Wani irin shiru ya ratsa wurin tsawon muntuna biyar, cikin gidan babu wani motsi kamar babu kowa, alhalin akwai mutum har biyar a cikin gidan.
“Wallahi wannan mara mutuncin ne!....”
Wani matashi ya faɗi daga cikin gidan, bayan ya sauƙe labulen ɗakin da suke ciki. A tsorace ya yi maganar, kuma daga yanda jikinsa ke rawa zaka fahimci hakan kalar tsoron da yake ji.
Cikin halin ko in kula wani cikin mazan dake ɗakin yace.
“Wai wa kake nufi?”
“KULIYA!”
Kusan a tare gabansu su duka ya buga, ciki kuwa harda wanda ya furta sunan, KULIYA!, wani suna. . .