Skip to content
Part 41 of 41 in the Series Labarinsu by Salma Ahmad Isah

RABI’A POV.

Da sanyin safiya ta farka a gidan Kawu Habu, duk da jiya da daddare bata kwanta da wuri ba, kasancewar ramakon sallollinta da ta ci gaba da yi, sai da ta yi ƙoƙarin taya Mama Laure aikin gidan, amma tace ta hutar da ita ta kwanta ta yi ramakon baccinta.

Kuma ba ta musa ba, sai ta kwanta ɗin, don ba ƙaramin bacci take ji ba, wajajen ƙarfe bakwai ‘yar Mama Laure ta farko ta tasheta dan ta tashi su ci abinci, abincin suka ci, sannan ta sha magungunanta da ta taho da su. Ba daɗewa kuma ta ƙara komawa baccin.

Sama-sama ta soma jin hayaniya a tsakar gidan, da farko ma kamar a mafarki take jin hayaniyar, jin hayaniyar ta ci gaba ne ya sa ta buɗe idonta. Muryar Abbansu ta ji a tsakar gidan, hakan ya sa ba shiri ta miƙe zaune, mayafinta ta raruma ta yafa a kanta, sannan ta fita tsakar gidan, don ganin meke wakana.

A dai-dai lokacin da ta fita, a Ɗan Lami ya fice daga gidan, Mama Saratu da Mama Ramatu duk sun tsa-tsaya a tsakar gidan, ga kuma Kawu Habu daga gefe. A raunane ya kalleta, sannan yace.

“Rabi sai de ki yi haƙuri, amma ba zan iya haƙura da ɗiban albarkar da Ɗan Lami ya zo ya min ba, dan haka kawai ki zo ki tafi!”

Ta ɗauka cewar ita da tashin hankali sun yi hannun riga, ta ɗauka cewar rayuwarta za ta huta da masifun da suke samunta, ta ɗauka cewar tashin hankalin da ya ɗan yi nisa da rayuwarta ya tafi har abada, ashe yajin aiki ya yi, ashe be je ko ina ba, ashe kawai ya ɗan barta ta huta na kwana ɗaya ne, ina ake so ta sa kanta?, ta fita titi ta yi karuwanci?, a’a, wannan babban kuskure ne, ko kafin Umma ta rasu sai da ta gargaɗeta a kan hakan, to gwara dai ta kashe kanta, hakan zai fi sauƙi!…

Waɗanan su ne ire-iren maganganun da take ta rayawa a ranta yayin da ta fito daga gidan Kawu Habu, babu yanda Mama Laure ba ta yi da ita ba kan kada ta fita, amma tace tun da me gidan ya koreta me za ta zauna ta yi?.

Har ta hau kan titi ba ta cikin hayyacinta, ƙafafunta har harɗewa suke gurin tafiya, ta riga ta saddaƙar da gwara ta mutu, gwara ta bi Baby da Umma ko kowa zai huta, idan ta mutu duniyar za ta fi zama dai-dai, wata ƙila iyaka nan Allah ya hukunta ƙarewar labarinta.

“…Wallahi daga Haɗejia nake!…”

Kalaman suka biyo iska tare da silalowa suka rufta cikin kunnuwanta, nan take ƙwaƙwalwarta ta tuno mata da wani wuri ɗaya da zata iya zuwa dan ta huta, ƙwaƙwalwata ta hasko mata wani wuri ɗaya da ta saba samun farin ciki a duniya, gatanta, tushen mahaifiyarta, Haɗejia!.

Fall in love when you’re ready, not when you’re lonely…

Brickhall School, Kaura District, Abuja

KULIYA POV.

Ya na tsaye daga bakin gate ɗin fita daga makarantar, kamar yanda Mishal ta bashi shawara kan ya je da yaransa sannan ya je a matsayinsa na ɗan sanda, hakan ya yi, kuma ya yi nasarar samun damar yi wa duka ma’aikatan makarantar tambayoyi.

