“Dan Allah, kada ka ƙara kusanta tata, kada ka ƙara nema na, kada ƙara bin ko da hanyar da kasan za mu haɗu ce, wannan roƙona ne gareka...”
Kuma ta na kaiwa nan ta fice daga motar. Raja ya yi murmushi ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama, wai kada ya ƙara nemanta, ai abun da ba ta sani ba shi ne; shi da ita kuwa yanzu suka fara haɗuwa, don ba zai rabu da ita haka ba, dole zai san yanda ya yi ya aureta. Sai da ya gama shawaginsa a duniyar tunani, kafin ya tayar. . .