiko mata a jiyan, maganin murar ma da yawa ta sha, wai duk don ya mata magani da wuri, saboda ita ba ta san murar nan, kasancewar idan ta na yi takura mata take yi. Kuma bayan hakan ita ba ta tuna komai ba.
Kuliya ya miƙe zaune ya na kallonta, abun da ta yi jiya ya dawo masa sabo, hakan ya sa shi murmusawa a fili.
“Kin tashi lafiya?”
Kallonsa Mishl ta yi a firgice, ta na san ta tuna wani abu da ta yi a daren jiya, amma ta kasa, ta kasa tuna komai, dole akwai wani abu da yake ba dai-dai ba.
“Har rana ta take ba ki yi sallah ba, ki je ki yi sallah”
A hautsine Mishal ta sauƙa daga kan gadon ta faɗa banɗaki da gudu, Kuliya ya yi murmushi ya na sauƙa daga kan gadon ya fita daga ɗakin.