Da yake lokacin tashi ne, gaba ɗaya ɗalibai sun firfito, ‘yan day na ya ƙoƙarin tafiya gida, idan ya ɗan tsaya ya saurari bayanan megadin, sai ya ɗan juya ya ɗan yi kalle-kalle ko zai ganta. Kuma cikin wani ikon Allah a wannan karon sai ya gantan, sannan cikin kyakkyawan gani, dan tana tsaye da wani yaro wanda ke sanye da uniform, yaron na mata wata magana ita kuma ta na dariya.

Nan take Kuliya ya ji wani abu me kama da allura ya caki ƙahon zuciyarsa, ya ji kamar ya ƙarasa inda suke ya kwarfe yaron da mari, hakan ya sa duk sauran bayanan da me gadin ke masa ba ya fahimta.

Idonsa ƙuri a kansu, ya na kallon ikon Allah, juyowar da Mishal za ta yi karaf suka haɗa ido, hakan ya sa ɗan gutin murmushin da take ya ɗauke ɗip, kamar ruwan sama. Ta san yau akwai dabi a gidan nan.

No.181, Guzape, Abuja…

10:30 PM.

MISHAL POV.

Safa da marwa take a ƙofar ɗakin Kuliya, tun ɗazu ta ya dawo, kuma ta yi maganar duniyar nan amma ya ƙi kulata, ko abincinta ya ƙi ci, ta rasa inda za ta sa kanta, ba ta san ya za ta yi ba, amma dole ta bashi haƙuri a daren nan, dole su sulhunta a daren nan, dan ba za ta iya kwana ita kaɗai ba, ta riga da ta saba da kwana tare shi, bata jin yau za ta iya bacci idan babu shi kusa da ita.

Juyowa ta yi ta kalli ƙofar, sai da ta shaƙi iska, sannan ta furzar, hannunta har karkarwa yake wajen buga ƙofar, amma haka ya mata banza, kuma ya na jinta, dan ya na ganinta ta ƙaramar camerar dake maƙale a ƙofar ɗakin, wadda ido ba ya iya ganinta, kuma ba ma iyaka ƙofar ɗakin nasa kawai ke ɗauke da camerar ba, akwaita a gurare da dama a cikin gidan, kuma ta cikinta ne ya ga abun da ya faru tsakaninta da su Siyama a waccan ranar, a sanda ya ga vedion ba ƙaramin mamaki ya yi ba.

Hannun Mishal ya ƙara buga ƙofar a kusan karo na tara, zuwa lokacin har ta fara hawaye. Kuma ganin ta fara kukan ne ya sa zuciyarsa karyewa, dan haka ya miƙe ya nufi ƙofar, sai da ya yi kicin-kicin da fuskarsa, sannan ya buɗe ƙofar ya na wani cin magani.

“Ya aka yi?”

Ya tambaya ya na kallon fuskarta wadda ta yi ja saboda kuka, kallonsa ta ci gaba da yi tana kuka. Da ta rasa abun yi sai kawai ta faɗa jikinsa, ta saka hannayenta ta kewaye shi ta baya, sannan ta saki kuka me sauti, Kuliya ya ƙi ya riƙeta, duk da zuciyarsa na motsawa da ko wani ɗigon hawaye da take zubarwa. Jin bai riƙeta ba ya sa Mishal ɗagowa daga jikinsa ta na jan zuciya.

“Abu Aswad ka yi haƙuri”

Kansa ya ɗauke ya na wani shan ƙamshi.

“I am sorry”

Ya ƙi ko kallonta.

Haka ta yi ta bashi haƙuri amma ya ƙi ya ko kalleta, da ta gaji da magiyar sai ta juya jiki a sanyaye tana hawaye, taku biyu ta yi ya sa hannunsa ya janyota, bata tashi tsayawa a ko ina ba sai cikin jikinsa, tana jin hannayensa a bayanta kuwa ta sakar masa kuka sosai.

“Ka yi haƙuri please… Note book ɗin chemistry fa kawai ya tambayeni…”

Kuliya ya ƙara matseta a cikin jikinsa.

“Dariya fa na ga kuna yi Teddy Bear, kinsan ai dole na ji ba daɗi”

Ita ma sai ta ƙara riƙe shi ta na faɗin.

