Skip to content
Part 42 of 47 in the Series Labarinsu by Salma Ahmad Isah

T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.

RAJA POV.

It was just two lovers…

Sitting in the car, listening to blonde

Falling for each other

Pink and orange sky

Feeling super childish

No donald glover…

Waƙar dake tashi kenan a cikin sifukun gidan, wanda Raja ya ƙure volume.

Tsaye yake daga gaban mirror, ya na taje sumar kansa, sanye yake cikin wata ash shadda, a hankali bakinsa ya ci gaba da biya waƙar Golden hour ɗin dake tashi a falo.

“I was all alone… With the love of my life… She’s got glitter for skin… My radiant beam in the night… I don’t need no light to see you… Shine… It’s your golden hour…”

Sai kuma ya yi shiru ya na kallon kansa a mirror, yayin da ya aje matajin hannunsa, bayan wani lokaci me tsayi yau shi ne sanye da manyan kaya, ya daga kafaɗarsa ya na murmushi, ya gyara wuyan rigar jikinsa, ya ƙara fesa turare a jikinsa, sannan ya finciki hularsa ya fito.

“Huh?! Dude? Yau ina zuwa?”

Cewar Rhoda kenan, yayin da ta fito daga kitchen, hannunta na dama riƙe da plate, Raja ya kama kumatunanta ya na ja.

“Zance zan je”

Rhoda ta shafa kumatunta da ya saki da hannunta na hagu.

“Guys, ku shigo ku ga ikon God!”

Kiran da ta ƙwalawa su Jagwado ne ya sa suka afko cikin gidan babu shiri. Kallon Rajan su ma suka tsaya suna yi, a karo na farko tun bayan saninsu da Rajan da kuma Rhoda, ba su taɓa ganinsu da mabanbantan kaya ba, a ko da yaushe kaya kala ya suke sawa, sai yau.

“Allah de ya biya oga Raja, ina za ka fasa haka?” Alandi ya tambaya.

“Zance zan je”

“Kutumar dumadu, Kaga Oga Raja namu, Allah ya biya, gayu, oga fa ya rufta ramin ƙauna Allah Wallahi”

Cewar Zuzu ya na wani ɗaɗɗaga hannu. Raja ya yi murmushi ya na girgiza kansa.

“Wai Zuzu ban hanaku magana irin haka ba?”

Zuzu ya shafa kansa ya na kallon ƙasa.

“Sabo ne oga Raja, amma za mu dena da yardar me duka” ya faɗi muryarsa babu wani banbanci da ta ɗazun.

“Ku fa?”

Raja ya tambaya yana kallon sauran.

“Aah, ai muma hakan take oga, ko ya kuka ce gayu?”

Alandi ya faɗi ya na kallon su.

“Haka ne”

Jagwado ya amsa.

“Na zo na raka ka?”

Rhoda ta faɗi ta na aje plate ɗin hannunta, wanda ke ɗuke da alale. Raja ya maka mata harara.

“Wa za ki bi?… Kama hanyar ki can joo!”.

Unguwar Madallah, Suleja, Niger State.

Da gudu Fatima ta shigo gidan har tana bangaje Saratu da ta fito daga banɗaki.

“Ke Fatima mi ye hakan?”

Inaa, sam ba ta tsaya ba sai da ta dangana da ɗakin Habiba.

“Ke dallah mi ye hakan za ki faɗo kaina?”

Habiba ta tambaya ta na miƙewa. Fatima ta dafe ƙirji ta na zaro ido, hannunta ta ɗaga tana nunawa Habiban ƙofar ɗakin.

“Wa… Wani na… na ga a waje… Kamarsu ɗaya da… Da Rabi!”

Wani irin juyi kayan cikin Habiba suka yi, don a sanda fatiman ta ambaci kamar mutumin da ta gani da Rabi, ƙwaƙwalwarta ta hasko mata ‘yan uwan Maryam na Haɗejia. To ko su ne suka zo kamata ?, wata ƙila Rabi ta sanar musu da duk irin abubuwan da ta mata, shi ne suka zo dan su kamata. Muƙut!, ta haɗiye yawu, tunawa da ta yi da labarin irin kuɗin baban Maryam ɗin da aka bata. Ba shiri gumi ya shiga tsatsafo mata, cikinta har wani ƙugi yake.

