T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.
RAJA POV.
“Wai ina za ka je?”
Rhoda ta tambaya, a sanda ta shigo ɗakinsa ta tarar da shi ya na haɗa kaya a cikin jakarsa.
Ba tare da ya juyo ya kalleta ba ya furta.
“Haɗejia!”
Trayn hannunta ta aje ta na faɗin.
“Haɗejia?... Me za ka yi a haɗejia?”
Ya zuge duffle bag ɗin da ya saka kayansa kala biyar a ciki, sannan ya juyo ya kalleta.
“Yayar Ammata ta ce min ta na can... Dan haka dole na je nemanta, wata ƙila. . .