“Wallahi ba komai muke ba, ka yarda da ni, ai ni ma na san hakkin aure, ba zan tsaya da wani saurayin ba… Ka yi haƙuri”

Kuliya ya saketa ya na goge mata fuska, ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na faɗin.

“Is okay, ki dena kukan to”

“Ka yafe min?”

Ya gyaɗa mata kai ya na ɗaga kafaɗa.

“Na yafe miki, amma kada ki ƙara masa magana… Ba ma shi kaɗai ba, ko wani yaro a school ɗinku babu ke babu shi”

Ta gyaɗa masa kai ta na jan hanci, fuskarta ya riƙe ya na kallonta, kafin ya sunkuyo da fuskarsa kan tata, sannan a hankali ya haɗe bakinsa da nata ya na kissing, hakan ya sa ba shiri Mishal ta saka hannayenta ta kewaye wuyansa ta baya tana mayar masa martani.

Unguwar Jama’are, Haɗejia…

08:40 PM.

Kusan mutum gome ne suka sa salati a tare, bayan da Rabi’a ta kai ƙarshen labarinta, tun bayan barinta gidan shekaru biyar baya har zuwa yau babu abun da ta ɓoye musu.

A ɗazu da yamma ta sauƙa a garin Haɗejia, farkon ganinta sai da ‘yan uwan nata suka yi murna, amma kuma ganin yanayinta da kuma damejin dake fuskarta ne ya sace musu gwiwa, haka suka shiga jero mata ruwan tambayoyi, amma bata samu ta amsawa kowa ba.

Har zuwa ƙarfe takwas, kafin kakanta ya aiko kiranta, kuma daga lokacin da ta iso falon kakan nata sai ta tarar da ba shi kaɗai ne a ciki ba, duka kawunnenta da ‘yan uwan kakan nata duka suna ɗakin. Sannan ko da suka tambayeta ba ta ɓoye musu komai ba, tun daga wahalar da ta yi ta sha a gidansu, har zuwa aikatau ɗin da take, har kan fyaɗen da aka mata, zuwa korarta da Ɗan Lami ya yi.

Kakanta Alhaji Ali ya ci gaba da kallonta, wani abu na yawo a cikin kansa, ɓaro-ɓaro ya na ganin yanda tarihi ke maimaita kansa, irin abun da ya faru da me sunanta ne ya faru da ita, ‘yarsa ta cikinsa da ya kora saboda ta yi cikin da ba na aure ba, wanda ya zo ya yi nadama daga baya, har ya shiga fafutukar nemanta, amma kuma ko da ya samu inda take sai aka sanar da shi ya je a ƙurrarren lokaci, don kuwa ita Rabi’an ta rasu, yaranta ‘yan biyu da aka ce ta haifa kuma ba a san duniyar da suka shiga ba. Tsoho Alhaji Ali ya ji ƙwalla ta cika idonsa.

“Irin cin amanar da Ɗan Lami zai mana kenan?, Bayin Allah a nan a gabanku fa nake tura masa kuɗi duk sallah na ce a yi wa Rabu ɗinkin sallah, amma kun ji, rabonta da sabin kaya tun wanɗanda ta bar gidan nan da su”

Cewar kawu Abdullahi, babban ɗa a wurin Alhji Ali, haka kuma babban wa a wurin su Maryam.

“Ni ai ba wannan ne ya bani mamaki ba, kadarorin Maryam ɗin da ya ɗaga ya siyar su ne suka ba ni mamaki”

Cewar Kawu Hassan, ƙani a wurin kawu Abdullahi.

Haka dai suka ci gaba da maida zance, har da masu cewa ƙarar Ɗan Lami ɗin ya kamata a yi, Rabi kuwa jinsu kawai take, dan ita kaf duniya yanzu ba wannan ne a gabanta ba, farin cikinta ɗaya, da danginta suka karɓeta, suka nuna mata ƙauna kamar yanda suka saba. Sai kuma matsalarta; Raja!.