Sallamar da Saratu ta ji a waje ya sa ta leƙa, kasancewar akwai hijabi a jikinta. Ita kanta sai da ta firgita, ganin wani mutum sak Rabi, tsaye a soron gidan nasu, amma sai ta ɓoye tsoronta ta amsa sallamar tasa. Ba tare da ta tambayeshi wa yake nema ba, ta masa lamini da ya shigo cikin gidan.

Wata kujerar roba ta bashi, tace ya zauna a kai. Ya na zama a kan kujerar Habiba ta bankaɗo labulai ta fito, Fatima na biye da ita.

Curko-curko suka yi daga bakin ƙofar ɗakin Habiban suna kallon ikon Allah. Saratu ce ta kawo masa ruwa, sannan ta zauna suka gaisa.

“Am… Rabi’a nake nema”

Wani irin ƙara cikin Habiba ya saki, da saida ta saki wata siriyar tusa, shikenan, wata ƙila tata ta ƙare, kenan da Rabin ta bar gidan Abubakar ba can ta yi ba, tun da ga shi su ma nemanta suke, amma garin yaya har aikin nan ya karye?, don kuwa ita ta san ta sa a yiwa ‘yan uwan Maryam aikin da duk tsawon shekarun da Rabi za ta yi a gidan ba za su taɓa neman ganinta ba.

“Amma waye kai bawan Allah, ko daga Haɗejia kake ?”

Raja ya sosa kansa ya na faɗin.

“Sunana Zaid, kuma ba daga haɗejia nake ba”

“Laaa!, da ma kai ne Zaid ɗin, ai ko Rabi ta na yawan bani labarinka, sai dai ko da wasa ba ta taɓa faɗa min cewar kuna kama ba”

Raja ya ɗaga kafaɗarsa ya na faɗin.

“Allah sarki”

“To Rabi dai ba ta gidan nan, satin da ya wuce Umma ta koreta, ita kuma sai ta koma gidan kawu Habu, gidan na ɗan gaba da mu”

Da farko har hankalin Habiba ya kwanta, jin shi wannan bawan Allahn ba daga haɗejia yake ba, amma kalaman Saratu su ne suka dawo da tsoron sabo. Kuma cikinta bai ƙara rikicewa ba, sai da Raja ya juya ya kalli side ɗinta. Hatta da idanuwansa irin nata ne, banbancin kawai shi ne na sa a lumshe suke, kuma ƙwayar cikinsu kalar ruwan toka ce.

Raja ya dawo da dubansa kan Saratu.

“Ko za mu je ki raka ni gidan shi kawun?”

Ya faɗi wani abu na masa ɗaci a maƙwagoro, dole ya san yanda zai yi da matar nan, dan ko me ya samu Ammatansa ita ce sila.

“Innallillahi wa inna ilaihi raji’un… Zaid wai sun ce tun washe gari shi Abba ya zo ya yi masifa kan sai Kawu Habu ya koreta, kuma tun a ranar ta bar gidan nan ɗin”

Abun da Saratun ta faɗi kenan, bayan da ta shiga gidan kawu Abubakar ta fito, Raja dake jingine da ƙofar gidan ya gyara tsatuwarsa ya na kallon bakinta, dan so yake ya fahimta shin, da wani yare ma take magana ne?, shi fa bai gane ba, Ammatansa ba ta gidan nan?, to ina ta tafi?.

*****

Look out for those who look out for you. Loyalty means everything…

Unguwar Jama’are, Haɗejia…

RABI POV.

“Wai har kun dawo?”

Cewar kakarsu Hajiya ta na binsu da kallo, dawowarsu kenan daga kasuwa, sun je siyyayar kayan biki, don a yanzu haka bikin saura wata ɗaya, sai shirye-shirye ake a gidan, duk sun zuzzube a falon Hajiyan suna maida numfashi.

“Wallahi Hajiya, kin san yau Lahadi… To kasuwarce a cike, ko siyyayar ma ba mu gama ba, kawai mun dawo ne, kin ga ko zuwa gobe ne sai mu ƙarasa siyyayar”

Cewar Kairiyya ta na cire hijabin jikinta, Hajiya ta gyaɗa kai ta na kaɗe ƙuda daga kan furarta. A dai-dai lokacin Nafisa ta shigo, wadda take daga ɓangaren mahaifiyarta, dan ita bata bisu kasuwar ba. Zama ta yi suka shiga firfitar da kayan da suka siyo.

“Ku wai ni yanzu wa za mu nema ya mana lalle?”

Momi ta tambaya ta na ɗaga wata doguwar riga cikin kayan da suka siyo.

“Akwai wannan Balkisan, ƙawar anti Shafa (Yayar Kulsum), ita ma ta iya lalle”

Cewar Nafisa.

“Ku na iya lalle fa, ku bari sai na muku”

Rabi ta faɗi tana dudduba nata kayan da ta siyo.

“Ke kuma a ina kika koyi lalle?”

Jidda ta tambaya.

“A can mana”

“Ai kiwa ke za ki mana”

“To ke wa zai miki ?”

Fati ta tambaya.

“Sai ku kira min wadda kuka ce za ta muku da farko, sai ta min”

Kamar yanda suka saba a kwanakin haka suka shiga hirar bikin, dan daga zarar sun zauna kamar haka ba su da hira da ta wuce ta bikin.

Rabi’a ta saki jikinta a cikinsu tana sha’aninta, sai a yanzu take jin kamar rayuwarta ta setu, sai a yanzu da ta dawo cikin ‘yan uwanta farin cikinta na da ya dawo, har wata ƙiba ta yi a cikin satin.

Kuma babu wani abu dake damunta face shi, wannan sunan; Raja!, har zuwa yau ba ta manta shi ba, ta yi iyaka i yinta amma ta kasa, ko bacci za ta kwanta da ta rintse idonta za ta hango waɗanan lumsassun idanuwan nasa. Ba za ta yi wa kanta ƙarya ba,ta san a cewa tana kewarsa!.

KULIYA POV.

Ya na daga zaune a falo ya na dudduba wani aiki a cikin ipad ɗinsa, hannunsa na dama riƙe da mug ya na shan coffee. Kamar daga sama ya ji muryarta a kansa.

“Abu Aswad… Barrow me your phone please”

Kansa ya ɗaga ya kalleta, mug ɗin kare da bakinsa, kamar kullum sanye take cikin ƙananu kuma ɗangallallun kayan da ta saba sakawa, shi har mamaki ma ya yi, a sanda ta faɗa masa cewar kaf cikin kayanta babu atamfa da lace ko makamantansu, ban da ƙananun kaya ba ta da wata sutura, hannunta na dama riƙe yake da littafi, yayin da na hagu kuma yake riƙe da pen. Gashin kanta nannaɗe cikin bun.

“Me za ki yi?”

Ya tambaya ya na ɗaga kafaɗarsa, tare da aje mug ɗin hannunsa a kan coffee table.

“Assignment zan yi please”

Sai ya ɗan kalleta na wasu sakkani, kafin ya aje ipad ɗin hannunsa, ya kamo nata hannun na hagu ya zaunar da ita kan cinyarsa. Ya na shirin sakin hannunta ya lura da hannun nata ya yi jajir sosai, kamar wadda ta ƙone. Hannun nata ya saki ya na kama waist ɗinta da hannunsa ɗaya.

“Me ya samu hannunki?”

Ya tambaya ya na gyara mata gashin kanta na gaba, Mishal ta shaƙi wata iska, kafin tace.

“Wani malami ne ya dake ni”

Kuliya ya miƙa hannunsa ya ɗauko wayarsa ya miƙa mata.

“Me kika yi?”

Ya tambaya a hankali. Sai ta turo bakinta gaba.

“Note ne ban yi ba… Ai Wallahi da da ne shi ma bai isa ya dake ni ba… Yanzun ma de kawai…”

Sai ta yi shiru tana daddana wayar tasa. Kuliya na kallon fuskarta yace.

“Yanzun ma dai me?… Yanzu kin girma ko?… Kin zama matar aure”

Ta ɗan yi dariya, ta na kallon wayarsa ta amsa masa da.