Har yanzu tunaninsa bai bar cikin kanta ba, har yanzu ta na iya hango fuskarsa a cikin kanta, har yanzu ta na iya hango kanta a tsakanin hannayensa, har yanzu akwai sansa a cikin zuciyarta, amma ko ta ƙi ko ta so dole ta cire wannan son, don ba zai amfaneta da komai ba, face ya wagalar da ita, aure tsakaninta da makashi ɗan daba ba abu ne me iyuwa ba, wai ita ya aka yi ma ta yarda da shi har haka?, ina hankalinta ya shiga da har ta bari zuciyarta ta yarda da shi, ta inda har ta kasa tambayarsa wani aiki yake. Me ya sa idonta ya rufe ta kasa ganin gaskiya?. Wani abun farin cikin ma shi ne; da bata faɗa masa cewar shi ɗan uwanta ba ne, wannan shi ne kaɗai arziƙin da aka yi. Ta raya hakan a ranta, don ita ta manta da maganar da ta faɗa masa a sibiti.

Haka suka yi kiɗansu suka yi rawarsu, amma ba ta ƙara cewa kanzil ba, har suka babbata haƙuri, kawu Abdullahi ne yace ta shirya zuwa gobe zai kaita a mata gwaje-gwaje, sai a lokacin ta yi magana, ta sanar masa da cewar duk wasu gwaje-gwaje da suka dace babu wanda ba a mata ba, amma yace shi bai yarda ba, kawai ta shirya zai kaita a sake mata wasu, ba ta ƙara masa musu ba tace to, sannan ta miƙe ta koma cikin gidan.

Kai tsaye ɓaangaren kakarsu ta yi, inda ta san ‘yan matan gidan suna tare a can, dan a dai-dai lokaci irin wannan a can suke taruwa. Kuma kamar yanda ta ayyana a ran nata sun taru a can ɗin.

‘Yan mata shida ne sa’o’inta a gidan, Momi, Nafisa, Fati, Jidda, Kulsum da Kairiyya, su na ganinta su ka yi shiru, kowa ya zuba mata ido ya na kallo, dan kaf cikinsu babu wanda ya san da zuwanta, a sanda ta shigo garin ma suna islamiyya.

Gaba ki ɗayansu so suke su ganeta, kammaninta na musu kama da na wata da suka sani, kallon ƙurillar da ta ga suna mata ya sa tace.

“Ya da kallo haka ‘yanmatan Waliki family?”

Kusan a tare suka fashe da dariya suka iyo kanta. A dai-dai wannan lokacin kakarsu ta fito daga ɗakinta ta na ɗingisa ƙafa, kujera ta samu zauna ta na kallonsu.

“Rabi’a?, wai yaushe ma kika zo garin?”

Cewar Kulsum ta na dariya. Rabi ta zauna a kujera ta na faɗin.

“Ɗazu da yamma, kuna islamiyya lokacin”

“Wayyo Allah, wallahi na ji daɗin zuwanki, kusan shekara biyar fa rabonmu da ke”

Cewar Fati ta na matsawa kusa da ita.

“Ke Allah ya yi da ke kina nan za ayi bikin Nafisa”

Kairiyya ta faɗa, baki buɗe cike da mamaki Rabi ta kalli Nafisan da ta kawar da kanta, saboda Hajiya kakarsu dake wurin.

“Wai dan Allah?”

“Wallahi kuwa, nan da wata ɗaya da sati ɗaya” Jidda ta amsa mata.

“Ke Rabi a ina kika ji wannan raunin na fuskarki?”

Momi ta tambayeta, Rabi ta kai hannu ta shafa gefen fuskarta na hagu, sai da ta haɗiye wani abu sannan tace.

“Haɗari ne… Kai ni yanzu ku ba ni labari, ya ake ciki ?”

Daga haka suka shiga hira a kan batun bikin, suna bawa Rabin labarin yanda suka tsara bikin, da yanda zai kasance, har kusan ƙarfe goma suna can, dan abincin dare ma tare suka ci.

Kasancewar ‘yan matan su duka ɗakinsu ɗaya, ya sa ita ma ta kwana a cikinau, dan dana tun can tare auke kwana, gadon Rabin ma na da yana nan, kuma yanzun ma a kansa ta kwana.

<< Labarinsu 38

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.