“Ba haka ba ne… Kawai de dan Anti Adawiyya ta min faɗa ne, ita tace duk malamin da ya min wani abu na ƙyaleshi kawai, malamai ba sa cuta sai dai gyara, idan kuma mutum ya cuceni na barshi da Allah, Allah zai saka min, shi ne fa ya sa na yi sanyi, amma ni da akwai malamin da ya isa ya dake ni!…”

Kuliya ya ci gaba da kallon bakinta dake furta kalaman, tsakaninta da Allah take bayananta, duk abun da Mishal za ta faɗa daga zuciyarta yake fitowa, ba ta san wani abu ba wai shi ƙarya, kanta tsaye take furta zantikanta, maganar ta ci gaba da masa idonta kan wayar, yanda ta sauƙe su ƙasa sai ka ce rufe su ta yi, dogayen gashin idonta sun kwanta a kan fuskarta, hasken wayar ya ƙara haska masa fuskarta, sai ya ji kamar ya saka makulli ya buɗe zuciyarsa ya sakata a ciki ya kulle, ya nesanta ta daga duk wani abu na cutarwa da ɓacin rai.

“Me nene wannan a haƙorinki?”

Sai ta tsaya da maganar da take masa ta kalli fuskarsa, gira ya ɗaga mata cikin sigar tambaya. Sai ta maida idonta kan wayar ta na faɗin.

“Datti ne… Dama haka haƙorina yake, duk wata Aki yake kaini a wanke min, da braces aka saka min ma, kwanaki aka zire min su”

“Ok gobe zan je na ɗauko ki a school… Daga nan sai mu wuce asbitin a wanke miki”

Ta kuma kallonsa.

“Angelica ta ce min ma wai an kawo wasu sabin teddies a Jabi Lake Mall, za ka kai ni?”

Kuliya ya yi murmushi ya na ƙara matse hannunsa a ƙugunta. Shi ne ya kamata a kira da mijin yarinya.

“Har Magic land ma za mu je”

Bakin Mishal ya tale cikin dariya. Ta kwantar da kanta a ƙirjinsa ta na ci gaba da danna wayarsa.

“Abu Aswad?”

Muryarta ta kira sunansa bayan wani lokaci, ipad ɗin ya kawar daga fuskarsa ya kalli ƙasan kanta, don har zuwa lokacin ta na kwance a jikinsa.

“Hmm”

“I hate you”

Sai ya yi murmushi ya na ci gaba da kallon ipad ɗin.

“And i love you”

Unguwar Madallah, Suleja, Niger State

RAJA POV.

“Ku kamata!”

Wannan shi ne umarni da ya bawa jami’an da ya zo da su, a yayin da ya shigo cikin gidan su Rabi ba tare da ko neman izini ba, ya jure abubuwa da dama, amma ba zai iya jure rashin Rabi’a ba, zai fiye masa sauƙi ma a ce ya rabu da rayuwarsa, da ace ya rasata, Habiba ta azabtar da ita bakin gwargwado, dan haka lokaci ne da ita ma za ta ɗanɗani kuɗarta, ba ma ita kaɗai ba, har da Ɗan Lami ya sa an kamo shi, dan sai sun faɗa masa inda Rabi’a ta shiga.

Habiba ta fashe da kuka a sanda ‘yan matan jami’an suka yi kanta, ciki kuwa har da Rhoda, Fatima da Mahmud har da Saratu suna tsaye suna kuka, haka aka kama Habiban aka fita da ita ta na ta roƙonsu.

Da ƙyar Raja ya iya dai-daita kansa, sannan ya lalubo ainahin muryarsa ya na kallon Saratu yace.

“Ka da ku damu, tambayoyi za a mata kawai, insha-Allah idan ta amsasu da wuri ina me tabbatar muku da za ta iya dawowa a yau ɗin nan, idan kuma ta yi taurin kai, ba zan iya muku alƙawarin dawowarta gareku da wuri ba!…”

Ko kafin ya kai ƙarshen maganarsa, Fatima ta ƙarawa kukanta volume ta shige ɗaki, Mahmud ma bayanta ya bi ya na nasa kukan, duk da shi ba wani wayi gareshi ba, shi dai ya ga an tafi da Uammansu. Saratu ta share hawayenta tana faɗin.

“Babu komai Zaid, Allah ya bayyanar da gaskiya!”

“Na gode”

Ya faɗi ya na gyaɗa mata kai, tare da juyawa.

“Ammm, baka ji ba”

Tsayawa ya yi tare da juyowa ya na kallonta.

“Maganace akan Rabi, ina zaton duk inda take a yanzu ba za ta wuce Haɗejia ba!”

<< Labarinsu 39Labarinsu 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×